← Book details Ana Zaton Wuta A Makera Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 50

Sashe 47

Ana Zaton Wuta A Makera Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

murmushi. Mr Handsome tafaɗa tana faɗawa jikinsa. Look tafaɗa tana ware zanen da tayi. Wowww Masha Allah cewar Yarima yana kallon zanen. Fatherr tafaɗa ganin Ruhaan yayi shiru yana kallon zanen. Murmushi yayi yace yayi kyau sosai. Nawa yafi kyau cewar Zaid yana amsar ɗayan paper dake hannun Du'a. Nawa yafi koh? cewar Du'a tana kallon Ruhaan. Uhmm yafaɗa yana kallon zanen. Duk kun iya. Both you guys are very good at different things yafaɗa yana amsar zanen. Du'a finishing ɗinki is perfect while Zaid yasan yadda zaiyi using shades din pencils correctly. Let's do this yafaɗa yana riko hannunwasu. Ku taimaki junan ku, you guys will be recognised in the world of art. Okay Father suka haɗa baki wajen faɗa. Nidai bazanyi zane ba. Doctor zan zama kamar Uncle Yarima yafaɗa yana tafawa da Yarima. Hira sukayi sosai kafin su kwanta a tsakiyar Yarima da Ruhaan. Da safe Ruhaan ya tafi gida, yayi wanka ya shirya cikin suite navy blue inner milk. Ɓakin shades dinsa ya saka. Ɗakin Ummi ya shiga ya gaisheta, amsawa tayi cikin damuwa. Lafiya kuwa Ummi? Ba dole in damu ba Ruhaan kwata-kwata kwana biyu bana gane maka. Bama a gidan kake kwana ba. Sosa keyarsa yayi yace Ummi ina studio dinane, kuma Amira batajin dadi. So kusan koda yaushe muna tare. Subhanallahi mai yasameta? She is pregnant yafaɗa yana murmushi. Allah ya dayyaba cewar Ummi tana murmushi. Gobe zan koma Masarauta. Eh Ummi da kaina zan kaiki airport karki damu. Parking yayi ya sauko, ya shiga ciki rike da wata classy shopping bag. Yarima ne dasu Zayn suke ta hira dayake sunyi hutun school. Ina Mammi yafaɗa yana kallonsu. Tana sama itada da Mummy cewar Du'a tana kallon shi. Zama yayi suka cigaba da hirar tare. Ƙarar heel din da Amira tasane yaja hankalinsu daga shi har yaran banda Yarima dake waya.Da sauri ya miƙe yana kallonta. Sanye take da fararen suit na company Cavallaro Napoli. Duk taku daya da take ji yake kamar tana yankar naman jiknshi. Tsayawa yayi ta sauko, ya riko hannunta ya zaunar da ita, ya tsugunna a gabanta.Good Morning tafaɗa tana murmushi. Hararata yayi ta cikin shades din. Wai hararata kake ganin ya tsaya kallonta. Cire shades din yayi ya maka mata harara yace yanzu ai kin gani. Ɓata fuska tayi tace ni kake harara? Kauda kai yayi yace stop looking at me like that. Before i do something we will both regret yafaɗa yana daga nata gira ɗaya. Hannun ya yasa ya dauki kafarta dake sanye da bakin heel ya daura akan cinyarshi. Belt din ya cire ya cire mata takalmin. Hasken Flash kawai suka gani, murmushi duk sukayi suka juya suna kallon Zayn dake rike da camera. Wani ya kuma dauka yace kuce chesse yafaɗa yana murmushi. Murmushi duk sukayi suna kallonshi. Cire mata dayar kafar yayi. Ya buɗe bag din daya shigo da ita a ciro wani karamin box. Buɗe box din yayi ya ciro wani sabon black shoe.Canvas ne amma bawai irin regular canvas ba. Kai da ganinshi kasan yaji kudi. Saka mata canvas din yayi kasa-kasa yadda ba wanda zaiji su yace Noor Banason kina min wasa da ajiya. Karki kuma sa heel dinnan banso! Toh Moh tafaɗa tana miƙewa tsaye. Murmushi yayi dan ya manta yaushe rabon data kirashi da wannan sunan. Humaira dake gefensu ce tayi dariya, harararta Amira tayi dan batamasan sanda ta sauko ba. Kids ku zauna da Uncle Mukky zamuje mu dawo cewar Humaira. Motoci biyu sukayi ɗaya Ruhaan da Amira daya Humaira da Yarima. Toh ya zaman kotu zai karke? Mu haɗu a next page 📄📄📄 ANA ZATON WUTA A MAƘERA.......🔥 ✒️IBNATU-UMAR✒️ PAGE 71&72 Supreme Court Abuja. Parking yayi gaban kotun yana kallon yadda wajen ya cika da yan jaridu da kuma mutane da yawa dake son jin wannan ƙara. Parking yayi ya sauko, ya riko hannunta suka shiga ciki. Flash din camera kawai kake gani. Yan Jaridu na tunkaro ta saiga Mukhtar da mutanen sa da suka dade da zuwa. Zagasu suyi suna blocking yan jaridu su kuma suka wuce ciki. Ciki suka shiga, duk da sunzo 20mins earlier amma da mutane ba laifi a cikin kotun. Tsayawa yayi ya kalleta yace Allah ya bada Sa'a. Komawa yayi wajen dasu Humaira suke zaune ya daura kafa daya kan ɗaya yana kallon abinda ke wakana. Alƙali ne ya shigo, duk suka mike tsaye. Zama sukayi, bayan gabatarwa. Shigowa Rafik Adebola yayi, ya tsaya a stand. Bayan gabarwa aka fara Shari'a. Barrister Khadijah Abdulkarim Kurfi you have pressed charges against Mr Rafik Adebola. Yes, My lord tafaɗa tana kallon Judge din. Bayani ta farayi akan case din. Duk abinda ke wakana a cikin court din da harshen turanci sukeyinsa. File din da Rafik ya yadda ranar ta miƙama alƙali. Waɗannan hujjojin sunyi proving cewa Mr Rafik Adebola yana da hannu Mutuwar Alhaji Abdulkarim Kurfi. Objection my lord cewar Lawyern Rafik Adebola. Wadannan hujjojin might prove akwai wani abu a tsakanin Alhaji Abdulkarim Kurfi da Mr Rafik Adebola amma batada hujjar dake nuna cewa yana da hannu a kisan shi. Kowa a nan yasan waye client dina kuma kowa yasan Alhaji Abdulkarim Kurfi, sannan kowa yasan masu kuɗi suna harƙalla da juna. Harkallar kwaya? Cewar Amira tana kallonshi da jajayen idanunta. Muhawara suka dinga yi mai zafi. Inda daga ƙarshe ya koma ya raɗa ma Rafik cewa ya amsa harkallar kwaya akan a kamashi da kisan kai. Zasu iya fito dashi idan case din ya lafa. Sam Rafik yaki yarda. Ana haka aka tafi hutun rabin awa.
Chapter 47 · 0% Book details