← Book details Ana Zaton Wuta A Makera Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 50

Sashe 48

Ana Zaton Wuta A Makera Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Zama tayi akan kujerar dake wajen court room ta dafe kanta dake sara mata.
Uhmmm yafaɗa yana zama a gefenta. Ɗagowa tayi ta kalleshi, ta sunkuyar da kanta. Ɗago kanta yayi ya mayar kan cinyarshi yace mai ya faru? Ƙishi nake ji tafaɗa tana kallon shi. Tashi yayi ya tafi ya dauko mata ruwan. Humaira ce ta karaso wajen rike da ruwa a hannunta tace tashi kisha. Murmushi tayi ta amshi ruwan da Humaira ta buɗe mata.
Sha tayi ta miƙa mata tace idan Rafik yabar wajen nan ba'a matsayin criminal ba, i will never forgive myself.
Waya gaya maki zai bar nan, ba'a criminal ba? Let's bet cewar Humaira tana bata karamar yatsarta. Am betting because you're my sister i trust my genes you know tafaɗa tana murmushi. Murmushi Amira tayi tace am not betting. Cheaterr cewar Humaira tana jan hancinta. Stopeettt Amira tafaɗa tana tureta. Tsayawa Ruhaan yayi yana kallon su, ganin yadda take dariya kamar ba ita ya bari ba. Yarima ne yace zo muje ka kyale su.
A GURGUJE PLEASE 🤣🤌🏽
Ammi tace zatazo fah, kuma ban gantaba cewar Amira tana kallon Humaira. Gatacen cewar Humaira tana nuna mata Ammi dake ƙarasowa wajen.
Ammii tafaɗa tana rungumeta, murmushi Ammi tayi cirota a jikinta. Zama sukayi a gefe suna hira. Ina zuwa zan shiga toilet cewar Amira tana barin Ammi da Humaira.
Harta fito a bayin ta hangi Rafik Adebola ɗaya ke zaune akan kujera. Kallonta yayi, yayi murmushi yace you're born to be a Lawyer. Smirking tayi tace maiyasa ka kashe mahaifina? Shiru yayi yana kallonta kafin ya dauke kanshi. Okayy i have no choice tafaɗa tana fito da wayarta. I can do anything for my parents and there honour. Kalli nan tafada tana miƙamai wayarta. Sakin wayar yayi zata fadi, ta rikota tace i can agree with you that am born to be a lawyer but i am Lawless Lawyer. Tafaɗa tana saka shades dinta. Mai kike so inyi yafaɗa muryarsa kamar zaiyi kuka. Just tell the truth! The absolute truth! Tafaɗa tana wucewa. Can you handle the truth yafaɗa yana kallonta. Tsayawa tayi kamar zata juyo sai kuma ta fasa tace just tell the truth. Zama tayi a gefen Humaira tace yanzu i can rest i assured komai zai tafi daidai. Mai kika ce mai? Cewar Yarima yana maiƙa mata meatpie din daya shiyo masu. Amsa tayi tace Thanks tana kallon sai da ya buɗe ma Humaira nata sannan ya bata. Laaa ai kuwa bazan maka takwara ba tafaɗa tana harararshi. Ruhaan ne yace mai ya miki kuma? Shi ai ya sani, cewar Amira tana murmushi. Amii ayi min afuwa cewar Yarima yana risunawa. Shikenan an maka tafaɗa tana murmushi. Imann mai kike cewa Rafik wai?
Murmushi tayi tace kasan kowa a rayuwar nan, duk muguntar sa, duk rashin imanin sa. Akwai certain mutanen daya kema soyyaya taban mamaki koh? Gyaɗa mata kai Ruhaan yayi yana kallonta. Toh yana da wadannan mutanen kuma suna hannu na tafaɗa a hankali kamar mai raɗa. He has a mistress and a child. Amii don't play dirty cewar Humaira tana kallonta. Well I have to tafaɗa tana cin meatpie dinta. That's my girl cewar Ruhaan yana bata hannu suka tafa. Murmushi yayi yace muje lokacin break din ya ƙare.
Riko hannunta yayi har cikin court room din yace Allah ya bada Sa'a. Ina Ammi tafaɗa tana kallonshi. Gatacen yafaɗa yana nuna mata Ammi da ido.
Alƙali ya kalli Ameerah yace tanada wasu sheɗun.
A'a tafaɗa tana kallon Rafik. Rafik ne yace yana da magana. Rantsuwa aka bashi yayi kafin ya haɗiye yawu da kyar yace.
Ni banyi harƙallar kwaya ba, amma nasan mai yi. Alhaji Abdulkarim Kurfi munso jawo shi siyasa saboda dukiyar sa mai tarin yawa. Amma a kullum amsarshi ɗaya. Bazai yi abinda za'a kawo shi gaban Ubangiji da sarkoƙi ba. Akwai wani babban yaron Alhaji Abdulkarim Kurfi Mukhtar. Ya kasance yana kula da duk wasu harkokin shi. Toh a hakan ya gano cewa ɗaya daga cikin driver trailers din safara kayan abincin A.K Group na amfani da wannan damar yana safarar kwaya. Bincike suka tsananta daga nan Alhaji Abdulkarim Kurfi ya haɗa zama dani. Koh a lokacin da mukayi maganar nace mai ni bansaida kwaya amma nasan mai kayan so shiyasa binciken sa ya nuna kamar nine mai kayan.
Yaƙi yadda, inda daga baya ya fara bincike akan case din wanda ni bansan dalilin sa ba. Kwatsam saiga labarin mutuwar shi. Iya abinda nasani kenan.
Kallon Ameerah alƙali yayi yace kinada tambayar da zaki mai?
Eh, mai sharia cewar Amira tana nufar Rafik.
Kace kason mai harƙallar kwayoyi? Tabbas hakane yafaɗa yana kallonta.
Shin mai harƙallar kwayoyin nada Alaƙa da mutuwar Alhaji Abdulkarim Idris Kurfi? Tabbas akwai ALAƘA.
Shin waye mai harƙallar kwayoyin?
Kallon Yarima yayi sannan ya kalli Ruhaan, sannan ya juyo ya kalleta yace can you handle the truth?
Rolling eyes tayi tace karka wahalar da Shari'a.
Huci ya furzar yayi jim kafin yace Khadija Muhammad Bubayaro. Heyyy! Cewar RUHAAN yana mikewa tsaye, jijiyoyin kansan na fitowa.
Baya Amira tayi jiri na dibanta ta dafe kujerar dake kusa ita.
Excuse me... Tafaɗa tana kallon shi. Khadija Muhammad Bubayaro. Guduma alkali ya buga yaja ma Ruhaan kunne. Zaunar dashi Yarima yayi yace ka nustu please.
Aisha Muhammad Bubayaro idan tan nan kotu nason ganinta. Tasowa Ammi tayi ta nufi wajen mai bada sheda.
Rantsuwa tayi ta tsaya. Lawyer Rafik na mata tambayoyi. Tsaye Amira tayi gabaki ɗaya ta kasa motsi.
Miye Alaƙar ki da Rafik Adebola? Babu wata Alaƙa a tsakaninmu.
Bakida wani magana akan claims din dayayi? I deny it tafaɗa tana kallonshi.
Kanada wata hujja dake nuna cewa abinda kafada gaskiya ne? Flash ya ciro a aljihunsa. Jonawa Lawyer shi yayi saiga fuskar Ammi ta bayyana. Duk wasu harƙalla na kwaya da take yi. Sanda take aika trailer accidents uku da suka faru. Sanda ta tura Nisa wajen Amira. Sanda ta turo Mahmud wajenta.
Sanda ta tasaka Mahmud yana Abbi alurar data tsayar da zuciyarsa. Sanda tasa akayi kidnapping Du'a. Ita ta kaita har gaban orphanage din Humaira.
Kallon Ammi Amira takeyi kamar wata mutum-mutumi. What can you say about this? Cewar Lawyern Rafik ,yana kallon Ammi. Shiru tayi ba tare da tace komai ba. Just say no! Ammi kice karyane i will believe you! Ko kowa bai yadda ba. Nina yadda dake cewar Ameerah tana kallonta.
I admit cewar Ammi tana dauke idanunta daga kan Amira. Okay it's fine Ammi kece! Naji but give me your reason atleast, ki bani excuse please, ki gayamin dalilinki, zan yafe maki Ammii. Nice Amira babu wani excuse.....Kafin ta rufe baki Amira ta yanke jiki ta faɗi. Da sauri Humaira tayi kanta tana jijjigata. Ruhaan ne ya miƙe kamar wanda kwai ya fashe mawa a ciki ya dauki Amira kamar gawa ya fice da ita. Da sauri Yarima ya buɗe mai mota yasata a baya. Ruhaan ya shiga bayan ta daura kan Amira a cinyarshi ya tsura mata ido. Gaba Humaira ta shiga tana kuka itama. Key Yarima yama motar da gudun gaske ya fice a asibitin.
Buɗe bakinta yayi a hankali ya dinga ƙoƙarin janyo numfashinta.
Hawayen dake bin kumatunshi ya share. Ganin suna ɗiga akan fuskarta.
Parking Yarima yayi, cikin sauri Ruhaan ya daura Amira akan gadon marasa lafiya. Da gudu suke tura gadon shida Yarima.
Suit dinshi ta sama Yarima ya cire ya yar. Ya haye kan gado ya haɗe hannunshi waje biyu, yana danna kirjin Amira. One, Two, Three.....get the oxygen yafaɗa a tsawace yana cigaba da danna kirjinta. Bata responding! Cewar Humaira tana kuka. Shut up you sisters enjoy putting me in this state yafaɗa yana tuna sanda Humaira tayi accident.
Move cewar Ruhaan yana hada Defibrillators din hannunshi waje guda. Raba su yayi ya daura akan kirjin Amira yace chargee! Da karfin gaske yaja shi amma haka ta koma kamar gawa. Kuma jona shi yayi yace chargee 200. Nan ma still bata tashi ba. Yayi yakai sau hudu. Dafashi Yarima yayi da jajayen idanunshi yace she is no more. Mari mai zafin gaske Ruhaan ya sauke akan fuskarshi yace bakada hankali ne. Matata ce bata mutu ba. She can't die because of that wicked woman! Wallahi idan Amira ta mutu sai na tabbatar tayi mutuwar wulaqanci. Mahaifiyar ka ce Ruhaan don't talk like that, nasan kaima ka damu da halin da take ciki a yanzu cewar Humaira tana kuka.
Yanason Amira sosai kamar kanwarsa
Ni ban damu ba, i never expected anything from her. Damuwar danayi halin da matata zata shiga saboda soyayyar da kuma yaddar da take nuna mata.
Duk mai rai mamaci ne cewar Yarima yana share hawayensa.
Patient Name: Khadijah Abdulkarim Kurfi
Time of death: 1:06pm yafaɗa yana dauke idonsa akan agogon.
Riƙo kwalar rigarshi Ruhaan yayi yace ubanwa yace maka ta mutu? Ganin kamar ya zauce yasa Yarima ya kyaleshi bai cemai komai ba. Illa tsayawa yayi da yayi yana kallon shi.

Toh mu haɗu a next page 📄📄📄

ANA ZATON WUTA A MAƘERA.....🔥
✒️ IBNATU-UMAR ✒️
Page 73&74
Chapter 48 · 0% Book details