← Book details Ana Zaton Wuta A Makera Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 50

Sashe 17

Ana Zaton Wuta A Makera Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Juyawa drivern yayi, suna yin horn Humaira ta fito da gudu, bai yi mamaki ba, dan HUMAIRA tafi jinshi a ranta fiye da Ameerah. Ameerah kafin tace Abbee sau ɗaya tace Ummii sau ɗari.
Rungumeshi tayi ta fashe da kuka, shhhh yafaɗa yana share mata hawaye. Riƙo hannunta yayi suka shiga ciki, kallonshi kawai yaga Khadijah tayi ta dauke kai. Murmushi yayi yace ba'a maraba da dawowata ne? Ko ɗaya tafaɗa tana kallonshi. Amma in ka biye masu bazaka tafi da wuri kayi abinda kakeso ba. Ki duba inda nake ajiye agoguna na. Zaki ga chains din gold guda biyu ki kawo min. Zuwa tayi ta dauko mai. Ameerah ce ta fito a kitchen rike da plate din cinnamon buns tace Ummii in cinye dana Humaira. Koh kallonta Humaira batayi, balle ta kula ta. Toh bara naci ta fara cin abinta batare data kula da Abbee dinsu daya dawo ba. Ganin tayi amanta ta lashe Humaira bata kulataba yasa ta fara mata masifa, shiru tayi tana kallonta tana murmushi. Hakan kuma ƙare kuleta yake yi. Zo habibty cewar Abbee yana murmushi.
Ajiye plate din tayi ta taho taga shi dinne da gaske. Da gudu ta ɗaleshi.
Ganin Khadijah ta dade yasashi binta saman.
Zaune yasameta gaban mudubi, karasawa yayi ya rungumeta ta baya yace mai ya faru tunanin mai kike? Babu mai ma kace in kawo maka. Ruko hannuwanta yayi yace ya tabbata tunanin kike kenan. Faɗamin mai yake kai idan nace maka ga abinda ke damuna nayi karya. Amma banjin dai-dai ajikina. Shima kawai dauriya yake da za'a buɗe kirjinshi da tabbas zasu ga ya fisu damuwa.
Rungumeshi tayi, sun dade a haka tsawon lokaci kafin ya janyeta a jikinshi ganin yayi latti. Hawayen idanunta ya share yace mai ya faru? Kinsan ina ganin damuwa a tattare dake bazan iya tafiya ba. Abdulkarim tafaɗa tana kallonshi, nutsuwa yayi ya saurareta da tunda yasanta bata taɓa kiranshi da sunan shi haka ba. Duk wata kaunar dazaka nunamin bazan gane kanaso naba sai ka bama ya'ya na wannan kaunar a bayan idona. Tana gama fadin haka ta sauka ƙasa, da kallo ya biya dan bai gane kan zancen taba.
Chains din ya dauka ya sauka ƙasa.
Guɗa biyu ne daya anyi ado an rubuta A a jiki ɗaya kuma K. Sama Humaira yayi a wuyanta.Sannan ya sama Ameerah itama. Pecking goshin Ummii dake kallonsu yayi. Ya juya har ya kai kofa ya juyo ya kalleta,murmushi ta sakar mai daya tsaya mai rai.
Juyawa yayi ya fita dan idan ya biye masu bazai tafi ba.
Awa 17 Abbee yayi a hazo kafin ya isa Australia. Yana sauka ya kirasu suka gaisa. Ameerah ce ta mika ma Aunty Mami wayar tace Abbee your sister is here to see us. Murmushin jin dadi yayi, yanason yadda kanwar tashi ke nuna sonda kula ga ya'yan shi. Allah ya bata nata ita yafaɗa a ranshi.
Kamar yadda Abbe yama su Humaira alkawari. Kwana biyu yayi a Australia.
Yana shirin kiran Ummii yace mata zai taho sai ga shi ta kirashi. Kamin izini inje Katsina. Lafiya? Ya faɗa cikin tashin hankali jin yadda muryarta ke rawa. Allah yama Hajiya rasuwa. Hajiya ita kaɗai ce dangi ta kusa data rage ma Ummii (matar baba dattijo ce) Innalillahi Wa Inna Ilayhi Raji'un, Allah yaji kanta ya gafarta mata. Amma daga Abuja Flight zaku bi zuwa Kano daga Kano kuma zusa Katsina a mota za'a kaiku, bari na kira Mukhtar. Ki kwantar da hankalinki.
Kashe wayar kawai tayi ta haɗa masu kayansu ta sauka ƙasa neman su taga Ameerah tayi kacha-kacha da kitchen, Humaira tama faɗa akan mai batasa ido ba har Ameerah tayi wannan barnan. Hakuri Humaira tabata Ameerah kuwa guduwa tayi ta boye, ganin Ummii ta fashe da kuka yasa Humaira fara bata hakuri. Ummii dan Allah kiyi hakuri zan dinga sama Ameerah ido. Girgiza mata kai tayi kawai ta rungumeta tace ba haka bane Humaira Hajiya ta rasu. Duk da kasancewar ta karama amma tasan mutuwa kwantar ma da mahaifiyarsu hankali Humaira tayi.
Karfe biyu na rana jirginsu ya sauka a Kano daga nan Mukhtar ne ya tuƙa su, suka dauki hanyar Katsina.
Tuƙi Mukhtar yake cikin kula da nustuwa, Ameerah da Humaira ne ke faɗa, kuma Ummiii bacci ya dauketa, juyawa yayi yana masu magana kan ya farga, trailer ta taho da gudun gaske ta bige motar nan take motar tafara kundun bala a titin tana ci da wuta.
Mu haɗu a next page 📃📃📃

ANA ZATON WUTA A MAƘERA.....🔥

✒️IBNATU-UMAR ✒️
Chapter 17 · 0% Book details