← Book details Ana Zaton Wuta A Makera Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 50

Sashe 11

Ana Zaton Wuta A Makera Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

Toh fah😂🤌🏾 ana yi muna jin dadi.
Shin mai ya kawo Hajiya Hamdiyya wajen rabon gadon Aunty Mami? In baku manta ba Hajiya Hamdiyya matar baban Ameerah ce, kunga kuwa batada gadon kanwarshi.
Shin mai Mahmud ke shiryawa?
Kuna ganin za'a tashi wannan taron lafiya kuwa?
Mai yasa Aunty Mami tabama Ameerah kusan duka dukiyar ta?
Mijinta fah?
Miye asalin labarin waɗannan mutanen?
Ku biyoni bada jimawa ba zamu tafi danjin tushen wannan badaƙala.
Mu haɗu a next page 📃📃📃

ANA ZATON WUTA A MAƘERA.....🔥

✒️IBNATU-UMAR✒️

Page 17&18
Duka ɗaya ba ƙari ya ke masu ya shige ciki. Murɗa kofar yayi yaji a rufe, kallon gefen kofar yayi yaga fire alarm. Ƙasa lemar yasa ya fasa shi, nan take wajen ya cika da ƙara, wuta, wuta fah cewar Mahmud yana kallon Naseer daya tsaya akan Khadijah da tayi nisa cikin tunanin abin yi.
Ruwa ne ya fara zuba a dakin sanadiyyar alarm din wutar da Ruhaan ya fasa, fice suka farayi da gudu ba tare da sunbi takan Khadijah ba.
Ganin yadda ruwan ke jiƙa ta yasa ya ware lemar, yasa akanta. Ɗago jajayen idanunta tayi ta zuba mai. She felt alone for a second tayi tunanin bata da kowa, hatta Mahmud dake mijinta abandoning dinta yayi akan kuɗi. Amma shi yazo batare daya jira umarnin ta. He is the one i need tafaɗa a ranta.
Walk straight your enemies are watching yafaɗa yana kallonta, tashi tayi tana tafe yana binta a baya da lema.
Wani mugun kallo ta watsa ma Mahmud, buɗe mata mota yayi ta shiga, ya miko mata towel, zaki yi mura yafaɗa yana kallonta, amsa tayi tafara goggoge jikinta. Mohammad tafaɗa tana kallonshi, kallonta dan bai taɓa jin ta kira sunan shi, News Buzz tafaɗa tana kallonshi, cikin sauri yayi reverse suka wuce. Kallonta Mukhtar yayi yace Miss kiyi hakuri wallahi sai da naja mai kunne akan bakya son shishigi, laifi nane banyi training dinshi da kyau ba. Hannu kawai ta ɗaga mai, alamar bata son magana.
Koh parking bai gama ba ta sauka, ta shiga ciki, bin bayanta sukayi.
Faith assembly all the securities we have here, D.S.S agent na zuwa nan da minti 10. Zaro ido Faith tayi, will you stop staring and do as i say! Tafaɗa a tsawace, wuce wa Faith tayi cikin sauri dan aiwatar da abinda ta sata, cikin sauri Nisah ta nufi Ameerah tana goge mata kanta daya jiƙe, bar wannan dan Allah tafaɗa a fusace. Zama tayi tana tunanin mafita, Ma'am the job is done cewar Faith, kice masu kadda koda sauron D.S.S ne ya wuce kofar shiga News Buzz, duk yanda zasu yi, suyi amma banson su samu damar shigowa, balle har wani information namu yayi leaking.
Ishaq ne da Aminullah suka zo bisa umarnin ta. Ishaq tafaɗa tana kallonshi, Yes Ma'am ya faɗa yana gyara tsayuwar shi, nasan securities din mu zasu iya dragging D.S.S minimum minti 30 maximum minti 60. Kafin nan da minti ashirin duk wanda kasan yanada kusanci kuma yana da iko da shugaban D.S.S ka nemo duk wani laifi da zamu iya mai barazana dashi susa shugaban D.S.S ya janye mutanen shi.
Yes Ma'am yafaɗa yana juyawa zai fice, kira ne ya shigo wayarta, dauka tayi.
Kallon Ishaq tayi tace ya dawo, dawowa yayi ya kalle ta, murmushi tayi tace disassemble the securities, sun janye.
Amma taya suka janye cikin kankanin lokaci, Shugaban D.S.S na yanzu yanada amana da gaskiya, so mai yasa zai janye.
Allah masani tafaɗa tana kallonshi, bara naje gida, Alhamdulillah tafaɗa tana mikewa.
Rakiya suka mata har mota, jingina tayi da kujerar ta lumshe idanunta, today was very hectic tafaɗa a ranta.
Allah nagode maka tafaɗa tana dafe kanta dake mata wani irin ciwo kamar zai fashe.
Parking Ruhaan yayi ya buɗe mata ta shige ciki.
Ruwan sanyi ta sakar ma kanta, tana tunanin duk abubuwan da suka faru yau. Lallai mutum mugun icce, tabbas babu abinda mutum bazai iya ba akan kuɗi, Mahmud da Daddy Tahir bata taɓa tsammanin haka daga garesu ba.
Kuka taji ya zo mata tayi saurin maida shi, har abada bazan kuma zubar hawaye na akan yaudarar ɗa namiji ba, anyi na farko gana, biyu ba za'a yi na uku ba tafaɗa cikin ƙunci.
Fitowa tayi sanye da bathrobe, Mahmud ne ya shigo dakin, Babee.....karka soma tafaɗa tana ɗaga mai hannu. Babee pleasee listen to me, yafaɗa yana rungumeta tsam a jikinshi hannusi yakai kan igiyar rigar ta, tureshi tayi tana mai mugun kallo, you fuck? I didn't fuck you yet baby yafaɗa yana rikota, Mahmudddd!!! Tafaɗa a tsawace, ba shi ba dai-dai da ita da tayi tsawar sai da taji wani iri a saman kanta. Wallahi Tallahi ka kuskura ka ƙara taɓa ni sai na lahanta ka. Bari fa kaji ni ba jahila bace, kuma ni ba dakiƙiya bace tafaɗa a fusace.....babee please i can explain, listen to me yafaɗa yana nufota, hannunta ta ɗaga alamar kar ya matso kusa da ita. Dama ku maza duk haka kuke mayaudara, koh zuciya za'a ciro a danƙa maku a hannu sai kun nuna ba'a maku dai-dai ba. Wa toh kun san cewa bazan iya siyar da abinda Aunty Mami ta mutu ta barmin ba, koh kuwa hakan zai yi costing na rasa News Buzz, a lokaci ɗaya kuka so kumin lahanin da sai Allah ya bani karfin zuciya ne zan iya rayuwa, so kukayi ku rabani da komai zuciyata ta buga koh? Akan kuɗin Mahmudddd!! Fita wallahi kafin na illa taka tafaɗa tana huci. Ganin yadda ranta ya ɓaci kamar mai aljanu yasa shi ficewa. Murmushin takaici tayi, abinda Mahmud yayi she can forgive him inda haka ne, saboda tasan dan adam ne ajizi, duk da bai chanchanci yafiyarta ba.
Amma tana sane tamai hauka-hauka so take ta gani, mugayen abubuwan da yake a bayan idonta.
Tun da taga abinda yake tana kyamar shi, tasan kuma idan ba haka tamai ba, ba tada excuse din da zata sa ya nisance ta.
Yau asabar tunda ta tashi, ta kasa saukowa daga gado saboda wata irin kasala data tashi dashi, Zaid ne ya shigo da sallama. Hawa gadon yayi yace Ummii mai ya sameki? Murmushi tamai tana kallonshi, are you okay? Yafaɗa yana kallonta, hawaye taji suna taruwa a idanunta saurin maida su tayi tace am fine my boy, come here tafaɗa tana buɗe mai hannunta, rungumeta yayi yace come here Ummiii, dariya tayi tayi pecking kumatunshi. Danne ta sukayi.Zaynnn tafaɗa tana leƙo da fuskarta waje, Ummiii yafaɗa yana dariya, bacci kike ji? Yafaɗa yana leka fuskarta, no na tashi, toh ki tashi Ummii muje yawo yafaɗa yana jan hannunta. Ku ɗaga ni toh, tafaɗa tana mike masu hannuwanta, janta suka dinga yi har suka gaji. Naɗe hannun riga Zayn yayi yace i can do it yafaɗa yana riko hannuwanta duka biyu dan Zaid ya gaji ya kwanta, janyota yayi ta tashi kawai dan itama ta gaji daja mata hannu da sukeyi. Yesss sai ni Muhammad dan Muhammad kuma jikan Muhammad, a firgice ta kalleshi tana tuna sanda wani ya taɓa gaya mata irin wannan statement din.
Har zata mai magana sai kuma ta kyale shi, ku koma parlour ku jirani bari na yi wanka. Parlourn saman suka zauna suna jiranta, tv suka kunna suna kallon su.
Wanka tayi ta fito ta zauna a gaban mudubi tana ƙarewa kanta kallo. A dan tsakanin nan gabaki ɗaya ta rame sosai, duk da cewa siririyace ita, amma tun bayan haihuwar su Zayn ta dan yi kumari.
She needs to spend time with her children, watakila taji sauƙin abinda ke ranta, idan ba haka ba any moment zata iya ganinta a gadon asibiti.
Fitowa tayi a shirye, kallonsu tayi tace sun ƙarya suka ce a'a. Mai yasa baku ci abinci ba tafaɗa tana kallonsu? Ke muke jira, Daddy ma da wuri ya fita suka faɗa suna kallonta.
Okay ku taso muje tafaɗa yin gaba, binta sukayi, Zayn na nata daukanta hoto da camera dinshi.
Uncle Moh!! Suka faɗa suna rugawa da gudu suka rungumeshi. Murmushi yayi yana rage tsayinsa dai-dai su, how are you doing? Yafaɗa yana kallonsu, fine Uncle Moh, hira suka fara, ganin Ameerah ta shige mota yasa shi bude masu, suma suka shiga, haɗa ido sukayi yayi saurin dauke nashi idon yace Good morning Ma'am, Morning tafaɗa tana haɗe rai. Murmushi yayi ya rufe mata motar, ya zagaya yaja motar.
Restaurant sukaje suka karya, sannan ta kaisu park sukayi wasan su, daga nan takaisu shopping suka siyo duk abinda suke so, they had alot of fun.
Sai wajen hudu da rabi suka dawo gida.
Bashi tashi ledar da suka mai siyayya Zayn da Zaid sukayi. Duk yadda yaso yayi rejecting sunƙi. Amsa yayi yana jin daɗi. Wannan ne karo na biyu a rayuwarshi da aka taɓa mai shopping kyauta aka bashi.
Ciro abubuwan Ameerah tayi, dakin Mahmud ta shiga ta saka ƙananun camera's. Tabi gidan lungu da tsako duk da camera's din.
Tana jin dawowarsa, bai jima ba ya fice masallaci. Fita tayi ta saka tracker a karkashin motocin sa guda biyu, yar karamar sound recorder. Sannan ta koma dakinta.
Tana zaune a dakinta tana aiki cikin computer, Zayn da Zaid ne suka shigo, Mamii kizo kiga surprise suka haɗa baki wajen faɗa. Murmushi tayi ta miƙe ta bi bayansu. Ɗakin su Zayn ta shiga, Sip and Paint cewar Zayn yana nuna mata drawing board dinta da sukayi setting. Murmushi tayi tana tuna sanda rana bata wuce wa ba tayi zane ba. Da ace tana bawa zanen ta lokaci yadda take bashi a baya da duk damuwa bata mata yawa haka ba. Apron ta dauka ta saka, ta zauna gaban drawing board din, for the first a rayuwarta tunda take zane ta dauke brush tana tunanin mai zata zana. Tasan haka kuma bai rasa nasaba da abubuwan dake ranta.
Ummiii ki zana mana Uncle Moh, sai ayi mana framing hoton musa a daki. Da mugun mamaki take kallonshi, mai zakayi da hoton Uncle Moh? Tafaɗa tana kallonshi, nothing much i just love him. No ku zaɓi wani abun dai tafaɗa tana kallonsu......da kyar suka hakura sukace ta zana masu Baby Girl suna son kanwa. Murmushi tayi tace toh kawai bawai dan taso din ba sai dan bata son ta kuma ce masu a'a ne.
Tsab ta zane masu baby girl, tayi painting 🎨🖌️ tana yi suna bata juice da snacks a baki. Wowww cewar Zaid yana washe baki, Mamiii you're the best, well she is my mother afterall cewar Zayn yana murmushi.
Zan bawa Uncle Moh dinku gobe yakai ayi framing. Tafaɗa tana cire Apron dinta, La'asar tayi ku tafi Masallaci.
Rike hannun juna sukayi bayan sunyi alwala suka tafi masallaci. Ita kuwa dama ba sallah take ba, dakinta ta koma tana zuwa ta janyo laptop dinta. Harta gama sauraren muryoyin mutanen da Mahmud ya haɗu dasu a yau bataji na wata mace. Amma kuma tracker din ya nuna yaje News Buzz kuma daga nan ya wuce Hotel.
Murmushin takaici tayi, ta kashe laptop din, duk da ba wani son Mahmud take ba,amma abinda yake yi sosai yake ƙona mata rai, kasancewar mai shegen kishi.
A bangaren Mahmud kuwa yana dawowa ya nufi dakinta, a kwance a sameta tana juyi a gaɗo tama rasa mai ke mata daɗi. Babeee yafaɗa yana shafa gefen fuskarta, bige mai hannu tayi ta miƙe zaune tace mai kake so? Banason zaman mu haka, kiyi hakuri. Just leave tafaɗa tana nun mai kofa. Fita yayi yaja mata kofar. Zama yayi yana nazari, anya bata gane sirrinshi ba kuwa? Idan ma bata gane ba zarginshi take, zai tabbatar ya goge wannan a ƙwaƙwalwarta.
Mu haɗu a next page 📃📃📃
ANA ZATON WUTA A MAƘERA......🔥
✒️ IBNATU-UMAR ✒️
ANA ZATON WUTA A MAƘERA.....🔥
✒️IBNATU-UMAR ✒️
Chapter 11 · 0% Book details