← Book details Ana Zaton Wuta A Makera Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 50

Sashe 7

Ana Zaton Wuta A Makera Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Page 11&12 Juyawa tayi ta rungume Nisah ta fashe da kuka mai dauke da mixed feelings. Sakin Nisah tayi a hankali ta taka zuwa gaban gadon, riko hannun Zaid dake wasa da drip din hannunshi tayi, tana kallonshi sai yanzu ma ya kula da cewa da mutane a dakin. Magana zai mata sai kuma ya fasa, yana haɗe rai. Babana tafada tana leka fuskarshi. Maaa yafaɗa yana hawaye, rungumeshi tayi kamar wani zai kwace mata shi. Tapping bayanta ya dinga yi da cute little hands dinshi. Murmushi tayi tana kallonshi tace are you okay? Akwai inda ke maka ciwo tafada tana dudduba jikinshi, Relax am fine yafaɗa yana murmushi. Da murmushi Mahmud ya ƙaraso dakin ya kalli Zaid yace Alhamdulillah, Allah shine mai bayarwa shine mai hanawa. Yau Allah ya baka lafiya Zaid, ya tsina fuska yayi yace who are you? Zaid he is your father cewar Ameerah tana kallonshi, no bashi bane babana. Babana yazo kuma na ganshi kuma yace zai dawo yafada yana daura kafa daya kan ɗaya. Da mamaki Ameerah da Mahmud ke kallonshi, Babe ku bincika ƙwaƙwalwar yaron nan, dan bansan wa ya gani ba, kuma a ina ya ganshi ba. Am totally fine yafada yana kallonta. Karki damu cewar Mahmud, daukanshi Mahmud yayi Ameerah na biye dasu a baya suka nufi dakin MRI scan, cikin Machine aka saka Zaid dan daukan hoton ƙwaƙwalwar shi, kallon Zaid take cikin damuwa. Dafa kafaɗarta Nisah tayi tace karki damu Ameerah, In Sha Allah. Babu wata matsala, gyaɗa mata kai kawai tayi kawai dan tama rasa abin cewa. Kallon Ameerah Nisah tayi tana tunanin jarabawar data gani a rayuwa, amma duk da haka babu wanda ya isa yaga karaya akan fuskarta indai ba abin akan ƴaƴanta bane. Waɗannan yaran sune weakness din Ameerah, ta rasa masoyi, ta rasa mahaifa, amma kwata-kwata bata karaya ba, she is a strong woman, lallai taci sunan mai asalin sunan. Bayan awa ɗaya aka fito da result din, duba result din Mahmud yayi yace babu wani problem a tattare da shi fah. Subhanallahi ta faɗa tana rike kujerar dake kusa da ita, wai nai yake faruwa ne? Nurse ce ta shigo rike da hannun Zayn, hango Zaid yasa shi ya fisge hannu shi da gudu ya rungume Zaid da'aka zaunar akan gado. Murmushi Zaid yayi ya ciro Zayn a jikinsa, Akhi yafaɗa yana kallon Zayn, ka samu lafiya? Ka warke? Yafada yana dudduba jikin Zaid. Am fine yafaɗa yana kallon Zayn. Maaa yafaɗa yana kallon Ameerah data dafe kanta dake sara mata, kallon Mahmud tayi tace mu tafi gida, na gaji ta faɗa tana zama a kan kujerar, daukan Zaid yayi dake har yanzu bazai iya tafiya ba saboda dadewar da yayi a kwance, riko hannun Zayn yayi ya kaisu mota. Kallon Muktar yayi daya kasa zaune ya kasa tsaye yace ka kwantar da hankalin ka ta tashi. Alhamdulillah yafada cikin jin dadi. Sallama tayi da Nisah, Mahmud ya rike hannunta ya kaita mota, suka wuce gida. Wanka tayi a daddafe ta sha maganin ciwon kai ta kwanta bacci. Mahmud ne ya tsaya akan Zaid da Zayn suka ci abinci suka shirya suka kwanta. Dakinta ya nufa dauke da plate din tea da toasted bread 🥪, tsayawa yayi yana karewa fuskarta kallo, har tayi wata irin rama sosai. Shafa fuskarta ya dinga yi harta buɗe idanunta da sukayi nauyi ta zuba mai, not now please tafaɗa tana kallonshi. Ni nace maki wani abu nake so ne yafaɗa yana mikar da ita, tray din ya daura mata akan cinya, kici abincin yafaɗa yana tsareta da ido. Kaɗan taci sannan ta miƙa mai tray din ta koma bacci.Kitchen yakai tray din ya dawo ya kwanta gefenta shima. A gaggauce take shiri danta makara, dakin su Zaid ta shiga, suna bacci abinsu, da yake Zayn an masu hutu jiya. Shafa kansu tayi ta masu addu'a, sannan ta sauko ƙasa. Kwata-kwata Muktar ya ƙasa haɗa ido da ita, murmushi tayi tace Muktar it's fine, ba komai ne zakayi ta blaming kanka akai ba, you tried your best. Miss you're not angry? Yafaɗa a sanyaye. Murmushi tayi tace da ace bakayi cleaning accident din kamar ba abinda ya faru ba, da zanyi fushi, amma duba da cewa yan jaridu basu cika mana gida ba, kuma babu a news prove how capable you're. Tana gama faɗan hakan tayi tana cewa follow me. Cikin sauri ya buɗe mata bayan motar ta shiga, gaba ya shiga gefen driver. The driver? Ma'am muna bincike ne kan shi, saboda route din daya bi dake, let him go tafaɗa tana batare data kalli inda Mukhtar yake ba, Misss? Shine silar komai fa daya faru dake, kuma taya zamu gane asalin mai laifin idan muka sake shi? Nasan waye mai lafin, ku sake shi, kusa ido sosai akan shi tafada tana kallon sabon drivern dake tuƙa ta. Ina son inyi scheduling interview na bodyguard dinki, okay ai gaka ga security din basai ka gayamin ba Mukhtar. No Miss outside our comfort zone, yafaɗa yana murmushi. As you wish tafada tana cigaba da aikin ta. Babbar damuwar Mukhtar security din Ameerah. Parking motar tayi ta sauko rike da tap dinta, Faith (sectary) ta dauki jakarta da sauran tarka cen ta dake motar. Aikin dake gabanta tayi saboda jiya dama batayi komai ba, tana shigowa office ta wuce school dinsu Zayn. Shiyasa aiki ya tarar mata. Harta fara aikin taji bazata iya ba, gabaki ɗaya hankalinta yayi wajen su Zaid. Musamman ma shi daba lafiya bace dashi sosai. Nisah duk wasu takardu dake buƙatar sa hannu na, ki haɗasu ki bama Faith ta kawo min mota ta faɗa tana rufe laptop dinta. Lafiya kuwa? Cewar Nisah tana kallonta. Lafiya i will work from home for this week. Tana faɗin haka ta fice zuwa mota, koh minti biyar batayi ba saiga Faith da files din. Key driver yana mota ya dauki hanyar gida, securities nabinsi a baya. Kallon drivern tayi tace ya tsaya a Mall. Cikin girmamawa ya amsa mata, ta sauka ta shiga ciki, rasa mai ma zata sai ma Zaid tayi. He is home after 2 years, murmushi tayi tunawa da tayi cewa Zaid nason Cake dinta, so zata mai baking da kanta. Abubuwan decorating cake din datason bata dashi a gida, ta siya ta biya. Ta fito zata wuce, ta ciro da wani, Are you lost, Baby Girl? Yafada da husky voice dinshi, hannunta daya fara trembling ta riƙe ta ɗago ta kalleshi. Haɗa ido sukayi ta saurin dauke idonta tana faɗin Astagfirullah jin wani abu na neman ɗarsuwa a ranta. Noorr yafaɗa yana kallonta, murmushi ta kakalo tace ykk, sai an jima tafaɗa tana ƙoƙarin wucewa. Abinda zaki ce min kenan bayan shekaru 6 yafaɗa yana shan gabanta, Moh please am married now tafaɗa tana kallonsa. I know yafaɗa yana kallonta, then please leave me aloneee. Na tsareki Noorr tunda kika tafi kin kara ganina a gabanki idan ba yau ba? And i thought bai kamata a ce after all we had between us, in wuce without asking how you're doing. Am fine, thanks. Tafaɗa tana wucewa. Jikin motarta ta tsaya, dafe kirjinta dake mata suya tayi, ta lumshe idanunta wasu irin hawaye masu zafi na fitowa daga idanunta. Why? Why him? Mai yasa take rabuwa da duk masu sonta, mai yasa take nisantarsu. Ji tayi duk ta tsani kanta saboda yadda ta mai magana. Motar ta buɗe ta batare data rufe ba, tasaka kanta tsakiyar cinyoyinta ta fashe da kuka mai tsuma rai, abu taji ya fado jikinta tashi tayi taga farin handkerchief, shakar kamshin dake jiki tayi ta ware shi daga gefe tana kallon yadda akayi embroiding M.R.M. Share hawayenta tayi, ta kalli drivern tace su tafi. Yanason tambayarta lafiya amma yana jin tsoro, haka yasa yaja bakin shi ya tsuke. Gyara fuskarta ta shafa hoda, sannan ta sauko daga motar, ta nufo cikin gidan. Kitchen ta ajiye kayan bayan ta gayama mai aikin ta abubuwan da take so ta ajiye mata na baking cake din. Dakin su Zayn ta nufa, tana jin hayaniyar su,who is having fun without me tafaɗa tana murmushi, Ummiii, Maaa suka hada baki wajen faɗa. Kallonsu tayi Zayn ya rike kwankwason Zaid a dole yana koya mai tafiya, dariya tayi tace Zayn bazaka iya ba ai. Ta faɗa tana supporting Zaid. Shafa kanshi tayi tace ya jikin ka? Am fine yafada yana kallonta butt.... Butt what? Tafaɗa tana kallonsa...Am missing Daddy, kallon Zayn tayi tace Daddy bai zo nan ba? Ya shigo shi yakai Zaid bayi yayi mai wanka, kuma da Zaid ya gama shi ya dauko shi. Not him cewar Zaid a faɗace, ni ba shi nake magana a kai ba, my real Daddy. Wai ina kika samo shi Ummiii, Zaidd!! Ta faɗa cikin ɗaga murya, shiru yayi dan ya hango ɓacin rai a cikin fuskarta, kar in kuma jin wannan zancen, he is your father!! Ka jini? Naji yafaɗa a sanyaye. Sauke shi tayi ta juya ta fice zuwa dakinta. Wanka tayi ta saka riga mara nauyi, sannan ta nufi kitchen din, cikin awa ɗaya ta gama cake dinta mai 3 layers yayi kyau sosai tayi shi blue saboda she favourite colour din Zaid. Ɗakin ta nufa, ta buɗe kofar TADAA 🎉 tafada tana murmushi, cakeee cewar Zaid yana kallonta da fara'a a fuskarshi. Bashi wukar tayi ya yanka, no Maa it's so cuteee yafaɗa yana blushing, dariya Zayn yayi yace nidai ina son inci Akhi ka yanka, but Maa put alot of effort to make this yafaɗa yana pouting face, but tayi dan kanci ne Zaid look "WELCOME HOME" yafaɗa yana nuna mai abinda Ameerah ta rubuta a akan cake 🎂 din. Muhawara sukayi tayi akan a yanka cake din koh kuma a barshi, tsayawa tayi tana kallonsu tana jin wani irin dadi a ranta, sai taji kashi tamanin din damuwarta bayan haduwarta da Moh ta ɓace. Icing din da Zaid ya dangwala mata a hanci ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin daya tafi. Mamiii yafaɗa yana ɓata fuska. Am sorry tafaɗa tana cin cake din daya nufi bakinta dashi ashe har ya yanka. Zayn ne ya shigo rike da plates da forks yace serve us guy yafaɗa yana zama a kan lallusan carpet din dake dakin, yankawa yayi ya saka mashi shida
Chapter 7 · 0% Book details