Sashe 20
Ana Zaton Wuta A Makera Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read
ANA ZATON WUTA A MAƘERA.....🔥
✒️IBNATU-UMAR✒️
Page 31&32
(Na kula akwai rudarwa,sunan mahaifin Ameerah kuma Abbee kumana Ruhaan ma haka. Na chanza sunan mahaifin Ruhaan zuwa Abbu, sorry for the inconveniences 😐🙏🏽)
Am sorry Baba but i can't do that, wannan ba burina bane ni kadai, burin mahaifinane kuma Ruhaan yasan da haka shima tafaɗa tana jefa mai kallo.
Ummi ce ta daka mata tsawa tace ana magana kina magana waye sa'an ki. Today i will talk and you will listen, tunda nazo masarautar ku baki taɓa barina nayi kwana uku cikin kwanciyar hankali ba, matsalar yau daban ta gobe daban. Ba kya barina da mijina mu samu lokacin juna, bakya bamu privacy? Wai miye matsalarki? Ke ba kishiyata ba amma kin hanani kwanciyar hankali.
IMAANN Ruhaan yafaɗa cikin ɗaga murya. Karki kara koda wasa kada murki ta dinga tashi akan ta Ummi. Dan uwace ita a wajena, kin fi kowa sanin son da take min ne ya jawo haka. Ohh Please tafaɗa sounding pissed 😡 tace na gaji fah! Na gaji bazai yiwu ba ko wace mace na aure da fatan samun kwanciyar hankali a wajen mijinta ni kuma ina fama da akasin haka. Inason yin aiki, na gaya maka, kai ka ajiye ni a nan, kuma kace ka yarda toh miye matsalar ta?
Kuka Ummi ta fashe dashi tace Ruhaan saboda bani na haife ka shiyasa matarka take gayamin magana haka ba komai. Ni ina yin haka ne dan yarku. Kwata-kwata nawa yarinyar take, Ummi kiyi hakuri bazata yi aikin ba. Dan Allah kiyi hakuri yafaɗa hankalinshi duk ya tashi jikinshi har rawa yake yi.
Murmushin takaici Ameerah tayi ta dauki yarta ta fice, Ruhaan na kiranta ko juyowa batayi ba.
Koda ya shigo flat dinsu yana ta kwala mata kira tayi banza dashi, harya shigo dakin ya sameta tana bama yarinyar nono.
Imaan yafaɗa yana zama kusa da ita, kallonshi tayi kawai ta dauke kai. Imaan kinsan ina sonki koh? Yafaɗa yana kallonta. A da kam a yanzu kam bansani ba. Tafaɗa tana hararshi. Imaann bayan tafiyar mahaifiyata nasha wahala sosai, amma Ummi was there for me through every stage of life. Har aikinta ta ajiye dan ta kula dani sosai. Saboda yarki fa tace ki ajiye aiki. Mohammad Ruhaan tafaɗa tana kallon cikin idanunshi. Wallahi duk son danake maka akan maganar nan saidai mu rabu. Saboda kasan ni na tsani harkar karanta. Dan karanta ke sa mutum magana biyu. Yarinyar fah yafaɗa yana kallonta, sai in bar maka abinka da ita nazo. Ganin tana neman haukace mai yasashi yin murmushi yace su waye zasu rabu wai? Nida ke? Yafaɗa yana amsar yarinyar ya sata a gadonta dake gefen gadon. Bansani ba tafaɗa a fusace. Ai kuwa baki isa ba ke aure har aljanna yafaɗa yana riko hannunta. Nidai na gaya maka i won't compromise my dream for anything dan bazai yiwu ubana ya kashe min kudi ba ka ganni da haƙorana talatin da biyu kace kana sona ka aureni kuma ka hanani cikawa mahaifina burinshi ba. Allah yafaɗa yana kallonta, toh bari na tabbatar talatin da biyu ne haƙoran yafaɗa yana haɗe bakinshi da nata.
Haka dai suka bar maganar, Ameerah ta cigaba da zuwa aikinta.
Yau da zazzaɓi Dua ta wuni, Ruhaan yanata kiran numbern Ameerah tana court bata dauka ba.
Asibiti ya wuce da ita, likita ya dubata ya bukaci mahaifiyarta tazo ta bata nono. Kiran wayar ya cigaba da yi amma still bata dauka ba. Ya mata messages kala-kala duk bata dauka ba. Ba'a jima ba Dua tace ga garin kunan. A bangaren Ameerah kuwa gabanta nata tsinkewa tun safe, yau gashi aiki ya mata yawa sosai koh ruwa bata sha ba. Batama son inda ta jefa wayarta ba.
Sai wajen bakwai ta koma gida, Ruhaan ta gani zaune ga gawa a gabanshi, kallo daya ya mata ya dauke kai, hannunta takai zata buɗe ya rike mata hannu yace you have no right to touch my daughter. Kallonshi tayi a firgice tama rasa mai zata ce. Eh ta mutu Dua ta tafi ta barmu! Kinji dadi ai? Sai kije kiyita aiki har karshen rayuwaki!
Dafe bangon dake gefenta tayi tana jin wani irin jiri na ɗebanta.
Tana gani aka fitar da gawar Dua amma Koh ganinta Ruhaan ya hanata.
Juyawa yayi ya kalleta sannan ya maida kallonshi ga waje. Runtse idanunshi yayi yace KHADIJAH, kallonshi tayi kamar wata wawiya dan bata taɓa jin ya kira sunanta haka ba. Na sake ki saki daya, lumshe idanunta tayi hawaye na gangarowa daga idanunta suna yawo akan kumatunta. Wani irin zafi taji zuciyarta na mata, da mai zataji da mutuwar yarta koh kuma da sakin daya mata.
Share hawayenta tayi, ta shiga ciki. Ta haɗa takardunta masu mahimmanci, ta fito. Saboda karfin zuciyarta bazakace ma wani abu makamancin hala ya faru da ita ba idan ka kalli fuskarta.
Fitowa tayi tana karewa dakin kallo a shekara daya da rabi da aurensu. Kukan dake taho mata ta haɗiye tana tafiya a hankali kamar wacce aka zare ma lakar jiki. Karo taci da Abbu (baba Ruhaann) saurin ja baya tayi tace ya hakuri batama kula shi bane. Ameera ina zaki da jaka haka? Duk tunanin shi mutuwar ce ta sata haka, sosai ta bashi tausayi. Zo muje ciki yafaɗa yana kallonta. Abbu Ruhaan ya sake ni tafaɗa tana yin gaba. Kamar saukar aradu haka yaji maganar ta.
Nana Khadijah yafaɗa yana ɗaga murya. Tsayawa tayi ba tare data juyo ba. Zo muje yafaɗa cikin bada umarni. Bata taɓa jin ya mata magana haka, hakan yasa ta gane ranshi ya ɓaci sosai.
Tana ganin girman shi bazata iya jayayya dashi ba, hakan yasa ta bishi kamar yadda ya buƙata.
Mohammad yafaɗa cikin ɗaga murya yana shiga cikin sashen. Kallonshi Ruhaan daya kwanta a parlourn kamar mara lakar jiki yayi yace Abbu gani.
Ashe kai bakada hankali ban sani ba? Macen data rasa yarta zaka saka a ranar saboda rashin imani! Kallon Ameerah dako kallon inda yake batayi ba yayi. Sannan ya kalli Abbu yace am sorry amma zamana da Ameerah ya ƙare.
Haka kace Abbu ya faɗa cikin ɓaci rai, sunkuyar da kanshi Ruhaan yayi yace i have my reasons. Good badai nine waliyin taba? Kallon Abbu yayi da mamaki. Ya sani tabbas Abbu ne ya bashi auren Ameerah Baba ya amsarmai. Kasancewar Abbu da Abbi abokan juna sosai hakan yasa Abbii karrama Abbu ta hanyar bashi matsayin waliyin Ameerah.
Eh Abbu amma mai ya kawo maganar nan. Murmushi Abbu yayi yace wallahi idan dai nine waliyin Ameerah nasan data fita takaba zata samu miji. Kuma kaji na rantse maka muddin tana sonshi sai na aura mata shi.
Zan gwada maka nine na haifeka Ruhaan, da kafarka zakazo neman aurenta idan zakayi kukan jinin bazan baka ba. Ni ba mutumin bazan bane kuma kai bazaka maida ni mutunim banza ba.
Shashasha kawai Abbu yafaɗa yana juyawa, kallon Ameerah yayi yace wuce muje,binshi tayi har sashen shi.
Kiran mai kula da sashen shi yayi wata tsohuwa haka ta manyanta yace ta kula da Ameerah zuwa washegari.
Koda da safe da Abbu ya tashi baiga Ameerah, yasan tabbas ta riga da ta wuce. Kunyar kanshi yaji yafara tunanin ta inda zai samu Abbee ya mai bayani.
Koda Ameerah ta sauka a Nigeria she is broken and shattered. Abinda bata sani ba shine zata je ta tadda wani abin da zai girgizata.
Taxi ta tara ta wuce gida, Mukhtar dake jiran Abbe ya fito ne yaga saukarta daya Taxi din kamar bata cikin hayyacinta. Wajen mai Taxi din yaje dake kiran Ameerah ta amshi kayanta amma ina ta wuce ciki, burinta kawai tasa Abbe a idonta.
Shiya biya mai Taxi din ya amshi jakar Ameerah ya shiga gidan da ita.
Idonta ne ya sauka akan Hajiya Hamdiyya dake zaune cikin shiga ta alfarma tare da Abbe dake zaune a Dinning tana serving dinshi.
Spoon din hannunshi ne ya faɗi cikin sauri ya nufi Ameerah data shigo. Khadijahhh?? Yafaɗa cikin tashin hankali, mai ya same ki? Rungumeshi tayi ta fashe da kuka, shafa bayanta ya dinga yi. Ya riko hannunta ya zaunar da ita. Ruwa sanyi Hajiya Hamdiyya ta kawo a glass cup. Amsa Abbi yayi ya bama Ameerah da kanshi. Share hawayenta tayi tace Abbeee, kallonta yayi yace Ameerah ina jinki cikin sanyin murya. ABBEEE Ruhaan ya sake ni. Lumshe idanu Abbe yayi sannan ya kuma bude su ya kalleta, bakinsa yayi masa wani irin nauyi. Ya rasa kalaman dazai furta mata. Abbee Du'a tafaɗa tana idanunta nan cika da hawaye. She left us, she is gone. Ruhaan is blaming me for her death.... Abbee taya uwa zata zama silar mutuwar yarta da gangan Abbee.
Rungumeta Abbee yayi yana jin zafin halin da Ameerah take ciki.
Tashi tayi ta share hawayenta tace Ruhaan baiyi deserving hawaye naba. Zan rufe babin shi a rayuwata Abbee har abada babu ni babu Ruhaan tafaɗa cikin kunar rai.
It's fine, Ameerah saki bashine karshen rayuwarki ba. Amma dole zanyi magana da Ruhaan din. Abbe idan dai kansona kana kaunata karka kira Ruhaan balle wani nashi. Tana gama faɗin haka ta wuce sama. Wayarshi dake kara ya kalla, ganin Abbu ne yasa ya saisaita nustuwar si ya dauki kiran. Ganin yadda Abbu keta kame-kame yasa Abbee cemai karka damu Muhammad Aure rai ne dashi idan lokacin yinsa yayi dole ayi, haka zalika idan lokacin mutarsa yayi dole ya mutu. Allah ya zaɓa masu abinda yafi alheri. Yana gama fadin haka ya kashe kiran.
Kisa a hada abu mara nauyi, yafaɗa yana kallon Hajiya Hamdiyya, toh tafaɗa cikin nuna damuwa da lamarin.
Dakin Ameerah ya nufa, knocking yayi ya tsaya jiran amsarta. Tasowa tayi ta buɗe mai, ta bashi hanya ya shigo.
Kafin ya kaiga cewa komai sai ga Hajiya Hamdiyya ta shigo dakin dauke da tray a hannunta. Ajiyewa tayi ta koma gefe ta zauna. Kallo rashin sani Ameerah ke mata. Murmushi Abbee yayi yace Ameerah wannan Antyn kice she is my wife. Lumshe idanunta tayi tana jin yadda furucinsa na karshe ke yawo a cikin ƙwaƙwalwarta. Abbee zai yi aure bai sanar mata ba??? Abbe dako contract baya signing sai yaji ra'ayinta.... Shine ya yanke wannan hukuncin ba tare daya sanar mata ba. Tafi kowa jin dadin auren da Abbee yayi, dan batason zaman shi, shi kadai. Amma mai yasa bai gaya mata. Kallonsa tayi da disappointment a cikin idanunta wanda shima zai yaji kunyar kanshi.... Allah ya sanya alheri tafaɗa tana mikewa daga gabanshi ta koma bakin window dakinta dake kallon wajen gidan. Khadijahhh yafaɗa yana kallonta.... Juyowa tayi tana share hawayen dake sintiri akan fuskarta tace Abbe let's talk later bacci nake ji tafaɗa tana kallonshi. Fita yayi cikin sanyin jiki, dama Hajiya Hamdiyya Abbee na fara magana ta fice.