← Book details Ana Zaton Wuta A Makera Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 50

Sashe 24

Ana Zaton Wuta A Makera Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

Toh mu haɗu a next page 📄📄

ANA ZATON WUTA A MAƘERA....🔥

✒️IBNATU-UMAR✒️
Page 37&38
Wanka Ameerah tayi ta zauna bakin gado, tana saƙa abubuwa da dama. Motsin taɓa handle din yasata juyawa ta kalli mai shigowa, Zayn da Zaid ta gani rike da hannun juna. Murmushi ta sakar masu, ta buɗe masu hannuwanta. Rungumesu tayi tana jin wani irin sanyi a cikin ranta. Mammi are you okay? Cewar Zayn yana leƙa fuskarta, am fine tafaɗa tana share hawayenta cikin dabara. Liess Mammi kince karya babu kyau kuma kinayi. Cewar Zaid yana kallonta. By the way, who is that strange man that brought us here? I don't know him tafaɗa tana kallon Zayn daya tafi duniyar tunani. Mammi wai mai yake faruwa? Kai stop asking it's adults business cewar Zaid yana kallon Zayn.
Dr ce ta shigo rike da tray din abinci, kallon su Zayn tayi tace muje ku kwanta. Tafaɗa tana riƙo hannuwansu, who are you? Cewar Zayn yana kallonta, you look like our grandfather. Murmushi tayi tace ofcourse am his daughter afterall. Kaii karki kuma cewa hala cewar Zaid yana kallonta. Why? Tafaɗa tana kallonshi. Saboda Mammi is his only daughter, okay yafaɗa yana rike kugunsa. Murmushi tayi tace ni yayar maman kuce. No wayyy cewar Zayn yana kallonta da mugun mamaki. Mammi ba sister dinki ta rasu ba? Waye ita? She is my sister cewar Ameerah....no elder sister cewar Humaira tana masu murmushi.
You're our Aunt? Su haɗa baki wajen faɗa, yess tafaɗa tana jan kumatunsu. And that noisy girl is our cousin cewar Zaid kamar zai yi kuka. Hakane cewar Humaira. Nooo, Mammi Zayn shi kadai ciwon kai yake samun, gashi wancen yarinyar Ammi take kowa ta cika surutu itama. I can't stand the two them. Mammi do something yafaɗa kamar zaiyi kukaa.
Murmushi tayi tace it's fine you can survive it, tafaɗa tana jan kumantunsa. Juyawa sukayi zasu fita ya kalli Humaira yace Aunt, murmushi tayi tace mai kake so. Tare da yarinyar cen zamu kwana? Gyaɗa mai kai tayi. Kallon Ameerah yayi yace kin gani koh Mammi. You can do it, Fighting 👍🏽 tafaɗa tana mai murmushi. Fighting shima yafaɗa yana mata murmushi. Hararar Zayn dake mai dariya yayi.
Kallon Ammi dake danna waya Dr tayi tace Ammi zoki kwanta. Ajiye wayar tayi tana turo baki ta kwanta, Zayn ma ya kwanta sai Zaid. Addu'a tasa sukayi ta kashe wutar ta kullo kofar ta fice.
Kallon Zaid dake gefen damansa Zayn yayi, sanna ya juya ya kalli Ammi dake gefen hagunsa. Let's play cewar Zayn yana murmushi. Eh cewar Ammi tana kallonshi. Wasan su suka fara su biyu. Tsaki Zaid yaja yace quiet you guys are noisy I can't think straight. Tunanin mai kake toh cewar Zayn yana kallon shi. Ban sani ba, i feel like something is wrong amma Mammi taƙi faɗa mana. Kee yafaɗa yana kallon Ammi, kinsan mai yake faruwa? Zaro ido tace bansan raini, address me by my name. Waye kee? Bakasan sunana bane? Juyowa Zaid yayi a fusace, Zayn ne ya shiga tsakanin su yace don't fight please. Sunanta Ammii kace mata Ammii yafaɗa yana kallon dan uwansa. Shafa kanshi yace well saidai Little Ammi dan na girmeta idan kuma bazata amsa ba shikenan. Kaii cewar Ammi tana matsowa kusa dashi. Zo kiji cewar Zayn yana ma Ammii raɗa a kunne, kinga Ammi sunan wata Grandmother dinmu, toh shiyasa yace maki Little Ammi. Ohh he should have explained tafaɗa tana haɗe rai. And i think am older than you guys tafaɗa tana nunasu. Murmushi Zayn yayi yana kallon Ammii, hannunshi yasa ya taɓa dimples dinta dake lotsawa koh batayi magana ba yace you're cute 🥰. I know tafaɗa tana komawa gadon ta kwanta.
Abinci Humaira tasa Ameerah a gaba taci. Kallonta tayi tace Sister, are you really my sister?🥹 Murmushi Humaira tayi tana jan kumatunta tace yes i am. Amma taya hakan ta faru? How did you survive?
Gyara zama tayi tana share ma Ameerah hawayenta tace.....
A ranar da mukayi hatsari, Mukhtar ne ya ciroki, ni kuma Ummiii ce ta turani waje ta ɗaya glass din ta faɗa cikin wani irin yanayi. I lost memory, kwata-kwata ban iya tuna komai a kaina ba. Nasan dai nayi rayuwa a gidan marayu na tsayin lokacin kafin Baffa (Alhaji Munir Jikamshi) yazo yayi adopting dina. Na taso cikin gata da kuma kulawa nida Mukkaram shi ne kaɗai dan Baffa. Da muka gama secondary Baffa ya kaimu Harvard University dan yin karatun mu na gaba da secondary. Na karanci medicine inda Mukkaram ya karanci criminology. Kamar wasa da ƙadan da ƙadan na dinga recollecting memory na, har na tuna komai da komai. Ranar da mukayi graduation memory ya zama intact na tuna komai ke, Ummi da Abbee. A lokacin Baffa yazo graduation dinmu na gayamai. Ruko hannuna yayi muka fita a cikin jama'a. Ruwa ya bani na sha ya kalleni yace Humaira, ni nasan koh ke wacece, saboda a kallo ɗaya duk wanda yasan Abdulkarim yasan ke jinin shi ce. Abdulkarim ne da kanshi yasa na nemoki. Da kuma na ganki, shi yace na rike ki. Kuma duk halin da kike ciki yana sane. Dadalinsa na yin haka ban sani ba nima Humaira. Amma koma miye Abdulkarim yayi, yana yin sane saboda ya'yansa. I insisted ina son ganin Abbee and he came to see me. Wanne ne gani na karshe da namai tafaɗaa tana hawaye.
Koda Abbe yazo nayi kuka sosai, i asked him why? Mai yasa ya rabu dani.
Kinsan mai yace? Cewar Humaira tana murmushi mai ciwo. Rayuwarki na hatsari dake da yar uwarki. Na kusa rasa ku gabaki ɗaya, shiyasa na yanke shawarar rabaku Humaira. Nasan ke zaki iya surviving amma Ameerah bazata iya ba, babu Umminki kuma babu ni. When the time comes, zaku haɗu zaki ganta.
Akwai abubuwan danake son yi tukunna, kiyi hakuri Humaira. Trust me and wait.
Tun daga wannan ranar, duk halin da kike ciki ina sani. Na kasa hakuri kamar yadda Abbe yace sai da nayi hiring wani yana bibiyar ki. Komai ma rayuwarki na sani Ameerah. Na kasa nustuwa sa barinki musamman idan na tuna alƙawarin dana ma Ummii. Kwatsan naji labarin mutuwar Abbee. Ameeerah ni kaina bansan mai yake faruwa a rayuwar mu ba. Amma one thing is for sure, Abbe ba mutuwa yayi ba kashe shi akayi.
I know cewar Ameerah a hankali kamar ba ita ba. Mahmud ne ya kashe shi tafaɗaa tana kallon Humaira.
Mahmudd?? Why? Mai yasa Mahmud zai kashe Abbee? Miye motive dinshi dazai kashe Abbee?
Nima ban sani ba, i don't know what is going on cewar Ameerah tana hargitsa gashin kanta. Ji take, kamar tayi hauka. Naji na gani Mahmud yace shine ya kashe Abbee🥹.
Just sleep, dare yayi gobe zamuyi magana, kwanciya tayi Humaira ta gyara mata bargon,sannan ta kwanta a gefen Ameerah tana tunanin abubuwa da dama.
Da safe kuwa bayan sun karya, kallon Ameerah HUMAIRA tayi tace Ameerah yanzu ba zaki nunawa Mahmud cewa kinji shiya kashe Abbee ba. Kallonta Ameerah tayi cikin tsantsan bacin rai tace bangane mai kike nufi ba, akan mai? Ƙara zan shigar ma kotu.
Murmushi Humaira tayi tace everything has changed expect your bad temper tafaɗaa tana riko hannunta. Fisge hannunta Ameera tayi tace karki ƙara taɓani. Okay fine, if you're a lawyer think like one, tafaɗaa tana kallon Ameerah. Mai kike nufi cewar Ameerah tana kallon Humaira. Abinda nake nufi shine bamuda hujja yanzu haka, so mubi komai a sannu idan kin kula Mahmud baida Motive din kashe Abbee akwai yiwuwar wani ne yasashi. Yanzu kawai nuna mai zakiyi kinsan komai akan affair dinshi. Shima da baki nuna ma Nisah kin gansu ba da cewa zanyi ki kyale su, but kinyi gaggawar nuna mata kinsan mai yake faruwa.
Whatever naji zamuyi yadda kikace amma Wallahi sai ya sakeni, daga yau bazan kuma kwana da aurenshi a kaina ba.... ringing din wayarta ne ya kaste masu zancen...kallon jakar Ameerah Humaira tayi tace ba wayarki bace ke ƙara? Ta wace tafaɗaa tana ciro wayar daga cikin jakar, Mukhtar ne tafaɗa tana kallon Humaira dauka mana cewar Humaira kafin Ameerah takai ga dauka ya katse ganin miss calls din Mahmud rututu yasa taja tsaki. Kiranshi tayi maimakon ta kira Mukhtar din daya kirata.
Bab..tsaya don't waste my time and your energy. Misunderstanding ne wallahi ki saurareni, Nisah babu wani abinda.....yimin shiru bakin munafuki, zan tura maka da address kazo ka kawo min takarda ta. Nisah of all people ka cuceni ka cutar dani Mahmud, Azzalumi....fisge wayar Humaira tayi ta kashe ganin numfashin Ameerah yafara daukewa. Keee tafaɗaa tana shafa bayanta a hankali, amma ina harta fara fita hayyacinta. Inhaler ta dauko tana sa bakin Ameerah tana ta kokarin ta shaka amma ina, kawai faduwa tayi a sume a wajen.
Mukkarammm cewar Humaira cikin ɗaga murya, cikin sauri Mukkaram dake tare dasu Zayn a parlour ya shigo, help..help... cewar Humaira jikinta yana rawa. Daukan Ameera yayi ya sata a back seat, amsar mukullin daga hannun HUMAIRA dake koƙarin kunna mota yayi amma ta kasa. Riko hannunta yayi ya sata a bayan itama yama motar key, kallon mai gadin yayi yace karka buɗe ma kowa gate dinnan idan bamu bane muka dawo. Toh yallabai yafaɗa yana kallon Mukkaram cikin al'ajabi...da wani irin gudu Mukkaram ya fice a gidan.
Parking Mukkaram yayi a asibiti ya dauki Ameerah kamar gawa suka shiga da ita ciki, likitaa, likitaaa. Kallon abokinsa Dr Usama yayi yace ankawo patient condition dinta is very critical Aliyu koh zaka duba mana ita.
Koh kallon inda Usama yake wanda aka kira da Aliyu bai ba. Har Usama ya cire rai ya juya zai fita yaji muryar Aliyu yace muje a daƙile yana kallon Usama. Girgiza kai Usama yayi yana mamakin hali irin na Aliyu.
Kallon Ameerah dake kwance akan gadon yayi sannan ya maida kallonshi gun Humaira dake rike da hannun Ameerah tana kuka. Gajeran tsaki yaja sannan ya matsa kusa da Ameerah yana sauraren Mukkaram dake faɗamai abinda ke faruwa. Tanada Asthma ne? Eh cewar Humaira tana kallonshi, banda wannan fah patient din VSD ce cewar Humaira muryarta na rawa.
Bayanin condition din Ameerah take mai harya gama dubata, ya saka mata oxygen. Kallon Humaira yayi yace are you doctor? Jin yadda take tamai bayani, yes tafaɗaa tana kallon shi. If you're a doctor then act like one. Kamar baki taɓa ganin patient bah... yafaɗa yana jan tsaki, shan gabanshi tayi tace you are not in a positive to judge dan bakasan ita din wacece a gareni ba. Koh tari hankali na tashi yake balle suma. If you are a human being act like one atleast have something like humanity tana gama faɗan haka taja tsaki ta fice.
Baki saƙe ya bita da kallo, Murmushi Usama yayi kawai batare daya ce komai ba, a ranshi kuwa dariya yayi yace maganin ka.
Chapter 24 · 0% Book details