← Book details Ana Zaton Wuta A Makera Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 50

Sashe 26

Ana Zaton Wuta A Makera Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ANA ZATON WUTA.....🔥
✒️IBNATU-UMAR ✒️

Page 41&42

Kallon Mukarram tayi tace agaba na wannan brainless guy din ke faɗa maganganun banza akan Amii, wai ubanwa zai yi threatening? Mukarram tafaɗa tana kallon Mukkaram da yayi shiru yana mamakin anya Humaira daya sani ce kuwa, bai taɓa ganin ɓacin rai koh fushi a tattare da ita ba sai yau, maganar tace ta dawo dashi hayyacinsa. Two days ina son sanin komai game da rayuwar wannan mara kunyar tafaɗa tana kwafa. Murmushi yayi yace yes Ma'am, harararshi tayi tace what is funny? Babu yafaɗa yana yin hanyar fita, ka dawo muci abinci, ina zaka? Sakon Daddy zan amso, munyi waya dashi ɗazu yace jibi zasu dawo, murmushi jin dadi Humaira tayi tace the house is so empty tunda Mommy ta rasu Daddy yaƙi zama gidannan. Wani irin murmushi mai ciwo Mukarram yayi yace Allah yaji kanta sister, Ameen cewar Humaira tana wucewa ciki.
Kiran su Zayn tayi tasaka akayi serving dinsu, ta wuce ɗakinta dan tashin Ameerah tayi sallah.
Amii tafaɗa tana tapping hannun Amirah, Uhmm cewar Ameerah tana ƙara juyawa, ki tashi kiyi sallah 5 tayi fah. Buɗe ido Amira tayi tana dafe kanta dake dan mata ciwo tace sister yaushe lokaci ya wuce haka, ki tashi kiyi sallah muci abinci.
Tashi Amira tayi tana daukan Iphone 15 pro max dinta dake gefen pillow data ke kwance. Godd tafaɗa ganin miss calls da yawa a wayarta, an kira taya ban tashi ba tafaɗa tana saukowa daga gadon. Ni nasa wayar a silent, kiyi sallah ko fito parlour muci abinci. Alwala tayi ta gabatar da sallar La'asar, sannan ta fito parlour koh data fito Zayn da Zaid sun gama cin abinci amma har yanzu Little Ammi bata gama ba.
Thanks tafaɗaa tana amsar plate din abincin da Humaira ta miƙa mata bayan ta zauna a dinning table. Mammii! cewar Little Ammi tana murmushi. Da mugun mamaki Amira ta kalli Lil Ammi kafin tayi magana Ammi tayi saurin cewa Naji haka Zayn yake ce maki, i wanted to call you that, can i? Tafaɗa tana marairaice fuska of course darling tafaɗa tana shafa kanta. Zama HUMAIRA tayi gefen Amira tana harararta Lil Ammi tace ke kullum sai ki kusa awa ɗaya kina cin abinci, har sai ya huce. Mummy am i slow eater and it's healthier. Toh Dr.Khadija cewar Humaira tana murmushi. Dariya jin dadi Ammi tayi tace In Sha Allah Mummy i want to like you. Fork Humaira ta miƙa ma Ammi ita kuma tayi using chopsticks 🥢, suka fara cin abinci. Nama Ammi ta dauka daga plate dinta using chopsticks din da take cin abincin dashi, tasa a gaban Amira tace Mummy eat and be very strong karki ƙara zuwa asibiti.Thanks cewar Amira tana murmushi tana mamakin manyance irin na Ammi.
Mammii cewar Zaid da sai lokacin ya ganta, da gudu yaje ya tsaya a gabanta, ajiye fork dinta tayi tana kallon shi, murmushi yayi yadda kasan Ruhaan ne ke tsaye gabanta, huci ta furzar tana tunawa da maganganun da tayi da Ruhan. Tasan Ruhaan bazai taɓa kyale maganar su Zaid ba. Kallon Zayn da yazo shima tayi tace boys how are you? Mammi i missed you karki kuma tafiya asibiti cewar Zayn yana hawaye. Idiot are you a man? Cewar Zaid yana tsaki, Addu'a zamu mata Allah ya bata lafiya, stop crying cewar Zaid yana kwalla. Murmushi Amira tayi, dan tasan shima Zaid din kiris yake jira yayi kuka. Ajiye fork din tayi ta rungumesu tace i promise to be healthy, kuyi hakuri tafaɗa tana murmushi. Allah yabaki lafiya cewar Zayn a sanyaye. Kubarta taci abinci kun dameta cewar Ammi tana ɓata fuska.
Dariya Zayn yayi yace kin kasa gama cin abinci tun ɗazu, murmushi Zaid yayi yace Zayn ka tuna idan muka kaiwa Uncle Moh breakfast shima haka yakeyi, noo shi Uncle Moh abinci ne bayasan ci bakaga yana ɓata fuska ba idan yana cin abinci.Mammii ina Uncle Moh...kwarewa Amira dake shan ruwa tayi, saurin mika dangwalar gishiri Humaira tayi ta lasa mata a baki. Sorry Mammi ki gama cin abinci we have alott to tell you cewar Zaid yana wucewa parlour, sorry 😐 shima Zayn yafaɗa yana bin bayan dan uwanshi.
Kallon Amira data cigaba da cin abincin Humaira tayi tana kurbar smoothie tace waye Uncle Moh? Kallon Humaira tayi da fararen idanunta tace Ruhaan. Zaro ido Humaira tayi tace taya suka sanshi? Thought you wanted to keep their existence a secret? Yeah zan baki labarin eat first tafaɗa tana kallon Humaira. Ajiye chopsticks din tayi tace ni na koshi tafaɗa tana goge bakinta. Bangane kin koshi ba mai kikaci sister? Har yanzu kina nan da rashin son cin abinci, cewar Ameerah tana hararar Humaira.
Kinsan ban iya cin abinci da yawa, idan kin gama ki sameni sama tafaɗa tana wucewa.
A bangaren Ruhaan kuwa tun daga randa Amira tamai kacha-kacha ya kwanta rashin lafiya, Ummi ta rasa gane kanshi. Shi kanshi bai san mai yake damun shiba.
Yau da safe ya shirya ya tafi gidan, cikin shigar aikinsa daya saba zuwa. Mahmud dake shirin shiga mota ne ya ganshi, kai yafaɗa cikin ɗaga murya. Waigawa Ruhaan yayi yaga koh da wani Mahmud ke magana ba shi ba. Dakai nake cewar Mahmud yana ƙarasowa kusa da Ruhaan. Kallon shi Ruhaan yayi yana jiran yaji mai zaice. Matar gidan bata gidanan nasan zata kiraka ta gayamaka idan zaka aiki, so karka ƙara zuwa gidan nan. Okay Sir, amma lafiya? Mun rabu cewar Mahmud yana, juyawa da niyyar tafiya. Ka sake ta? Cewar Ruhaan yana zaro ido. Eh na sake ta, yafaɗa yana shigewa motarshi yabar wajen. Ruhaan yafi minti biyu yana comprehending abinda Mahmud yace mai, Ohhh ya saketa yafaɗa yana daka tsalle. Ya sake ta kuma faɗa yana fashewa da dariya. Alhamdulillah yafaɗa yana kallon gabas yayi sujudda.
Wayarshi ya ciro yanata kiran Amiraa amma bata dauka ba, tsaki yaja ya maida wayar aljihunsa, ya fice a gidan.
Kallon Amira Humaira tayi bayan tagama bata labarin yadda su Zayn suka san Ruhaan tace tirkashi. Amma Amii mai yasa baki saurare shi ba? Wani mugun kallo tama Humaira tace don't even start that. Murmushi Humaira tayi tace ba haka nake nufi ba, I promise. Yanada kyau ka saurare mutum, duk abinda ya maka kuwa sai ki yanke hukunci daga baya. Kinsan yarannan ya'yan shine kuma yanda hakki akansu. Idan fah yayi deciding amsar su? Kallon Humaira tayi a firgice kwalla na taruwa a idanunta, i can't leave without them, sister don't say that again, karki kuma cewar Amira a tsawa tana toshe kunnuwanta. Rungumeta Humaira tayi tace it's fine, tana shafa bayanta, a hankali Amira ke sauke numfashi.
Gashi wannan Mahmud yazo ɗazu cewar Humaira tana bata paper da Mahmud ya kawo. Buɗe wa tayi ta karanta, ubanmai yaci sauran biyun da zai man saki ɗaya? Tafaɗa a hasale, it's fine tunda yayi yanda kikeso din ba tare daya ɓata maki lokaci ba.
Hira suka cigaba da yi, wayar Amira ce ta fara ringing, oppss 😬 tafaɗa tana dafe goshinta. Mukhtar must be very worried ban gaya mai komai ba, kuma naga miss calls dinshi sunfi goma, tafaɗa tana ɗaukan kiran. Ma'am are you ok? Yafaɗa cikin muryar damuwa. Sorry Mukhtar wallahi naso kiranki, but i was sick.... labarin abinda ya faru ta bashi. Innalillahi yanzu kun rabu? Sosai mutuwar auren nan yamai ciwo dan yana tuna yadda Abbee yayi murna ranar auren. For now ka kula da Company da kuma News Buzz, nan da 3 months zan dawo, amma for now inaso ka kwashe motocina ka kai su Gidan dake Aso rock wanda Abbee ya bani. Amma at the same time yana murnar ganin Humaira da Amira tayi. Sannan valuables dina suna floor a wata black travelling 3 weeks ago na haɗa su, ka kaho min gidan su sister, zan tura maka address dina.
Just 3 months zan koma aiki, tafaɗa tana sauke ajiyar zuciya. Kallon damuwar data bayyana a saman fuskarta Humaira tayi tace do you love working that much? Yes, i love it ❤️ cewar Amira tana murmushi. It gives me peace 🕊️. Allah ya kaimu ki gama Iddan. Muje kitchen....saurin katse ta Amira tayi tace karkice zaki sani girki wallahi tafaɗa tana haɗe rai. Murmushi Humaira tayi yace ce maki akai inason kwana kumburarren ciki, Allah yayi ki kina mace amma bakison girki. Ni tiruri ƙona ni zaiyii tafaɗa tana narke fuska, ni ai da icce akayi ne cewar Humaira tana harararata. Cooking is not my thing tafaɗa tana zama a kitchen island.
Humaira na haɗa kayan girkinta ita kuma tana ta mata hira.
Kallon Humaira dake haɗa ingredient din Naan bread a mixer tayi tace sannu, Yawwa cewar Humaira tana shafe mata flour din hannunta a fuska. Sisterrr tafaɗa tana ɓata rai, murmushi tayi tace miyee. Flour ce ba guba ba, wallahi sai na rama tafaɗa tana dumbuzar flour a hannunta ta nufi Humaira, haka suka dinga zagaye kitchen din suna guje-guje kamar yara.
Zubewa sukayi akam couch sin dake cen gefe a kitchen din suna maida numfashi. Evil Child cewar Amira tana shafe fuskar Humaira da flour dake hannunta.
Ba kya yafiya cewar Humaira tana goge fuskarta.
Tashi tayi tana karkaɗe hannunta tace banyi din, you ruined my pretty face. Tafaɗa tana ficewa.
Tashi Humaira tayi ta kashe mixer dan dough din yayi. Tafara haɗa gas meat sauce. Shigowa Amira tayi bayan ta wanke fuskarta rike da handkerchief. Gogewa Humaira dake aikin juya gas meat fuska tayi tace you're looking like a ghost. Thanks to you tafaɗa tana murmushi. Woww ji kamshin tsammin tafaɗa tana miƙa ma Humaira hannunta, bige mata hannu tayi tace ba kyau roƙo😂💔 kaiii Sister tafaɗa tana ɓata rai. Okay haa tafaɗa tana nufar bakinta da piece of gas meat bayan ta gama hura shi. Uhmmm deliciousss sister mijinki yana jin dadi... Mijiii?? Cewr Humaira tana zaro ido. Yes now baban Ammi.
Ke am not married tafaɗa tana tuntsire da dariya. Ammii?? Tafaɗa cikin mamaki.
Zan baki labari, bari muyi sallah kuyi dinner first tafaɗa tana lakartar hancin Amira data kusa suma da mamaki.

Toh mu haɗu a next page 📄📄📄
ANA ZATON WUTA A MAƘERA...❤️‍🔥

IBNATU-UMAR 🖋️♥️
Chapter 26 · 0% Book details