← Book details Ana Zaton Wuta A Makera Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 50

Sashe 40

Ana Zaton Wuta A Makera Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

ANA ZATON WUTA A MAƘERA...🔥
✒️IBNATU-UMAR ✒️

Page 61&62

Na daya abinda kuke tunani bai zama dole shine gaskiya ba.
Na biyu karku yarda da kowa, ku hudun nan kuzama inuwar junaku, kuma ku zama masu rike sirri.
Abu na ƙarshe ku kiyaye! Humaira nan Nigeria ce, wannan bingidar da kika zo da ita daga Italy.....sai kuma yayi shiru. Ki kiyaye dai!
In Sha Allah duk suka amsa mai. Sannan inason sanar daku cewa karkuyi tunanin inada wata manufa na hada ku aure. Saboda ina guje maku hallaka ne, kuna tare kusan koda da yaushe duk da kasancewar ku ba muharraman juna ba.
Toh Abba mun gode, amma zamu koma saboda aiki. Allah ya kiyaye maku hanya, amma inason a shirya maku walima. Idan kun yanke lokacin sai ku sanar dani. Mun gode Abba cewar Amira tana murmushi.
Sallama suka mai bayan sunmai godiya. Mohammad yafaɗa yana kallon Ruhaan. Fita sukayi suka basu waje.
Mohammad cewar Mai Martaba yana kallon Ruhaan. Ya Khadija take? Ɗagowa yayi da niyyar gayamai baƙar magana, amma suna haɗa ido yaji ya kasa, wani irin kwarjini yamai. Ganin yamai shiru yasa yace Mohammad fushin ka is justified, amma zanzo wajen Khadija muyi magana.
Allah ya muku albarka, baki ɗaya.
Juyawa yayi ya fice suka wuce.
Koda suka sauka a Airport Amira batace mai ƙala ba, shima baice mata ƙala ba.
Motocin da suka zo daukan su, suka shiga. Ɗaya shida Amira da Ammi. Dayar kuma Humaira, Yarima da Zayn da Zaid.
Dafe kafaɗunta dake ciwo tayi, ta jingina jikin kujerar. Hannu yasaka ya fara matsa mata a hankali, bige mai hannu tayi tace don't touch again. Hannushi ya kuma mayarwa ta bige mai hannu. Janyota yayi jikinsa ya cigaba da matsa mata kafaɗar. Saitin kunnenta yace fushin na miye Wifey. Harararshi tayi idanunta da kwalla tace ba karyani kaso yiba? Am sorry 😐 yafaɗa yana jin ba dadi a ranshi. Kin hakura yafaɗa yana rungumeta. Uncle Moh! Cewar Ammi da suka matse a tsakiyarsu. Sun ma mance da ita.
Sorry suka haɗa baki wajen faɗa suna dariya. Stop smiling Uncle Moh! Laifin mai nayi yafaɗa yana jan kumatunta. You hurt Mammi. Am sorry my bad,i didn't mean to do that. Mammi zaka bama hakuri bani ba. Am sorry Mammi yafaɗa yana jan hancin Amira bigemai hannu tayi ta harareshi. Riko hannuwanta yayi ya lumshe idanunsa ya jingina da kujera.
Gida Mukarram yasa aka kawo su. Dinning suka nufa, aka yi serving dinsu.
Tashi Amira tayi daga kujerarta ta koma kusa da Humaira. Dafata tayi tace Sister tunanin mai kike? Eat please tafaɗa tana nufar bakinta da abincin, kallon abincin tayi tace banda appetite, tafaɗa tana niyyar mikewa. Zaunar da ita Amira tayi, tace eat for my sake please. Buɗe baki Humaira tayi Amira ta dinga feeding dinta, kadan taci tace saida safe ku. By now cewar Yarima yana kallon agogon shi dan yanzu ma ake kiran Maghrib. Do you have a problem with that? Tafaɗa tana tsareshi da ido. Girgiza kai yayi yace Allah ya kaimu. Good Night Mummy su Ammi suka haɗa baki wajen faɗa.
Good Night kids tafaɗa tana musu murmushi.
Sallama suka ma Amira suka wuce. Mukarram ya rakasu.
Sister Amira ta faɗa tana faɗawa kan Humaira dake kwance. Amii tafaɗa tana tureta. Bacci fa nake, tafaɗa tana mikewa zaune. Sister muga gun din! Wace Gun? Cewar Humaira tana mikewa zaune, Italy? Yeah sister mu gani. Ami idan kin gani mai zakiyi da ita tafaɗa tana janyo bedside drawer dinta, ta dauko bingidar. Woww cewar Amira tana kai hannu zata dauka, no you can't touch it cewar Humaira tana matsar da bingidar. Why? Muna submitting dinta wajen aiki, every month, kuma ganin fingerprint dinki zai iya zama matsala. Tafaɗa tana maida bingidar inda ta dauko ta.
Sister what more secrets do you have? Cewar Amira tana kwanciya akan cinyarta. Babu tafaɗa tana jan hancinta. Wai ku miye damuwarku da hanci na? Kuu?? Cewar Humaira tana kallon ta. Keda Ruhaan mana. Ohh really cewar Humaira tana yin wani irin munafukin murmushi. Stopeettt tafaɗa tana boye fuskarta cikin cinyarta. Tashi, tashi cewar Humaira tana mata chakulkuli. Ki bari, ki bari banso cewar Amira kamar zata shiɗe.
Okay fine na bari, seems you're so excited. About whatt? Cewar Amira tana jingina da jikin Humaira. Ruhaan and You.... Sisterr! Murmushi Humaira tayi tace it's fine you can tell me. Sister stop mana. Shikenan na bari, ku dai bi a hankali i can see the excitement in your eyes daga ke har Ruhaan din. Su Zayn sun kwanta nima bacci nakeji cewar Ameerah tana jan bargo ta rufe fuskarta. Murmushi Humaira tayi tace gyara kwanciyarki toh. Anki din cewar Amira tana rungume Humaira. Murmushi Humaira tayi ta rungumeta suka kwanta.
Da asuba bayan sunyi sallah suka koma bacci dayake ba aiki sai gobe.
Ammi ce ta fara zuwa da kayan bacci, ta shige tsakiyar su ta kwanta. Sai Zayn sa Zaid suma kwanta. Sai wajen goma Humaira ta buɗe idanuta, kallon Amira dake cen karshen gado tayi, tayi murmushi tace yar ganin dama. Hannu taji akan cikinta, buɗe duvet din tayi da mamaki take kallon Ammi dake kwance kusa da ita, ɗaga duvet din tayi a hankali taga su Zayn da Zaid, murmushi tayi ta gyara amsu bargon ta shiga bayi. Brush tayi ta saka band akanta ta sauka ƙasa.
Mukarram tagani a kitchen yana girki. Buɗe warmers tayi tace ahh yau Sa'ar ta muce. Pancake yayi masu sai stir fry potatoes, sai tea daya dafa masu.
Tayashi tayi suka jera a dinning table, ta koma ta tashi su Amira.
Amii, kids wake up tafaɗa tana yaye duvet din da suka rufa.
Mummyy cewar Ammi tana gyara kwanciya kamar zata shige cikin gadon. Good Morning Mommy cewar Zayn yana pecking kumatun Humaira. Morning Dear, oya kuje ayi brush. Sauka yayi ya fice, shima Zaid ya tashi ya mata haka, ya fice.
Amii keda yarki zan sheƙa maku ruwa tafaɗa tana kallon Amira da Ammi da suka rungume juna suka cigaba da bacci.
Ku tashi tafaɗa tana janyo Ammi daga kan gado. Mummy pleaseee, daukan tayi direta a bayi ta wanke mata fuska, tace oya je kiyi brush.
Amii tafaɗa tana jan Amira. Sister stopeettt, baccii nakeji. Bacci awa nawa zakiyi, tashi kici abinci. Tashi Amira tayi tana zumbura baki ta shige toilet.
Breakfast sukayi, kowa ya nufi daki dan yin wanka.
Kiran RUHAAN ne ya shigo wayar Amira, kamar bazata dauka sai kuma ta dauka. Good Morning Wife yafaɗa yana murmushi. Ni zaka ma dadin baki? Murmushi yayi yace na isa inma Barrister dadin baki? Yanzu dai kuzo Studio dina keda Sister ASAP. Tun takwas muke jiran ku nida Yarima. Okay gamu nan tafada tana kashe wayar.
Bayan 30mins suka isa Studio din Ruhaan, gaisawa sukayi. Yarima ya fara masu bayanin abinda yasa ya kirasu. Yakamata mu buɗe safe dinnan muga abinda yake ciki koh? Hakane duk suka faɗa suna kallonshi. Buɗewa yayi ya ciro wani file a ciki. Zaro ido yayi ganin abinda ke cikin file din, this is huge yafaɗa cikin mamaki. Saurin tashi Humaira tayi ta dauki file din tace Narcotics Case! Bincika file din suka fara yi.
So wannan file dinne silar mutuwar Abbi cewar Humaira kwalla na taruwa a idaunta. Dafata Amira tayi cikin wani irin yanayi, juyawa tayi suka rungume juna suka fashe da kuka. Guyss stop crying cewar Ruhaan yana dafa Amira, juyowa tayi ta rungumeshi tana yin wani sabon kukan, shafa bayanta yayi yace it's fine! Abbi yana wuri mai kyau In Sha Allah. Allah yaji kanshi cewar Yarima yana mikama Humaira handkerchief. Amsa tayi tace Ameen,Thanks.
I will keep the file cewar Humaira tana saurin daukan file din. Dan tasan haka Amira zatace, kuma zaman file din a hannunta na iya sa rayuwarta a matsala.
Am against it! Cewar Yarima yana kallonta. Kallonshi tayi tace wannan bai shafeka ba! It's about our parents, so it will be better of you stay out of...sister cewar Amira tana dafa Humaira ganin ta dau zafi da yawa. Please Amii tafaɗa tana ɗaga ma Ameerah hannu. But you can't be so mean to him, taimakon mufa yakeyi cewar Amira. Did we asked him to help us? Murmushin gefen baki Yarima yayi yace your safety is my responsibility! Ban amince ba. Stop me then tafaɗa tana daukan jakarta, riko hannunta yayi yace i said no! Kinfi kowa sanin hatsarin irin wannan case din, balle ace kuma mutum yana rike da hujjoji masu karfi kamar wannan. Let go tafaɗa tana kallonshi da rinnannun idanunta. I refuse yafaɗa yana rike hannunta da kyau. Murmushi tayi tace for the last time, kasake ni tafaɗa cikin ɓacin rai. Brot...stay out of this Ruhaann cewar Yarima yana kallon Ruhaan.
Fisge hannunta tayi, ta murde hannun da Yarima ya riko mata hannu dashi, ta daki gwiwarshi ya zube a kasa. Auchhh yafaɗa yana dafa hannunta..ki sake ni. Tureshi tayi tace don't mess with me again. Tafaɗa tana ficewa da file din.
Wayyo cewar Yarima yana dafa kafaɗarshi, dariya Ruhaann da Amira sukayi.
Ruhaann ne yace haba Brother kaban kunya. Wannan yarinyar anya ba aljana na aura ba? Karfi ne da ita wallahi. Kamanta Secret Agent din NIS ce? Cewar Ruhaan yana dafa kafaɗar Yarima. Amma manyan kasar nan nada hannu a cikin case dinnan she won't be safe, cikinsu harda Ex Vice President. I think you are the one that won't be safe cewar Ruhaan yana dariya.
A bangaren Humaira kuwa, file din tasa a mota, ta nufi asibiti.
Parking tayi ta sauko dauke da file din ta shiga cikin asibitin.
Gasiheta suka fara yi kamar koda yaushe, duk da sunyi mamakin ganinta saboda sunsan bata shigowa weekend.
Ganin asibitin a cike yasa ta tambayar abinda ke faruwa. Nurse Gloria ce ke gaya mata baki akayi a asibitin. Lifter ta danna ta shiga. Budewa lifter tayi ta fito karo sukayi da wani sanye da bakin suit, file din hannunta da nashi suka watse a kansan. Sorry please tafaɗa tana daukan files din, mistakenly sukayi musanya. How dare you cewar daya guy din dake sanye da suit yana ɗaga hannunshi. Rike hannun shi tayi ta tureshi gefe tace don't mess with me. Stopp cewar wani babban mutum yana fitowa daga wani daki. Ex Vice President tafada a ranta, dunkule hannunta tayi idanunta na kaɗawa. Murmushi yayi yana kallon kiyayyar dake cikin idanunta yace have we met before? Juyawa tayi kawai ta nufi office dinta.
Wani karamin akwati ta dauko ta ciro wasu files tana dubawa. Takusa minti arba'in kafin ta buɗe file din data shigo dashi. Innalillahi Wa Inna Ilayhi Raji'un tafaɗa tana kallon abinda ke cikin file din. Hannunta na rawa ta ciro waya ta kira Amira. Amii! Kina ina tafaɗa cikin tashin hankali. Muna tare dasu Yarima lafiya? No..bari kawai gani nan zuwa, i lost the file. Whatt? Cewar Amira tana mikewa tsaye, bangane ba? Ina file din yake. I found something even huge ina zuwa tafaɗa tana kashe wayar. Kallonta Yarima yayi yace mai ya faru? Tace batasan inda file din yake ba amma ta samu abinda yafi file din. Dangerr! Cewar Yarima yana daukar mukullin motarshi ya fice.
Shiga motarta tayi ta nufi hanyar studio din Ruhaan. Kiranta Yarima ya dinga yi amma bata dauka. Shittt yafaɗa yana dukan sitiyarin motarshi. Kiran asibiti yayi ya tambayi tazo? Akace yanzu ta fito.
Hanyar asibitin ya nufa.
A bangaren Humaira kuwa birki ta taka ganin tazo traffic amma yaki yi, motar ma gudu take ƙarawa. Duk yadda taso yi birkin yaƙi yi. Avoiding motoci kawai ta dinga yi a titin. Sauke glass dinta tayi ta dinga ihun, moveee birkin bayayi, moveee!
Clashing sukayi da Yarima yana shigowa ita kuma tana fita.
Toh mu haɗu a next page....📄📄
Chapter 40 · 0% Book details