← Book details Ana Zaton Wuta A Makera Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 50

Sashe 23

Ana Zaton Wuta A Makera Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

BY IBNATU-UMAR 🖋️♥️
Page 35&36
Koda Ameerah ta tashi daga aiki, bata biya ta dauki su Zaid ba. Driver ta tura ya dauko su.
Gabaki ɗaya ta rasa abinda ke mata daɗi. Mahmud ne ya shigo dakin ya sameta, Ruko hannuwanta yayi yace Babee. Kallonshi tayi da idanunta dasuka fara ja saboda bacci. Dan cikin magungunan da Dr. Jikamshi ta bata akwai mai sa bacci. Janye jikinta tayi tace can you please leave. Bansan ganin fuskarka! Tafaɗa a kausashe, mai na maki? Au bakasan mai kamin ba maci amana! Wallahi maza duk inda kuke sai kun nuna haliku.... Mai na rageka dashi a zaman takewar auren mu? Da mai na rageka! Tafaɗa a tsawace. Khadijah ki nustu ki saurareni....nutsuwa?? Tun daga randa Mahaifina yabar duniya itama itabar tawa duniyar. Tun daga ranar ban ƙara sanin miye ake kira da nutsuwa ba. Kaima na tabbata da yanada rai da bazakayi min abinda kamin ba. Bin mata, sex chat and all.....you disgust me! Tafaɗa tana mai wani irin mugun kallo.
Duk da bason Mahmoud take ba, amma ranta har suya yake idan ta tuna da abinda ya mata.
Kiyi hakuri, sharrin shaidan ne kuskure ne, wallahi bazan kuma ba. Hannu ta ɗaga mai alamar batason jin mai zai ce. Sannan ta nuna mai kofa da hannunta, yana fita ta kulle kofarta taja tsaki.
Yau Saturday Ameerah bata aiki, koda ta tashi da safe wanka tayi ta shirya cikin simple gown, mara nauyi kuma armless.
Mahmud ne ya shirya ya fita, koh kallonshi bata yiba. Bayan Magrib tana , zaune tana yanke ma su Zaid farce, wayarta tayi ƙara. Kamar bazata duba dan karar shigowar message ne. Amma sai ta dauki wayar ta duba. Room 48, second floor, Classic Heaven Hotel, Katampe Extension. Anan zaki samu amsoshin tambayoyin da kike dasu.
Shiru tayi tana so tama sakon fashin baki. Mammi lokacin Isha yayi cewar Zayn dake kallonta. Ohh sorry na gama ai tafaɗa tana duba kafarshi. Tace kuje ɗaki kuyi sallah ku kwanta. If you need anything, ku sami Nanny kunji? tafaɗa tana kallonsu.
Yes Mammi, suka faɗa suna wuce wa dakinsu.
Hijab dinta ta dauka ta saka ta tura ma Mukhtar address din ba tare da tace komai ba. Koda ya gani, ya kirata amma bata dauka ba sai ya kyaleta.
Parking tayi, ta dauki face mask ta saka sannan ta sauko daga motar.
Wajen receptionist din ta nufa, ta gaya mata room number din. Kallonta tayi tace tana da appointment ne? Eh tafaɗa tana kallonshi. Bara na tambaya mai dakin. Dan baice wata zata zo yanzu ba. Waittt tafaɗa tana kallon shi. I just need access to the room, tafaɗa tana kallon shi. Gaskiya Ma'am it's not possible hakan baya cikin tsarin aikin mu. Zan iya rasa aikina, murmushi tayi ta ciro bundle din yan dubu ɗai-ɗai guda biyu tace bazan dade ba please.
Waigawa yayi yaga bamai kallonshi ya dauko wani card ya bata, ya mata kwatance dakin. Godiya tamai ta wuce sama, tsayawa tayi zuciyarta na bugawa da karfi.
Card din tasa ta buɗe kofar, babu kowa sai motsin ruwa da taji a bandaki.
Mai kofar tayi ta rufe a hankali, ta boye a bayan kujerar dake dakin, ta kunna recorder din wayarta.
Fitowa Mahmud yayi rike da wata mace, suna shewa. Yanzu haka gani takeyi kamar ta fara samun tabin hankali ne, batasan nine nake mata wasa da hankali ba. Camera's din data saka a gidan mu bata san na san dasu ba. Kinsan mai yafaɗa yana riƙo hannunta, girgiza mai kai tayi alamar a'a, nine nan aka bama kwangilar kisan mahaifinta. Dafe bakinta Ameerah tayi tana jin kuka na ƙoƙarin kwace mata.
Danta yaji sanda Mahaifinta keyi min wasu maganganu akan cewa sai asiri na ya tonu shiyasa namai allurar data sashi yin dogon suma, ya kuma mance da abinda ya faru. Dukiya nakeso amma duk bautar dana mata koh tsinke taki saka sunana akai, sai sunan waɗannan tsinannun yaran nata.
Ita a tunanin santa nake, batasan haɗuwa ta da ita da komai shiri bane, yafaɗa yana dariya. Kiyi ki sameni a mota yafaɗa yana ficewa. Murmushi Budurwa tayi tace Toh babe. A firgice Ameerah ta kalli Nisah dake dakin, fitowa tayi daga wajen data boye tace Anisaa!!!
A firgice Nisah ta kalleta, Meerah mai kike a nan....bata rufe baki ba Ameerah ta kwashe ta da mari, idanunta har sun fara chanza launi. Tace kinci amana ta Nisah, kinci amana tafaɗa tana hawaye.
I don't know what's going on in my life da fari na rasa Mahaifiyata, Yayata, Mahaifina, Aunty Mami mai sona, and now my husband, mijina dake aurena shi ya kashe mahaifina.
Ke aminiyata kike cin amanata, Innalillahi Wa Inna Ilayhi Raji'un. Allah ya isa, Allah ya isa tafada tana hawaye.
You destroyed our 5 years friendship because of a man, namijin da ya ci amanar matar shi? Wanda yaci amanar aure kina tunanin ke ba cutar ki yake ba, share hawayenta tayi tace you know what? If i want to i would have made a lot of friends but i didn't because i thought i would never need that. I felt safe with you. You were my best friend, bayan na rasa yar uwata na dauke ki a matsayin yar uwa kuma Aminiya but you took that away from me. Kin ci amanata, kin ci amanar aminci, kinci amanar soyayyar dana nuna maki, Allah ya isa tafada tana fashewa da kuka.
Ficewa tayi tabar Nisah da tarin nadamar abinda tayi.
Tuki kawai takeyi batason inda zata ba, parking tayi a gefen titi, ta saka kanta akan sitiyarin motar ta fashe da kuka mai tsima zuciya. Zuciyarta zafi take mata, daukan wayarta tayi ta rasa wa zata kira taji sanyi. Haka kawai ta tsinci kanta da kiran Dr. Jikamshi. Har ya kusa tsinkewa ta dauka...kafin ta gama sallama Ameerah ta fashe da kuka mai ban tausayi.A hankali ta mike daga kujerar parlour ta, tace Ameerah! Mai ya faru? Kuka kawai takeyi tama rasa mai zata ce mata. Kina ina Khadijah ta faɗa jin horn din motoci. Turamin live location dinki idan bazaki iya magana ba, right now! Hannunta na rawa Ameerah ta tura mata, amma ta kasa kashe kiran. Haka zalika itama Dr. Jikamshi. Mukullin motarta ta dauka ta fice.
Buɗe kofar motar tayi ta ɗago Ameerah dake numfashi da kyar, tace Ameerah kalleni, faɗawa tayi jikinta ta fashe da sabon kuka. Rungumeta Dr. Jikamshi tayi, hawaye na taruwa a idanunta tace mai ya faru, talk to me Amiiii you're scaring me.
Numfashin Ameerah ne ya fara ɗaukewa cikin sauri, ta maida ita motar, ta zagaya ta dayan side din mai zaman banza, ta fara neman Inhaler Ameerah cikin Sa'a kuwa ta ganta. Dauka tayi ta sa mata a baki, breathe in breathe out tafaɗa tana shafa kan Ameerah a hankali numfashinta ya fara dawowa. Ajiyar zuciya, Dr JIKAMSHI ta sauke.
Ta kama Ameerah ta sata a motarta, ta dawo ta kulle ta Ameerah. Parking tayi tana kallon Khadijah da mai aikinta da suka fito wajen harabar gidan suka tsaya. Riko hannun Ameerah tayi ta sauko da ita, ta nufi cikin gidan da ita.
Ɗago ki kalleni ta faɗa tana kallon Ameerah da tarin damuwa a fuskarta. Maa cewar Khadijah tana shigowa dakin da fara'a a fuskarta, Maa we have a visitor, tafaɗa tana taɓa Ameerah da cute little hands dinta. Kallonta Ameerah tayi da jajayen idanunta, tace Hi..ii, ɓata rai Khadijah tayi tace waya saka Namesake dina kuka? Ammii outt cewar Dr. Jikamshi a tsawace. Fita tayi jikinta har rawa yake dan bata taba jin mahaifiyarta ta mata tsawa ba.
Look at me cewar Dr tana riko hannu Ameerah. Kallonta Ameerah tayi ta fashe da kuka, tace kawar dana dauketa kamar yar uwa, taci amanata. Mijin daya kamata ya zame min kariya, ya zame min akasin haka. Banda kowa, tafaɗa tana fashe da kuka. Wa yace baki da kowa tafaɗa tana kallon Ameerah da hawaye a cikin idanunta 🥹 you got me. I will never live or betray you Amii. Kallonta Ameerah tayi, yanzu da take kallon fuskar Dr. Jikamshi da kyau, taga mugun kamar da takeyi da Abbee. Are you my sister...?? Tafaɗa tana kallon Dr. Jikamshi da mugun mamaki. Shafa kanta Dr tayi tace no... wani iri Ameerah tayi sai taji farin ciki daya fara zuwar mata ya tafi...Am not your sister but am your elder sister tafada tana jan kumatunta. Tureta Ameerah tayi tace mai yasa baki gayamin ba. Where were you all this years? Nayi kewar ki, haka zalika Abbee? Mai yasa tun randa na fara ganin ki baki gayamin ba. Ameerah cewar Dr tana riko hannuwanta, fisge hannunta tayi tace don't touch me, i hate you. Do you...toshe mata baki Dr tayi tace taya zan gayamaki when you never listen to me. Yanzu ma kinki bari na nayi magana.
Cire hannunta tayi daga bakin Ameerah tace zauna, anki din tafaɗa tana harararta, you should have told me, da kin gayamin cewa ke yar uwata tace, you should have drag my ears idan naki saurarenki. Tafaɗa tana fashewa da kuka, hawayenta itama Dr ta goge, ta buɗe ma Ameerah hannunwanta, tana cewa you still have a bad temper 🥹. Rungume juna sukayi, suna tuno yarintar su da abubuwa da dama.
Ummii itama tana da rai? Cewar Ameerah tana kallon Dr JIKAMSHI da wani kallan hope. Girgiza mata kai Dr tayi, tace sai dai mu mata addu'a Ameerah, Ummii tun a lokacin da mukayi hatsari ta rasu.
Lumshe idanunta Ameerah tayi hawaye masu zafi na sauka akan kumatunta.
Now tell me, who made my sister's life miserable? Waye yake son yasan wacece Aisha Humaira tafaɗa tana kallon Ameerah da bacin rai a idanunta.
Tiryan-tiryan Ameerah ta bama Humaira labari. Mamaki ya hana Humaira motsi, da kyar ta tattaro jarumtarta tace they will have to pay the price for there actions. They messed with the wrong person.
Sister su Zayn suna gidan karya masu wani abu, don't worry cewar Humaira tana shafa kan Ameerah.
Ammii tafaɗa cikin ɗaga murya, da sauri yarinyar ta shigo, get my phone.
Fita tayi ta dawo dauke da wayar.
Mukkaram kayi hakuri, i know it's late, amma gidan Ameerah zakaje ka dauko su Zayn da Zaid, ka kawo su gidana as soon as possible. Koh kuɗa kada ya taɓasu. Ita dai Ameerah tana sauraren Humaira na magana ne kawai, amma gabaki daya a cikin duhu take. Taya Humaira tasan gidanta, taya tasan yaranta.
I need to make a call cewar Ameerah tana kallon Humaira. Wayar ta bata numbern Mukhtar ta saka ta kira bai dauka ba. Kallon Humaira tayi tace bazai iya shiga gidanan ba idan ban ma securities din magana ba. Murmushi Humaira tayi tana zuba ruwa a glass cup ta miƙa mata tace idan securities ɗari ne masu makamai a gidan nan. Mukkaram zai shiga ya fito Ameerah trust me.
Ruwan wanka ta haɗa ma Ameerah, sannan ta fito ta wuce kitchen da kanta ta dafa mata abinci.
Chapter 23 · 0% Book details