Sashe 35
Ana Zaton Wuta A Makera Part 1 Complete Hausa Novel · about 11 min read
Toh mu haɗu a next page 📄📄📄
ANA ZATON WUTA A MAƘERA....🔥
✒️IBNATU-UMAR ✒️
Page 55&56
Ruhaan cewar Ammi tana kallonshi ganin ya juya zai fita. Tsayawa yayi ba tare daya juyo ba. Ka saurareri ne Ruhaan, i can explain, Wallahi ban rabu dakai saboda bana sonka ba....please yafaɗa yana ficewa.
A bakin motar yaga Amira ta jingina ta lumshe idanunta. Baice mata komai ba ya buɗe motar ya shiga. Yafi minti goma a ciki, yana jiranta, sannan ta shiga ta rufe motar ba tare datace mai komai ba. Kallon window kawai take, hawaye na fita a idanunta tana sharewa cikin dabara yadda bazai gane ba. Parking yayi ya a bakin hanya, ya kashe motar shima ya lumshe idanunshi. Ganin sun dade a wajen kuma baida niyyar mata magana, yasata kalleshi tace mai muke jira? Kukan mai kike? Yafaɗa yana kallonta da idanunsa da sukayi jaa kamar an watsa mai borkono. Dauke idanunta tayi daga kansa ta koma kallon window tace tausayi kake bani. Kasan masifar dake cikin bata ma mahaifiyarka balle har takai ga kana daga mata murya? Nasan kasani, i won't say much. Sai kuma haushin kaina dana keji, ace kaine mutumin dana zaɓa ma ya'yana a matsayin mahaifi. Wanda baisan darajar mahaifiyar saba! Am starting to regret loving you. Da mugun mamaki ya kalleta, tace yess am starting to regret! Ina ma ace tawa mahaifiyar nada rai! Kai fa dan gatan Allah ne, amma ka kasa gane hakan. Ka gyara ALAƘAR ka da mahaifanka, tun kan lokaci ya kure maka!
Ammi is the most sweetest soul i have ever known. Bari kaji in gayamaka, idan ni da bata haifeni ba zata soni haka, kai da ta haifa wani irin so take maka? Can you imagine? Numfashi taja tace take me home, i need to rest. Tafaɗa tana dafe kirjinta dake mata wani irin zafi. Baice komai ba har suka isa gida ya sauketa. Ya dauki motarshi ya wuce gida.
Tana shiga gida, tayi wanka ta kwanta. Allah ya taimaketa Humaira bata dawo ba, balle ta tambayeta abinda ke damunta.
A bangaren Ruhaan kuwa, koda ya koma gida, Ummii ta bashi abinci yaci, kasa ci yayi.
Kallonta yayi yace Ummii, Na'am Mohammad tafaɗa tana kallonshi. Ammu..sai kuma yayi shiru. Kallonshi tayi da mugun mamaki dan tasan wayake kira da sunan nan duk da kuwa anyi kusan shekaru talatin rabon da taji sunan a bakinsa. Nevermind yafaɗa yana ficewa daga gidan. Studio dinsa yaje, baiyi tsammanin ganin Asadullah ba, duk kuwa yasan shiya bashi mukullin studio din.
Punching bag din dake rataye a din area gym dinshi ya nufa. Cire suits din jikinshi yayi ya rage singlet, Boxing gloves 🥊 dinshi ya dauka ya fara punching bag din yana tunanin abinda ya faru.
Kallon shi Asadullah ya tsaya yi, yana mamakin miye ya fusata shi haka.
Yafi awa biyu, har saida ya jiri ya debe shi, ya faɗi a kasa. Da sauri Asadullah ya ɗago shi, yana mai sannu. What happened? Cewar Asadullah yana rike da hannun shi. Shiru yayi baice komai ba, dama shima baiyi tsammanin zaice mai komai ba saboda zurfin cikin Ruhaann.
Wanka ya shiga yayi, ya shirya yayi sallar Magrib. Ruwa Asadullah ya miƙa mai yace koma miye yake damuka, stop avoiding it Ruhaan, face itt. Yana gama faɗa mai haka ya fice.
Hannuwansa yasa ya rike kugunsa, ya kusa minti uku. Kafin ya dauki wayarshi ya kira Amirah. Cikin bacci taji wayarta na ƙara, buɗe ido tayi ta dauki kiran. Hi tafaɗa da wata irin murya irin tamai bacci. Runtse idanunshi yayi, sannan ya buɗe su yace this bedroom voice....bacci nake tafaɗa tana mikewa zaune. Am confused and scared zaki rakani? yafaɗa a takaice.Uhmmm kawai tace dan ta gane inda ya dosa. Listen to your heart tafaɗa tana kashe wayar.
Mukullin motar shi ya dauka, ya nufi gidan Ammi.
Parking yayi ya sauko, ya rasa ta inda zai shiga gidan. Kallonshi mai gadin yayi, yace kaine kazo ɗazu da Hajiya Amira. Gyaɗa mai kai yayi, sannan yace kace mata Ruhaan ne.
Kamar minti uku saiga Ammi ta fito da kanta, Ruhaan tafaɗa tana ruko hannunshi. Am.muu yafaɗa yana kallonta da unsaid feelings. Riko hannunshi tayi suka shiga ciki.
Ruwa ta kawo mai da kanta, haɗe da zobo mai sanyi ta zubamai ta bashi. Kurba daya yayi ya ajiye.
Ammu ki faɗa min abinda ya faru daban sani ba. Can you handle the truth? Yawu ya haɗiye yace yes i can. Ina zuwa tafaɗa tana wucewa sama.
A bangaren Amira kuwa wanka tayi, ta shirya tana tunanin taje gidan Ammi, koh kuma karta je. Humaira data shigo yanzu ne tace ke wai tunanin mai kike? Zan gaya maki anjima bara naje gidan Ammi. Yanzu da Maghrib ? Tafaɗa tana kallon agogon dake dakin. I don't have a choice, ki gayama Daddy. Tafaɗa tana daukan mukullin motar ta ta fice.
Dayake daga gidan Daddy zuwa gidan Ammi na Nisa hakan yasa cikin minti goma Amira ta isa gidan. Parking tayi tans kallon motar Ruhaann daya faka, murmushi jin dadi tayi ta nufi cikin gidan.
Da sallam ta shiga tana kallon Ruhaann dake zaune da Ammi. Tana ƙoƙarin buɗe wata safe.
Murmushi Ruhaan yayi ya mika mata hannun shi, ta make hannun tana hararshi. Zama tayi a gefen kafar Ammi tace Ammi ina wuni? Nayi fushai Nanarh Khadijah. Haba Ammi tafaɗa tana ɓata rai. Murmushi tayi tace shikenan na hakura. Buɗe safe dinnan Nanarh cewar Ammi tana kallon Amira. Bude safe din tayi ta matsa a jiki. Wani album Ammi ta ciro ta buɗe ta mika ma Ruhaan tace kaga wannan? Kallon mutumin yayi yana shafa hoton yanason tuna inda yasan fuskarshi. Wannan dakake gani, shine Sarki Mohammad Lamido, kuma shi din cousin dina ne. Kuma shine Mahaifinka. A firgice ya kalleta Album din na faduwa a hannunshi. Abbuu?? Waye shi? Numfashi taja tace dogon labari ne Mohammad. Amma yanzu zan gaya maka komai. Hannunshi dake rawa Amira ta dafe da hannunta, kallonta yayi ta girgiza mai kai.
Kamar yadda na gaya maka shidin cousin dina ne. Kuma daga Sarki Abdullah sai Baffana iyayensu suka haifa. Haka yass akwai shakuwa sosai a tsakanin su. Ni kuma ni kaɗai Allah ya bawa iyaye dan har sun cire rai da haihuwa. Amma Sarki Abdullah ya'yan sa shidda, matansa biyu. Mama Fulani da Dada. Ya'yan Mama Fulani uku, Mohammad Salis, Mohammed Rabiu sai ba Baffana Mohammad Ruhaan. Dada ma ya'yan ta uku, Mohammed Khamis, Aisha da kuma Fatima.
Tun bamusan miye soyayya ba muke yinta, hakan yasa kowa yasan da soyayyar dake tsakanin mu. Koda aka naɗa shi matsayin Yarima da zai gaji kakan ka Sarki Abdullah, bai so ba. Saboda a lokacin shine ɗa na uku ga sarki Abdullah kuma yanada yayye maza. Baison samun saɓani da yan uwansa. Amma mai sai yan uwansa suka nuna mai ba komai tunda shi sarki yazaɓa. Hakan yasa hankalinsa ya kwanta. Ba'a jima da sa ranar bikin mu ba, kakan ka Sarki Abdullah ya rasu. Bayan ya rasu da wata uku Baffana yabi dan uwansa tafaɗa tana share hawayenta.
A kwana a tashi ba wuya har akayi auren mu. Bayan auren mu shekara biyu ban taɓa koh ɓatan wata ba, a lokacin ne abubuwa suka fara chaɓewa a masarautar mu. Dan shekarar Sarki Mohammed Lamido ta biyar a mulki. Dada tace sai ya ƙara aure, Mama Fulani ta kirani ta ban hakuri. Dan kwata-kwata batason karin auren, amma bataso Dada taga kamar tana mata iko ne tunda ita ta haifeshi.
Nace mata babu komai, Allah ya kawo rabo.
Ya karo aure, ya auri yar kanwar Dada Zaituna. Ita ma shiru babu rabo har aka shekara biyu. Kuma a lokacin ne Inna ta ta rasu tafaɗa tana share hawayenta.
Mohammed tafaɗa tana sauke ajiyar zuciya. Kallon ta yayi yana ganin pain din dake cikin idanunta. Banzan so kaji abinda ya rabani da mahaifinka daga bakina ba, duk da nasan dole zaka sani. Amma ina son kasani, aure rai ne dashi idan lokacin mutuwarshi yayi zai mutu, tafaɗa tana share hawayen data zubo mata.
A haka na koma Saudi da zama, duk da kasancewar Masarautar tushe na, amma ta zama haramiya ta.
Saudi na koma da zama, bani da kowa, a lokacin na haɗu da Abbunka shine ya zamemin kamar dan uwa, ya kula dani. Ya zama gatana a Saudi. Sai bayan zuwa na Saudi nasan na cikin ka. Nayi farin ciki sosai, kuma nayi bakin ciki dan Mahaifinka baison da cikin ba.
Kasancewar Abbunka baban mutum a Saudi yasa mutane suka fara raɗe-radin ai yafi ɗa ba aure. Koda babansu ya kirashi bai musa cewa kai danshi bane, nima har yau bai faɗa min dalilinshi ba nayin haka. Haka yasa akayi nullifying inheritance dinsa. Wannan dalilin ne silar aurena da Abbunka.
Munyi wani irin zama da Safiyya (Ummin Ruhaan) kwata-kwata batason bansan kuma dalili ba. Kwatsam ranar daka cika shekaru biyar a duniya, Kakan ka yace sai dai Abbun ka ya sake ni saboda abinda suke zargin mun aikata yana kawo tangarda a mulki. Banyi musu ba ko kadan. Amma koda akayi sakin, suka matsa akan cewa bazan tafi dakai ba, saboda kai magajin masarauta ne. Nan nace bansan zance ba. Naso gaya masu gaskiya lamarin, amma kuma hakan sai sa Abbunka a matsala ne saboda hukunci yiwa Sarki karya, hukunci ne mai tsanani. Hakan yasa nabarka badan zuciyata taso ba. Amma mai nasan cewa indai kai jinina ne, kuma nina haifeka zaka neme ni. Amma sai naga wata irin kiyayya kake min wacce bansan dalili ba... tafaɗa kuka nacin karfinta.
Haka na dawo Nigeria na cigaba aiki har na haɗu da Nanarh Khadijah.
Kallon Ruhaan dake kuka sosai kamar wani yaro Amira tayi da mugun mamaki dan bata taɓa tsammanin zata taɓa ganin shi yana kuka ba. Hawayen idanunta ta share, ta saki hannunshi, kallonta yayi da jajayen idanunshi. Da ido tamai nuni da Ammi. Rungumeta yayi yana fashewa da wani irin kuka. Ki yafeni Ammu, am deeply sorry. Banda wani excuse, koma mai aka gayamin ya kamata ace nayi bincike akai. Kiyi hakuri, ki yafemin na tuba yafaɗa yana riko hannunta.
Shafa kanshi tayi tace ban rike kaba Mohammad. Zamewa Amira tayi ta fice ta barsu. Huci ta furzar ta jingina da jikin motarta tana tunanin maganganun da Ammi ta faɗa. Yanzu Sarki Mohammed Lamido shine baban Ruhaan.
Why?? Tafaɗa tana dakan tayar motarta. Yana ɗaya daga cikin mutanen datake zargin ALAƘAR shi da Abbi. Rungumeta taji anyi ta baya, shiru tayi tana sauraren yadda yake sauke ajiyar zuciya akai-akai. Raba jikinta tayi da nashi ta juyo tana kallonshi. Hawayen na miye? Tafaɗa tana share hawayen dake yawo a saman kumatunshi. I don't want to loose you again, yafaɗa yana riko hannuwanta. Kallonshi tayi tana mamakin maganar shi. Gyaɗa mata kai yayi yace yes nasan Sarki Mohammed Lamido ne main suspect dinki akan mutuwar Abbi. Kallonshi tayi da mugun mamaki dan bata taɓa zaton wani zai gano manufarta na dagewa akan Mamman Oil ba. Idan ya tabbata shine, what will happen to our relationship? Kallonshi tayi tace ban sani ba nima. Amma koh iska bazan iya haɗawa da ahalin wanda yasa aka kashe Abbi na ba. Sakin hannunta yayi, wani irin tsoro taga ya bayyana a saman fuskarshi.
Motarta tama key, ta fice a gida. Komawa ciki yayi waje Ammu gabaki daya ya rasa mai yake mai dadi.
Koda ta isa gida gida, daki ta wuce straight duk da taji motsin mutanen gidan a dinning hall. Shower 🚿 ta sakar ma kanta ko zataji dadin abinda ke damunta amma zafi ma takeji ruwan yana mata a jiki. Wanka tayi kawai ta fito ta zube akan gado. Kallonta Humaira tayi tace what on earth happened to you today Amii? Juyowa tayi dan bata kula da ita bama sai yanzu. Tashi tayi ta tsaya gabanta tana hawaye. Sai kuma ta rungumeta, shafa bayanta Humaira tayi tana jin wani iri a ranta tace Amii...Amii. Sakin Humaira tayi ta haye gado ta kwanta, maganar duniya tayi taki bata amsa. Cikin dare Humaira ta farka ta shiga toilet amma bataga Amira ba. Fitowa tayi ta shiga dakin su Zayn a corridor taganta tsaye tana leken abu. Taɓata tayi tace keee.. saurin rufe mata baki Amira tayi tace shush 🤫.
Lekawa tayi taga mai take kallo, Zaid ne zaune kamar rana hankali shi kwance yana painting 🎨🖌️ da drawing. Shiga sukayi dan ganin mai yake zanawa. Saurin mikewa yayi, yana kallonsu. Uhmm cewar Humaira tana kallon abinda ya zana. Amii drawing din Zaid kamar naki wallahi da kina karama. Yanzu kin dena drawing ne? I can't draw anymore! Tun sanda nayi......Am sorry 😐 cewar Humaira tana shafa kanta dan tasan yadda Amira keson zane. Mai ya zane wai cewar Amira tana amsar takardar daga hannun HUMAIRA... zaro ido tayi ta saki takardar ta faɗi ƙasa. Ruko hannun shi tayi tace Zaidd! You got your memory back! Kana iya tuna abinda ya faru randa Abbi ya mutu. Shiru yayi ya tsaya kallonta. Talk to me tafaɗa tana riko kafaɗunta shi. Mammi bansan miye ba nima, mafarkin wajen nakeyi kullum, shine nake zanawa. Try to remember Zaid, kayi kokarin tuna wani abu. Amii cewar Humaira tana dafa Amira, girgiza mata kai tayi tace yarone fah, karki stressing dinshi, zai iya loosing memory din gabaki ɗaya.