Sashe 15
Ana Zaton Wuta A Makera Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Zaman Khadijah da Abdulkarim sun yi shine cikin soyayya mai tsafta dakuma ilimin addini.
Makaranta Abdulkarim yace zai saka Khadijah ta cigaba da karatun ta tunda yaga tanaso. Sam tace bazata cigaba ba, idan na maida hankalina a karatu wazai kula dakai, shine abinda ta gayamai.
Wannan furuci yasa Abdulkarim ƙara ganin kimar Khadijah da kuma iyayenta da suka rasu. Nasan da haka amma ya kamata ki koma, ya dage sai ta koma ita kuma ta dage bazata koma ba.
Har faɗa sukayi akan maganar ranar. Ya wuce ɗakinshi ya kwanta, wanda a tunda sukayi aure shekara ɗaya kenan. Hakan bai taɓa faruwa ba. Har ya kwanta ya tuna da kalaman Baba Dattijo na amanar Khadijah daya bashi, kuma yasanta da tsoro anya zata iya kwana ita kaɗai.
Koda ya koma dakin kuwa tana kwance ta kankame waje ɗaya amma bazata bishi ba. Murmushi yayi ya bata hakuri, sukayi settling issue din.
Ba jimawa da auresu Allah yama Baba Dattijo rasuwa.Daga Khadijah har Abdulkarim sunji mutuwarsa. Sosai Khadijah ta shiga damuwa da kyar Abdulkarim ya samu ta fara dawowa daidai.
Abinda ya ƙara daga ma Khadijah hankali ganin har sun shekara bakwai da aure amma koh ɓatan wata bata taɓa yi. Kuma koh a fuska Abdulkarim bai taɓa nuna mata ba duk da tasan cewa yana bala'in son yara. Dan farkon aurensu har yadda zamu tarbiyyantar da yaransu da komai yana tsarawa. Duk sanda ta nuna damuwa sai yace mata ai haihuwa ta Allah ce. Bayan shekara uku da aurensu, Khadija ta samu ciki. Ta sha wahalar laulayi, kamar mai. Haka Abdulkarim yaita kula da ita har takai lokacin haihuwa. Ta haifo danta namji, mai kama da ubansa, aka samashi suna Abdullah. Suna ta rainon dansu, har ya kai shekara uku. Wata rana laraba da basu taɓa mantawa ba, sun shirya sun tafi Trade Fair, Abdullah ya ɓace. Babu irin neman da ba'a mai ba. Khadijah tayi kuka sosai, shima Abdulkarim hankalinshi ya tashi. Ya kashe kuɗade wajen nemam Abdullah amma ba'a ganshi ba.
Wasa wasa har suka shekara goma, ba'a ga Abdullah ba kuma koh ɓatan wata Khadija bata ƙara yiba, zuwa yanzu sun hakura sun zubama sarautar Allah ido. Amma kunsan ance uwa da ɗa sai Allah. Abin na nan a ran Khadijah kuma shima Abdulkarim bai basa hayar private detectives ba. Rashin haihuwar na na ƙara damunsu, sunce sunga likitoci a cikin Nigeria dama kasashen waje amma amsar ɗaya ce Yawon ƙasashe, Lafiyar su kalau.
Sadaka, Azumi da sallar dare babu wanda Abdulkarim da Khadija basayi.
Kwatsan wata rana Abdulkarim ya dawo daga aiki, ya samu Khadijah cikin matsanancin ciwon ciki. Asibiti ya akaita cikin gaggawa. Likitane yace Alhaji ai da kun dinga kawo ta awo yanzu haihuwa tazo gadan-gadan kuma da tazo da matsala.
Subhanallahi wallahi bamusan da cikin ba.
Wannan shine ake cema cryptic pregnancy koh mai cikin bata sani, wasu kuma su kan sani idan haihuwar ta matso koh kuma haihuwa tazo.
Yanzu dole aiki zamu mata ka saka hannu. Hannu ya saka jikinshi na rawa. Ya rasa ma mai zaiyi farin ciki koh akasin haka. Ga dai haihuwa tazo amma kuma matarshi abar kaunarshi na kwance rai a hannun Allah.
Yaronsa amintatce Mukhtar ya kira yace ya kawo mai kayan babies da dabino ajwa yana asibiti yayi sauri. Kayan Mukhtar ya kawo ya bama Nurse din.
Aiki aka ma Khadijah aka ciro yaranta mata masu kyan gaske yan biyu.
Murna wajen Abdulkarim ba'a magana, murmushi yayi ya miƙa ma Mukhtar daya daga cikin yaran yace kaga ikon Allah koh, duk da lokacin Mukhtar bai da wani girma dan kwata-kwata shekarunsa 20 amma yasan wahalar neman dansa da kuma neman haihuwa da Ogan nashi yayi. Allah kuma ya bashi ba tare da yayi tsammani ba.
Murna ya taya shi, kallon likitan yayi yace ya mai jikin? Anyi aikin lafiya? Murmushi likitan yayi yace Alhaji bamu kaiga yin aikin bama ta sauka lafiya da kanta ta haihu.
Masha Allah, Allah ya rayasu cikin amincin Allah da kuma addinin musulunci. Ameen duk suka haɗa baki wajen faɗa. My wife? Yafaɗa yana kallon likitan tana ciki cewar Doctor din, amma ana gyarta ne idan an gama zasu maka magana.
Kiran sallah ya masu a kunne, sannan ya tauna dabino ya basu a baki. Nurse na fitowa ya shiga cikin dakin dauke da jariran a hannunsa.
Kallonta yayi ganin yadda ta fita hayyacinta a dan kankanin lokaci. Sannu Yar Aljanna yafaɗa yana murmushi. Murmushin iya ta mayar mai. Miƙa nata yaran tayi tana kallonsu sai hawaye. Murmushi yayi ya share mata hawaye yace Allah kenan Mai iko, mai yin yadda yaso a sanda yaso. Khadijah ki dena kuka. Godema Allah zakiyi. Uhmm Abdullah nake tunawa... Tafaɗaa tana shafa fuskar jaririyar dake mugun kama da ita, kamar su daya sai dai ita ba fara bace ba kuma baka ba. Kalar jikin mahaifinta gareta. Dayar kuma da tayi mugun kama da AbdulKareem da kuma Abdullah sanda aka haifeshi, farace tass kamar mahaifiyar ta.
Murmushi yayi ya dauki mai kama da Khadijah ya mata huɗu ba. Mai za'a sama mata yafaɗa yana daukar farar mai kama dashi sak. Aisha tafaɗa tana kallonshi. Aisha sunan mahaifiyarta data rasu ne. Aisha Humaira yafaɗa yana kallon yarinyar. Na sa mata suna yafaɗa yana daukan mai kama da Khadijah. Bata tambaye shi sanin cewa bazata tambaya ba yasashi ce mata Nanah Khadijah da mamaki ta kalleshi. Murmushi yayi yace dole in samata sunanki. Saboda burina in haifi ya in sama mata sunan mace mafi soyuwa da daraja a rayuwa. Wata macen nake da a rayuwata bayan ke Khadijah yafaɗa yana ruko hannunta. Kin kula dani kamar kin haifeni, in kuma girmamani kamar ni na haife ki. Kin kuma so ni matsayina na mijinki. Kin jani a jiki kin nuna min kauna. Idan ban sa maki sunanta ba Khadijah sunan wa zan sa mata.
Rungumeshi kawai tayi tana sakin kuka, mai kunshe da farin ciki, so da kuma godiya ga Allah. Ya dauke iyayenta amma ya bata miji data zame mata uwa, uba kuma miji nagari.
Mu haɗu a next page 📃📃📃
ANA ZATON WUTA A MAƘERA......🔥
✒️IBNATU-UMAR✒️