← Book details Ana Zaton Wuta A Makera Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 50

Sashe 49

Ana Zaton Wuta A Makera Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

Amii please wake up, for my sake cewar Humaira tana rungumeta tana fashe da kuka. Tana tuna memories dinsu tun suna yara. Sanda suka rabu, time din datake ganinta a boye. Sanda tazo wajenta asibiti.
Amii you can't die. I want to take care of you more. I want to love you more. Amii ni kadai zaki bari? Ummi ta tafi, Abbi ya tafi. Karki tafi please. Ke kaɗai nikeda, i promise to take care of you. So kika na haɗu da Ummi a aljanna na kasa kallonta saboda ban cika alƙawarin dana daukar mata ba? You're my twin sister tare aka haifemu. You are not allow to leave me tafaɗa tana riko hannu Amira hawayen na diga a hannunta. Amii please cewar Humaira tana surutai.
Nuna yatsar Amira dake motsi Yarima yayi, sannan ya nuna hawayen dake fita ta gefen idaunta. Oxygen, Oxygen yafaɗa kamar mahaukaci. Oxygen ya jona mata tana numfashi da kyar. Ɗaga Humaira yayi a jikinta ya zaunar da ita akan kujera. Ruwan sanyi ya kawo ya bata a baki. Amma da kyar take hadiyar ruwan. Kifa fuskarta tayi a kirjinsa ta fashe da kuka. Rungumeta yayi yana shafa kanta a hankali yana gaya mata kalamai masu kwantar da hankali.
Gyara tie dinshi Ruhaan yayi yana jan wani iri dogon tsaki. Ball yayi da kujerar dake gabashi, yana tuss hannunshi cikin gashin kanshi. I warned you Imaan, maiyasa bakya jin magana.
Dafashi Yarima yace brother it's fine. Kallon Yarima yayi da jajayen idanunshi yace she is my mother, i hate the fact that i can't change that. Kallii Imaan....... taci amanar ta, tasota kamar yadda zataso mahaifiyarta. But she killed her parents! My mother is a murderer yafaɗa yana hawaye kamar ba Ruhaan ba.
Lallashinsa Yarima yayi yana mai tuni da imani da ƙaddara mai kyau da mara kyau.
Daukan suit dinshi yayi ya fice daga asibiti baki daya.
Parking yayi, ya sauko ya shiga cikin gidan. Wanka yayi da ruwa mai zafin gaske, sannan ya dauro alwala.
Kabbara yayi ya fara sallah. Ya fi minti talatin yana Sallah kafin ya sallame ya fara karatun Alqur'ani cikin muryarsa mai dadin sauraro.
Mikewa yayi ya dauki mukullin motarshi yana shirin fita, yaji an buɗe kofar. Kallonshi Imran yayi ya saki ajiyar zuciya dan bayan yaga abinda ya faru a news hankalinshi ya tashi sosai. Zuwa yanzu kowa yasan abinda ya faru. Are you ok? Yafaɗa yana kallonshi. Do me a favour cewar Ruhaann yana kallon Imran. Take this case and wrap it up. Kasan mai kake cewa kuwa Ruhaan. Gyaɗa mai kai yayi yace nasani. Kuma ka tabbatar ta girbi abinda ta shuka, she is a danger to the world.
Butt...for me Imran yafaɗa yana kallonshi, ganin yayi shiru yasa ya cigaba da cewa if not for me do it for Amira that you consider a sister.
Yana gama faɗin haka ya fice a gidan.
Parking motar yayi a harabar asibitin, ya sauko ya.shiga ciki.
Kallon su Yarima dake kallonshi yayi yace lafiya? Ina ka shiga wayarka a kashe cewar Yarima cikin damuwa.
Am fine 😊 yafaɗa yana wuceshi ya zauna a gaban Ameerah dake numfashi a hankali.
Riko hannunta yayi for the first time ya rasa kalaman mata magana. Tsayawa yayi kawai yana kallon fuskarta yana tunanin abubuwa da dama. Kallon Yarima yayi yace ka kira Mukarram yazo da su Zayn. Na kirashi tun ɗazu yana jira a tashe su a school tukunna. Daddy mai bai jima da tafiya ba ka shigo.
Suna zauna kamar masu zaman makoki, Mukarram ya shigo dasu Zayn.
Mammii cewar Zayn yana zaro ido, Mummy what happened to her? Yafaɗa yana dafa Humaira dake kwance da idanunta a kumbure.
Yarima ne yace masu rashin lafiyar tane ya tashi, su kwantar da hankalinsu. But why is Mummy crying? Cewar Du'a tana kallon Humaira. Murmushi tayi tace am fine, my eyes are itchy tafaɗa tana sosa idanunta.
Dafata duk sukayi suka mata addu'a kamar yadda Ruhaan yace suyi sannan suka bi Mukarram da duk hankalinsa ya tashi ya maida su gida.
Bayan wasu kwanaki.
Kamar yadda Ruhaan yace Imran ne ya karbi case din, inda aka yanke ma Ammi hukuncin daurin rai da rai tare da horo mai tsanani.
Zaune yake a gaban Amira kamar kullum, ya rasa abin ce mata saidai ya zauna yayi ta kallonta yana karatun Alqur'ani mai girma.
Hawaye ya fara gani suna fita ta gefen idanunta, hannunshi yakai ya taɓa hawayen cikin mamaki baigama mamaki ba saida yaga ta cire oxygen din ta buɗe idanunta da sukayi jaa ta kalleshi.
Amsar oxygen din yayi zai mayar mata, ta rike hannunsa gam a hankali tace i...i..i want to..say..... Numfashinki is not stable Imaan kiyi hakuri kinji? Rike hannunshi tayi tana kallon shi da so much love. Are you okay? Yafaɗa yana kallon cikin idanunta. I love...I love you! I love you from the moment i met you I've loved you I don't want to die without telling you that... rungumeta yayi yana share hawayensa yace you won't die.
I think i will die soon. Tafaɗa a hankali tana rungumeshi da duka karfin daya rage mata. Ruhaan zan mutu, zuciyata bazata iya dauka betrayals dinnan ba. Ka yafemin kaji? Tafaɗa a hankali ta kallonshi. Dafe kirjinta tayi saboda yadda zuciyarta ke mata ciwo. Are you okay yafaɗa yana riko fuskarta. Murmushi kawai tamai tana kokarin boye ciwon da take ji. Ruwan zam-zam din dayake shafa mata kullum ya bude ya kai bakinta yace sha. I don't want to eat or drink anything tafaɗa tana lumshe idanunta. Hannunshi yakai kan mararta yace what about this little one? Buɗe idanunta tayi ta kalli hannunshi kamar zataga babyn daura nata hannun tayi akan nashi tana hawaye tace zuciyata namin zafi, ina jin kamar zan mutu. I want to give you something to look at again kafin na mutu tafaɗa tana kallonshi. I will give birth to this baby and die peacefully... saurin rufe mata baki yayi da hannunshi yace bazaki mutu ba. Zakiyi rayuwa mai tsayi kuma mai amfani. Zakiyi farin ciki mara adadi Imaan. Meerah don't you think about me idan kika mutu ya zanyi? And Humaira she has only you, kinsan halin da Humaira ta shiga kuwa? Zayn, Zaid and Du'a what about them? If you want to die so bad then you have to kill me first! Ki kasheni kafin ki mutu yafaɗa yana kallon ta da ɓacin rai a tattare dashi. Ashe waccen matar ta fiye maki mu? Ta fimu mahimmanci? Saboda ta yaudare ki zaki bari duniyar ki ta zama babu salama a ciki?
Ina Khadijah dana sani mai tawakkali? Ina Khadijah shugaba ta kwarai?
Khadijah dake son ya'yan ta?
Sauka tayi akan gadon ta zube a kasa ta fashe da kukan data dade tana sonyi. Kuka tayi sosai kamar ranta zai fita. Kwata-kwata bai hanata ba, zama yayi a gefen ya lumshe idanunshi yana saurarenta.
Why must the law always cost me so much 😭 whenever i try to practice the law that i worked hard for, it always cost me my loved ones. Am i cursed or what? Don't i deserve to be happy? Duk wanda naso either leave me or betray me! Zuciyata namin ciwo, bazan iya dauka ba. Mutuwa zanyi tafaɗa tana fashewa da kuka.
Ganin kukan yaƙi karewa kuma tana yin abu kamar mahaukaciya yaasa ya janyo ta jikinshi ya rungumeta yana pecking gefen gashinta yace it's okay not to be okay. Allah yana tare da mai hakuri. Khadijah ke YAR GATAN ALLAH ce!
Sunan daya kirata dashi tayi shiru tana maimaitawa a cikin kanta. Do i even deserve that name? A ranta tayi maganar amma batasan zancen ya fito fili ba. Murmushi yayi yace Allah yana jaraba waɗanda yakeso ne! Allah na sonki Khadijah kinga kuwa ke yar gatan Allah ce! Koh kowa bayasonki Allah na sonki. What about you? Tafaɗa tana ajiyar zuciya. Murmushi yayi yace uhmmmm kamar mai tunani. Kuka ta kuma fashe dashi tace you also don't love me! Tafaɗa tana shirin miƙewa. Rikota yayi yasata a jikinsa yace Love?
Forget about love you're the gravity that holds my universe together! Khadijah i always knew a part of me was missing but bansan miye ba. Amma randa na ganki i knew you were the part!
I was so scared of lossing you, when i saw you in that terrible state. I have been thinking what if..... God Forbid if you leave us i will be miserable forever. I can't seem to stay away from you! So saying just i love you to you is an understatement yafaɗa yana murmushi.
Hawayen idanunta ya share ya miƙa mata hannunshi yace put it here. Kallon rashin fahimta tamai. Murmushi yayi yace put all your worries here i promise i will take care of everything for you. Shiru tayi ta tsaya tana kallon shi.
It's fine! Take your time but when you come to me, i promised to show you the most beautiful love ever. I promise to be your slave! Just put the bullet and give the gun to me i will fire on your behalf my Queen. You... rungumeshi tayi unexpectedly hakan yasa yayi shiru ka kasa ƙarasa abinda zai faɗa.
Ɗaukanta yayi ya mayar da ita kan gadon dan kasa akwai sanyi.
Kwantar da ita yayi a jikinsa ya lumshe idanunsa ya cigaba da karatun da yake.
Shiru tayi tana sauraren yadda yake karatun nan da nan nutsuwa ta fara shigarta.
Leƙawa yayi yaga tayi bacci, murmushi yayi mai ciwo sannan ya ciro wayarshi dake ƙara ya kashe gabaki ɗaya ba tare daya duba mai kiran shiba.
Buɗe kofar dakin Humaira tayi, amma ganin suna bacci yasa tayi murmushi ta koma ta kulle kofar.
A waje ta zauna tana tunanin rayuwa. They had everything, komai da duk wani dan Adam ke buri. Kudi, Fame, Ilimi da boko da addini, amma kash sun rasa babban jigo na rayuwa wato iyaye.
Da'ace za'a bata zaɓi ta zaɓi duk wadannan abubuwan koh kuma ta rayu da iyayenta a jeji da rayuwa da iyayenta zata zaɓa a kowani hali. Mutane na masu kallon they have made it in life, amma basu san kuncin rayuwar da suke ciki ba.
Dafata Yarima yayi, murmushi tamai tana riko hannun shi tace bazaka zauna ba? Zama yayi gefenta yace karki damu! I assure you she is going to be fine.
In Sha Allah tafaɗa tana kallonshi da tarin damuwa a fuskarta.
Buɗe ido Ameera tayi tana kallon Ruhaan dake bacci ya daukeshi bayan tayi baccin. Dan shima ya kwan biyu baiyi bacci ba.
Kallonshi kawai takeyi kamar yau ta fara ganinshi.
I know am very handsome but stop making it that obvious Babyy, yafaɗa yana buɗe idanunsa.
Kallon shi tayi tace you know what? Idanunshi ya zuba mata yana tattara hankalinshi gurinta.
Abbee once told me "Ameerah it's good to have someone beside you, wallahi duk wata damuwarki komin girmanta zata zamar maki kankanuwa" i felt that now tafaɗa tana tusa hancinta a kirjinsa. Lumshe ido yayi yana jin yadda hawayenta masu zafi suke diga a kirjinsa.
Imaannn yafaɗa yana ɗagota. I want to ask you for a favour? Zaki kimin? Yafada yana zaunar da ita. Gyada mai kai ta zubamai ido. Give me your words no more tears! Kallonshi ta tsaya yi kamar baza tace komai tace it's fine na bari ai tafaɗa tana share hawayenta.
Knocking kofar da'aka yini yasa ya fasa fadan abinda yayi niyyar karasa faɗa mata.
Yes yafaɗa yana sauka daga kan gadon.
Sister cewar Ameerah tana kallon Humaira data tsaya a bakin kofar ta kasa karasowa ciki.
Come, come to me cewar Ameerah tana mata murmushi. Da gudu Humaira ta ƙarasa ta rungumeta. Ahh i can't breath, you're hugging me tighly. Am sorry tafaɗa tana hawaye. Murmushi Ameerah tayi tace uhmmm yau kuma kece kike kuka bani ba.
A gurguje please 😂🙏🏽
An sallami Ameerah bayan ta warke gabaki ɗaya daga asibitin.
Mai Martaba ne ya kirasu Adamawa.
Akayi yar walima ba babba saboda jikin Ameerah. Ya kuma sanar ma da duniya dawowar Ruhaan.
An bama Ruhaan sashe kamar na Yarima a masarautar.
Inda Mai Martaba yaso bama Ruhaan matsayin magajin shi. Amma Ruhaan yaki, a cewarshi Yarima ya taso yana ma masarautar nan hidima shida baison komai ba, kuma a dauki matsayi kamar wannan a bashi. Besides yanason zama da Ameerah koda yaushe saboda lalurarta musamman yanzu ma dake da ciki.
Murmushi Mai Martaba yayi yace Muhammad kenan. Nasan bakasan mai ya rabani da mahaifiyarka a baya ba. Kuma baka tambayeni ba! Nasami amsoshina bayan abinda ya faru a watannin baya.
Tabbas nasan halin mahaifiyar ka, shine abinda ya rabamu. Har yau inason Khadija amma babu yadda zanyi. Amma kasani duk da haka uwa-uwace ka dinga zuwa ganinta koyaya ne?
In Sha Allah cewar Ruhaan yana mikewa ya fice.
Chapter 49 · 0% Book details