← Book details Ana Zaton Wuta A Makera Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 50

Sashe 6

Ana Zaton Wuta A Makera Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Page 9&10
Sauka yayi ya shiga ya bada I.D din Khadija, ya bukaci ganinta. Amma suka hana saboda tsaro, juyowa yayi kawai ya wuce.
Ameerah kuwa ta dukufa wajen duba aikin datake a Laptop dinta, kwata-kwata bata kula da hanyar da drivern yabi ba.
Ɗagowar da zatayi taga trailer ta nufo motar da mugun gudu, Hasbinallahu Wani'imal Wakil.....ta faɗa a sanda motar ke tumbling a hanyar har ta isa gaban bishiya, reverse drivern yayi ya ƙara bi takan motar.
Da jiniya sosai ambulance 🚑 ta shigo asibitin Mahmud tare da rakiyar Muktar da duk yabi ya ruɗe, sosai ya shiga damuwa, a take a lokacin ya kori wadanda suke on duty, faɗa ya masu kamar zai bigesu, akan mai basu kira shi ba da tace ita kaɗai zata fita.
Cikin tashin hankali Mahmud ke tambayar abinda ya faru da Ameerah, am sorry sir, kasaka amintattu su ceci rayuwar ta dan a yanda ake farautar rayuwar ta, kawota danayi nan zai iya zama a banza.
Cikin sauri Mahmud ya tura likotocin daya yadda dasu wajen Ameerah koh kwakwaran motsi Mahmud ya kasa duk ya ruɗe.
Ga asthma ga heart disease taya za tayi coping, Innalillahi Wa Inna Ilayhi Raji'un, shine abinda Mahmud ke ta maimaita wa.
Har wajen Magrib ana abu ɗaya, hankalin kowa dake wajen ya tashi har su likitocin.
Wani likitane ya shigo, fuskarshi rufe da mask ya nufi inda Ameerah take, kallonta yayi sannan ya ruko hannunta na dama, faintly take ganin shi, tanason tantance waye. Look at me heyy, heyyy, yafaɗa yana tapping fuskarta da dan karfi, kallon likitocin yayi yace dai-daita numfashinta shine priority dinmu okay? Yafaɗa yana kallonsu, kamar wasu wawaye haka suke kallonshi, dan basu taɓa ganin shi ba. Rage tsayinsa yayi dai-dai kunnenta yace Baby Girlll, jin rukon datama hannunshi yasa shi sakin wani irin murmushi, dai-dai ta oxygen din yayi. Abinda suka gagara yi cikin awanni gashi, shi yayi cikin yan mintina,mamaki likitocin suka dinga yi.
Allurar daza su mata bugun zuciyarta ya dawo dai-dai ya gaya masu, dressing din ciwon gefen kanta ya mata, hannunta da yaga targaɗe ya gyara, ƙara ta saki a hankali saboda yadda muryarta bata fita, kallon fuskarta ya tsayi, kamar wanda aka tsikara yace Astagfirullah ya bar wajen. Dai-dai Mahmud na shigowa shi kuma yana fita. Kwata-kwata bai kula da waye ba. She is stable doctor cewar ɗaya daga cikin likitocin dake wajen, Alhamdulillah Mahmud yafaɗa yana shafa kan Ameerah da'aka ma allurar bacci.
Har yakai karshen corridor din wajen zai fita Muktar ya tare shi, Who are you? Ya faɗa yana kallonshi, koh motsa bai yiba kuma bai bama Muktar amsa ba.
Baya Muktar yaja ya ciro bindiga daga jikinshi, Who are you!! Yafaɗa a tsawace.
Baya ya juya yaga duk mutanen Muktar ne suka zagaye shi, da gudu yayi kansu dan yasan bazasu taɓa harbi a asibiti ba. Boye bindigarshi Muktar yayi ya bi bayan shi yace guys catch him, kar ya gudu.
Koda suka sauka 2nd floor neman shi sukayi suka rasa, hango wani daki yayi buɗe ya shige, ajiyar zuciya ya sauke ganin ba kowa sai wani yaro dake kwance anmai jone-jone a kirjinshi.
Karasawa yayi gaban gadon dan ya kwaɗaitu dason ganin yaron.
Tsaye yayi akanshi amma bai ganin fuskarshi saboda Oxygen din da'aka samai. Daura hannunsa yayi akan yaron yamai addu'a, ya juya zai tafi kenan yaji an riko yatsarshi, juyawa yayi ganin yaron ya buɗe ido, yana son mai magana.
Cire mai Oxygen din yi, ya tsaya kallon fuskar yaron, mamaki na neman sumar dashi, Daddy cewar yaron yana murmushi, cire mask din shi yayi yace am not your dad you're mistaken. Yafaɗa yana da niyyar juyawa ya gudu, mikewa yaron yayi sai kuma ya faɗi saboda dadewar da yayi a kwance, dawowa yayi ya dauke shi ya maida shi gadon, yace calm dowm okay am your daddy yafaɗa yana murmushi, murmushi ya mayar mai, juyawa yayi zai tafi yaron ya tashi zai yi kuka, Don't cry i promise i will be back.
Kayi bacci yafaɗa yana shafa kanshi, har yaron yayi bacci sannan ya wuce.
Ta gabansu Muktar ya wuce amma kwata-kwata basu gane shi ba.
Gida Mahmud ya koma dan hankalinshi yayi wajen Zayn. Koda ya isa gidan duk hankalin Zayn ya tashi dan Ameerah bata ce mai zata wani waje ba, amma kuma gashi har anyi Isha bata dawowa ba.
Yana ganin Mahmud ya fara tambayar shi Ummii fah? Ina Ummina? Murmushi Mahmud yayi yace she is bit sick, tana asibiti, kuka ya fara da kyar Mahmud ya lalashe shi, ya dauke shi suka koma asibitin dan yaganta.
Da gudu ya karsasa gaban gadon da Amirah take, kuka ya fashe da shi yana shafa ciwon goshinta, Ummii ki tashi Please, Ummii yafaɗa yana rungume cikinta. Mai yasa aka sama Ummii irin abin Zaid, itama haka zata zama kamar shi? Yafaɗa yana kallon Mahmud, No dear zuwa jibi ma Ummii zata iya komawa gida...basai jibi ba, yau zan bar nan tafada a hankali tana cire oxygen din fuskarta. Babe kiramin Nisah please tafada tana kalloshi, da mamaki Mahmud ke kallonta anya Ameerah ba aljana bace kuwa, kasa mata musu yayi ya kira Nisah.
Amsa tayi tace Nisah kizo Wellness Hospital. Before that ki biya office dina, my laptop ki kawo min ita, ki duba drawer dake cikin office dina wannan sabuwar ipad din ki kawo min ita.
Cire drip din da'aka sa mata ta cire, ta sauke kafafunta a hankali tayi mika, ta jujjuya kanta ya bada wata irin ƙara.
Kallon Mahmud da Zayn da suka saki baki suna kallonta tayi, lafiya tafada tana kallonsu.
Ummiii you are sick cewar Zayn da mugun mamaki, murmushi tayi tace no darling i was sick.
Kaci abinci tafada tana rage tsayinta dai-dai shi, yes Ummii yafaɗa yana mamaki, ɗagowa tayi jiri ya ɗebeta sauri rike karfen gadon tayi. Kin ga abinda nake faɗa miki koh Mahmud yafada yana daukanta ya daurata kan gadon.
Look i have alot of things to do, besides nasan hakan na iya faruwa. Ba kuma wannan bane karo na farko da'aka fara bige motar da nake ciki da trailer ba. Ina da makiya da yawa, idan ace kowanne su zai samu dama a kaina kullum ina asibiti, shikenan kuma sai na dena aiki na? Yanzu haka nasan aiki ya tarar min....shiru tayi jin a na knocking.
Come in cewar Mahmud yana kallon kofar.
Shigowa Nisah tayi dauke da kayan da Ameerah ta faɗa mata, da sauri ta ajiye kayan tana kallon Ameerah, murmushi tayi mata tace stop staring, ɗago haɓarta tayi tace wannan ramar da kikayi fa, a lokaci ƙalilan? Kayan marasa lafiya tafaɗa tana karewa jikin Ameerah kallon. Not now i have alot of things to do, firstly i need to change, babe i need pad tafaɗa tana kallon Mahmud da mamaki ya hana shi cewa komai. Bari naje na kawo maki yafada yana ficewa. Laptop dinta ga kunna ta fara dubu abubuwan da suka wakana a wunin ranar. Nisah ce ta dameta data faɗa mata mai ya faru, Na kusa mutuwa ne, Allah ne yayi lokaci na bai yiba tafada tana kallon Nisah da murmushi sannan ta maida hankalinta zuwa kan Laptop dinta.
Banson iskanci Khadijah, labarin abinda ya faru ta bata, Subhanallahi kuma shine kike aiki ta faɗa tana dauke computer a gaban ta, kin ma ci abinci? Tsareta da ido kawai Ameerah tayi, Ni bansan mijinki wani irin mutum bane, wannan dai ba so yake nuna maki ba, ace duk abinda kike so shi zaki yi, dai-dai koh akasin haka? I will amma i need to see Zaid first tafada tana kallon wrist dinta daya kumbura.
Mamakin karfin zuciyar Ameerah ne ya hana Nisah magana.
Tana ji a jikinta kamar taga wani, duk yadda taso ta tuna abin yaci tura.
Ganin hakan na niyyar haddasa mata ciwon kai yasa ta hakura.
Rikota Nisah tayi zuwa dakin da Zaid yake duk da cewa ta matsa cewa lafiyar ta kalau amma Nisah taki sakinta.
Turus tayi a sanda ta tura kofar dakin, da mugun mamaki take kallon cikin dakin, tama kasa magana... Mahmud ne daya taho yazo dan ganin abinda ta gani, amma mai, yama fita girgiza da lamarin.
Toh mu haɗu a next page 📃📃📃

ANA ZATON WUTA A MAƘERA.....🔥

✒️IBNATU-UMAR✒️
Chapter 6 · 0% Book details