← Book details Ana Zaton Wuta A Makera Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 50

Sashe 3

Ana Zaton Wuta A Makera Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Abinda yasa Sa'ad Wambai yaƙi amincewa da merger nan duk da zai fimu samun benefits shine.. na ɗaya yana tsoron Miss Khadijah, wanda is a normal thing duk wani babba a kasar nan, da bai riƙe gaskiya ba decision din da zaiyi Miss Khadija na affecting decision din.
Na biyu saboda bambancin shares dinki dana Miss Khadija 10% ne kawai hakan yasa kike managing company din.
Toh ya duba pros and cons din idan Miss Khadija ta rinjaye ki da shares zata zama Managing Director na wannan company, which means zata juya companies dinshi idan kukayi maja. Mafita daya zuwa biyu muke da ita.
Na daya : Kija Miss Khadija a jiki kuyi managing company tare.
Na biyu: Ki nemo shares yadda zai zama impossible ta taddo ki.
Nasan keda Miss Khadija baza ku taɓa zama inuwa ɗaya ba, so na biyun zamu dauka.
Weldone Zully, shi yasa kike P.A na, i trust your brain capacity.
Bello! yes ma'am yafaɗa yana matsowa gaban kujerar ta, a nemo min shares, inma takama ayi blackmailing masu shares din su siyar min ayi, if they refuse in ta kama ayi kisa ayi! Ba kuma su za'a kashe ba, na kusa dasu za'a kashe.Tafaɗa tana sakin wani mugun murmushi.
Yau weekend AMEERA bazata shiga News Buzz ba. Koda ta tashi bayan ta gaya ma chef din abinda zai dafa, dakin painting 🖌️ dinta ta nufa, ta zauna zane.Muryar Mahmud da Zayn taji, murmushi tayi tana juyawa ta kalli Mahmud daya saɓo Zayn a kafaɗarshi, Good morning Ummii suka haɗa baki wajen faɗa.
Murmushi tayi ta harari Mahmud sannan ta kalli Zayn tace Morning Baby, ɓata rai Mahmud yayi yace nifa ummyy? Ya hakuri Daddy tafaɗa tana murmushi dan tasan ya tsani tace mai Daddy. Kwafa yayi ya ajiye Zayn akan coffee table din dake wajen. Ya nufeta, murmushi tayi tace Allah kaga dai da yaro kuma yana kallonka, harararta yayi yace zan riƙe kine. Mammi su waye kika zana? Cewar Zayn yana kallon wasu yara guda biyu mata. Nida da Sister tafaɗa tana ficewa daga dakin. Bin bayanta sukayi suka nufi Dinning cin abinci.
Abincin ta gama ta zuba masu suka karya. They spent the day as a family, sai dare Khadija taje wajen Zaid kamar yadda ta saba, sannan ta dawo.
Washegari kuwa karfe biyu na rana ta shirya cikin doguwar rigar leshi mai shegen kyau da tsada, peach and coffee brown, anyi mata beadwork. Ta bala'in yin kyau, fitowa Mahmud shima yayi cikin Shadda coffee brown dinkin south-south. Yasa hular shi, suka sauko hannunsu a sakale da juna.
Murmushi Zayn yayi ganin iyayen nashi, da gudu ya dauko camera dinsa da Khadija ta sai mai, dan Zayn nada interest akan photography so bata rabuwa da siyo mai abubuwan da zasu taimaka mai, haka shima Mahmud.
Daukansu hotuna ta farayi, murmushi sukayi, Mahmud ya riko hannun Ameera sukayi posing Zayn yaita daukan su, ganin hotunan sunƙi karewa yasa Ameerah cewa yi hakuri dan Allah Zayn, munyi latti we need to go.
Bye Daddy, yafaɗa tana riko hannun Mahmud, murmushi yayi, yayi pecking kumatunsa yace bye son.
Kiran Nanny din Zayn Ameera tayi tace tasa ido akan Zayn zasu fita.
Gidan Abdullahi abokin Mahmud suka je. Taro ne na abokan Mahmud su 4 (Abdullahi, Bashir, Khalid da Habib) dasuke yi da iyalansu duk ƙarshen wata amma banda yara. Daga su sai matan su, su ci su sha suyi hira, wani bin mazan har games sukeyi. Da murmushi matar Abdullahi Na'ima ta tarbesu, lokacin kowa yazo, su kaɗai ne sukayi latti, iyayen soyayya ba cewar Nafisa matar Khalid, murmushi kawai Ameerah tayi dan dama ita bata cika son magana ba. Mahmud ne nan ke bada amsa in suna zolayarta.
Gaiswa tayi da Aisha matar Habib, da kuma Zara matar Bashir duk da basarwar da Zara take yi, hakan bai sa Ameera ta nuna mata wani abu ba.
Kamar kullum Nafisa ce keta matsawa Ameera dan ta samu tayi magana.
Sai bayan Magrib mazan sunje masallaci sun dawo sannan suka tafi. Kallon Ameerah dake kallon window Mahmud yayi yace tunanin mai kike? Kallonsa tayi taga ya maida hankali kan tuƙin dayake tace babu. Faɗi dai yafaɗa yana riko dayan hannunta, I miss spending time with Ammi....murmushi yayi baice komai ba ya cigaba da tuƙin sa, ita kuma ta ciro tab daga cikin handbag dinta tana aiki. Jin yayi parking yasa ta ɗago idanunta, ganin inda ya kawo su, yasata buɗe kofar cikin murna ta shige ciki, batare data jira shiba.

Toh mu haɗu a next page 📄 📄📄

ANA ZATON WUTA A MAKERA...🔥
Chapter 3 · 0% Book details