Sashe 37
Ana Zaton Wuta A Makera Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
✒️ IBNATU-UMAR ✒️ Page 57&58 Am sorry Zaid, tafaɗa tana rungumeshi. Idan ka tuna wani abu just draw it and show it to me kaji? Anytime tafaɗa tana mai murmushi. Okay Mammi yafaɗa bata takardar. Har gado Humaira takaishi ta kashe wutar dakin. Tace mai kuma ya kwanta yayi bacci. Riko hannu Amira tayi suka koma daki, suka kwanta. Zaune take a office dinta Amira tana kallon drawing din da Zaid yayi. Kiran Faith tayi ta fadi abubuwan da take so ta kawo mata. Kallon kayan painting din tayi zuciyarta na bugawa tana a duk sanda ta tuna cewa bazata kara iya zane ba.Apron ta saka ta zauna akan kujerar ta dauki brush 🖌️ din hannunta na rawa. Dafe hannunta tayi tana kokarin zana abinda take so ta zana, amma wani irin zafi takeji har cikin ƙwaƙwalwarta, kuka ta fashe dashi, tana kallon brush din a kasa. Hannun daya dauki brush din ta tsaya kallo, mika mata brush din Ruhaan yayi, ganin ta tsaya kallonshi yasa ya riko hannunta ya saka mata brush din a ciki, ya daura hannunshi akan nata. Yace tell me, what do you want to draw yafaɗa yana mata murmushi. Hawayen idanunta ta share, tace it's fine babu komai. Tafaɗa tana mikewa, zaunar da ita yayi yace If you can't see, i will be your eyes. If can't talk, i will be your voice.If you can't walk, i will be your ride. If you can't draw, i will be your hand. Murmushi tayi ta gaya mai abinda take so, ta bayanta ya riko hannunta suka fara zanen. Duk da zanen it's a bit rough amma tasamu abinda takeso. Thanks tafaɗaa tana murmushi. Lunch dinta Faith ta kawo mata, one more plate please. Cikin girmamawa Faith ta amsa mata ta juya dan kawo ma Ruhaan abincin. Zama yayi opposite dinta yana buɗe mata abincin. Harta fara cin abincin ta rufe tace yawwa yaushe zamuce wajen amaryar ka tafaɗa tana ɗaga mai gira. Girgiza kai kawai yayi baice komai ba, buɗe ruwa tayi ta sha tace kaban amsa mana. Anjima yafaɗa yana fara cin abincin da faith ta kawomai. Kadan yaci ya rufe yasha ruwa. Kai har yanzu kananan da rashin son cin abinci tafada tana kallon plate dinshi daya rufe. Ganin bai kulata ba yasata cewa wata rana sai na zaneka saboda karfi na. Dariya yayi yace sai aukin ci ba kiba. Anji din tafaɗa tana hararshi. Zama tayi kusa dashi tace bafa kaci abincin ba Babe? Murmushi yayi yace na koshi but if you can feed me i will gladly eat. Murmushi tayi ta dauki spoon din ta dinga bashi har saida ya cinye. Bayan La'asar tayi niyyar zuwa A.K Group amma saboda zuwa wajen Suhaila suka fasa. Parking yayi a gaban wani haɗaɗɗen Cafe dake Maitama. Saukowa Amira tayi suka shiga ciki. Order Oreo Milkshake Amira tayi suka zauna. Kiran Suhaila yayi yace mata tana ina? Baiga kowa wajen ba. Kuma tace yazo ya sameta. Hakuri ta bashi akan cewa tana hanya traffic ne ya tsareta. Banason jira, na baki 6mins yafaɗa yana kallon agogon dake hannunshi daga nan ya kashe wayar. Straw ta saka a cikin Milkshake din da'aka kawo mata ta fara sha. Buɗe kofar wajen suka ga anyi, Suhaila ce ta shigo sanye take da wasu riga da wando. Tasha kitson attachment abinta,taci uban hills. Dariyar Amira ta fashe dashi, wani mugun kallo Ruhaan ya mata, tayi saurin haɗiye dariyarta. Hi Darling tafada tana dafa kafaɗar Ruhaan. Kallon hannunta data dafashi yayi sannan ya kalleta, yace dauke hannunki. Oh sorry tafaɗa tana zama. Kallon Amira tayi tace Hi wannan kanwar muce Darling? Tafaɗa tana jan kumatun Amira. Mamakine ya kusa kashe Amira a zaune. Murmushi Ruhaan yayi baice komai ba dan yaji dadin yadda Suhaila tayi pissing Amira, dama ita ta matsa mai yazo. Danne fushinta Amira tayi ta ƙaƙalo murmushi tace eh tana take kafar Ruhaann da takalmin ta. Banza yayi da ita duk da yaji zafi. Okay ga wannan takarda, sharudan auren mune , ka duba ka gani. Baki sake yake kallonta. Ni bazan zauna da kishiya ba. Sanna kuma...keehh cewar Amira tana kallonta. Amma bakida hankali koh? Watt Ruhaan Darling kanwar nan taka amma batada lafiya koh? Tafaɗa tana riko hannunshi. Huci Amira tace let go of his hand! Murmushi Ruhaan yayi ya tsaya kallonta. Murmushi Suhaila tayi ta saki hannun Ruhaan ta ajiye takardar akan table din tace bazan iya auren wanda zuciyarsa take wurin wata ba Khadijah Abdulkarim Kurfi. Da mugun mamaki Amira ta kalleta, don't be shocked you are very famous you know tafaɗa tana murmushi. Ba'a daura aurena da Ruhaan ba, half way na tsayar da daurin auren. A cikin wannan takarda zaki samu duk wasu bayanai da kike so akan ALAƘAR mahaifina da mahaifinki. Da sauri Amira takai hannunta kan takardar, dafewa Suhaila tayi tace amma zaki min alƙawarin abu ɗaya. Miye sharadin? Amira tafaɗa da seriousness akan fuskarta unlike sanda Suhaila ta shigo. No harm should come to my father! Idan dai kinsan baida hannu cikin mutuwar mahaifina babu abinda zai sameshi. Amma idan kinsan yana da hannu ki dauke file dinnan ki tafi dashi, dan babu wanda ya isa yasa in kyale shi, kuma bazan maki alƙawari ba. Murmushi Suhaila tayi ta dauke hannunta akan file din, dauka Amira tayi. Ta saka cikin handbag dinta. Tashi Suhaila tayi ta bama Amira hannunta tace it was nice meeting you. Kallon hannun Amira tayi ta dauke kai tace Thanks for your help. Murmushi Suhaila tayi ta juya ta bama Ruhaan hannu it was nice.....kasa karasa maganar tayi ganin Amira ta bata hannu tace Thanks. Murmushi Suhaila tayi kawai tana girgiza kai ta juya ta fice. Kallon Ruhaan da dariya ke cinsa Amira tayi tace what is funny? Girgiza mata kai yayi yana ƙoƙarin haɗiye dariyarshi. Kai baka da aiki sai washe ma mata hakora koh? Zaro ido yayi yace ni da yaushe nayi mata magana ma, baku kuke ta maganar kuba. Hararshi tayi tace don't talk to me again. Bin bayanta yayi ya buɗe mata motar ta shiga shima ya zagaya ya kunna motar. Kiran Asadullah yayi yace mai yazo da Humaira Studio dinshi. Parking yayi ya zagaya ya buɗe mata, ta sauko tana haɗe rai ta shige ciki. Jakarta ya dauko, yabi bayanta. Buɗe mata kofar yayi suka shiga ciki. Zama tayi akan kujera ta buɗe file din tana karanta abinda ke ciki. Fisge file din Ruhaan yayi yace nima ai inason ganin abinda ke ciki. Murmushi tayi tace Angon Suhaila bani abuna. Kin fara ba, yafaɗa yana kallonta. Na fara din, you were even smiling at her. Har tana wani dafaka Ruhaan Darling tafada tana kwaikwayon muryar Suhaila. Amma ai nace mata ta cire hannunta. Noo do not talk when am talking. Kanafa sonta ne, na sani. Kai mata nawa zaka aura? At first it was that annoying cousin of your Mifra. Yanzu kuma Suhaila nan gaba kuma banson wa zaka ce kanaso ba. Tafaɗa tana nunashi da yatsa, but... yimin shiru kaima son matan tsiya ne dakai, kuma duk abinda... toshe mata baki yayi da hannusa ya nuna mata su Humaira dake tsaye a bayanta suna dariya itada Asad. What is funny? tafaɗa tana kallonsu. Nayi shiru Amii yafaɗa yana zuge bakinsa. Hararshi Humaira tayi tace i won't warn you again. Okay guys kuzo ku zauna muyi abinda zamuyi cewar Ruhaan. Kujera Amira da Humaira suka ja suka zauna. Ruhaan ne ya fara masu bayani kamar haka. Mamman Oil ne mutum na karshe da zmau zarga amma hakan bazai sa mu fasa binciko Alaƙar dake tsakanin su, su Shidda ba. Mohammed Zayn kanin sarki Saudi, Mamman Oil, Daddy Tahir, Abbi, Alhaji Ibrahim Jikamshi (Daddyn Humaira) sai kuma Sarkin Adamawa Mohammad Ruhaan yafaɗa yana kurawa hoton sarkin ido. Abba?? Cewar Asadullah yana kallon hoton Sarkin Mohammad Ruhaan. Waitt!! Cewar Amira yana mikewa tsaya. Wannan Sarkin Adamawa shine Mahaifinka? Of course cewar Asadullah yana kallonta. Kallon Ruhaan tayi that means.. gyaɗa mata kai yayi. That means what? Cewar Asadullah yana kallon su. Babu komai back to business cewar Ruhaan. Miye Alaƙar su? I will tell you cewar Humaira tana amsar marker hannunshi. Dukkan su, su biyar dinnan, sun kasance masu yiwa kasa hidima a baya. Ma'anar sun kasance International Secrets Agents. Whatt?? Cewar Amira da Asadullah. When did you know that? Cewar Amira tana riko Humaira. Yesterday tafaɗa tana kallonsu. How did you know that? Cewar Asadullah. Saboda ina aiki irin nasu tafaɗa tana kallonsu. Whatt! Cewar Ruhaan da Asadullah suna nufar Humaira. You will have to resign cewar Asadullah. Idan naki fah tafaɗa tana kallonshi. Listen Sister cewar Ruhaan yana tsayawa a gabanta. Duk manyan dake wannan tafiyar munafukai ne. Manyan kasar nan bazasu taɓa bari ayi wani abun cigaba a kasar nan ba. Nafiki sanin mutanan nan yafaɗa damuwa na bayyana a saman fuskarshi. I will think about it tafaɗa tana komawa ta zauna. Ajiyar zuciya Ruhaan yayi yace Hakan na nufin mutuwar Abbi nada Alaƙa da aikin nan? Bingo cewar Humaira tana kallonshi. Miye silar? Yafaɗa yana kallon Humaira. I don't really know kasan yadda security wajen yake idan aiki bawai ya shafeka bane, baka samun full access to it. Amma yakamata muje muga Sarki Mohammed Ruhaan Lamido, tafaɗa tana cire glass din idonta. Weekend will do cewar Ruhaan yana kallon Asadullah da Amira da suka haɗe rai. As you wish cewar Amira tana daukar mukullin motarta ta fice. Bin bayanta shima Asadullah yayi nashi ran a ɓace shima. Kallon juna Humaira da Ruhaan sukayi da mamaki. Haushin miye suke ji? Cewar Humaira tana kallon Ruhaan. Ohh shitt Amii tafaɗa tana dafe goshinta, ta dauki mukullin motarta ta fice itama. Murmushi Ruhaan yayi ya bi bayansu amma ko sanda ya fita Asadullah da Amira sun wuce. Reverse Humaira tayi, tabi bayan motar Amira. Amira na gama parking Humaira nayin horn, koh tsayawa Amira batayi ba ta wuce ciki. Garden din gidan ta zauna, tana kokarin danne fushinta. Tsaki taja tayi ture yar karamar flower vase din dake gabanta. Zama tayi ta haɗe kai da gwiwa tana jin wani irin haushin Humaira. Ace tanada wannan information din amma bata sanar da ita komai ba. Zama Mukkaram yayi a gefenta yace Amiraa. Ɗagowa tayi da kalleshi, sai kuma ta juya ta kalli