← Book details Ana Zaton Wuta A Makera Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 50

Sashe 1

Ana Zaton Wuta A Makera Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Marubciyar
ALAKA BY IBNATU-UMAR
FANSA BY IBNATU-UMAR
GAGARARRU
RUHI BIYU ZUCIYA ƊAYA
HANTA DA JINI
DUNIYARMU A HAƊE TAKE
Whatsapp Number:0911 462 2686
BISMILLAH AR-RAHMAN AR-RAHEEM..
Da sunan Allah Mai rahma Mai Jin Kai.
Godiya ta tabbata ga Allah da ya bani damar fara wannan rubuta, ina rokonsa ya bani ikon rubuta alkhairi ya kuma haneni daga rubuta sharri. Allah ya sa wannan rubutu ya amfane ni da duk wanda Allah ya bawa ikon karantawa.
Kamar yadda kuka sani littafai biyu nake rubutawa a lokaci ɗaya amma a wannan karan guda ɗaya tamkar dubu nazo maku dashi💕
ANA ZATON WUTA A MAKERA....🔥🔥
BY IBNATU-UMAR ✍️
PAGE 1&2

*KING CENTER TOWER, RIYADH, SAUDI ARABIA*

Zaune yake cikin duhu yana kallon view din wajen dakin da yake ciki, idanunsa rufe sai ka rantse bacci yake yi, amma a zahiri ba baccin yake ba. Saurin bude ido yayi saboda motsin dayaji a dakin. Bai motso ba ya saka hannunsa a karkashin centre table din dake gabansa, bindiga ya ciro, amma bai fito da hannunsa ba.
1,2,3...haka ya dinga irga sahun tafiyar mutane nawa yakeji, har daina jin tafiyar su, goma yafada yana smriking, murda kofar yaji anyi, yayi saurin komawa bayan kujerar da yake zaune yana duba bullets din dake cikin bindigar hannunsa. Maza ne suka shigo da bindigogi a hannunsu su goma. Ganin gadon kamar da mutum yasa suka dinga harbin gadon, jini nata fito har saida suka kusa karar da bullets dinsu. Cikin harshen larabci daya daga cikin su yace ‘Ya mutu” kafin ya rufe baki yaji saukar harbi a kafadarshi, faduwa yayi kasa, kafin su hankara duk ya harbesu a inda ya harbi na farkon.
Bakar jacket da hula hana sallah baka yasaka ya sabi backpack dinsa, daukan wayar ɗaya daga cikin su yayi ya kira asibiti ya bada sunan apartment dinsa yace akwai marasa lafiya, su aiko da agaji cikin gaggawa. Yana fadin haka ya kashe wayar ya juya ya fice.
Power bike ya hau ya nufi bayan gari, yar karamar wayar hannu ya ciro ya duba sakonnin shi, cikin gaggawa, ya sauya shigar jikinsa ya kuma tada mashin din yabar wajen.
Tafiyar minti talatin kafin ya isa a bakin wani haddaden apartment. Cikin ya shiga ko’ina ma’aikata ke aiki kamar safiya, wasu na aiki a computer wasu na shirya files.
Lifter ya nufa ya danna 5th floor, tana tsayawa ya fito ya nufi ofishin dake kallonsa, ciki ya shiga ya sara ma balaraben dake kan kujerar a zaune a kalla shekarun sa zasu kai 60.
A fausace dattijon ya kalleshi yace “BURKAN” miye nake gani haka ya fada yana wulla mai file din gabansa, runtse ido wanda aka kira da Burkan yayi cikin harshen turanci kamar yadda dattijon yamai magana ya fara kokarin bashin amsa. Sir, operation failed yafada yana taune lips dinsa, zazzafan tea din dake gabansa ya watsa mai a fuska, nan da nan fuskarshi tayi ja abinka da farin mutum. Babu wani abu mai kama da failure a cikin aikinmu Burkan.
Sanin mahimmancin aikin nan ya sa na baka shi, saboda baka taba faduwa ba. Kasan mai yasa muka maka lakani da BURKAN? Nasan kasan ma’anar Burkan (VOLCANO)"Dutse mai aman wuta" saida kacinye mutane badai a cinye kaba....kafin ya karasa, Burkan ya makureshi da tie din suite din jikinsa, jijiyoyin kansa sun fito radau yace address me with respect, daga sanda ka karamin haka sai na soye fuskarka ya fada yana huci, ya sake shi ya koma gaban tebur din ya kame kamar yadda ya tsaya da farko.
Kallonsa yayi yace kuskurene sir, da an min ba daidai ba nake mance hierarchy.
Kallon wannan ya gama raina mai wayau dattijon yamai yace da ka kuma failing wani operation din kasani korace!!
Batare da Burkan yace mai komai ba ya dauki ya file din ya sara mai ya fice.

*ASOKORO, ABUJA,NIGERIA*
Pent house ne hadadde, duk wasu kayan jin dadi na more rayuwa akwai su a gidan, tun daga first gate, second gate, har zuwa third gate wanda shine zai sadaka da kofar main parlour din shiga gidan. Securities ne cikin suite black, shirt dinsu ce kawai fara, amma takalmi, tie da komai nasu baki ne. Kowanne su ya sakala abin ji a kunnensa, wani magidanci ne mai kimanin shekaru 45 yake dubasu daya bayan dayan. Kallonta wani matashi maji karfi yayi a tsawace yace miye a takalmin ka? A gigice ya kalli takalmin sa kura ce kadan ta taba takalmin, bayan haka babu wani aibu a tattare da shigar shi ko kuma wani datti.
Wata matashiya ce ta fito yar kimanin shekaru 25, sanye da suite sky blue and white, ta daura turban akanta. Ba fara bace cen, amma baza’a ce mata baka ba, tana da round face, da kuma manyan fararen idanu, dogon hancine da ita, pink lips dinta sun sha lip gloss sai bakinta yayi kamar tayi lining baki, amma haka bakinta yake.
Kallon wanda aka kira da Anas tayi sannan ta kalli wannan magidancin tace CHEIF SECURITY, matsowa kusa yayi ,ya sauke kansa kasa bai hada ido da ita yace “Yes Ma’am” DISCARD HIM! Tafada tana wucewa, wani irin kallo yama Anas, cikin sauri yabar wajen. Bude mata mota Cheif Security yayi har zata shiga ta tsaya sanadiyyar muyar wani matashi dan kimanin shekaru 35 dataji ya kirata. Babe shine zaki tafi koh sallama yafada yana balle button din shirt dinsa, gajeran murmushi tayi tace inada meeting ne shiyasa tafada tana tayashi adjusting tie dinsa, pecking kumatunta yayi yace bye bye, murmushi kawai tayi ta shiga motarta driver yaja suka wuce.

*NEWS BUZZ, MAITAMA*
Tun kafin motar ta, ta tsaya, ta securities din dasu ka taho tare ta tsaya, a jere sukayi layi suka kame, motarta na tsayawa, Chief Security ya bude mata tayi gaba, kofar tayi sliding suka shige ciki. “Good Morning Ma’am” cewar wata matashiya baza sufi shekaru daya ba, Morning Nisah. Sectary dinta ce mai suna Faith ta miko mata ipad dinta, amsa tayi tana kallon schedule dinta, lifter suka nufa, cikin sauri Chief Security ya danna button din, ya danna floor din da zasu.
Kallonsa tayi sanda lifter din ta bude daidai ofishinta tace MUKTAR you can rest, akwai securities a nan, you can go to your office. Cikin girmamawa ya amsa mata ya juya ya nufi lifter din, ita kuma Faith ta nufi reception dan nan ne wajen aikinta, hannuwanta ta saka kofar tayi scanning sannan kofar ta bude.
Kallon Nisah tayi dake bayanta tace kira min landline ya kamata Zayn ya tashi by now ya tafi school. Telephone din dake kan table dinta Nisah tayi using ta kira landline. Magana Nisah tayi da Nanny din Zayn sannan ta kashe wayar. Kallonta Nisah tayi tace Ma’am yanzu za’a kaishi school. Gyada mata kai kawai tayi tana kokarin cire suit dinta ta rataye cikin hanger din dake office din. Kallon Nisah tayi tace stop being formal with me, ba kowa nan ai bare kice da workers. Ke kadai ce friend din danake da, ki daina min magana kamar kina karkashi na. Murmushi Nisah tayi tace ba kamar bane ina karkashin ki nake Ameera, toh ki cigaba tafada tana jan dogon tsaki. Murmushi Nisah tayi ta nufi desk dinta dake katon office din AMEERAH.
Bayan mintina kalilan AMEERA ta kalli Nisah tace lokacin meeting din yayi, muje tafada tana kokarin saka suit dinta. Files dinta Nisah ta dauka suka fito, Ameera na gaba Nisah na bayanta. Sliding kofar tayi suka shiga, duk wanda ya kamata ya hallacci meeting dinnan ya hallara.
Mikewa sukayi ta zauna sannan suka zauna, daya bayan daya take kallonsu, gabaki dayan su, su biyar ne, harda ita da Nisah.
Kallonsu tayi cikin harshen turanci ta fara magana, Mai matar cen take ciki, kallon Muktar yayi yace Ma’am daga bayanan da muka samu daga mutanen mu dake bibiyarta, tana bukatar kudi dan cigaba da gudanar da company din, saboda duk shareholders dinta kin hanasu bata funds. Gyada kai Ameerah tayi tace dole mu turata bango ta yanda zata fara tunanin amfanin da kudin AK GROUP, data taba kudin zamu mata talala mu hada meeting a cireta daga matsayin Chairwoman din company a bani matsayin, bazan taba barin abinda mahaifina ya gina da guminsa ya lalace ba ta sandiyyar ta. Wani ne ya kalleta yace Ma’am sai kinada kimanin 50% shares na company din zaki iya zama Chairwoman din company din amma a yanzu kinada 30% ne kawai, kina bukatar 20% idan plan dinmu ya tafi daidai. Murmushi tayi a duba wadanda zasu iya siyar da shares dinsu a sakar masu kudi ko nawa ne a siya, ba darajar kudin bane matsala ta, abinda Abee yafi cherishing a rayuwarshi yafi min mahimmanci. Kallon wani matashi tayi tace Aminullah! Ganin kamar hankalinsa baya wajen su, Sorry Ma’am yafada yana zama da kyau, flash ya mika mata yace bayanai ne kan SA’AD WAMBAI, yatsina fuska tayi ta jefa mai wani irin kallo, na kamin bayani, murmushi yayi ya mike ya jona masu a flash din video din na loading ya kalleta yace shahararren dan kasuwar nan SA’AD WAMBAI mai kima da mutunci a idon jama’a turns out to be a gay yafada yan masu playing video din. Dauke kawai tafada tana kauda idonta daga screen din. Yana sa ana kawomai yara maza kanana yana lalata dasu..
Kallonta Ishaq yayi yace Ma’am wannan labari zai kara daga darajar gidan jaridan nan idan muka wallafashi. Kallon bakada hankali tamai, kafin ta kalli Aminullah tace dig more, tafada tana amsar flash din. Maida kallonta tayi zuwa ishaq tace kayi abinda na saka, nayi ya fada cikin girmamawa yana mika mata tab din dake hannunsa daka dauke da tambarin News Buzz a bayanta, murmushi tayi bayan ta gama kallon abinda yake ciki tace Good Job.
Nan suka cigaba da meeting dinsu har karfe 1 na rana sannan ta sallamesu itama ta koma office.
Chapter 1 · 0% Book details