← Book details Abdulmajid Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 53

Sashe 48

Abdulmajid Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tuni su Inna sun tare sabon gidansu dake Shagari Quarters, ganin zamani ne irin mai kyau d'in nan Sosai fa, Wanda Ameena, Asma'u, Mansur suka had'u suka Gina, abinda yasa nasaka Asma'u saboda gadonta hadda shi aka hada akayi ginin da sunan ta, Mansur ma yanzu harka ta bud'e dan ya samu aiki a Navy, so yanzu familyn Abubakar sunfi k'arfin a kirasu talakawa, hakan baisa musu girman kai ko k'yamatar talaka ba face wata hanya ta taimako data bud'e musu dan sun dage gurin taimaka yan uwa da gajiyayyu(abinda ya yakama ta ko wane mai hali yayi kenan ba gina manyan gidaje a koma Abuja a lafe ba, dan sadaka haske ce gobe k'iyama, Allah ka wada tamu da halal ka bamu ikon ciyar dashi ga bayinka dominka ya Allah).

************

Su iya Hari an isa Kaduna cikin yardar Allah, akayi mata aiki, dan Dr Abdool yana da k'wararrun likitoci da suka shafi kowanne b'angare ga ingantattun kayan aiki, cikin nasara aka yanke k'afafun tare da yi mata na roba, aikin da ya d'aukesu sati d'aya, anyi aiki successfully, Iya Hari sai kuka take tana nadama abinda ta shuka a rayuwar ta ga Ramlah data wulakanta ta d'oketa a banza ta zamo silar samun lafiyar ta duk da tasamu ciwon ne a gurin cutar da ita amma ta yafe mata har da kuma taimaka mata, lallai d'an hakin da ka rena shike tsole naka ido, kuma hak'uri jigon rayuwa ne, gashi Ramlah tayi hak'uri da cutarwar Iya Hari a gareta gashi Allah ya d'aukaka ya bata komai da ake nema a rayuwa saidai godiya da hamdala ga ubangiji kawai da Neman gafararsa.

Duk da yanayin da suka shigo garin na tsananin ciwon iya Hari hakan bai hana su bawa idanun su hakkinsa ba lallai garin dad'i na nesa haka kawai su Shatu ke fad'i a ransu basu k'ara tsurewa da lamarin ba saida suka isa gidan Mami k'amshin nan daddad'a da furannin ke fitarwa da iskar ni'ima dake gidan as usual, nan fa a shiga bawa ido abinci, suna girmama Allah, ashe Laure tana cikin aljannar duniya, da aka kawo musu better sukaci nan santi ya tashi Anji girki.

Da sukaje asibiti nan ma k'auyenci tsabage suka baje abinsu wai asibiti kaman gidan wani sarki ba doyi ba komai sai k'amshi da sanyin A.C dake kad'asu a haka sukata baje gidadan cinsu har akayi aikin aka kammala, bayan ta warware sosai aka shiga dasu zaga gari kusan tashi zaucewa sukayi hadda su Iya Hari sai wasar baki ake kamar gonar auduga, banki, hanci, ido sai kallo suke, wuni sukayi zungur sunje malls, da parks sosai sun cire kwarkwatar ido, anci ansha.

Adan watan da sukayi sun murmure sosai musamman Shatu tayi ja sosai tayi jiki Ashe duk wahala ce ta lalata ta, sosai suke kama da Ramlah d'an kammaninta d'aya da marigayi Abdulrahim, Iya Hari ma da Lanti sun murmure abinsu sunyi kumari da haske, saidai har yanzu sun k'asa sakewa dasu Mami suna ganin kamar suna kallonsu da cutarwar da sukayi wa Laure, duk da Mami na iya k'ok'arin ta gurin jansu a jiki, itama dai Ramlah kullum tana tare dasu, su kuma sun dage da renon su Amatullah.

Watansu Ramlah 2 amma har yanzu shiru Mami tak'i bashi matarsa tun yana ma Ramlah naci har ya gaji ya saka mata ido ga gidan a cike ba damar ya samu ya keb'e da ita, ko gidan yaje yace tazo ta kawo mai Abu a d'akin sa, cewa tace ai haihuwa d'aya horon abin..ba abinda zai kai k'afarta ya sakeyi mata wani cikin, shi dariya ma ta basa wato har yanzu akwai sauran k'uruciya tattare da Ramlah, wato ma a d'akin sa ne, takeyin cikin tun da anyi na farko.

Mami ya samu da maganar komawarsu Ramlah, b'ata rai tayi ta shiga balbale sa da fad'a tace ba zata koma ba sai yaran ta sunyi k'wari tukun, ganin ta ko'ina ba nasara yasa ya shirya nashi plan, Mami kuwa bayan tafiyarsa tace ma Ramlah ta fara shirye-shiryen komawa dam tasan halin d'an nata zai iya k'ara wata tabargazar dan idanunsa sun riga da sun soye tuni, yanzu Sam baya kunyarta Indai akan Ramlah ne.

Washe gari da wuri ya shigo a parlour ya samu su iya Hari suna ta faman kallo, gasu Abdool a hannunsu, gaisawa sukayi cikin sakin fuska, sannan yayi wa su Amatu wasa da sai b'angalar baki suke suna dariya Sam basu da matsala indai tumbinsu ya d'auka, junior rik'e a hannunsa yana masa surutun nasa daya iya, tambayan Mami yayi suka gayamasa tana ciki.

Mami na zaune gefen gado tana yiwa Ramlah bayanin kayan dake hannunta ita kuwa tana tsaye gun sif tana gyarawa Mami kayanta duk a kunyace take da bayanin da Mami ke mata, da eh kawai take binta shima can ciki ta maida hankalinta ga aikin da take.

Turo k'ofar yayi tare da sallama a bakinsa a tare suka amsa masa, zama yayi kan sofa yana gaida Mami, amsawa tayi tana tambayan sa aiki, gaidashi Ramlah tayi tana satar kallon sa dan ba k'aramin kyau yayi mata ba a Cikin k'ananan kayan da ya saka jean blue da shirt yellow mai dogon hannu an rubuta i'm d prince a gaban rigar da bakin penti sai zuba k'amshi yake.

Ko inda take bai kalla ba ya amsa gaisuwar tata ba yabo ba fallasa, shiru ne ya ratsa na d'an lokaci dan Mami ta aje kayan da takewa Ramlah bayani ta d'auko wata jarida tana dubawa, ita kuma Ramlah sai aikin gabanta take.

"Um Mami dama magana ce dani".

"ina jinka" tace a tak'aice ba tare data d'ago ba.

"Am dama Aure nakeso na k'ara am.." Sai yayi shiru.

Smiling tayi tare da kallon na d'an lokaci "to ai ba matsala sai kayi magana da Alhaji ko 'Yar inace yarinyar?" Ta fad'a cikin kwanciyar hankali, shiru yayi kansa k'asa "oh God I totally fail" ya fad'a a ransa, a fili kuwa yace "anan take Kaduna" a nashi tunanin idan yace haka Mami fad'a zatayi sannan ta bashi Ramlah cikin lokaci.

Ramlah Kuwa jinin jikinta ne ya daina aiki na d'an dak'ik'u, yadda maganar ta daki zuciyarta, k'arfin halin tattaro nutsuwarta tayi zuciyarta sai suya take tuni k'walla ya cika mata idanu, ji take kamar taje ta rungume shi tace ya fasa Neman auren su wuce gida Indai akan tak'i komawa ne.

"Ok ka samu Alhaji kuyi magana sai ayi bincike ko?" Mami ta katse musu tunani "tom" yace tare da mik'ewa yana kallon inda Ramlah take dan ya ga yanayin ta, ganin sai aikinta take kamar bataji me yace ba yasa jikinsa k'ara yin sanyi a sukwane ya fice.

"Ki kwantar da hankalinki kinji dota, ruba ce kawai yake ba wani Aure da zaiyi" sunne kai kawai Ramlah tayi tana murmushi, itama Mami murmushin tayi sannan ta fice zuwa parlour gurinsu iya Hari.

Bayanin komawar Ramlah tayi musu tace su shirya zasu rakata gidanta da anjima da dare, sannan ta basu labarin bazanar Abdool, cewa iya Hari tayi "kema dai Hajia ke rik'e mai mata da yawa ai dole yayi muku barazana kinsan yaran yanzu babu hank'uri" dariya sukayi gaba d'aya.

*************

8:00pm su Iya Hari suka kai Ramlah gidanta bayan Mami tasa an tsantsara mata Jan lalle da kitsonta mai kyau, ga gyaran jiki tasha sai shek'i take, susucewa su Shatu sukayi da ganin gidan Ramlah ashe na Mami nafila ne ga farilla anan, Dak'yar Mami ta tattarasu suka wuce sunata santin gidan.

Yara biyu Mami ta samo mata dan tayata renon yaran, nan suka shiga k'yalk'yale gidan da kimtsa sa, duk da dama a tsare yake dan Abdool akwai tsafta da k'amk'ami kullum cikin gyaran gidan yake, Nihal ma an kawo jiki dama tasan da dawowar dan tun rana Ramlah tayi mata waya dan kullum cikin damunta take yaushe zata dawo, zaman kad'aici ya isheta gashi Hakeem ya daina kaita gidan kullum yace bai son ana wahalar masa da baby da yawon hanya, abincin da ta shirya musu ta kawo musu nan ta bige da hira sai 9 ta koma kada Hakeem ya shigo bai sameta ba dan Ramlah tace kar ta gaya masa dawowarsu dan tasan tsaf zai iya tuntub'ar Abdool da maganar gashi surprise takeson bashi.

Sai 10:00pm ya shigo gidan dan a gajiye yake lilis yasha aiki, ko gidan Mami bai samu ya koma ba duba yaran sa, dan yanzu yayi giving up ya barsu in an gama ja masa rai ai ta dawo.

Tun a harabar gidan ya fara cin karo da daddad'an k'amshi, saida ya lumshe ido daya shiga parlour saboda yadda sanyin A'C ya had'e da wani tattausan k'amshi bai gama mamaki ba saida ya hango dinning d'auke da kulolin abinci aiko shawara bai tsaya ba ya haye ya kwashi gara, shi a tunanin sa Nihal ce da yake tana da spare ke na gidan kuma takan shigo tayi masa gyara girki kam kullum zata kawo mishi duk da kullum yake ci ba, wani sa'in da yaci a gidan Mami shikenan dan Sam bayacin abincin kasuwa k'yamarsa yake.

Saida yaji dai2 sannan ya wuce d'akin sa yayi wanka tare da shirya wa Cikin kayan baccinsa, parlour ya dawo dan rufe k'ofa, motsi ya ringa shi a part d'in Ramlah, rufo k'ofar yayi sannan ya nufi part d'in.

A parlour ya samu mai renon su Abdool tana bawa Amaturrahman madara, kallon mamaki ya bita dashi, ita kuma saurin sunkuyar da kanta tayi tana kwasar gaisuwa amsawa yayi tare da tambayan Mamansu bayan ya Amshi Amatu data koma bacci, "tana ciki" ta bashi amsa, wucewa yayi ita kuma ta wuce d'akin da aka keb'e musu.

Zaune take gefen gado tana feeding din Abdullah tasha kwalliya cikin wata fitinanniyar half sleepy gown Brown my santsi shara-shara sai k'amshi take zubawa, tsaye yayi ya jingina da k'ofar ya kafeta da kallon fitina.

D'ago wa tayi tare da sakar mai k'ayataccen smiling hadda kashe masa ido d'aya, da sassarfa ya isa gareta tare da kwantar Amatu gefe, matseta yayi yana hararanta matsa Maman yayi yana kallon ta " zaka sa ya kware ka tayar mana da rigima" tace Cikin slow voice nata.
Chapter 48 · 0% Book details