← Book details Abdulmajid Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 53

Sashe 33

Abdulmajid Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

✨ *Servant of Majesty* ✨

Na
💄 _Meryerm Abdool_ 💄

© *Pure moment of life writers*
P.M.L💪🏽

(We don't just entertain and educate we touch the heart❤ of the readers📝)

```Manzon Allah S.A.W yace da d'an Abbas:-```

_"yakai yaro ka kiyaye Allah zai kiyayeka, ka kiyaye Allah zaka samesa a gabanka, idan zakayi roko toka roki Allah, idan zaka nemi taimako toka nema gurin Allah, ka sani da ace al'umma zasu taru gaba d'aya akan su amfaneka da wani abu, to bazasu iya amfanarka da komai ba face abinda Allah ya kaddaro maka, kuma da ace zasu taru akan su cutar kai da wani Abu, to ba zasu iya cutar da kai da komai ba face abinda Allah ya kaddara maka, takardu sun bushe, an d'auke alk'alami,_tirmizih

A wata ruwa daba ta tirmizih ba cewa yayi _ka kiyaye Allah zaka samesa a gabanka, ka tuna da Allah yayin farinciki sai tunaka yayin ki'unci, ka sani duk abinda ya sameka ba'ayi shi dan ya kubuce maka ba, haka duk abinda ya kubuce maka dama ba'a yishi dan sameka ba, ka sani dukkan nasara tana tare da hak'uri, haka bakinciki yana tare da farinciki, kuma dukkan tsanani yana tare sauk'i_ ( Arba'una Hadith).👌🏻

*😘 k'anwata Jannart lamed'o ki sani kina raina kullum, bazan mantaki ba koda kuwa ke kin mantani ne😁 #ana mugun tare iya wuya# 🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀*

📝 *Episode* 186--190

"What nonsense u done here Nusaiba?" Dr Ma'aruf ya fad'a cikin tsawa yana fitowa daga theatre room d'in.

"Sorry sir" ta fad'a cikin tsoro, "get out in my sign, ki jira query dan bakisan aikinki ba" sum2 ta fice cike da fargabar abinda zai faru, umarni yabayar na d'aukar Dr Majeed sannan yaje gun Mami dake tsaye kamar an dasa jikinta sai rawa yake kamar mazari, Allah ya tsare yaron bai fad'i ba.

"Mama don Allah ki kwantar da hankalinki kada abun yayi yawa, dukkan rai bata wuce lokacin ta, don Allah ki zauna, barin duba Dr" babyn ya ansa tare wucewa d'akin da aka shiga da Abdool.

Taimakon gaggawa ya shiga bashi cikin 'yan mintuna ya fardad'o da sunan Allah a bakinsa, sannan a hankali ya fara bud'e idonsa ganin d'akin da yake ciki ya tabbatar masa ba makarki yake ba komai ya faru da gaske kenan, sauke idonsa akan Mami dake gefensa yayi, sai Dr Ma'aruf dake tsaye Kansa, bakinsa ne yayi masa nauyi yana son magana amma ya kasa sai bakinsa dake motsi, hannunsa Mami ta kama "ka daure Son" shine kawai ta Iya fad'a, saboda yanda zuciyarta ta tsinke, tasha ganin mutuwa kuma tasan zafin mutuwa saidai wannan akwai tausayi a ciki musamman ma jaririn da d'anta su tafi tausayawa.

"Mami na daure fa kikace kina nufin, da gaske Zainab ta tafi ta barni da tabar jaririnta?"

Dr Ma'aruf ne ya dafashi tare da bubbuga masa kafad'a "Abokina kada ka mantafa kaine mai bawa wasu hak'uri da nuna musu yadda da k'addara idan sukayi rashi, kayi hak'uri Addu'arku kawai tafi buk'ata yanzu"

"Hakane Dr Ma'aruf, na yadda da k'addara kuma na yadda kowace rai bata wuce lokacinta, Zainab inshaa Allah ke 'yar Aljannace, ke matar kirki ce, ke mai addine, ina miki kyakkyawan zato, Allah yasa mutuwa ta zamo hutu a gareki Allah ya arbarkaci abinda kika bari" sai hawaye kebin fuskarsa kaman fanfo, haka Mami, Dr Ma'aruf ma saida ya zubar da nasa hawayen gwanin tausayi.

"Dr ina abinda aka Ciro" yace ganin ba baby a d'akin, "yana hannun nurses bari na karb'oshi" dawowa yayi tare da babyn, ansarsa Abdool yayi tare da kafesa da ido, tuni k'auna da tausayin yaron suka rufesa, sai bacci yake abinsa, baisai mai ake ciki ba, maganar Zainab ya tuna.

_Dr pls idan namiji na Haifa ka maida mishi sunanka, idan kuma mace ce, ka saka mata sunan Aunty Ramlah_

Wasu hawaye ne suka zubo masa yasan yayi rashin mai k'aunarsa da gaskiya mai son duk abinda yakeso, hud'uba yayima yaron da _Abdulmajid_ sannan ya mik'a shi ga Mami, "Dr Kaine gurin Gawar Zainab" yace tare da sakkowa.

Addu'a sosai yayi mata, yana hawaye ganin ta a kwance kamar me bacci amma kuma ba barcin duniya bane.

_Duniya! Bakida tabbas_ 😭

Wani envelope Dr Ma'aruf ya bashi yace Inji marigayiyar ta bayar a bashi, ansa yayi sannan suka d'auki gawar zuwa gida dama tuni Mami ta kikkira kuma duk sun taso don samun jana'izar.

***************

Wasik'u ne guda 3 cikin envelope d'in, ta sama a rubuta zuwa ga mijina, bud'ewa yayi ya fara karanta wa.

_"Amincin Allah ya tabbata a gareka mijina, nasan koda wasik'ata zata sameka, watak'il bana numfashi a duniya, kayi hak'uri da rashina inada tabbacin Aunty Ramlah zata maye maka fiye da gurbina, addu'arka nafi buk'ata a yanzu mijina, naso ace na rayu a dai2 wannan lokaci da nake buk'atarku saidai Allah yafimu sanin gaibu, naso na rayu koda na minti gudane da abinda na Haifa naso naji duminsa shima yaji nawa, ina rokonka daka zame masa uwa da uba dan Allah karka barshi ya koka da rashina kaida Aunty Ramlah, ina muku fatar Alkhairi, sannan ka sani ina k'aunarka har numfashina na k'arshe, ka bawa aunty Ramlah wasik'arta a ranar da ta tare gidanka, d'ayar ka bawa iyayena, pls kazo ga gawata ka wankeni kamin sutura sannan ka sadani da gidana na gaskiya, nagode da k'aunar da ka nunamin a iya zaman mu mijina_

Zainab Salis.

Sanda ya gama karantawa hawaye kwance a idonsa, yana tuna rayuwarsu da Zainab tun daga ranar da ya fara saninta har yau data barshi, bari na har abada, murmushi yayi irin na k'unci "ina miki fatar Alkhairi Zee ta".

Kamar yadda ta buk'ata shi yayi mata wanka da sutura, cikin ikon Allah natsuwa ta saukar masa, sai addu'a yake mata har ya kammala.

Tuni gidan Mami ya cika da mutane masoya da mak'ota sai zuwa suke ta ko'ina haka abokan Abdool su Hakeem duk sun zanzo duka ma'aikatan asibitin sunzo maza da mata dan itama Zainab can take aiki.

Flight mutan sokoto da Kebbi suka biyo ciki kuwa hadda Ard'o, bayan sallar La'asar aka sallaceta aka sadata da kushewarta.

Iyayen Zainab duk da sunji mutuwar 'yar tasu saidai sunyi farinciki yadda ake yaba kyawawan halayyarta musamman mijinta, sun San ta dace dan duk maccen da mijinta ya koka da rashinta ya kuma yaba halayyarta bayan bata ana mata kyakkyawan zato.

Bayan anyi addu'a uku da zasu wuce sun so wucewa da babyn saidai Mami tace a barshi anan zata kula dashi da tsakani da Allah, basu Musa ba saboda sun san zata iya kamar yadda ta kula da uwarsa, dan sunajin labarin kirkinta a gun 'yarsu.

Ranar suna ba wani taro da akayi yanka kawai akayi masa tare rad'in suna kamar yadda sunna ta tanadar a masallaci akayi, Inda su Husna sukayi masa inkiya da junior, dukkan kulawa junior na samunta ga ingantattun madara wad'anda zasu taimaka masa da Abdool ya siyo masa saidai ko yayane basuyi ya maman uwa ba, kullum Abdool ya kallesa tausayinsa ne ke rufewa dan yasan yayi rashi.

Tarraro duk wani mahimmin abu da yake buk'ata yayi na gidansa ya dawo gidan Mami tsohon d'akin sa dan bazai iya ci gaba da zama gidanda yayi rayuwa da Zainab ba, bayan bata a doron k'asa.

*****************

B'angaren su Ramlah kuwa wasa-wasa Uncle Lukman ya sakota gaba ya takura mata, ta rasa ya zatayi dashi tana tsoron ta gayamasa matar Aure ce a samu matsala yakai report a koreta, daga k'arshe dai ta yanke shawarar in Abdool yazo visiting zata gayamasa kawai.

Sadee kuwa ta saka Nihal gaba ita Ya Abdool yakeso ta yadda taje ata biyu, Nihal dai cewa tayi tabar maganar kuma kada ta bari Ramlah taji data tambayeta dalili tace tadaiyi shiru kawai.

Hakan yasa ta shiga tunanin dalilin Nihal na fad'ar tayi shiru tunawa tayi da kallon da taga yana yiwa Ramlah ranar da sukazo musu da "oh no wonder soyayya suke kenan shiyasa komai zatayi tace ya Abdool kuma aiba biological sister nashi bace, idan ko hakane dole na lahe dan bazan iya breaking heart d'in Besty ba" da wannan tunanin tabar zancen kuma ta daina mata zancen uncle Luku.

Haka ranar visiting tazo su Ramlah basuga kowa daga gida for d first time da suka rasa visiting duk da basuda matsalar komai, saidai hankalinsu ya tashi sunaji ba lafia ba, Sadee CE ta ringa kwantar musu da hankali, akan kila wani uzirin ne ko kuma kila Aunty Zainab ce ta haihu.

Sharewa kawai sukayi amma idan haihuwace aiya kamata a gaya musu, koma dai meye zasuji idan sun koma tunda an kusa Hutu..

Ranar da suka koma gida sukaji mummunan labarin Rasuwar.........

_still in sick ur pray is needed my Fans_
🤢😔

💄Meryerm Abdool💄
[9/23, 8:51 PM] 💄Meryerm Abdool💄: 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬
🖤 ```ABDULMAJEED``` 🖤
🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬

✨ *Servant of Majesty* ✨

Na
💄 _Meryerm Abdool_ 💄

© *Pure moment of life writers*
P.M.L💪🏽

(We don't just entertain and educate we touch the heart❤ of the readers📝)

Ga shafukan mu nan da zaku ringa samun k'ayatattun novel namu👇🏻

*#[email protected]*
*#IG PML WRITERS*
*#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
*#http://maryamsbello.blogspot.com*

```An karbo daga shugaban mummunai, uban hafsy umar bin khattab (A.R) yace:- naji manzon Allah (S.A.W) yana cewa```

_"dukkannin aiki baya yiyuwa saida niyya, kuma kad'ai abinda mutum ya kudurce a ransa yake samu, Wanda yayi hijira domin Allah da manzonsa to hijirarsa tana ga Allah da manzonsa, wanda kuma yayi hijira domin duniya da k'alek'alenta ko kuma wata matar da yakeso ya aura, to hijirarsa tana ga abinda yayi dominsa._ ingantaccen hadith ne daga sahihan nan Bukhari da musleem.
(Arba'una hadith).

📝 *Episode* 191-195

Ranar da suka sukayi Hutu suka koma gida sukaji mummunan labarin Rasuwar Aunty Zee ba k'aramin girgiza sukayi ba, sunyi kukan rashinta dan Aunty Zee ta zama wani b'angare nasu, sunji mutuwar matuk'a dan kusan itace mutuwa mafi kusanci wacce suka ji da girmansu, tunda koda akayi wad'ancen basu da wayau.
Chapter 33 · 0% Book details