← Book details Abdulmajid Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 53

Sashe 10

Abdulmajid Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dariya sosai Hakeem yayi har saida Abdool ya nuna b'acin ransa sannan ya saurara.

"Aure fa kace dude! Kuma in a week, common kace u r joking, hw come wane irin aure kenan?"

Tab'e baki yayi "koma me zakace, I don't care, nidai nasan Aure zanyi kuma a satin nan, that all I know" ya fad'a tare da daga kafad'a.

"Tau naji Amma dai ba wancen yarinyar ba ko?"

"Ha'ah see u se trouble meye naka a ciki, ina nine me Aure ko, kai naka ido ne kawai, so put ur eyes and shout ur mouth".

Dafasa yayi saboda yaga da gaske ransa ya baci, " cool down! Nifa abin mamaki ne yake bani kawai, kuma naji kace yarinyar is too young" danshi bai tab'a ganinta ba.

"Hmm ai Kaine da abin haushi, na gayamaka dalilin auren nan, ba zuwa zamuyi mu zauna zaman Aure ba, ita Kanta nasan batasan ma me auren ke nufi, Hmmm kuma ai tayi k'ank'anta ba zata iya dani ba" ya fad'a ya shafo sajensa daya kwanta lup.

"Shegen kaya! Wlh bakaji Dr, kai killer ne in silent way, baki kawai na fika".

Smiling din gefen baki yayi "kaga ni ka tashi muje, time is going" tare suka fita gwanin Sha'awa, suka Lula zuwa Argungu.

A can d'imma ba'a samu matsala ba sunyi na'am da da abin da yazo dashi, Innah hadda tsokanarsa wai daga zuwa Har da yi mata kishiya, saboda yanzu ya daina yinta sai ta had'a shi da Ayatul kursiyyu yace ya fasa.

Dariya yayi yace kada ta damu zai bata eating noise, nan dai sukayi ta barkwancinsu sai marece suka koma Sokoto.

Washe gari sukaje Kilgori tare da Alhaji da Hakeem, Ardo ya tarbesu cikin karamci da mutuntawa kuma yaji dad'in ganin Alhajin hakan ya nuna yaron d'an gidan girma ne.

Amininsa Malam Garba kawai ya kira ya tabbatar da ya bawa Abdool, Ramlah ya dawo nan da sati d'aya a d'aura musu Aure, kuma baya buk'atar komai face sadaki.

Godiya sosai Alhaji yayi masa da wannan Karamcin da yayi musu, sannan yace yayi hak'uri amma zasuyi komai da akeyi a al'adance saboda itama a nuna mata 'yace kamar kowa, Ardo yaso su barshi kawai amma Alhaji ya nace shi zaiyi komai, dole ya Hak'ura amma da sharadin komai sai ranar Auren za'ayi, anan take suka bada kud'in nagani inaso dana gaisuwar iyaye, haka dai suka rabu cikin farinciki kowa na ganin karamcin d'an uwansa.

********************

"Ramlatuna!" D'agowa tayi ta kallesa k'irjinta na dukan Tara2 dan tunda Baffa ya kirata taji, gabanta na fad'uwa "na'am Baffa" ta ansa cikin siririyar murya.

"Ke yadda ina k'aunar ki?"

"Baffa ba Wanda yaka k'aunata duk duniya baya gareka".

Murmushin jindad'i yayi " yawwa Ramlatuna tunda harke yadda bani cuta miki, inason sanar dake inshaa Allahu, juma'a mai zuwa za'a d'aura miki Aure".

"Aure baffa!" Kalmar da ta fito bakinta kenan cikin firgici da zaro ido.

"Ko bakison Auren ne Ramlatuna?"

Girgiza tayi alaman aa dan ita bamasan maganan ta fito fili ba "Baffa nasan Bazaka cutar dani ba, Allah yasa hakan shine mafi Alkhairi".

" Ameen Ramlatuna, inshaa Allahu zakiyi hwarin ciki da wanga Aure, da yadda Allah k'arshe k'arshen wahalarki ya zaka, sannan kiyi shiru kakki hwadama kowa kinji?"

Kai ta daga masa "yawwa 'yar Albarka tashi ki tahi Allah yayi miki Albarka".

" Ameen " ta fad'a tare da fita jiki a darare ba k'wari...

B'angaren Mami ma sai shirin zuwa takeyi, tunda Abdool ya kira ya gayamata an tsaida magana sai shiri take sosai, amma sai ana gobe aure zata zo...

"Mutumina wai sai yaushe za'a buga I.V kaga fa lokaci sai k'urewa yakeyi".

"Kaidai ka cika neman rigima wlh, ai sai kaje kaita bugawa" ya fad'a tare da juya masa baya.

Dariyar ciki yayi, "Yawwa wai ka gayama Zainab kuwa?"

"Oh! Allah wlh shaf na manta, abubuwa sun sakani a gaba" ya fad'a bayan ya tashi daga kwancen.

"Wo sabon Ango duk rud'un bikin ne".

" kaji dashi, magulmaci" yana gama fad'a ya bar parlour gaba daya, da murmushi ya bisa "wannan yarinyar ta rikita min Aboki da yawa".

Bedroom ya shiga tare da zanyo wayansa ya kira Zainab, yasan zataji ba dad'i amma gara taji a bakinsa da taji wani gun.

Bayan sun gaisa nan yake gayamata maganar Auren nasa, dif taji ta daina ji, wani k'olulun bakin ciki ne ya tokare mata mak'oshi cikin rawar murya tace.

" Allah ya sanya Alkhairi "ta fad'a kawai tare da kashe wayar gaba d'aya, dama yasan za'ayi haka amma toya zaiyi, gara ya gayamata gaskiya taji Haushinsa a lokacin zuwa gaba tasan bai yaudareta ba daya rufe dan tayi farinciki zuwa gaba ta gane yaudaranta yayi(komai zakayi da mutum ka tsaya akan gaskiyarka, dan k'arya fure take bata 'ya'ya, gaskiya kuma dokin k'arfe Allah yasa mudace).

Kuka takesonyi amma yak'i zuwa, lallai ta tabbatar Dr Majeed baya sonta, har iya fad'a mata, zaiyi Aure, shikenan ta yayi mata nisa, nisan da bazata iya cimmasa ba, juyi kawai takeyi duk duniya tayi mata zafi, lallai rashin masoyi bala'i ne.

Tana haka ne ilham k'anwarta ta shigo wai tayi mata assignment, hantararta tayi tare da cewa tafice ta bada guri, kota takata anan, aiko a guje ta fita tana kuka dan bata tab'a mata irin haka ba.

Ganin tana kuka ne yasa Momyn su ta tambayeta meya faru, ta gayamata Zainab ta korota.

"Zainab kuma Ilham? Me kika mata" dan tasan yadda takeda sauki ga k'anninta.

"Banyi mata komai ba Momy, nadai ganeta kwance ranta a bace" mik'ewa kawai Momyn tayi zuwa d'akin Zainab.

Harta zauna daf da ita batasan tazo gurin ba, saida ta d'ora kanta kan cinyarta tana Shafa mata kai alaman rarrashi sannan tasan da zuwanta, fashewa tayi da kuka kamar ita take Jira "Momy na rasashi, shikenan na rasashi".

" Haba Zainab ki idan hankali ya gushe hankali ake sakawa ya nemosa, d'aure kiyimin bayani yadda zan fahimci abinda ke damunki" duk taji a jikinta bazai wuce Dr Majeed bane.

Saida ta gama kukanta, da sai yanzu yazo, uwar bata hanata ba sannan ta gayamata abinda ya faru.

Sosai ta tausayawa 'yar tata saboda tasan yadda takeson Abdool, sai dai bata nuna mata ba, saboda kada tasa ta k'ara karaya.

Cikin taushi da rarrashi ta shiga bata baki "kiyi hak'uri Zainab dama ita duniya haka take bafa komai da akeso ake samu ba a rayuwa, sannan duk abinda kikaga ya kub'ucewa mutum to dama ba'a k'addara zai samesa ba, kuma duk abinda ya samu mutum, dama ba'a k'addara zai kub'uce masa ba, dan haka ki kwantar da hankalinki idan da rabon Aure a tsakaninku sai kiga yazo har gida ya aureki, kedai ki dage da Addu'a da Neman zabin ubangiji".

Lafewa tayi jikin Momyn nata tana ajiyan Zuciya, sosai jawabin uwar tata ya ratsata tana k'ara godewa Allah daya azurtata da uwa ta gari mai maida ita kan seti idan ta juye(Allah ka k'ara ma iyayenmu baiwa da fasaha, ka k'ara muna k'aunar su da kyautata musu ameen, mungode da ni'imar iyaye na gari).

Saida ta tabbatar ta samu nutsuwa sannan ta fito ta barta.

Ana saura kwana biyu Aure Laure duk abin duniya ya mata yawa ita dai tasan bata murna da wannan aure haka kuma bata bak'in ciki dashi, ga rashin Aboki mai glass, tun ranar bai k'ara dawowa ba, dan ranar da sukaje bata nan.

Kilama Baffa cewa yayi kada ya k'ara dawowa saboda zaiyi mata Aure shiyasa ta ganshi wani iri a ranar, gashi za'ayi Aurenta ba tare dasun k'ara had'uwa ba, wata kila sai lahira ji kawai tayi tana hawaye, da sauri ta share kada wani ya ganta dan Iya Hari da Gwaggo Lanti, tsakar gidan, taci gaba sharan turken dabbobin da take yi.....

Iya Hari kuwa da basusan meke gudana ba sai nanayensu Suke ita 'yarta, Ardo ne ya shigo bayan sunyi mishi sannu da zuwa daga can zaune, k'arasawa yayi inda Suke hannu ya zura aljihu ya zaro kud'i ya bata.

Nan da nan ta Washe jajayen hak'oranta "Malam wanga kudd'i na minana?"

"Auren Ramlatuna, gobe idan Allah ya kaimu" ya fad'a mata kai tsaye.

Cikin zaro ido da masifa "Aure? Wa zata aura?"..................

_pls kuyi hak'uri da juna shiru da kukayi hakan ya farune akan rasuwar da akayi mana_ 😞

💄Meryerm Abdool💄
[7/29, 9:10 PM] 💄Meryerm Abdool💄: 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬
🖤 ```ABDULMAJEED``` 🖤
🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬

✨ *Servant of Majesty* ✨

Na
💄 _Meryerm Abdool_ 💄

© *Pure moment of life writers*
P.M.L💪🏽

( We don't just entertain and educate we touch the heart❤ of the readers)

❣❣❣❣❣❣❣❣❣❣
```ina kuke masoyan Abdulmajeed, ga shafinku, ina matukar kaunarku a duk inda kuke Allah yabar kauna.```
❣❣❣❣❣❣❣❣❣❣

*Yan uwa masu yimin ta'aziyya, da masu yimin sannu da jiki, nagode sosai da kulawarku, Allah ya barmu tare nagode bunch of love#❣#*

📝 *Episode* 76--80

"Gara ma kace ba'a ta kakai, dan bai tab'a yuyu ayima Laure Aure gobe, ni kuma a hwadamin yau, sai kace ban da had'i da ita, kuma ai Laure da mijinta" shidai Ardo ido kawai ya zuba mata.

"Nasan ko Jauro dani yaka magana bada kai ba, ni nibbashi Laure ba kaiba, to k'ak'a akai mata Aure gobe ace sai yau zan sani, ai wanga maganar banza ta" duk cikin d'aga murya da masifa take magana, ganin ta dasa aya, murmushi yayi.

"Hmm khadijatul kubra kenan" ya kira Iya Hari da anihin sunanta "kamar yadda na fad'a gobe da izinin Allah za'a d'aura wannan Auren ba hwashi, danni adda ikon aurar da Ramlatu, maganar kin tsayar mata da miji ko minana ma, ke kissani kuma ke yashahwa, bakida hurumin tsayarwa da Ramlatu miji, wadda baki k'auna, taya za'ayi ki zabar mata miji na gari? Kina tunanin bansan komi da kukeyi ba, ina sane nadai tsaya naga iyakar gudun ruwanku ne, daga ke har ita lantana nasan baku k'aunar Ramlatu saboda hauka irin taku, kullum tunaninku yaya zakuyi Ku ganta cikin k'unci shine tunaninku, toshi zakaran da Allah ya nufa da cara ko ana muzuru ko ana shawo to sai yayi" cikin kwanciyar hankali ya shiga zare musu magana kai ba kace cin mutunci yake musu ba.
Chapter 10 · 0% Book details