← Book details Abdulmajid Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 53

Sashe 24

Abdulmajid Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abdool kuwa zame jiki yayi ya kira Maminsa dan yanzu network a kilgori har d'akin ka, bayan ta daga ne sun gaisa yace.

"Mami yau naga wani bak'on Al'amari".

"Meya faru Abdool?"

"Hmm Mami zakiyi farinciki da abinda naji yau, nasan har tukuici zaki bani".

"Oh nikam meye wannan fad'amin mana".

"Mami maganar tafi k'arfin a fad'eta gani yafi, ki shigo mota yanzu ki ganema idonki".

"To ai bansan gurin ba matsalar".

"ki taho yabo daga kin iso kimin waya zanzo na d'auke ki"

"OK" kawai tace dan ta k'agu taga meye wannan da baya fad'uwa, shima da sauri ya koma saboda jin an fara Hudubar juma'a....

********************

Delu ce ta gifto ta masallaci ta fito da gida gurin d'akko kayanta, dai2 lokacin taji mai shela na fad'in "madallah aure ya dauru an d'aura Auren *Abdulmajeed Auwal da Ramlah Abdulrahim* kan Sadaki naira dubu 50k, lakadan ba ajalan ba fatar Allah ya d'aure ya basu hak'uri" tanajin haka cikin farinciki ta kwasa da gudu sai gidan Gwaggo Shatu tana haki tana fad'in.

"Laure Ashe dama dan binni ne mijinki, shine kika k'i hid'imana" Ramlah cikin tsananin kad'uwa ta kalleta dan son tabbatar da maganar daga bakinta take fitowa.

Gwaggo Shatu ce ta dafata tare da girgiza mata kai alaman gaske ne, da yake ita tasan komai, sauke idonta kasa tayi tama rasa gane yanayin da take ciki, jinta take kamar ba ita ba kuma kamar mafarki takeyi.

Gwaggo Shatu ce ta mik'ar da ita tsaye tare da Kama hannunta janta zuwa d'akin ta, wani hadd'ad'en material ne milk color anyi mishi ado da fulawowi coffee color, lallausa dashi sai k'amshi ke tashi Ard'o ne ya dinka mata, Cikin sa Shatu ta shirya ta tare yi mata kwalliya mai kyau irin ta 'yan binni, mayafi coffee da shoes coffee suma wow Masha Allah zanso Ku hango Laure a kwalliyar dama gata mai kyau ce.lol ba Irina ba

A can masallaci ana maga d'aurin Aure, Abdool yaji vibration din k'aramar wayarsa dake cikin aljihu, sallat ya zare jikinsa ya fice, Maminsa ce ke kiransa ta iso yabo, hakan yasa bai tsaya ba yaja mota zuwa d'auko ta.

Jauro kuwa Wanda kamar an aiko sa yau ya halarci sallar juma'a Wanda salla sai tayi masa suger yakeyi, cikin kaftan kamar mutumin arziki, bayan an gama salla yaji ana sanar war za'a d'aura aure har zai tafi kuma sai ya tsaya, abinda kunnensa ya jiyo masa ne yasashi dask'arewa nan wai Laurensa aka aurawa wani, ihu yayi iyakar k'arfin sa Wanda ya janyo hankalin jama'a cikin d'aga murya yace.

"Kan ubanga waiisa ya Armi Laure bayan ni, kai liman maza warware armen nan dan bai d'auru, ni kad'ai ne mijin da zai Armi Laure, dan tawa ce nid'ai" sai sambatu yake, mutane kuwa sai kallonsa suke, 'yan gari kam basuyi mamaki dan sun san waye Jauro.

A hankali Ard'o ya tako zuwa inda yake, "Lamiru" Ard'o ya kirashi da asalin sunan shi, kallon shi yayi tare da ansawa dan duk iskancin Jauro yana shakkar Ard'o, duk zuwa gidansa da yakeyi sai tabbatar bayanan.

"Na tab'a alk'awarin baka Ramlatuna koda da rana guda ta?"

Girgiza kai yayi tare da cewa "Aa" murmushi Ard'o yayi.

"Madallah, to ni adda hakk'in armar da Ramlatu ga Wanda nikaso kuma Lokacin da nisso, kuma gashi nayi, dan haka kama gabanka kuma kar in sakejin ka taka gidana" babu gardama ya juya tare da ficewa daga masallacin tare da k'udure haduwarsa da Iya Hari ba kyau.

Duk Wanda ke cikin masallacin abinda Ardo yayi ya burgeshi, dama sun san shi kad'ai ne maganin Jauro da d'iyar wani daban ce da Allah kad'ai yasa yadda zasu k'arke.

Bayan komai ya lafa ne aka dunguma zuwa masauki saidai koda aka duba Abdool babu shi, haka suka koma Wanda zuwansu yayi daidai da isowar Gwaggo Shatu da Ramlah da Ard'o yace suzo bayan D'aurin Aure, tun da Baba ya ganta zuciyarsa ta bashi itace Ramlah dan ga yanayin Asma'u a tartare da ita duk kuwa da basa kama, tafiyar su tsayuwa duk iri d'aya haka yanayin jikinsu saidai ita tafi Asma'u tsayi tun yanzu da take yarinya kuwa.

Itama tana ganinsu saida k'irjinta ya harba, ciki suka shiga gaba d'aya.

"Malam Abubakar ga Ramlah nan" kallon yayi tare da cewa "zonan 'yata" ba musu taje ta tsugunna a gabanshi Kanta k'asa.

"Ba shakka wannan 'yar Asma'u nah ce, wannan jinina ce"cikin firgici ta d'ago ta kalleshi jin ya ambaci sunan umminta, saidai me kama taga yanayi da Umminta duk da foto kawai ta Santa amma tabbas suna kuma ga abinda taji yana fad'i.

Kallon tambaya tabi Ard'o dashi " tabbas Ramlatuna duk Wanda ya dogara ga Allah to zai Isar masa, kuma akai hak'uri akan tabbas zai wuce akai ga nasara, lokacin da muke tunanin da yanke tsammanin ganin dangin mahaifiyarki sai gasu Allah ya kawo mana har gida".

Sannan yaci gaba, "kinga ikon Allah ko, wannan shine kakanki mahifin Asma'u" ya nuna Malam Abubakar, "wannan kawun kine, k'anin Asma'u" ya nuna Mansur, "wad'annan dangin mahaifin Abdoolmajeed ne" ya nuna su Alhaji.

"Kuma wani abin jin dad'i Abdoolmajeed yayanki ne na jini Ramlatuna d'an Innarki Ameena ne" hawaye kawai ke fita daga idonta tsabar farinciki tama k'asa magana......

***************

Tunda ya d'auko ta take tambayan sa ya gayamata menene hak'uri kawai yake bata tare da cewa ta kwantar da hankalin ta Alkhairi ne, kuma yanzu zata gani, hakan tasa taja bakinta tayi shiru taga inda zai kaita, daidai k'ofar shagon yayi parking tun kafin ya kashe motar ta fito.

Cikin shagon tasa Kanta saboda yadda taji k'irjinta na bugawa, bayan kawai take kallo tana tsugunne gaban Babanta ta bata baya, Sam bata kula da wad'anda ke Cikin shagon ba, Kanta tayi gadan gadan.

"Asma'u nah!"......

💄Meryerm Abdool💄
[8/18, 5:45 PM] 💄Meryerm Abdool💄: 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬
🖤 ```ABDULMAJEED``` 🖤
🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬

✨ *Servant of Majesty* ✨

Na
💄 _Meryerm Abdool_ 💄

© *Pure moment of life writers*
P.M.L💪🏽

(We don't just entertain and educate we touch the heart❤ of the readers📝)

_A sanadin *HAD'UWATA DAKE* nayi tunanin *WATAN WATA RANA* ni *ABDULMAJID* zan ciri tuta, saidai ina tsoron na shiga musiba kamar yadda *A DALILIN PRE-WEEDING PICS* wasu suka shiga matsala (my next novel inshaa Allah)_

*ina kike k'awata ta kaina, 'yar mutan Niger Raheenat mohmodou, Allah ya barmu tare ya kuma raya mana Nana khady😘*

_Momyn zee, Aysha D na fahimci kuna k'aunar sakwatanci to kuyi cooling zan koya muku😝, wallah kuna k'aunar Abdulmajeed nima ina yinku😘_

📝 *Episode* 141--145

Kallon kallo suka shiga yiwa juna cikin mamaki, "lallai Allah mai girma na, tabbas badan nasan Ummina mutuwa tayi ba, ba Wanda ya isa yace wannan matar ba itace ba wanga irin kama ta b'aci" Ramlah take fad'a a zuciyarta.

Itama Ameena fad'i take a ranta" wannan ba Asma'u bane, amma behaviors d'in Asma'u kaf irin nata amma basa kama wacece wannan" Baba ne ya bata ansa kamar yasan me take sak'awa "Ameena 'yarki ta, d'iyar Asma'u ce, jininta ce".

Jan Ramlah tayi zuwa gaban Baba " Baba ina Asma'u nah idan wannan 'yarta ce?"

K'wallar da ta taru idonsa ce ta zubo, kafin tace wani Abu Ard'o yace " 'yata Ameena saidai mu d'auki hak'uri" muryan sace ta ganar da ita da mutane a gurin "Kamar ya Baba?" Ta tambaya cikin son jin meke faruwa.

Nan fa labari ya dawo sabo, koda aka gama gayamata hawaye sun gama wanke mata fuska, "Allah sarki Asma'u ashe ba rabon mu sake had'uwa Allah ya had'a fuskokin mu a Aljannah don rahamarsa" Ameen suka ansa daga ta shiga gaida iyaye dake gurin sannan su Hakeem suka gaida ita.

"Zo nan 'yata Ramlah zo kiji domin uwa wanda kika rasa, daga yau baki ba maraicin uwa da yardar Allah" tare da ware mata hannayenta, cikin nutsuwa taje gareta tare dayin lup a jikinta wata sansanyar ni'ima na ratsata wacce bata tab'a tsinta a Cikin rayuwarta ba, lallai uwa rahama ce, dangin uwa ma rahama ne (duk Wanda yayi nasarar rayuwa da uwarsa ya godewa Allah)

Duk Wanda ke Cikin shagon sunyi matuk'ar bashi tausayi musamman yadda Ramlah ke sauke heart, Abdool dake tsaye bakin k'ofa ya rungume hannayensa a k'irji sai kallon su yakeyi, wani farinciki yakeji burin Maminsa ya cika kullum maganar ta kenan K'anwarta Ameena, yau gata ga d'iyar Ameena, gyaran murya yayi tare da Wanda yasa hankalin mutanen ya dawo kansa karaf idonsa ya had'e dana Ramlah wacce ta d'ago, dama shi ita yake kallo tayi kyau abinta kamar ba Laure ba, inji 'yan garin.

Kallonsa take bata ko kiftawa tsawon sati biyu rabon ta dashi, har ta d'auka sun rabu kenan, Ashe yayanta ne, Ashe shine mijin da Ard'o ya zaba mata, oh yau ina zata saka kanta don murna gata ga dangin mahaifiyarta, ga d'an binni mai glass a matsayin Yayanta kuma mijinta......

Ard'o yace "shigo ciki koni Abdulmajeed, kayi tsaye ga kulkin kohwa"

Murmushi ya sakar mata Wanda yasa tayi saurin sunne Kanta k'asa, shigowa yayi ya zauna kusa ga Alhaji Sada.

"Tau Alhamdulillah mashaa Allah dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah, daya nuna muna wagga rana mai cike da Albarka da farinciki, Abdulmajeed bakada buk'atar ince zan baka Amanar Ramlatuna, k'aunarka ta kuma matarka nasan zaka aza bisa inda nittsaya (zaka d'ora inda na tsaya).

Sannan yaci gaba da cewa " haka kema 'yata Ameena su duka d'iyanki na Allah ya baki ikon rik'o, Ramlatuna" ya fad'a yana dubanta jiki a sanyaye tace "na'am Baffa".

"Ke d'iyata ta gari mai hak'uri, karki canza daga halinki na kwarai da nissanki kici gaba dashi, gida zakina ba daji ba inda 'yan uwanki na, zakina don Allah Ramtuna kici gaba a yadda nissanki Allah ya arbarkace ku gaba d'aya" tuni idanunta suka kawo k'walla duk son da take na had'uwa da dangin ummin nata, gata kuma gaban su a yau amma kuma sai taji batason rabuwa da mahaifarta batasan rabuwa da Baffanta mai k'aunarta, shi kanshi Ard'o daurewa kawai yakeyi amma yasan zaiyi kewar Ramlatunsa...

Mami CE ta share mata hawayen da zuka zubo mata tare da bubbuga mata baya.
Chapter 24 · 0% Book details