← Book details Abdulmajid Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 53

Sashe 2

Abdulmajid Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ameen Maamii" ya fad'a sannan yace "my guy missing u" yace tare da rungumesu, suma rungumesa sukayi sukace "missing u too bro.

Dak'ar suka rabu yaja car d'insa cike da kewar familyn ya d'auki hanyar birnin Shehu..........

_wasa farin girki muje zuwa friends_ 🏌🏽⛹🏾‍♀

💄 Meryerm Abdool 💄
[7/2, 11:55 PM] 💄Meryerm Abdool💄: 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬
🖤 ```ABDULMAJEED``` 🖤
🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬

✨ *Servant of Majesty* ✨

Na
💄 _Meryerm Abdool_ 💄

© *Pure moment of life writers*
P.M.L💪🏽

```Manzon Allah (S.A.W) yace:-```
*Yana daga cikin kyawawan dabi'un musunci mutum yabar abinda bai shafesa ba.*

( _Tirmizih da wadansu suka ruwaitoshi, daga hadisai arba'in_ )

📝 *Episode* 1⃣1⃣⏩1⃣5⃣

Saida ya biya ta Unguwar Rimi ya d'auki friend d'insa Hakeem Wanda shima a Skk zaiyi horsemanship nashi saidai shi pharmacy ne, t'uki yayi cikin Jean vitae hankali suna tafe suna sauraren wak'ok'in larabawa na *Mishary Raseed Alfasy* dama Abdool ba rigima, tun Hakeem na mitar t'ukin har ya hak'ura dan ba yadda ya iya da mutumin nasa, gashi shi yace bazaiyi driving ba, dole ya bisa a yadda yakeso.

Basu suka isa ba sai after ishaa, direct family house nasu suka wuce, estate ne guda, mai d'auke da compartment 5 mafi girma daga ciki naga sun dosa, direct main parlour suka sauka.

Da sallama suka shiga, wani dattijone zaune kan kujera, ga wasu samari gefensa alaman magana suke dukkansu kusan tsaran Abdool ne, cikin farinciki suka juyo yare da ansa sallamar, tasowa sukayi suka rungume Abdool da Hakeem tare da fad'in.

"Ur highly welcome home bro" sannan sukayi musabaha, shima cikin murmushi, yace "fatar na sameku lafia?"

"Alhmdllh" suka fad'a tare da k'arasawa gurin dattijon gaba d'aya, fuskarka d'auke da murmushi ko ba'a tambaya ba kasan yana farinciki da zuwan jikan nasa.

Kan hannun kujerarsa Abdool ya zauna tare da rungumesa yace "tsoho mai ran k'arfe kaga jiya kaga yau."

"Zanga gobe da yardar Allah kuma, likkita bokan turai yau kaina a sakkwato?"

"Sharri kayan kwalba, sai yau ka saba ganina a sokoton?"

"Kai bature kada ka wayance yaushe rabonka da garin?"

Sudai samarin da Hakeem sai kallon drama suke suna dariya babu mai barin ta kwana cikinsu.

Saida suka gama rigimarsu sannan aka gaisa.

"Abdulmajeed ya Maman naku da kannenka duk kuna lahiya dai ko."

"Lafiya qlau Alhaji sunce a gaisheku sosai."

"Kai madallah, haka akason ji, kai sama'ila kuje dasu ciki sud'an huta, kasan halin likitoci basu son wahala" ya fad'a yana kallon Abdool.

Smiling yayi "haba tsoho nida nike sabon jini saidai kai daka kwana biyu jini yayi nisa."

"Ho dan nemanga tahi ka dawo ka taho mu gwada kaga aikin tsohon kashi"

Dariya yayi tare da bin bayan su Hakeem da suka fice suna dariya yace.

"Rufamin asiri dattijo A d'auri kashi ko a bata igiya" ya fad'a tare da ficewa.

Shima dattijon dariya yayi yana maijin dad'in ganin jikan nasa da aka kwana biyu ba'a had'u ba..............

^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^

Sumui-sumui ta shigo kamar munafuka taje bakin randa da niyyan d'aukar buta tayi alwala, taji muryar Iya Hari tace.

"Tau jikan mayyu, waje Musa ciki Fir'auna kinzo kina wani Abu kamat ta kwarai kewai ga musulma, ki gama gulmarki kizo ki sameni saike bani labarin ubanda kika d'auka a makarantar bokoko da ki k'wuk'wema zuwa dudda na hissheki ciki, ko wani salon karuwancin na a haka eye."

Itadai shiru bata motsa ba bare ta tanka, inda sabo ta sama da irin wad'annan cin fuskar da zagi daga Iya Hari, Sam bata ragamata ko k'adan akan laifin da ba ita ta aikatashi ba, amma kullum a Kanta take saukewa.

"Oho ina magana keyimini tsaye k'ik'am kamar icce niddasa ko, kedai anyi shegiyar yarinya mai bakin hali, maza ki aje butan nan ungu ki kaima Lanti saura ki wuce wurin gantalinki da kissaba."

Cikin sauri hadda hard'ewa ta amshi ledar tare da ficewa da sauri kamar mai jiran cas, da tsaki ta bita tare da cewa.

"Tai ki dawo ki iskoni kici na jaki, bak'ar iri."

Tafe take cikin nutsuwa idan ka ganta ba zakace 'yar kauye bace, saboda tafita daban dasu komai nata a natse kamar wata babbar mace duk kuwa da k'arancin shekarunta.

Daga sama taji ana kiranta, ko bata juyo ba tasan me kiran nata, tsayawa tayi ba tare data ansa ba kuma bata juyo ba.

Wani hargitsatsen matashi ne ya tsaya gabanta, kalar irin ta 'yan daban fulanin nan bakinsa bak'i k'irin irin na 'yan sha, ido jajir kamar gauta.

"Waike Laure minana abbusa kanki, walle keci azzikin ina sonki daba haka ba hmmm khattt...." Yayi kwafa.

Itakam kallo kawai ta bishi dashi ba tare da tace uffan ba.

"Ke halan icce kike ina magana sai kallona kikai ko nayi miki kyauna" ya fad'a yana wani k'wanbewa.

Sanin halinsa idan ba maganan tayi ba ba barinta zaiyi ta tafi ba yasa tace.

"Jauro daga ina haka?"

Wani dad'i yaji ya lullub'esa dan ba k'aramin so yakema Laure ba shiyasa yake daga mata k'afa lokuta da dama ita kadaice weak point nashi, ko Abu ya had'aku da kace don Laure tofa yanzu zai sarara maka, duk kuwa da tsagerancinsa dan duk garin kowa shakkunsa yake saboda dan Sara sukane kowanne lokaci yana tare da makami, ganin badan arziki bane yasa Iya Hari amincewa da soyayyarsu da Laure, saboda kawai ta musguna mata.

Ardo yaji duk abinda ake ciki amma bai nuna ya sani ba, ya barsu yaga iya gudun ruwansu, abinda kawai ya sani bazai taba Aurar da marainiyar Allah.

"Daga daji nike, kehwa INA zakina?"

"Hmm gidan Gwaggo Lanti" ta fad'a a takaice, tare da juyar da fuskarta ganin irin kallon da yake mata na k'urillah.

"To..toh mutai in rakaiki?"

Ganin no way 2 escape yasa ta yadda suna tafe yana mata hira, ita kam sai uh da uhum da to take binsa dashi.

Aiko har suka isa ba'a samu Wanda ya daga ido ya kallesu ba saboda sanin hali, haka yake gadinta kamar kwai, ba kuwa ubanda ya isa ya kalleta balle yace yana sonta duk kuwa da dimbin masoya da takeda shi, amma suna gudun rasa rai dan k'aramin aikinsa ne, kisa.

Saida yaga shigarta sannan ya juya zuwa sabgarsa..........

_Rikici ba gado ba_ 🤣😜

💄 Meryerm Abdool💄
[7/4, 10:31 PM] 💄Meryerm Abdool💄: 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬
🖤 ```ABDULMAJEED``` 🖤
🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬

✨ *Servant of Majesty* ✨

Na
💄 _Meryerm Abdool_ 💄

© *Pure moment of life writers*
P.M.L💪🏽

*DOLE NA JINJINA MUKU*

*MAMAN USSEY*
*ABDOOL AAJ*
*FATYY AZLAND*
*UMMI A'ISHA*

_kud'in daban kuke, kamar yadda halinku na k'aramci ke nuna Ku, bazan gaji da fad'a ba wato da bazarku nake takawa 💃🏻 halin kirkinku yabiku har gadon bacci_ 👏🏽

📝 *Episode* 16--20

Saida sukayi fresh up suka d'an ci abinci da yake an shirya musu better, amma Abdool kad'an yaci dan idan da abinda ke bashi wahala to cin abinci ne.

Maamii ya kira ya fad'a mata sun sauka lafiya tare da gaisawa da k'anninsa wad'anda ya fara missing tun yau, cikin gida suka shiga suka gaida da kakarsa wato Haj, Saude wacce ta ansa su sama2 ko halinta ne haka oho!.

Daga nan suka shiga sauran gidajen suka gaisa da iyaye, yayyi, da kanni, daga nan suka koma inda tsoho mai ran k'arfe inji Abdool fa.

Hira suka sosai kaman ba wad'anda suka sha hanya ba har 12, Alhaji Sada yace suje su huta zuwa gobe kuma aci gaba.

"Wane gobe Alhaji nida zanyi sammako saidai na barku da Hakeem."

"Au abun 'yar hakane shine ka gudu *Yabo* dan kada ka zauna Sakkwato ?" Alhaji ya fad'a yana hararan Abdool.

Dariya yayi "Alhaji aiba laifina bane kuma ai anan Sokoto akwai consultant doctors da yawa k'auyukan sunfiku bukatar likita."

"Ho dan nema badai iya fad'a ba, Allah ya taimaka, k'ilama acan ka samo 'yar budurwa, koda yake naga alaman tsoron mata kakeyi, kila sai munyi maka gangami an d'aura maka a k'afa."

"Hhhhhhh kajika da shirmen tsufa, an gayama ni Kaine, aini matata ba'ama haifeta ba" shidai Hakeem sai dariya yake suna burgesa.

"Aa kak'i cewa mamarta ma ba'a haiheta ba, ja'iri zanso naga wacce zata aureka da shirmen nan naka, kaidai ba abinda ka bari na 'yan fari"

Dariya sukayi banda shi murmushi kawai yayi tare lumshe ido.................

_wannan kenan_

^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^

Zaune suke a Dandali, wasu na gad'arsu yayin wasu ke samartaka, wasu na siye da siyarwa, "Laure kina zuwa Yabo ran juma'a kai nono?"

"Kai Delu kema kesan dolena intahi inhar inason in tsira da mutuncina, Iya Hari, tun yau tayo tatsarta baki ganai ba mai yawa kuma nid'ai."

"Aa na d'auka ko mutuminki ya hana kinsan shi dole yabi dokarsa koya taka ta."

B'ata fuska tayi tace "wane mutumin nawa?"

"Jauro mana ko kinada wani bayan shina?"

"Ni wallah Delu kibar had'ani da wannan mugun abu" sai hawaye sharrrr..

Tasowa tayi da sauri tare da rungumeta "yi hankuri abukkiyata nifa da wasa nikai miki, amma ai bana fatan ki kasance matarsa koda maza sun k'are ko."

Sauke numfashi tayi tare da share hawaye "wallahi Delu na tsani Jauro bansan ya nikai dashi ba, amma ita Iya Hari ba Wanda takaso saishi, saukina Ardo har yanzu baice komi ba, ina tsoron kar shima ya yadda."

"Ina Ardo bai tab'a aura miki, Jauro kuma inshaa Allah saikin auri d'an arziki kamar kowa, me ake da J......" Kasa isuwa tayi saboda arba ta tayi dashi yana zuwa, da alama a buge yake sai layi yake ya tunkarosu ga muk'arrabansa bayansa suna take masa.

Jin k'awar tata tayi shiru ne yasa ta d'ago dan ganin meke wakana, arba tayi dashi ya kusa kawowa wurin da suke, d'aure fuska tayi tare da d'auke kai.

Cikin muryan 'yan sha yake magana "ya ke Laure baki ganeni ba halan kiyi fuskar shanu tare da d'auke kai" sannan ya kalli Delu da tasha jinin jikinta "ke munahuka tashi wuce gulmammiya."

Aiko da sauri ta d'auki tirenta ta cika bujenta.

"Haba Jauro wai meyasa kakaimin haka, kaga banson haka, hakad'ai ka korar min abokiyata."

Tunda ta fara magana kallonta kawai yakeyi cike da sha'awa Sam shi bai gane fad'a take ko hira take masa saboda tsananin so.

Wani daga cikin yaransa ne yace "ke oga kika dagama murya saboda ke rammai?"

Tsawa ya daga masa "kai Shago Laure ce fa, kakewa fwad'a?"

Ya fad'a yana zare ido kaman ya maresa, "tuba nike oga."
Chapter 2 · 0% Book details