← Book details Abdulmajid Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 53

Sashe 42

Abdulmajid Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kullum zata kira Mami ko ita ta kirata, tana tambayan ta ba matsala tace ba komai, shima abinda yake gayamata kenan kullum inta tambayesa, kuma ko zuwa tayi basu bari ta gane komai.

Yau kam ya d'auki niyyan gyara zamansu dan ya fahimci in yabi ta tata saisu shekara ba ruwan ta, shiko ya gaji da zaman ga extra care da yakeson bata ita da unborn.

D'aure mad'aurin rigar baccin ta tayi tana k'ok'arin Sanya gashinta a net ya shigo, can ciki ta amsa sallamar kamar yadda ta saba, ba tare data juyo ba, dama normally duk dare zai shigo ya dubata kawai ya fice.

Zama yayi kan sofa, yana binta da kallo, itakam sai lamarin gabanta take, shiru ya ratsa su bamai magana na y'an sakwanni.

"Meye matsalarki da zama dani a yanzu?" Ya jefa mata tambayan.

Ba tare data juyo ba "babu" tace in short.

Smiling yayi yace "OK bakya k'auna tane?"

Wannan Karon saurin juyowa tayi tare kallon sa fuska d'aure "au nice ma bana k'aunarka?"

"Of course! Bakyasona, dan da ace kina sona danna kusanceki saboda kawai baki tare ba, ba zaki d'auki zafi haka, har da fad'in zaki zubar min da ciki imaging!"

Hawaye ta fara cikin k'unan rai ta fara magana "Yaya halin ko in kula da kake numanin ne k'auna, ko kuwa saboda ka sanni a 'ya mace kafin na tare gidan ka? Haka kayi ma Aunty Zainab, a gidan su kaje ka fara saninta kafin a kawo maka ita?"

Duk'ewa tayi gurin tana kuka "saini saboda kawai na damu dakai naje d'akin ka? Idan akayi ma 'yarka haka zakace so ne?"

Duk ya rikice ganin yadda take kuka akan wannan abun da bai isa ayi fad'a akansa ba, meye a ciki, tashi yayi ya taka zuwa Inda take tare da mik'ar da ita tsaye ya had'a ta da k'irjin sa, tura sa ta farayi, k'ara riketa yayi Sam baya son kukan nata, kuma ya shirya d'aukar duk laifin da zata d'ora masa, zai bata hak'uri dan dai a zauna lafia, tun ta d'auki abin da zafi.

"Saurareni Ramlah kinji, pls nutsu kiyi hak'uri na sani ban kyauta ba amma kiyi hak'uri kuma ki sani sonki ne ya kawo haka" ya fad'a da slow voice nasa.

Janye jikinta tayi ba tare datace komai ba, gefen bed ta zauna tana ci gaba da kukanta, binta yayi yana rarrashinta dan kukanta ba kad'an yake tab'a sa ba, "me kikeso nayi miki na goge laifina a gareki?"

Nan ma shiru tayi masa tanaci gaba da kukanta, sai rarrashinta yake amma tak'i kulasa, ita gani take dad'in bakine kawai yazo yayi mata dan wata buk'atar sa daya samu ya biya yaci gaba da sha mata omo.

"Aiba haka ka zauna da Aunty Zainab ba, zama kake tare da ita kana sake mata fuska, kana mata hira kana d'ebe mata kewa saboda takai mata budurcinta gidan ka, ni kuma daka amsa tun gida, ai ranar da aka kawo ni bakayi d'okina ba, hasalima had'e min fuska kayi tunda ka samu abinda kakeso dani tun gida, baka damu dani ba baka zama dani kaji damuwa ta, baka debemin kewa wannan duk son ne? Yanzu ma da abinda ya kawo ka shiyasa kakemin dad'in baki, daka samu ka watsar dani"

"Oh Allah" shine abinda ya fad'a, mezai gayama ta yadda dashi, shi baiyi hakan dan tozarci gareta ba, amma ta fahimceshi opposite, gashi ba ganin surutu ba, balle yai ta mata harta fahimceshi, Sam baison hayaniya duk ta birkita masa tunani.

"Ban iya tsari ba Ramlah, kamar yadda ban iya k'arya ba, a kanki na fara son mace, kuma banso wata bayanki ba kamar yadda nakeson ki, ki yadda dani, bazan tab'a wulak'antaki ba, kefa jinina ce, kuma matata pls believe me!"

Shiru tayi tabbas tasan bai iya k'arya ba kuma tasan yana sonta, to amma maganar baiso wata ba bayanta kamar yadda ya sota ne bata yadda dashi ba kuma zata k'arya ta shi akansa, don son da ya nunawa aunty Zainab yafi nata(ayya anaki ganin ba)

Jin tayi shiru yasa ya mik'e "ina zuwa yanzu" ya fad'a tare da fita, kiran Zainab da tayi ne ya tuna masa da sak'on da ta bayar ya bata, duk da baisan meke ciki ba, yaji ya kamata ya bata a yanzu, tunda dama cewa tayi idan sun tare.

Tana nan Inda ya barta, sunkuyawa yayi har sunajin numfashin juna "gashi Zainab tace na baki" ya mik'a mata takardar tare da zuba mata ido.

D'agowa tayi suna had'a ido tayi saurin d'auke nata, jiki a sanyaye ta amsa.

Ficewa yayi ita kuma ta warware takardar ta fara karantawa kamar haka...

_Zuwa gareki Aunty Nah kuma k'anwata Ramlah_...........

💄Meryerm Abdool💄
[9/29, 9:10 PM] 💄Meryerm Abdool💄: 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬
🖤 ```ABDULMAJEED``` 🖤
🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬

✨ *Servant of Majesty* ✨

Na
💄 _Meryerm Abdool_ 💄

© *Pure moment of life writers*
P.M.L💪🏽

(We don't just entertain and educate we touch the heart❤ of the readers📝)

*#[email protected]*
*#IG PML WRITERS*
*#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
*#http://maryamsbello.blogspot.com*

*_Manzon Allah S.A.W yana cewa:- yake Fatima 'yar ma'aiki zan iya baki komai anan duniya, amma ki sani bazan iya amfanarki da komai lahira ba, aikinki ne kad'ai zai ceceki da rahamar ubangiji._*

_idan har Manzon Allah zai fad'i haka akan mafi soyuwa gareshi a cikin 'ya'yansa, to ina gamu gama garin mutane? Ina mai tak'ama da ilimi, arzikin, darajar, kimar, muk'amin babanta? Nasan dai tasan koda wasa ba zata kimantasa da fiyayyen halitta ba, to ko idan hakane mu sani iyayen mu ba zasu iya ceton mu da komai ba, aikinmu ne kad'ai zai cecemu, dan haka mu dage, mu gyara gobenmu, Alla yasa mudace da rahamarsa👏🏽_

📝 *Episode* 226--230

_"Ina rubuta miki wannan wasik'ar ne a dai2 lokacin da nake tunanin zanbar duniya, ina mai rokonki da had'a abinda zan haifa da sauran yaran da zaku haifa nan gaba, nasan zaki iya dan na yadda da kyakkyawar zuciyarki, sannan ina mai neman afuwarki akan kiyafe duka laifukan da nayi maki both known and unknown, by may size bakiyin komai ba face Alkhairi idan kinyi na yafe maki har ga Allah, a tare na sameki da Dr Majeed gashi zan barku tare dama Allah ya k'addara sai mun zauna ne a sanadin wannan d'an ko 'yar ubangiji yafimu sanin dalilin sa na tsara hakan wata kil yasan Dr bazai iya adalci a tsakaninmu ba idan kika tare duk da dimbin kyawun halinsa da adalcinsa, Ramlah yayanki Mutumin kirkine mai adalci duk da kin zama tauraruwa a cikin zuciyar sa bai hana ya bani wani fili a rayuwarsa ba ya bani kulawa da soyayya da mata dubu suka rasa a wannan zamanin yayi zaman Aure dani kamar yadda Manzon Allah S.A.W ya umurce mu bai tauye da komai ba, Ramlah bayan Mami ba abinda yayanki yakeso a rayuwa sama dake, duk wani motsi da bugun zuciyar sa dake yake yinsa, nasha jin kishinki lokuta da dama amma innayi tunani sai inga ba dai2 ne ba, saboda yayimin karamci bai kamata naji haushin Abu mafi soyuwa a garesa ba, wallahi Ramlah tun da nike a rayuwa ban tab'a ganin soyayya irin wacce yayanki ke miki ba ana yiwa wani ita, Ramlah kin dace da masoyi na gaskiya, ki daure ki nuna masa soyayya a zamanku ki tarairayesa da dukkan kulawa kiyi hak'uri da buk'atarsa ki d'aure ki jure inada tabbacin zakuyi zama mafi kyau a rayuwar aurenku, ina muku fatar Alkhairi a zamanku, ina rokon Allah ya kawar da fitina da shaidan a ciki, wishing d most blessing, peaceful marriage life"_

Ur sister
Zainab Salis

Hawaye ne wani nabin wani ke sauka a idanunta, jimk'e takardar tayi da duka hannayenta biyu "nima nayi kishi dake sosai Aunty Zee, na d'auka kin kwace min Yaya Abdool ashe ba haka bane, na yafeki aunty Zee bakimin komai ba, kuma inshaa Allah, bazan tab'a banbamta junior da d'an da zan Haifa ba, ina sonsa sona gaske, Allah yakai haske k'abarinki, Allah ya sadamu a Aljannarsa mad'aukakiya don rahamarsa, missing u much Aunty Zee" duk Cikin kuka take maganar cike da nadamar abubuwan da tayi ma Dr Majeed, tasan komai ya faru laifin ta dan ita taja hankalinsa kuma tasan yaso ta tun kafin ta zama abarso, to yanzu ta ina zata fara bashi hak'uri?

Turo k'ofa akayi ganin tana hawaye yazo da sauri tare da rungume ta yana bubbuga bayanta, mamakine ya kamashi ganin bata tureshi ba saima k'ara lafewa da tayi a jikinsa, bai gama mamaki ba yaji ta zagayesa da duka hannayenta ta rungume shi.

"Pls yaya Sorry 4 everything I totally misunderstand u pls forgive me....!"

"Shitttt! U don't nothing wrong!" Ya katseta tare da d'ora yatsansa akan lip nata, bud'e baki tayi zatayi magana, kafin tace wani abu har had'e bakinsu guri d'aya, cikin wani irin salo yake kissing nata, itama ware wa tayi tana tayashi, sun kai 10mt haka, sannan ya fara zare bakinsa yana kallon ta k'asa-k'asa idanunsa sun canja launi zuwa ja, ita kuma sunkuyar da kanta tayi cike da kunya, mik'ar da ita yayi tare da d'aukar ta kamar wata baby doll, bai sauketa ko ina ba sai toilet, da kansa yayi mata alwala shima yayi sannan ya sake d'aukota direta yayi tare da shimfid'a musu darduma, sif ya bud'e ya d'auko mata zane da hijab, ita dai binsa kawai take da kallo, turare ya d'auko zai fesa "aa karka saka" tace, murmushi kawai yayi tare da mik'a mata, itama murmushin tayi masa Wanda rabon da yaga irinsa akan fuskarta har ya manta "nafayi sallah na" tace cikin siririyar muryarta.

Kashe mata ido d'aya yayi yana smiling "wannan special ce irin ta ma'aura wacce bamu samu damar yi ba zamuyi k'ara'i" turo baki tayi kamar wata yarinya, cikin wasa yasa yatsarsa ya buga bakin kad'an "common baby munada abubuwa a gabanmu masu yawa ga time na tafiya" d'aura zanin tayi tare da saka hijab d'in ba tare da tace komai ba.

Shigewa gaba yayi tare da jansu, raka'a 2 sukayi kamar yadda sunnah ta tanadar sannan ya dafa kanta ya shiga kwararo musu addu'a da harshen larabci da kuma hausa duka.
Chapter 42 · 0% Book details