← Book details Abdulmajid Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 53

Sashe 13

Abdulmajid Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tashi yayi ya fice jiki b k'wari, dan yasan halin mahaifiyarsa tasa tsaf.

**************************

A satin Alhaji Sada da kannensa sukaje akayi komai na Al'ada aka tsaida rana, wata d'aya bayan sunyi graduation, haka suka watse cikin farinciki da ganin girman juna, dan anyi abinne na mutunci, lokacin su Ameena sun koma tuni.

B'angaren Hajia kaltume jin bata k'ara ji daga Auwal ba ta d'auka yabar maganar taci gaba da sha'aninta, aiko ranar da Alhaji ya gayamata sunje an tsaida rana, tub'ure masa tayi hauka zallah, saida yayi Mata Jan ido tare daci mata mutunci sannan yayi mata kashedi da kada ta yadda tayi abinda auren zai baci muddin tayi to a bakin Aurenta.

"Shima so kikeyi kiyi masa mugun zabin nan da kika yima Ayuba ko? To ban aminta ba tunda ya nuna Wanda yakeso, kuma bata wata matsala to banga dalilin hanashi ba, akan wani bazan dalilin ki Mara asali da tushe" a babin dole ta hak'ura dan tanason aurenta, amma tace ba ruwanta da auren kuma ko sisinta bazai yi ciwon kai akan tsinannen aure ba.

Ba Wanda ta fad'ama maganar auren, ko 'yan uwanta ko, Rafia da taji batun Auren ba k'aramin tashin hankali shiga dan ita har ga Allah son Auwal take, dan batasan dashi ba sai bayan Aurenta da Ayuba, shiyasa take wani shige masa(wa'iyazu billah kina matar aure wani namiji na burgeki wannan wace irin rayuwa ce, Allah ya gyara).

Ga k'anwar ta Ummita datake mutuwar sonsa taso ya auri Ummita ko an ta d'anji sauk'i tunda ya auri jininta, nan take taji ta tsani wacce zai aura kuma tasha alwashin rabasu, musamman ma da taga Hajia itama batason Aure, Murmushin mugunta tayi(koma take sak'awa a ranta oho! Wai Ameena tun kan ki shiga kin fara samun mak'iya 😞 ).

Alhamdulillah su Ameena sunyi graduation successful, nan aka shiga hada-hadar biki ba'a kama hannun yaro, karma Firdausi taji amara k'irjin biki, itace amarya itace ango, a gefe d'aya kuwa Auwal da Ameena ji Suke kamar sun shekara goma tare saboda tsabar k'auna dake yawo a tsananin su.

Biki akayi mai k'ayatarwa inda kowane b'angare ya taka rawar gani, ba k'aramin k'ok'ari su Baba suka yi ba gurin gyara wa Ameena d'akin ta komai yaji dai2 dai k'arfi baifi jiki, sai fatan zaman lafia, haka aka gama lafia kowa na farinciki, inka d'ebe uwar ango data nuna k'iyayyarta baro-baro, danko dangin ta sai daga baya sukeji, kin gayyatar kowa tayi, duk Wanda ya kawo Kansa kuwa tas takeyi masa, tace munafukai ne.

A sabon gidansu da basu Dad'e da tarewa ba Wanda Alhaji Sada ya Gina, shida 'ya'yansa estate mai d'auke da apartment biyar, anan suka tare, akai amanar gurin surukarta, dutse idan yana magana tota tanka sai k'anwar ta ganin shirun yayi yawa tw ansa musu,haka suka dangana da ita sashinta cike da mamakin uwar mijinta, Allah ya kyauta sukace sannan suka k'ara yi mata nasiha,tare da fatar Alkhairi haka suka barta suka dawowarsu (aure kenan! Shakan yaro)

k'auna mai tsabta ma'auratan Suke gudanarwa, cikin tsantsar so da kulawa kowannesu tattalin d'an uwansa yake.

Duk safiya zataje ta gaida surukanta Alhaji har janta da hira yake dan yarinyar ta shiga ransa jinta yake kamar Maryam d'insa, sabanin Hajia da sai ta gaida ita kusan sau uku kafin ta ansa da lafia, ko inda take bata kallo, bare tayi tunanin tasan da ita haka take karake zaman ta dawo, bai hana gobe ta k'ara zuwa, haka komai ta dafa zata aika Musu, ko kallon abinci batayi balle tasaran zataci saidai in mai aiki ta taho taci ko taba almajirai.

Sabanin waccen 'yar iskar da bata iya komai ba sai fitsara da kinibibi, ko ruwan zafi bata iya dafawa saidai tazo nan inda Hajia taci ko kuma Ayuba yayi musu take away, gaisuwa ko sai tayi Mata suger takeyi, Alhaji kam saidai in hanya ta had'a su yake samun gaisuwarta.

Auwal duk yana sane da wulak'ancin da Hajia kema matarsa, shima baida bakin hanawa saidai ya sakata d'aki ya bata hak'uri da lallashinta, "lah ba komai wlh ai iyayenmu ne dole mu bisu" kullum maganarta kenan, hakan ba k'aramin dad'i yake mishi ba, yaji sonta ya k'ara nunkuwa ransa.

Kamar yadda yayi mata alkawali har makaranta yaje da kanshi ya anso mata foam, ranar tayi tsallen murna burinta zai ciki, saidai kash!.

Labari na jema Hajia tace batasan zancen ba in Aure, aure in karatu, karatu ..........

_wayyo silly Ameena_ 🙆🏾🤦🏽‍♀

💄Meryerm Abdool💄
[8/3, 2:09 PM] 💄Meryerm Abdool💄: 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬
🖤 ```ABDULMAJEED``` 🖤
🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬

✨ *Servant of Majesty* ✨

Na
💄 _Meryerm Abdool_ 💄

© *Pure moment of life writers*
P.M.L💪🏽

(We don't just entertain and educate we touch the heart❤ of the readers📝)

*wata rana manzon Allah yace da Mu'azu bin jabli "ya Mu'azu shin bana baka labari akan, kan al'amari ba da kuma gimshik'insa da tsororuwar tozonsa?".*

Sai yace *" fad'a mini ya ma'aikin Allah".*

*"kan al'amari shine musulunci, gimshik'insa shine sallah, tsororuwar tozonsa shine jihadi, sannan ya k'ara cewa shin bazan gaya maka abinda ya mallaki dukkansu ba?*

Sai yace *"sanar dani ya ma'aikin Allah"*

Sai ya kama harshensa sannan yace *"ka kiyaye wannan.*

Sai Mu'azu yace cikin mamaki *"ya ma'aikin Allah, dama ana kamamu da abinda muka fad'a?"*

Sai yace *"kaiconka ya Mu'azu, shin meyasa ake kifarda mutane da a cikin wuta da fuskokinsu ko da tsinin hancinsu sai face akan abin da harshensu yake girbarmusu.*

_Hadisul hasanu_

_to nidake dasu mu guyi fad'ar kowace kalar magana, musan mu muka fad'a, dan wallahi nidake dasu sai munyi bayanin kowace kalma bayan kalma gobe k'iyama ( Allah yasa mudace_ 👏🏽

📝 *Episode* 96--100

Koda Auwal ya gayama Ameena abinda Hajia tace, abin ya Sosa ranta don Allah ya sani tanason karatu, kodon halin rayuwa, amma saboda ta kwantar masa da hankali ganin ya shiga rud'u, bata nuna komai a fuskarta tana murmushi tace "ba komai mijina, bin Umarnin Hajia dole ne, koda kuwa yaci karo da nasu ra'ayin, ina k'aunar ka dole na k'auna ci, abinda Hajia takeso, saboda haka karka damu nina hak'ura da karatun".

Tsabar farinciki rasa bakin magana yayi sai rungume ta yayi yana Sanya mata Albarka, tare dajin k'imarta da darajarta cikin ransa.

Lokacin Alhaji Sada yaji zancen da kanshi ya kira Ameena akan meyasa ta yadda da barin karatunta, kodai dole akayi mata? dan baisan Hajia ta hana ba, Auwal dai yace ta fasa ne, " Ameena idan iyayenki sukaji ai ba zasuji dad'i ba".

"Baba aina gayamusu nice na fasa yi" duk da cikin ransa ya shakkar haka kawai kuwa, nan dai yayi mata nasiha kamar yadda ya saba tare da bata kud'i masu yawa akan ta fara Sana'a tunda batason karatu, godiya sosai tayi masa sannan ta wuce, girgiza kai yayi tare da cewa "Allah ya kyauta" dan yanaji duk inda aka zagayo aka dawo akwai sa hannun Hajia.

Ameena Nada wata 6 ta samu miscarriage, Wanda basu Masan da cikin ba, tsawon sati biyu tayi a asibiti, ba Wanda baije dubata ba, harda Rafia kusan kullum sai taje dayake ita 'yar duniyace bata nuna k'iyayarta a fili.

Hajia ce kawai bataje ba, saima cewa tayi ai gara da tsinannen cikin ya zube, kuma Allah yasa mahaifar ta lalace gaba d'aya, da dai a haifemata dangin tsiya, maganganu dai ba dad'in ji taita fad'a.

Ko bayan an sallamesu, saida Alhaji ya nuna b'acin ransa sannan taje ta dubata Wanda shine zuwanta na farko sasan shima daga k'ofar parlour ta tsaya tayi sannu tana wannan cika da batsewa, tayi mamakin ganin yadda aka gyarama Ameena guri, sai tab'e baki tayi tace ai duk dukiyar d'anta ce, dansu basu da komai sai tsiya (oh talaka bawan Allah, komai saidai anyimishi kenan?, kai sharri kayan kwalba😔).

*************************

Sani da Salisu sun kammala karatunsu lafia, kuma sun fad'a kasuwanci kamar 'yan uwansu dama karatun anayi ne saboda zamani da k'arin experience akan business d'in, nan maganar Auren su ta tashi to anyi sa'a sun d'auko diyan masu dashi, nan fa Hajia akayi biki na kece raini, sai bak'ak'en maganganu ake yab'awa Ameena, bawar Allah yi takeyi kamar batasan da ita akeyi haka akayi biki aka k'are amare suka tare.

Haka dai akaci gaba da zama yayin da Ameena ke k'ara fuskartar cin fuska da walak'anci ga surukar tata saboda dai ta kasance 'yar talakawa, banbancin launin fata ake nuna mata sosai, sauk'in abin mijinta ta na k'aunar ta kuma suma matan saurin nata ba wacce ke nuna mata raini a gabanta sai dai ko bayan idonta, haka share tace ci gaba da kyautata mata, dai dai da rana d'aya bata taba gayama iyayenta ba.

Haka rayuwa taita shurawa kwanci tashi hasarai rai, duk surukan gidan kowa na d'auke da ciki inka debe Rafia wacce tace haihuwa ba yanzu, sai ta gama shanawa ba zata tsofe a banza ba amma da yake 'yarso CE shiru kakeji, Hajia ko tari (ooh da Ameena ce da anga yakin basasa...hhhhhh) lol

Ameena CE ta fara haihuwa, murna gurin Auwal kamar ya taka kan jariri ya zama Baba, haka ma Alhaji anyi jikan fari, kowa ya nuna farincikinsa nan da asibiti ta cika da 'yan uwa da Abokan arziki, hadda su Rafia anje na munafurci, saida aka tabbatar lafiyar uwar da d'anta sannan aka basu sallama, gida suka wuce dama k'anwar Mamanta tazo Asma'u k'anwar Ameena da yake sunyi Candy, hadda su Firdausi amarya an iso, haka suka dunguma suka wuce gida dan kankanta mata guri dan yau zasu wuce Argungu.

Hajia dak'ar taje shima ko d'an bata ansa ba daganan ta ganshi a hannun Asma'u wacce tunda yaron yazo duniya, taji k'aunar sa ta mamaye mata ilahirin zuciyarta, tanajin jinsa har ranta...

Ranar suna yaro yaci *Abdulmajeed* anyi shagali an kashe nera dan Auwal yayi rawar gani Alhaji ma yayi tashi yace jikan farine, Baba ma yayi nashi k'ok'arin, sai fatan Allah ya raya Abdool, su Firdausi da Asma'u uwar da sune k'irjin biki, Hajia kam ko kallo basu isheta ba dan da alama k'iyayyar uwar ta shafi d'an.
Chapter 13 · 0% Book details