← Book details Abdulmajid Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 53

Sashe 26

Abdulmajid Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gata sosai Ramlah ta sameta gurin Mami gasu Husna suma suna nan nan da ita, gari aka zaga da ita Tasha kallo kamar idanu su cire, tun tana d'ari d'ari harta sake dasu, haka zatayi ta biyema su Husna, suyita wasansu da hira, maganar ta dad'i take musu suyita kwaikwayonta suka cewa ta koya musu, Mami dad'i takeyi a ranta ganin yadda ta saki jiki dasu, haka take tasata gaba suyi fira kamar k'awarta, dama haka take da 'ya'yanta tana jansu a jiki(sai mun ja yaranmu a jiki mun kusantosu damu muke gane damuwarsu harma mu samar musu mafita, yin watsi dasu ko d'aure musu fuska shike kaisu ga fad'awa a halaka, Allah ya shirya mu dasu baki d'aya).

*********************

4:00pm cikin Kd tayi musu Hakeem suka fara saukewa sannan suka k'araso gida, tarba sosai suka samu gurin Mami, dan tun safe suke kitchen ita yaran dama idai tana gida ita ke shiga da kanta kuma tare da yaranta saboda su koya, Ramlah da yake akwai kaifin baseera ga tambaya tuni ta fara gane makamar aiki irin na birnin, dama ta iya na k'auye tunda ita keyima Hari.

Baffa yaji dad'in yadda yaga Ramlatun sa ta saki jiki, tana mak'ale dashi sai firan birni take mishi dama Ramlah badai surutu ba.

Abdool kam tun da sukayi lunch yayi sallah ya kwanta so ko gaisawa sosai basuyi ba.

Baffa ne zaune da Mami suke fira, k'aramar jakarsa ya d'auko ya fito da takardu da ya mik'awa Mami "Ameena wanga takardu ne da suka shahi gadon Ramlah danaku na wajen Asma'u, sauran takardun haihuwar Ramlatu na, gasunan kuyi mata abinda ya dace dasu, ayi mata komai na d'aki irin naku na nan idan zasuyi, kuma don Allah kada Ramlatuna tazo garemu nan kusa, ni zan ringa zuwa da kaina ina ganinta".

Takardun ta duba kud'i ne masu d'an dama " to Baffa ban katse maka hanzari ba, amma ni ana tunanin tariyar Ramlah ba yanzu ba, karatu nakeso tayi".

Sannan taci gaba "idan akayi la'akari da k'arancin shekarunta, duka shekara 14 tayi karanta da Aure, to ana tunanin in siya mata shares da kud'in ta kamar yadda nayi ma su Nihal, ni zan d'auki nauyin karatun ta, sa'an Nihal ce to ina tunanin kaita school d'in su Nihal amma ya kake gani."

Murmushi yayi yasan karatu shine babban burin Ramlah duk kuwa da Hari ta tauye ta yasan hakan zai sakata farinciki, amma kuma ai Aure ya wuce komai "hakan nan na Ameena amma baki tunanin in ankai haka an tauye shi Abdulmajeed"?

Tasan Abdool na buk'atar Aure, dan tun yana 18year yake fama da ciwon Mara, Wanda ke nuni dashi mai k'arfin sha'awa ne, to amma ai ita Ramlah za'a cutar ita, abinda ba zataso ga Nihal ba, so duk d'aya da Ramlah gunta, mema ta sani da Aure as 14 kuma tashin k'auye tana buk'atar wayewar kai da ilimi "Baba bana tunanin akwai matsala amma zamuyi magana".

" to ai dan dai kuna nan binni ne amma ai warin Ramlatu ta isa zama d'akin miji".

Murmushi tayi "haka akeyi a k'auyuka shiyasa zakiga anata samun matsala da wasu yaran akan Auren wuri, aje haihuwa aita had'uwa da yoyon fitsari da wasu ciwuka k'arshe mijin yaji bazai iya ba yayi saki, a maida yarinya bazawara ga kuma ciwo ga yara da k'ananun shekaru" jinjina kai yai alaman gamsuwa d'anshi kanshi ansha kawo mishi irin wad'annan cases a can Kilgori, nan dai sukaci gaba da tattauna wa ya bata goyon baya 100%.

Washe gari ya koma kice da tsaraba, hadda nasu Hari, Mami ta kira Abdool sun tattauna game da karatun Ramlah, dama shima tunanin sa kenan, toshi me zaiyi da ita a hakan ko k'irjin kirki babu, ai bayama tunanin tasan me Aure ke nufi, k'aunarta yakeyi amma badan wani Abu nata ba.

Sun yanke idan anyi Hutu tunda third term ake sai akaita JSS 3 tare da Nihal tunda tana saurin d'aukar Abu, kuma zai cigaba dayi mata lesson kafin shima ya fara aiki.

Zai fita yaci karo da ita ta shigo tsayawa tayi tare da cewa "ina wuni" hararar wasa yayi mata "um baxan ansa ba, bayan kin manta dani da karatun mu kin manta d'an binni mai glass".

Dariya ya bata a yanayin yadda yai maganar kaba baki tayi tare da cewa " Laa Ya Abdool baka barin sunan ga ko?" Tana turo baki.

Shima dariya yai "to ai ke kika sakamin INA"?

" um tona d'ebe maka".

"To 'yar k'anwata Ramlatun Baffa, ya maganan karatun mu?"

"Yawwa Yaya Abdool muci gaba".

" Allah kinaso in sakaki makaranta" gira ta d'aga mishi tana murmushi.

"Lalalala! Yarinyar nan........."

_kuyi hak'uri ban Zauna bana yau, kuma yau kiwar typing ya kamani_

💄Meryerm Abdool💄
[8/20, 11:17 PM] 💄Meryerm Abdool💄: 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬
🖤 ```ABDULMAJEED``` 🖤
🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬

✨ *Servant of Majesty* ✨

Na
💄 _Meryerm Abdool_ 💄

© *Pure moment of life writers*
P.M.L💪🏽

(We don't just entertain and educate we touch the heart❤ of the readers📝)

```Abdulmajid fans, naga kuna k'aunar sakwatanci da yawa fa😜 to Ku kwantar da mind d'inku Ramlatun Baffa tace zata koya maku😝 love u guys bohot bohot👌🏻😘```

📝 *Episode* 151--155

"Lalalala! Yarinyar nan ni kike d'aga wa gira?" Tare da zare ido hadda kama baki, sunne kai tayi Rana dariya k'asa-k'asa.

"Yo ai e a nuhina" dariya yayi tare da lak'ace mata hanci "basakkwata kawai".

Turo baki gaba tayi " kaima ai" murmushi yayi yana feeling special "ai zaki koyamun" corridor yabi tare da fad'in "jirani ina zuwa".

Dawowa yayi da wata k'aramar leda mai kyau bata yayi " sako ne daga Zainab tace tayaki murnar Aure" cikin zumud'i tace "LA Aunty Zainab tana ina?" Harara yai mata "sai yanzu kika tunata, tana gidansu".

Rungume ledar tayi tana dariya " Yaya ka had'ani da ita ta waya inyi godiya" tau" yace tare da cewa "jeki nuna wa Maminki" da sauri tayi ciki tana murmushi, binta yayi da kallo tare da shafa sumar Kansa, yana murmushi, sannan ya wuce d'akin sa.

Cikin farinciki ta shiga nunawa Mami gift d'in ta "iyye kai madallah kinga ko 'yar cas da ita zatayi miki kyau, kin gode, taji jeki aje a kayanki" da yake Mami tasan da labarin Zainab d'in, gaban madubi ta tsaya tana gwadawa tayi kyau a wuyanta gwanin sha'awa, sai juyi take tana dariya ita kad'ai, dama Ramlah da kwalliya (Ramlatu hankali).

Da dare bayan sunyi dinner suna zaune parlour suna kallo tasa TV a gaba, duk wani attention d'inta ya tattara ya koma can, gani take kamar mutanen fitowa zasuyi saboda girman Tv gashi kuma ta zauna daf da ita, su husna kam rabi ne kallo rabi Assignment Mami kuwa nakan computer tana aiki, Abdool ya shigo har gaida Mami su Husna suka gaidashi, Ramlah kam batasan ma ya shigo ba.

Daf da ita yaje ya saka waiwaya mata hannun sa gaban idon ta "La Ya Abdool yaushe kazo?"

"Ina kuwa zaki sani duka imaninki na a watching, kinga ki dena zama kusa da TV haka kada ya bata miki ido".

Dariya Mami tayi " Ai Ramlah tawa ne da kallo" Tab'e baki yayi "aiko daga yau zata daina dan gobe zamu fara lesson ya zube mata text book da lesson book da sauran instrument a gaban ta.

" hada tadai rage amma ba maganar dainawa, kaima dai ka fad'a ne" Mami ta fad'a.

Itakam Ramlah ganin littafin birjik gabanta haka ta manta da maganan kallo sai tab'a littafan take tana murmushi, yadda takesan karatu aiki daina kallon zata iyayi....

**********************

Kullum da safe da marece suke lesson wata rana ma hadda su Husna akeyi idan basuje gurin lesson d'insu ba, islamiyya kuma da rana sukeyi anan ta unguwarsu mai had'e da tahfiz, uniform hijab har k'asa.

Garden suke shigewa suyi lesson d'in, idan aka gama ta koya masa sakwatanci, in yanayi taita dariya bai iya amma ya daga anan wai ya iya, musamman inya karemata bayan, sai yace "ke hwahinta" waita gane yake nufi aiko dariya takeyi harda rik'e ciki, shiko kallo yake bin ta dashi komai tayi burgeshi takeyi shidai yana k'aunar Ramlah, amma ai dole ya sota kodon k'aunar da Aunty Asma'u ta nuna masa.

Zuwa yanzu kam ta fahimci abubuwa da yawa, dama gata da saurin gane Abu, har turanci tana ji saidai bata iya mayar da kowanne, math ma haka take tsargesa tsab.

A General hospital ta Kaduna Abdool ya nemi aiki, dama Neman ma'aikata suke so nan take suka bashi upper, Hakeem ma anan ya nema shima dai sun dauk'eshi so ana tare har yanzu, kullum suka had'u zai ta tsokanar sa ina 'yar renonsa, banza yake yi masa wata kuma yake "kaji dashi aini naji dad'i tunda inada 'yar reno, kaifa ba wadda ta taya" dariya yakeyi "tab na daik'i rayawa aini matata Unique ce".

Tab'e baki yake "munji zamu gani".

Tuni aka kammala ginan asibitin an zuba komai na amfanin asibitin saidai yace saiya k'ara samu experience tukun zai bud'e ta.

Ranar da akayi Hutu Nihal ta dawo, tana ganin Ramlah nanfa murna ta k'aru dama Mami tayi mata waya gurin malaninsu ta gayamata komai, nan da nan suka sarke kamar dama sun San juna parrot ta had'u da parrot dan kowacce ba baya ba, musamman Nihal ga barkwanci kamar Yusuf, nan ta shiga bata labarin makaranta,

Ramlah sai murmushi take tana imaging irin gata a school a class ana damawa da ita a hostel suna shagalinsu, oh ji take Kamar ace gobe za'a koma duk ta matsu ta ganta da uniform a school, kamar yadda take ganin yara da safe idan sunje kaisu Husna, kaga yara da uniform kala2 kowa tsaf dashi zaije makaranta shi yake burgeta ba kamar k'auyensu ba da sai can suke zuwa kuma sai rana ta fito muraratan wani ma sai yayi sati baije ba, kuma ba wani kwakwaran dalili.

Yanzu Abdool ya rage zama gida tun safe idan ya fita sai shida yake dawowa wani sa'in kuma inyai fitar marece sai 10 yake dawowa shiyasa basu cika had'uwa ba, lesson kuma ya dawo end of week.

Yanzu girkin gida sukeyi sun hutar da Inna kande da Mami, komai sun iya dama ita Nihal ta iya tun can, Ramlah ma yanzu anyi expert........
Chapter 26 · 0% Book details