Sashe 1
Abdulmajid Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
[6/28, 11:15 PM] 💄Meryerm Abdool💄: 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬
🖤 ```ABDULMAJEED``` 🖤
🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬
✨ *Servant of majesty*✨
Na
💄 _Meryerm Abdool_💄
© *Pure moment of life writers*
P.M.L💪🏽
```zanyi amfani da wannan damar nayiwa dukannin masoya da abokai da 'yan uwa musulmi murnan kammala Ramadan lafia, sannan nayi muku barka da sallah fatar Allah ya karb'i ibadunmu ameen```👏🏽
📝 *Episode* 1⃣⏩5⃣
بسم الله الرحمن الرحيم
Dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah mad'aukakin sarki, mamallaki sarkin iya halitta, tsira da aminci su tabbata ga Annabi Muhammad(S.A.W)
Tare da sahabbansa da iyalan gidansu da duk wad'anda sukabi tafarkinsa har zuwa ranar ceto
_Banyi niyyan rubuta wannan littafin don cin zarafi ko fuska ga wani ba, idan kuma yaci karo da halinka/ki saiki/ka gyara, a guji zargi._
*Ban yadda wani ko wata ya juyamin koda kalma d'aya ne sai tare da izinina*
Tukuici gareku ahalina ina alfahari daku a duk inda naje, Allah yabar kauna ya rayamu a musulunci damu da sauran musulmi baki daya. *ILYSM❣
*KADUNA STATE*
*kofar mashi*
Garden ne matsakaici mai cike da furanni masu fitar da daddad'an k'amshi da itatuwa ma'abota fruits, gurin yayi kore sharr sai wata sayyayar iska ke kadawa wacce kowane ma'aboci halitta zaiyi sha'awar ya shaka, gurin d'auke yake da resting chairs farare, ga wata k'orama a gefe tana gudana abin gwanin sha'awa da burgewa.
Na shagala da kallon gurin, inata baza idona abinka da bakauyiya, can gefe cikin daya daga cikin rest chair na hango wani matashi a kwance.
Daf dashi naje domin naji dad'in d'akko maku rahoto dakyau, idanuwansa a lumshe sanye da wani siririn farin glass da alama medical ne, amma hakan bai hanani gane cewa matashin ma'aboci golden eyes bane saboda yadda eyes balls nasa ya fito akan fatar idon, hancinsa ba dogo bane hasalima za'a kirasa da guntu in short, kalar fatarsa abin burgewace wato chocolate.
Kallon nai masa da sama har k'asa na fahimci baida tsayi sosai, baida jiki ko kad'an saidai yana da k'irar k'arfi, gashin kansa irin na hausawa ne amma kan yasha gyara yayi kyau ya kuwa kwanta ba laifi, yana da round face kamar mace wacce ke zageye da man pride, bakinsa mai matukar kyawu d'auke da soft red lip, ina cikin nazari banyi aune ba naga ya mik'e tare da sauko da k'afafunsa kan shoes nasa, mashaa Allah k'afarsa abin sha'awace kamar a rangada mata lalli.
Mik'ewa yayi tare da d'aukar phone masa da iPad nasa dake kan desk yayi, sanye yake da shirt orange da jean baki, idonsa na kalla saida k'irjina ya buga kwayar idon brown ce yayin da farin ya surka da pink, bansan time d'inda nace subhanallah ba, ban tab'a gani irin idonsa ba before.
Inacan duniyar mamaki sai ganin nayi yakai k'ofar fita daga garden d'in, hakan yasa na bisa a 150 saboda ci gaba da samo maku rahoto. Lolz
Wata 'yar k'aramar k'ofa naga yabi sai kawai na gammu '' cikin wani matsakaicin parlour wanda yaji kayan more rayuwa dai2 irin na masu rufin asiri, wata matace zaune wacce i k'iyasce zatayi shekara arba'in da d'ori, a fizge tana kama da matashin, husnul musleem rik'e a hannunta tana dubawa.
Sai wata yarinya dake kwance gefenta tana barci a kalla zatayi ten year, sai yaro a k'asa sai faman zane yake a littafi sa'an wacce ke bacci da alama ma twins saboda kamar da sukeyi.
Zama matashin yayi kan 1seat bayan yayi sallama sannan YACE.
"Maamii sannu da gida."shima yaron yace " welcome ya Abdool. "
"Yawwa big boy me akeyine?"
"Homework ne."
"Ok a bada himma."
Itama Cikin kulawa bayan ta ansa sallamarsa tare da aje husnul musleem tace "yawwa Abdool dama ba fita kayi ba kenan?"
"Eh Maamii nad'an garden ne."
"A toh madalla, toya maganan horsemanship naka?"
"Eh Maamii inshaa Allah 2/3 week dai zasu kiramu."
"Sokoton dai koh" ta fad'a tare da kallonsa.
Shafa kansa yayi yace "itace Maamii."
"Nikam Abdool bansan meyasa ka nace sai Sokoto ba duk hospital d'inda ke Kaduna da zagaye ba wacce tai maka ne ko meye?"
Smiling yayi yace "ba haka bane Maamii inadai son naje gidane nayi wa garina hidima, kuma kinga zan k'ara sabo da 'yan uwana."
Nisawa tayi tasan abinda d'an nata ya gad'a gaskiya km hakan dazaiyi yayi dai2 saidai batason tayi nisa dashi ko kad'an.
Yaron da ke drawing jin yayan nasa na maganan tafiya yasa ya aje book d'in yaje kusa da yayansa yace "yace Ya Abdool da gaske tafia zakayi ka barmu?"
Shafa kansa yayi yace "Ajb ba dad'ewa zanyi ba, kuma zan ringa zuwa ina dubaku kaji my boy."
Girgiza kai yayi yace "nidai zan bika Yaya" ya fad'a yana narkewa jikinsa.
"To karatunfa Ajb?"
"Nayi a can."
Murmushi yayi yace "Ajb rigima, ita Husna tayi nata homework d'in?"dan ya d'auke masa hankali.
"Aa headache takeyi."
Mik'ewa yayi tare da zuga gaban seat ya dafa goshinta yace "Subhanallah tasha magani kuwa?"
"Aa batasha ba tai bacci."
Cikin nuna damuwa ya mik'e zuwa d'akinsa dan d'akko mata magani, Maamii kuwa sai kallonsa take tana k'ara godewa daya had'a mata kan 'yayanta suke tausayawa juna da k'aunar juna, sosai Abdool ke nuna kulawarsa akan kannensa ga saukin kai, yakan wasa dasu sosai sannan ya tsawatar musu idan sukayi ba dai2 ba( _shine gaskiyar rayuwa_).
^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^
*SOKOTO STATE*
*Garin kilgori dake*
"Laure! Laure!! Laure!!!" Firgigit ta juyo tare da baro tagar ajin tazo gun mai kiranta tace "Delu ahe kece ina zakina halan?"
"Kekam Laure bakijin maganar Iya Hari, hi yassa kullum taka bugunki kaman ganga tase bataso kiyi boko, missa kika dagewa sai keyi, wane dadi agga boko?"
Dafa kafad'ar Delu tayi tace "Delu bansan missa Allah ya jarabceni dason boko ba, kullum inaji cikin raina zanyi boko kuma nayi alfahari dahi, amma bansan sai yauhe ba, duk ni gitto ta makaranta ji nikai kamar an damremin kafwa inji hena tsaya naji kara2" ta K'arashe maganar tare da zubar da hawaye.
Cikin tausayawa k'awar tata ta share mata hawaye tare da rungumota jikinta tace "kiyi hank'uri Laure da nuhar Allah zakiyi boko wata rana, yanzu ki d'auko turenki mu wuce gida tun kafin ki husata Iyaa Hari ta jibgeki tunda ba mutunci gareta ba."
Haka taje bakin tagar daga k'asa ta d'akko tiren gyad'arta, suka bar makarntar mai d'auke da 'yan ajijuwa da basu wuce biyar ba, suka doshi cikin gari.......
_Tirkashi to ma'abota karanta novel d'in Meryerm ko biyoni a sannu kuji da wanne salon nazo wannan karon_ love u friends💞
💄Meryerm Abdool💄
[6/30, 6:44 PM] 💄Meryerm Abdool💄: 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬
🖤 ```ABDULMAJEED``` 🖤
🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬
✨ *Servant of Majesty* ✨
Na
💄 _Meryerm Abdool_ 💄
© *Pure moment of life writers*
P.M.L💪🏽
```Jinjinar ban girma gareku zak'ak'uran marubuta, da girman kujerarku manyan mata masu duniya, gareku members of pure moment of life writers, ❤ more Greece 2 ur shinning elbow💪🏽```
📝 *Episode* 6⃣⏩🔟
Da d'an jayawa kafin a isa cikin garin tafe suke k'awar tata naci gaba da bata shawara da k'arfafa mata gwiwa.
Gari wanda za'a kirasa k'auye kuma garin fulani kai tsaye duba da yanayin gine-ginenda ke cikin garin, amma da alama manoma ne kuma makiyaya dan ko'ina ka duba shukace tun daga dajin garin har zuwa cikin garin, kama da gero, Masara, maiwa, albasa, tomatur, ata, tattasai kai har noman taba sunayi, ga kuma dabbobin na ciwo, a takaice dai da alama ba talauci a garin.
Dai-dai k'ofar wani gida Wanda zance duk garin ba irinsa naga sun tsaya, nan k'awarta tace "to Laure ni zan isa gida saike hito anjima Dandali" ta fad'a tare da tafiya.
"Tau Delu ki gaida Gwaggo" cewar Laure tare da sanya kanta a soron gidan, amma kuma fuskar taf tashin hankali k'irjinta sai bugawa yake dan batasan yau kuma wane kalan zagi zata samu ba.
Wata dattijuwace zaune tsakar gidan tana tunka tsawo, bakace mai tsamuraren jiki, ba laifi fuskarta irin ta fulanice saidai ta tamure itama, ga taba ta k'unsa a bakinta redio gefenta tana jin wakar *Barmani toge* cikin sanyin murya tayi sallama.
Dagowa tsohuwar tayi ba tare da ansa sallama ba tace "to gantalalliya sai yanzu kikk'are gantalin naki, keman Laure anyi tambad'add'iyar yarinya yanzu tun abun Hantsi sai yanzu kika dawo mini."
"Subhanallah, haba Hari wanga bacin k'are dangi da kikai ma diyanga marainiyar Allah dami yayyi kama? Hari wai mi diyanga tayyi miki da baki tab'a nuharta da alheri ba se sheri?" Wani farin dattijo ya fad'a yana aje buta fitowarsa kenan daga bayi.
"Haba Ardo wai missa kullum kurkiiyarga tayyi min laihi baka gani? Saima nawa kaka gani sannan ka bini da ganin laifi, koni kabar yimin irin haka ai sai kasa ta hwandare dama yaya lahiyar kura bale tayi hauka" ta fad'a cikin nuna bacin rai.
Girgiza kai kawai yayi tare da cewa "Allah ya kyauta" inda sabo ya saba da halin Hari Sam batason gaskiya.
"Ramlatuna shiga daga ciki ki aje turen saiki kawomana ruwan alwala garka kejina 'yar Albarka" ya fad'a tare da ficewa daga gidan cike da tausayinta.
Matse hawaye tayi tare da shigewa d'aki ta adon aje tiren, da harara ta rakata tare da banka tsaki tace.
"Munahuka dangin mayyu tai ki dawo ki iskoni saike hwadamin inda kittsaya."...........
_tofa meye sanadin wannan k'yayyar? Nida Ku mubi a sannu harmu gano bakin zaren_🤔😔
^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^
*KADUNA STATE*
*3 weeks later....*
Gabadaya sun fito waje domin raka Abdool zai wuce Sokoto saboda an kirasu, sanye yake da jean blue da shirt purple yana sanye da glass nasa as usual, left and right nasa yana rungume da Husna da Ajb, momynsu na bayansa, sai k'anwarsa Nihal data dawo Hutu week before tana rataye da lodge nasa.
Bakin motarsa suka tsaya ana k'ara bankwana, su Husna sun lafe jikinsa Sam basaso ya tafi saidai ba yadda zasuyi saboda tafiya ta zama dole...
"Abdool ka kula sosai ka tsare mutuncinka da kimarka, ka kula da ibadarka ka rike Addu'a sannan ka sada zumunci da 'yan uwanka kada ka nuna musu komai sai Alkhairi, Allah ya kiyaye hanya, ya Baku sa'a da nasara akan abinda kukajeyi."
Ba kad'an yaji dad'in addu'ar Maamii tasa ba, yace "inshaa Allah Maamii zan kiyaye, aci gaba dayi mana Addu'a, Addu'arki itace silar cigabarmu."
"Addu'a ba fashi Abdool Allah ya k'ara shiryaku baki d'aya."