← Book details Zurfin Ciki Part 1 - 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 63

Sashe 8

Zurfin Ciki Part 1 - 4 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tamkar Alhaji yasan yadda
abba suka yi da antin bishira,da safe Abba yaje
gaida shi ya ce,"babana zuwa yanzun ya kamata
a ce mun shiga maganarku da yarinyar nan."
Abba ya sunkuyar da kai tare da ce wa,"um,dama
gidan antinta da naje dazu munyi zancen,yanzun
dai su ce sai an nemi izinin shi baban nasu. ta
ce,mijinta zai masa magana,in yaso sai kuji ranar
da zaku je din." Alhaji ya ce,"to shikenan.Allah ya
kai mu.yanzu yaushe zaka tafi kaduna?" kafin
abba ya bashi amsa,ya ci gaba da cewa,ban so
ba sam da wannan yin nisan da zaka yi damu
Abba." Abba ya ce,"ina hasashen cewa za a barni
nan kano da yardar Allah,bisa ga taimakon mijin
yayar yarinyar da nake zuwa gurinta." Alhaji ya
ce,"to Allah ya yarda,sannan in an fada maka
lokacin da zamu gana da waliyyan nata sai ka
sanar dani." Abba ya ce,"to." Alhaji ya ce,"ina son
mu danyi bincike kan yarinyar amma mahaifinta
sannanne ne,anata yabonshi." Abba ya ce,"to."
Ranar juma'a da misalin karfe biyu da rabi Alhaji
ibrahim (wato abban nasir,mijin anty farida),ya
samu sirikinsa a gida. bayan sun gaisa ya
tambayi yan jikokinshi sai Alhaji ibrahim ya
ce,"suna lafiya.dama makasudin zuwan shi
ne,akwai wani yaro da ke zuwa gurin
bishira,yawancinan gidanmu suke zance. to
gaskiya na yaba da hankalin yaron,sannan ya
damu yana son ya turo iyayensa.to shi ne nace
bari in nemar musu izini tukun." mahaifin bishira
ya kalli surukinsa ya ce,"aisha ko bishira?" Abban
nasir ya ce,bishira ce." ya gyara zama.

"bishira
ta gama sakandare ne?" Abban nasir ya ce,"ai
Alhaji ba yana nufin ayi auren yanzun bane,a san
dashi ne." Alhaji ya ce,"bana haka,ka sani sai dai
tayi abu daya,in karatun karatun,in auren to
auran.

Ibrahim kasan wani abu daya? duk lokacin
da kasa yarinya ta soma tsayawa da saurayi
bayan tana karatu,musammanirin bishira irin
wadda tasan tsarina amma ta danne ta turo min
saurayi to gara ayi mata auren.

Domin doguwan
soyaryannan bata da ma'ana,qarshe sai wata
shedana ta biyo baya,balan
tana bishira tana da
rawan kai.ya matsa kusa da wayan tangaraho
wadda aka jona ta ke amfani a daukacin gidan,ya
dannan nanbobin sannan ya kira hjy.ta amsa
daga sashanta,yace bishira na ciki? tace tananan,
yace ki turo mani ita,tace to.gaban bishira ya
badi,ganin mijin yarta a gidan dan tasan abinda
ya kawo shi.ta xauna can gefe tace,gani dady,ta
gaisa da abban nasir.mahaifinta yace nasan
kinsan dalilin xuwan ibrahim ko? kanta a qasa
tace,a'a. yace.yace to saurayin da ce xuwa gunki
ne yake san ya turo magabatansa,kuma nasan
kinsan da batun?sai dai inasan kisan abu daya
bana san doguwan soyayya,da xara nagama
buncike akan yaran wanda shari'a tace.inna
gamsu,to fa aurad dake xanyi kije can ki qarasa
karatun in kina so.ahj ibrahin yace yaran yace shi
ba dole sai anyi yanxu ba.nufin shi a amince
mashi.shi kuma xai jira har ta gama
makarantanta. ahj ya katseshi ta hanyan daga
mai hannu,ibrahin kaidai sheda ne bewan bana
haka, kuma ba a haka dani ko?yace auran yata fa
kakeyi,ka san tsarina.ibrahinyace na sani ahj.
yace yauwa,ina nan ban canxa ba.yace yanxu
abinda nake san ka dashi kafin na amince da
xuwan iyayan shi.ya dubu bishira yace kinasan
shi kin amince dashi? tace eh yace tashi ki tafi
angama.kai kuma inasan kashiga unguwa uku ka
binci komin labarin yaran da usilin shi.ahj ibrahin
yace angama.yace naso ace sai ta gana
karatu,dan sai anyi sa'a xata qarasa,anma hakan
xaifimin akan doguwan soyayya kafin inxo inajin
haushi.ibrahin ya miqe to ni xan tafi.ahj shima ya
yunqura xai tashi sai waya ta kama ruri dan haka
sukayi sallama anan. ummi ta shiga gida daga
makaranta take,akuyan umman bashir tagani ta
gani a gidansu tana masu barna a kicin da sauri
ta koma ta saka sakatan gidan,sannan ta
dawo.ta kama akuyan ta kaita bakin fanfo ta tara
kanta sai kuka akuyan take tayi.

Umman bashir
ta jiyo daga gidanta,da sauri ta fita taxo tana
buga gidan tana mashifa.yan baqin
ciki,mahassada,yanka min akuyan xaku yi?san
ummi bata ji ba, dan gidan ba kowa. umma taje
sheka can gidansu,hta kuma tsohuwa taje
gaisuwa n mutuwa nan kusa dasu.saida taga
akuyan ta galabaita sannan ta janyo wata leda ta
daura mata a bindi,sannan ta saketa.akuyan ta
tashi da gudu tayi hanyan fita,tace shegiya gobe
kixo ki bude mana abinci kici.taje ta bude qofar
ta jiyo muryan umman bashir,dan haka sai ta cire
sakatar sannan ta dan sanmata qofan akuya tayi
waje da gudu.saboda ledar da ummi ta qulla
mata,sai take ganin kamar binta ake,dan haka ta
nausa cikin unguwa da gudu.umman bashir na
ganin akuyarta tayi fitan bindiga,sai tabi tana
cewa,ku taremin.ummi ta koma ciki tana
dariya.ita kuma umman bashir daqar ta samu aka
ruqo mata akuyan ta.aka kwance ledan taruqo ta
xuwa gida.sai masifa take, tana isowa qofar
gidan umma na RFIN CIKI book 1 part 5
ZURFIN CIKI book 1 part 5
Posted by Bashir Sani Fesan on 14 Dec 2016 - 21:54
Ita kuma umman bashir daqar ta samu aka ruqo
mata akuyan ta.aka kwance ledan taruqo ta xuwa
gida.sai masifa take, tana isowa qofar gidan
umma na isa. tace yar baqin ciki kun kama min
akuya kun jiqata xaku kashe min,ta ta allah ba
takuba.umma tace akuya kuma wani iri?ni bana
gidan dawowa ta kenan.ta ce kina nan muna
fuka.umma sai ta shige gida,amma duk da haka
sai da umman bashir ta bita har ciki tace sai ta
doke mace akan akuyan ta.umma ta shige daki
can qurya tasamu ummi a kwance,tace ke uwar
yan daukan magana, ke ce kika jiqa mata akuya?
umma tace cinye min abinci tayi.nan abba ya
riske ta tana ta tsine tsine.yace meya faru?tace
kai ja can ka bani guri,dan baka san darajata
ba,banda an raina ni yaya xa'a kama min dabba
a jiqa?in nai magana sai a maidani mahaukaciya
ko haquri baxa a ban ba.abba yace to kiyi haquri
in sha allah baxa a qara ba.tace baxan haqura
ba,tunda inta mutu nike da asara.umma tafito
tace to yanxu ya kike san ayi?ni dai bananan
ummi ce da wannan tsiyan wai ta sameta ta
cinye mata abinci. umma tace kinsan halin ummi
kuma nima haquri nake da ita.tace to ni baxan
iya haqurin ba.umma ta finciko ummi ta hanka da
mata.ta gata na ki rama mata.ta juya cikin daki
ta kama harko kinta.ba kunya ta kama ummi
tana ta jibga.abba takaicin mahaifiyan shi ya cika
mai xuciya,amma bashi da daman cewa ta
bari.shin baxa tai tunani ba takama yar matan da
tariqe mata danta riqon adalci da amana,tana
duka haka? sai data gaji dan kan ta sannan ta
fito.abba ma fita yayi cikin takaici,ummi kuwa
kuwa tayi tayi har tsohuwa ta dawo,ta sameta
xaune tana dirxan kuka.

Dama taci karo da abba
a waje tace mai sunan mlm har ka dawo xaka
kuma fita?yace um.tace miskilin banxa saikace
mai ciwon hakori,ta riska ummi tana kuka,tace
umhum daman tunda naga ya fita yana ta
maxurai nasan yaci xalinci.kai na gaji da halin
mai sunan mlm.umma tace,ba ruwanshi.ummi
taqara satin kuka ba umman bashir bace taxo
tayi min duka.meki ka mata?wai din akuyan ta
taxo ta cinyemin abinci,shine na jiqata da
ruwa,shine taxo tamin duka kuma gashi banci
komai ba, ko qala bata ceba,ta juya sai gidan
umman bashir.ta sameta tana sinke kayan
miya.tace ke sahura saboda bakida mutunci shine
xakixo har gaban uwarta ki daka?sahura tace na
daketa,kamme xata jiqa min akuya?tace wane
shegen ne yace ki saki akuyan ki har taje taci
mata abinci?to kashedin ki mara mutunci da baki
san girman nagaba ba.bashir ya fito yace a'a
tsohuwa kidaina xagan mana uwa har cikin
gidanmu.tace iye!kaxone ka nuna min rashin
tarbinyan ka?nan har wata uwa gareka?nanfa sa
in sa ya tsarke a tsakaninsu.ummata juyo su
tarasa yadda xatayi,sai ga abba ya shigo.yauwa
abba shiga gidan can ka lallaso min tsohuwa taje
kasgedi ataba yar gwal dinta.ta dubi ummi tace
duk aka yar marajin can ni naji dadin dukan da
tayi mata,dan dukan algaki tayi.banda xalunci ya
xata kama dabba ta jiqa? abba ya fita ba tare da
yace qala ba. abba na shiga gidan bashir yana
tsigale tsohuwa tankar xai kai mata duka,abba ya
daga hannu ya wanka ma bashir mari,sannan
yace tsohuwa saankace da xaka dunga mata
wannan fadan.ya dubi umman bashir dan allah
kiyi haquri.sannan yaja hannu tsohuwa,shi kuma
bashir yana ta xagin abba yana cewa allah ya
isa. umman bashir ta ce abba tir da hauhuwan ka
tir!tir! kuma gab nake da in dagama ka nono.cak!
abba ya tsaya kalaman mahaifiyan shi sun shi
jeshi,a hankali ya saki hannun tsohuwa batare da
tasan ya tsaya ba.dan sababin da takeyi yaja
hankalinta.ya juyo har gabanta yace dan allah ki
yafemin ki ya femin.ba tareda ya jira amsan ta ba
ya fita. baiji muryan taba amma koda bata ya fe
maiba jikinta yayi sanyi.da yamma bayan su ahj
babba sun dawo kasuwa sai suka shiga dan
gaida tsohuwa.nan ta saka masu kuka suka rude
tare da fadin me aka mata?cikin kuka tace ni
sahura xatai ma rashin mutun ci tare da danta
bashir nan ta koro masu bayanin komai.
Chapter 8 · 0% Book details