← Book details Zurfin Ciki Part 1 - 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 63

Sashe 2

Zurfin Ciki Part 1 - 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zaune suke a kofar gidan
Alhaji babba kan katuwar tabarma,sun jere abinci
suna ci. kullum Alhaji babba da Alhaji karami nan
suke zama tamkar tagwaye,suna matukar kama.
mafi yawancin lokuta ma kaya iri daya suke
sakawa,domin Alhaji babba duk kayan daya saya
tare yake sai musu. haka nan hula ko
takalmi,haka nan matansu baya
bambantawa.shima Alhaji karami duk da bai kai
samun babba ba yana koyi dashi.

Alhaji babba ya
kalli karami yace,"Aminu ya zancen makarantar
bashir?" Alhaji karami ya dubi wansa ya ce,"Alhaji
bashi fa ya fadi jarabawa,jiya na tsare shi da
maganar sakamakon jarabawarshi yace bai duba
ba,saida yaji nace zan hada shi da Abba suje
sannan yace min yaje wai duk ya fadi.

Alhaji
babba yace,"Ash sha! sai ya maimata shekara
kenan?"Alhaji karami ya ce,"to in ma ba zai
maimaita ba Alhaji shi ya sani,ba sahura ta bata
su ba? shi Abba ai ba haka yayi ba,ka dubi fa
yadda yaki aikin kanikancin nan,uwarshi ta zuga
shi wai yayi karatu kadai yayi aikin gwamnati.
kullum haka sahura take kitsa ma yaran."Alhaji
babba yayi yar dariyar takaici,sannan yace"in
banda abin sahura yadda kasan nan tamu ta
zama waye zaici alwashin aikin gwamnati? ina ce
masu digree ne ke yawo ba aiki?" "har masu
masters." inji Alhaji karami.ya tashi zaune daga
kishingidar da yayi,yace dubi misalin dan
abokinnan naka Alhaji buhari." Alhaji babba ya
ce,"kwarai kuwa,mas'ud ba.yanxu ma fa kasuwa
yake zuwa,sai yanxun yake koyon kasuwancin."
Alhaji karami ya ce,"to daya dora shi a kasuwar
fa tun farko?shi yasa na fada ma sahura ta bar
yara su hada da sana'ar hannu.

Donni dai yaro
kamar bashir yanxun ba zan dauki kudina in ba
shi ba."Alhaji babba yace,"shi yasa kulum nake
kara son Abba,yaron nan da kanshi yace min in
kai shi shagon dinki.

Har naki suwaiba ta
ce,"Alhaji ka kai shi in ya iya sana'ar hannu ko
bai samu aikin gwamnati ba zai rike kanshi da
sana'ar nan." Alhaji karami ya ce,"to ai kasan ita
suwaiba tasan abinda take yi.amma sahura sai
addu'a." Sallamar Abba ce ta katse su,ya zauna
can gefe sannan ya gaishe su,duk suka amsa tare
da tara hankulasu gurinshi.

Ya mika ma Alhaji
babba kullin takarda tare da cewa "Alhaji gashi
maganin (ulser)ne" Alhaji babba ya amsa ya
ce,"Abba sarkin amsa magani, a gurin wa ka
samo wannan kuma?" ya ce,"Ahmad abokina na
raka ya amso ma babanshi,shine nace bari in
amso muku" yace to Allah ya saka da
alkairi."Alhajikarami yace"dame ake sha?" Abba
ya ce,"da madara peak." suka ce"to" daya mike
zai shiga gida Alhaji babba yace ya shige da
kwanikan abincin. yau kam Abba bacci yake ji da
wuri,don haka ya baro shagon dinkinsu wanda ya
kan kai goman dare a ciki ya nufo gida.

Ya bude
dakinshi ya shiga ya cire riga sai singileti da
gajeren wando na jeans.ya nufi ciki don ya kama
ruwa ya kuma yi wa ummanshi sallama. tsakar
gida ya sameta zaune ta zabga tagumi,inda
abinda Abba ya tsana shine,yaga ummanshi cikin
damuwa. da sauri ya isa wurinta,"umma
lafiya?"ta dube shi "ina fa lafiya,ummi ce tunda
tayi sallar isha'i ta fice kusan awa guda zance
jiya ka mata dukan fita wasan dare?" Abba yace
"to wai me za'a yi wa ummi ne ta zama irin
sauran yara?" umma tace,"addu'a ce Abba,kuma
muna yi kullum." ya juya cikin bacin rai,layin su
Amina kawarta ya nufa,don bata wuce can.duk da
cewa Amina bata kaita rashin ji ba. can din kuwa
ya sameta,ta tara zugan yayan layi sai tsokanar
fada suke yi,ita ce shugaba. wata falwaya Abba
ya samu ya jingina yana kallonsu,don yana iya
tunkararta su diba da gudu. shi kam ba za ya iya
guje-gujen nan ba,duk wanda yazo wucewa sai
sun tsokane shi,wani su jefe shi,wani kasa zasu
watsa masa su gudu wani kuma rigarsa zasu ja.
c can wani shida budurwarsa sun zo wucewa ta
fizge ledar hannunsu ta watsar,sannan suka ruga
da gudu. tayo gurin da Abba ke tsaye bata zaci
da mutum a gurin ba,sai dai taji anyi caraf da
ita.sai da Abba ya zabga mata koso a tsakiyar
kai har tayi fitsarin wuya,sannan ya tasata har
gurin mutumin data yaga ma ledar. suna
tsugunne suna tsintar lemunsu da ayaba ya
ce,"malam ga wadda ta yaga muku leda." da
zafin nama mutumin ya mike,Abba ya
ce,"gata"mutumin ya shakota yace yau sai naga
ubanki." Abba ya ce,"ko kara ka kai gidansu nine
zan hukuntata,don haka gata na kawo maka
kanwata ce kuma naga lokacin data tsokaneka."
jikin mutumin yayi sanyi ya ce,"na gode bawan
Allah,taje taci albarkacinka." Abba yace "daka
nade ta." mutumin yace,"ba komai,ke kuma ki
canza hali ke mace ce." Abba yace nagode"
sannan ya tasa ta zuwa gida.

Bokiti ya cika da
ruwa ya dora mata,,umma rasa bakin magana
tayi daya sanar da ita tsokanar daya tarar da
ummi suna yi.

Daga karshe ta ce,"Allah ya
shiryaki,abind ya sameki kada ya sami sauran
dangi.

Alhaji kuwa daya sameta dauke da bokitin
tana kuka tana fadin "yaya Abba na tuba,bazan
sake ba." ya ce,"uwata bakya ji ne fatan Allah
yashirye ki."ya nufi dakinshi.tsohuwa takaicin
Abba ne ya hanata fitowa tayi magana. nata
ganin,ummi bata wuce fita tayi wasa da
kawayenta ba,a cewarta ba laifi ba ne. amma an
bi an tsangwami yarinya,an hanata walawa.sai da
Abba ya gaji dan kanshi sannan ya sauke mata
ruwan.

Sannan ya mammaka mata
takalmi,sannan ta shige dakin
tsohuwa.tsohuwana daga kwance ta dubeta.

"yaga dama ya kyaleki?kai mai sunan malam
akwai mugunta.zo ki kwanta." cikin kuka ummi
tace,"kayana sun jike,bokitin ruwa fa ya dora
min."tsohuwa tace,"barshi da halinsa,ace mutum
ba zai sake ba?" ummi tace,"ai sai na rama,shima
din sai yayi kuka."tsohuwa ta ce,"a'a,kada ki
soma zancen ramakon nan.kin san ko kin rama
ke ce zaki kwan ciki." ummi ta ce,nifa sai na
rama."tsohuwa ta ce,"baki gaji da shan wahala
ba kema da shegiyar gaddama,ga zanina nan
kikin raki ciro ki daura kizo ki kwanta." ummi tayi
lamo bayan tsohuwa tana tunanin dame zata
rama abinda Abba yayi mata jiya.har bacci yayi
gaba da ita waiwaye.............

SULAIMAN shine
asalin sunan Alhaji babba,Aminu kuma shine
Alhaji karami. tsohuwa itace mahaifiyar su,kuma
su kadai ne yayan data haifa.Asalinsu yan
zamfara ne a kauyen daji a karamar hukumar
kauran-namoda. malam Idris mahaifinsu shine ke
zuwa yawon fatauci,har Allah ya zaunar dashi a
garin kano,da matarshi Habiba. sunzo da
yayansu guda biyu,sulaiman da Aminu.sun yi
karatun muhammadiyya mai zurfi,amma basuyi
karatun boko ba. sannan ya dora sukan harkar
kasuwanci,Allahya albarkaci kasuwancin Sulaiman
inda harkoki suka bude mishi cikin kankanin
lokaci. matsalar shi daya rashin boko,malam
idrisu mahaifinsu yana daya daga cikin wadanda
basu amshi boko ba lokacin da tazo.

Don haka
sam bai saka yayansa ba.Sulaiman ya auri
Suwaiba wadda suka dauki watanni suna
soyayya,ita yar unguwar sheka makaranta ce.

Amma asalinsu yan Daura ne jihar Katsina.kafin
aurensu sai da yayi gini a unguwa uku gidaje
guda biyu iri daya.

Ya ce Aminu kaninsa ya zabi
gida duk da cewa a lokacin baiyi auren
ba,wannan abu yayi wa mahaifisu dadi. yayi ta
shiwa Sulaiman albarka,don haka sai aka rufe na
Aminu,yayin da sulaiman ya tare a nasa da
matarsa Suwaiba. / ZURFIN CIKI book 1 part 2
ZURFIN CIKI book 1 part 2
Posted by Bashir Sani Fesan on 14 Dec 2016 - 21:40
Kwanci tashi 5yrs ta miqa suwaiba bata taba ko
batan wata ba. awannan yr ne mahaifinsu ya
cimma 1yr da rasuwa. saida aka watse makoki
danginsu na qauran-namoda suka koma. sannan
sulaiman yace da aminu, to ni xan dauki tsohuwa
in maida ta gidana,kai kuma aminu ka fito da
mata kayi aurenka dan mu xauna kusa da juna.
tsohuwa ta saka kuka tace wannan yaran nidai
da ka barni na xauna da gidan xai xama kufai.
sulaiman yace tsohuwa kiyi haquri, sai a saka
haya.aminu yace haka xa ayi. daqar tsohuwa ta
yarda dan tace ita wannan gidan mutuwane xata
rabata dashi, dan gidane me tsohon tarihi a
gurinta. ta ce gidan da mijinta ya rasu gidan da
ya kawo ta tun tanada jajayen sawunta. suka dai
lallabata. lkcn da aminu ya gabatar da sahura a
matsayin matan da xai aura, tsohuwa ta tuma ta
ce ba ta laminta ba, don kuwa kowa yasan
mahaifiyar sahura gun masifa. sanna sahurace ta
gajeta. aminu sai ya watsar da mgnn auran
gabaki daya har tsawan lkc. sulaiman yanata
roqan tsohuwa ta amince, dan ya lura aminu yayi
nisa.

Ba yadda tsohuwa ta iya, dole ta amince,
aka sha biki ta tare gidan aminu. mai hali dai
baya fasawa, dan sahura batasan hulda da
suwaiba da surukarta, gashi daga kawota ko
2mth bata yiba ta kama fada da yan unguwa. a
cikin 3yrs sahura aka samu ciki. lkcn sulaiman ya
samu xiyarta qasa mai tsarki shida tsohuwa dan
sauke farali. sunyi addu'a allah ya bashi xuri'a
shida aminu.suna durowa gida suka samu lbrn
cikin sahura, murna a gun sulaiman tamkar
matanshi ne keda cikin.lkcn haihuwa tahaifi da
namiji murna gun yan uwa biyu ba'a magana,
anyi shagalin suna inda yaro yaci sunnan mahai
finsu wato idris shine suke kiranshi abba.

Sannan
Ahaji Sulaiman ya biyama qaninshi kugeran
makka daga nan ne aka samu ahj Babba da ahj
qarami tun abba yana jariri ahj babba da
matanshi suke dawainiya dashi Sahura ba taso
saidai ba yan da xaitai da ita. domin alj qarami
na gama shirin fita xai saba shi sai gidan sai yayi
kukan nono ake maida shi, saidai tayi ta mitar
cewa anriqe mata yaro gidan,sahura dai in an
kawoshi bata isa taxoba dan tasan tsohuwa
tafita danja.duk da gugar xana da haibaici da
sahura take antayo ma suwaiba ta katanga ko
inta je gidan, baisa ta daina dawainiya da abba
ba. cikin hakane sahura wata ran sahura ta tashi
da xaxxabi mai tsanani da amai, shine taje asibiti
ganin likita ya tabbatar mata da tana dauke da
ciki.ko da ta fadama alj qarami ba qaramin murra
yayi ba ita kuma ta batarai, yace tunda abba
yana tafiyan shi ko ina ayaye shi.
Chapter 2 · 0% Book details