← Book details Zurfin Ciki Part 1 - 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 63

Sashe 3

Zurfin Ciki Part 1 - 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da yamma
bayan yadawo kasuwa ya shiga gaida tsohuwa
shine yake gayamata xa'a yaye abba. tace
saboda me? ku barshi yayi 2yrs. sai yace ai uwan
tanada juna biyune, shi yasa, daman sha waran
da nakesan fada maki shine xanba yaya shi
kyauta har abada.tsohuwa tace kai amma ka
kyauta.

Washegari da safe shine ma yayi ma
abba wanka tana kwance ya shirya shi, sannan
yace mata ta hada kayanshi duka dan xan kaishi
gidan ahj babba gaba daya. tace kana nufin kayi
kyauta dashi gaba daya? yace ea. tace tabdi!,ba
xai yiwu ba. infishari banxane kaxa tayi mana. su
wa yace kada su dage su samu nasu dan? nima
wahala nasha na haifi dan, ba shago na bude ya
fito ba....sam bai kulata ba, ya hada kayan yaran
ya fita. ya shiga gidan ahj babba da shi. dakin
tsohuwa ya shiga, nan ya samu ahj babba suna
gaisawa, yace yauwa, dama gurinka naxo yaya.
abba ya sauka daga jikin babansa yaje jikin ahj
babba da gudu, ahj ya dauke shi ya rungume.

Ahj
qarami ya keqa ya kira suwaiba,ta shigo ta xauna
sai ahj qarami ya soma jawabi da cewa. tsohuwa
ina san ki xama sheda, yaran nan na ba yaya da
suwaiba har abada.ahj babba yasake rungume
yaran a jikinshi wani saban son shi ya ratsa shi.
idanshi suka kawo qwalla, suwaiba ta sa kuka
tace mun gode da wanna abu da ka yi mana.

Allah ya bamu ikon riqeshi da amana. ahj babba
yace bani da bakin da xan maka godiya, saidai
ince allah ya qara xumunci. ahj qarami yace haba
yaya dana nakane, saidai inasan abba ya xama
xaka kai daya. tsohuwa tace allah ya maku
albarka daku da yayanku, kaima allah ya baka
haihuwa. sukace amin.

Sahura kuwa mijinta na
fita da yaro, itama ta xari hijabi ta nufi gidan
iyayanta, ta shaida ma mamanta cewan aminu
yayi kyauta da danta, kuma yaba mutanan da
basa qaunan ta. nan da nan uwar tahau masifar
cewan ba xai yuyu ba, ai dole ya baki danki.
shiko uban cewa yayi ai ikon sane, dan haka
baiga laifinsa ba dan yaba dan uwansa dansa.
sannan yace ,ta tashi ta koma. uwar tace ba xata
koma ba, ya ce ta xauna. bai sake bi ta kansu ba,
ya ci gaba da harkokinsa. shiko ahj qarami cewa
yayi baxai bita ba, lokacin da ya dawo ya samu
batanan, sannan bai fadama dan uwansa ba har
aka kwana. sukuma su suwaiba basu fahinci
sahura batanan ba dan ba hurda suke ba, saida
kukaxo cin abinki ahj qarami bai futo da kwanu
ba. sannan wan yace iyalin naka bata nanne?
yace yaji tayi, niko baxan bita ba. ahj babba yace
akan wani dalili ne? ahj qarami yace ban sani ba,
na dawo gida ban ganta ba. da safe ahj babba ya
tashi gaba sukaje gidan, sahura ba kunya tace
danta takesan ya dawo mata dashi, inhar yana
san xama da ita.

Ahj babba yace, indai danta ne
xai maido shi. ahj qarami yace shi kuma inhar sai
an dawo da dan to ya haqura da auranta. kuma
na cikin ta ma inta haife shi xaixo ya ansa ya
qarama wansa inya so yaga yadda xatayi. duk
juyin da akayi yaqi yarda daga qarshe ma tafiyan
shi yayi. ubanta yace da ahj babba kaima jeka
yadda suka so haka xasu yi. satinta guda taka
abincin kirki gagaranta yake yi, ita kuma uwan ta
daina samun wani abu daga gun sahurar ke kawo
mata. dan haka suka yanke shawaran ta koma,
duk da haka saida ya shareta na kwana uku
sannan ya sakar mata. haka ta haqura saidai
tasha alwashin dun runtsi sai danta ya dawo
hannunta. sannan ta kulla sabuwan gaba da ahj
babba da suwaiba kuma tace duk tsohuwa ce
takitsa abin. abba yana samun kulawa tare da
tarbiya mai kyau.sahura ta haihu ta sake samun
da namiji aka samasa bashir, daga nan haihuwa
akai akai..

Tun abba yana qarami ya koyi wasu
halaiya na ahj babba. da farko, sallar
asuba,axahar, laasar, magrib da isha. ahj babba
kan tasa abba suje masallaci da rana kuma
umman sane ke turashi. ranan jumaa ahj na
dawowa gida dan ya tafi dashi. dan haka sallah
ta xauna ma abba da xaran lkc yayi xai fara shiri
yi. sannan ya iya sadaka dan dasunje yana bashi
kudi ya rabama almajirai ko yasa a asusun
masallaci. sai xumunci aduk lkcn da ahj babba
xashi xanfara yana tafiya da shi. ya tashi da san
iyayan shi matuqa bai taba sanin basu suka haife
shi ba. duk da cewan duk lkc da ya shiga gidansu
umman bashi takan cemai bafa umman kace ta
haifeka ba, nice na haifeka. riqonka muka basu. in
yaji haka sai yace allah kiyaye. sai ya baro gidan
ita kuma taita xakinsa. inya fadama umman shi
saitai murmushi ta rungume shi. ya ce aidai kece
ummata ko? ita kuma tace nice ummanka rabuda
ita kaji. abba yanada tausayi dan haka ya
taimaka ma ummanshi aikin gida. shekara sha
biyu ya sauke kur'ani.a lkcn ne ya gama pry ya
samu xuwa js1 Abba makarantan masu kudi ya
ke yi.ita kuma sahura duk yaranta ta batasu,
musamman bashir. duk lkcn da akace yaje
makaranta inyace ya gaji, saitace ya xauna kaje
gobe. ko ahj babba ya korashi sai dai ya labe
inya tafi shi kuma ya dawo. yafi san xuwa qwallo
ko shagon game. to hakama qannansa duk sun
dau irin tarbiyyan uwarsu. cikin haka wata ran
umman abba ta tashi da matsananciyan mura,
lkcn ahj babba yaje legos don taho da kaya. ahj
qarami ne yakaita asibiti bayan gwaje gwaje, an
gano ciki wata biyu da yan kwanaki. murna gun
ahj qarami tamkar yayi tsuntsuwa yaaje ikko ya
fadama ahj babba. suna isowa ya shiga gun
tsohuwa ya sanar da ita. nan take tasa kukan
murna.ita kuwa suwaiba tamkar mafarki, sai
kunya ta isheta. lkcn da ahj qarami ya fadama
sahura, sai cewa tayi um, bana an tabuka, ni dai
gani da cikin na shida amma sai yauxu ta samu
daya. ahj qarami yace kinji matsalanki, ke ba dai
kiji wani ya samu qaruwa ki taya shi murna ba,
sai dai baqin ciki. ta ja tsaki bakin cikin me
xanyi? tunda ni ga nawan. ciki mai laulayi
suwaiba ta samu, wanda duk abin da taci sai ya
dawo. wannan lamari ya daga ma ahj babba
hankali da abba, duk aikin gidan abba ke yi, ga
makaranta, ko an hanashi sai yayi.dan haka aka
dauko harira qanwar suwaiba, wanda mijinta ya
mutu. umman abba dai bata samu kanta ba saida
cikin yayi wata biyar. sannan ta samu sauki.lkcn
sahura tanada cikin wata bakwai, lkcn haihuwa ta
haifa mace, murna gurinta kamarme, dan sai
yanxu ta samu mace. safiyar talata umma ta
tashi da naquda, hankalin ahj da abba ya tashi
matuqa. duk da tsohuwa tana ta kwantar masu
da hankali, ranan abba ko makaranta bai jeba,
duk da san makarantansa, har suka dawo sallan
axahar shuru. ahj babba yace tsohuwa bari na
samo mota akaita asibiti. tace to. yana fita ba
jimawa ta haihu. ta santalo yarta mace mai
matuqan kama da ahj babba. tsohuwa tace da
abba,mai sunan mlm bi su ahj kace sudawo ta
haihu. dama harira tasa ruwan wanka lkcn da
suka xo ta fito daga wanka.nan aka wanke
yarinya yan barka sai xuwa suke amma sahura
saida aka.

Sahura saida aka kwana sannan ta
shigo. ta dauki yar ta taba baki tace wannan yar
baqinqirin haka sai idanu daqwa daqwa. wata
mata da taxo barka tace ai wannan yar sak
abba,suna kama sosai. sahura ko kunya ta ce
basa wani kama da abba. da tasamu kyan abba
da tayi kyau, umma tayi ma matan alama da
haunu tai shuru. ranan suna taci sunan tsohuwa,
wato habiba, dan haka umma ke ce mata ummi.
abba yana ji da ita, saidai in yanasan tsoka nanta
sai yace dubeta ta ba ummata wahala, sai na
xaneki kika girma kika qi mata aiki. umma taita
masu dariya. tsohuwa ma naji da ita dan guta
take wuni. tunda ga kan ummi umma bata qara
haihuwa ba. abba yana aji uku suna qoqarin xana
(j.s.c.e)ya dage sai ahj ya saka shi shagon dinki.
ahj yace abba kabar batun dinkinnan ka tsaya a
karatunka. yace ahj nidai ina so kaga inna iya su
umma sun huta dakai dinkin su gidan laminde.
umma tace ka barshi yayi ahj sana an hannu ai
tanada dadi, kaga in ya gama bokon ba bai samu
aiki ba xaya riqe kanshi da sana anshi. ahj yace
to shi ke nan Ahj yace, to shi kenan, wane shago
ka ke san shiga inkai ka? yace, na can bakin titin
nan, in da kake saya na lemo. ahj yace shi kenan.
mafarin shigar abba gurin koyan sanaa kenan.
ummi ta taso da rigima, tsiwa tare da tsokana,
wanda yasa suka daina shiri da abba sam. abba
ne ya kaita makarantan boka da islamiya, kullum
yaje daukota sai ya raba fada ko ya bada hakuri.
umma kullum addua take fili da xuciya da lokutan
sallah, allah ya shirya mata ummi. ita kuma tata
kalan quruci yan kenan inta girma xata daina.
tsohuwa takance aini me sunana kingama min
komai, domin banasan ragon da, da in kai qara
gara akawo min na bada haquri. duk lkcn da tayi
wannan kalman sai sunyi fada da abba, dan cewa
yake ai dama tsohuwan nan tuni na ane kin daure
mata gindin ta siqa tsokanan yayan mutane. ita
fa mace ce ba namiji ba, shi kenan bata da aiki
sai dambe? tsohuwa takance batta tayi. tunda
ganan abba basa shiri da tsohuwa. ita kuma fati
yar sahura kamar ummace ta haifeta dan bata da
hayani. ummi kuma kamar sahura ta haife ta.
Chapter 3 · 0% Book details