Sashe 35
Zurfin Ciki Part 1 - 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta soma kuka haba Baban Walid, wane
laifi na maka da zaka yanke min irin wannan
mummunan hukuncin?
Ya ce, "Don Allah fita, ta
ce sai ka fada min dalilin yin auranka, ba za ka
bar ni in ji da rashin dana ba ko? ta mike an
zugo ka an ce kayi aure, to bisimilla.
Ta fita ta
zari mayafi tayi gidan Umman Bashir.
Abba ya
rungume 'yarshi ya yi laf a kan katifa shawara ya
yanke zai tura magabanshi gidan su Zainabu ba
tare da ya sake bi ta kan Zainabun ba. * Umma
ta leko dakin Tsohuwa, Ummi kin san na ce miki
kizo ki kwashe kayanki daga dakina ki adana su
ko?
Kin san dai yau duk na nesa za su iso, ki cire
wadanda za ki bada.
Tsohuwa ta ce, "Suwaiba
yarinyar nan ina kallonta jiya bata runtsa ba,
sannan da Asubahi a zaune tayi sallah.
Umma ta
shiga dakin warwas take a kan gado, Umma ta
tasheta zaune Ummi ciwon kai ta keya ga jiri da
ta ke gani daga zaune. 39..
Umma ta ce taso ki
dan watsa ruwa ki karya, mikewar da zata yi sai
ta sulale a kasa sumammiya, nan suka dau
salati, Toshuwa kam kuka ta saka.
Alhaji ya fito
wanka kenan ya ji Umma na salati, don haka
dakki ya shiga ya dauko waya ya kira Abba
lokacin yana kokarin shiga wanka.
Alhaji ya kira
shi, jin cewa Ummi ba lafiya zari mukullin mota
ya fito.
Sai da suka kai asibiti sannan ya lura da
silifas ya fito da jallabiyarshi ta wanka, Lkitan ma
bai zo ba lambarshi suka amsa Abba ya kira shi.
Ya duba Ummi sosai da kyar suka samu
numfashinta ya dawo, sun daura mata ruwa
sannan aka kaita wani daki.
Likitan ya ce su zo
ofishinsa, Ya kalli Alhaji ya ce, "Gaskiyar magana
yarinyar nan tana bukatar kulawarku, ciwonta
baya son sakaci.
Jininta ya hau ya wuce matakin
da zata iya samun mutuwar 6arin jiki.
Su Alhaji
suka dauki salati,, ya ci gaba da cewa yanzun dai
addu'a zamu ci gaba da yi.
Allah yasa in ta
farfado kada wata matsala ta biyo baya.
Sannan
ya basu takardar magunguna".
Alhaji ne ya amsa
don Abba fita yayi ya koma dakin da Ummi ke
kwance.
Idanu ya zub amata, sam bai san cewa
kuka yake ba, sai da Alhaji ya shigo ya dafa shi
tare da cewa, "Haba Abba ba girmanka ba ne
kuka.
Addu'a za ka yi Allah ya bata lafiya".
Ya
share hawaye.
Alhaji don Allah kada ka sanar da
Umma abinda Likitan ya ce, Alhajin ya ce ai
dama ba zan fada mata ba.
Bari in je sai tazo ga
takardar maganin inta zo sai ka siyo, ya ciro kudi
ya mika ma Abba, Abba ya ce a'a da kudi a
jikina.
Alhaji ya ce ka amsa ka kashe kudi cikin
kwanakin nan ina sane da duk lokacin da na ce
kazo ka siyo wani abu sai kawai in gan ka da shi
ban da kayan dakin da ka siya musu, Abba ya ce
ai ina da shi ne.
Bayan fitar Alhaji Abba yaja
kujera ya zauna ya zabga tagumi tare da tsura
ma Ummi ido, a zuciyarshi fadi yake ALLAH ka
tashi yarinyar nan lafiya, Allah kasa kar ko ina na
jikinta ya nakasa.
Alhaji ya fada wa Umma an ba
Ummi gado, don haka ta shirya su wuce.
Abba ya
tashi ya nufi ofishin Likitan, bayan ya kwank
wasa
Lokitan ya ba shi izinin shiga, ya same shi yana
rubuce-rubuce.
Ba tare da ya dago kai ba ya ce,
"Zauna sai da ya kai aya rubutunshi sannan ya
dago kai ya kalli Abba "Ba dai mai jikin ba ce
ko?" Abba ya ce, "a'a ina son ne nima agwada
nawa jinin, Likitan ya ce kana jin jikinka ba dadi
ne?" Abba ya ce, "Eh da har yasa a dauko fayal
din Abba kuma ya tasa ya dauki abin gwaji.
Bayan ya gama ya zaunar, ya tsare Abba da ido
wai kun yi gadon ciwon nan ne?
Abba ya ce,
"A'a, Likitan ya ce, "Jininka ya hau, sai dai ba
sosai ba.
Kila don kai namiji ne kana kokarin
kauce ma abubuwa.
Zan rubuta maka magani na
sati daya, kuma ka dinga kokarin yin bacci a kalla
na wa shida kada ka dinga yawan tunani.
Kaga
kanwar nan taka, sai sa'ar gaske zata tashi
lafiya.
Ku dai cigaba da addu'a, zata yi bacci na
tsawon awa tara ko goma.
Ina son daidai lokacin
da zata farka ya kasance ta soma dora ido a kan
wanda suke shiri ko wanda ta fi so a cikin
mahaifanta ko danginta, Abba ya ce "To."
Lokacin da ya koma dakin su Umma sun zo har
da tsohuwa, nan Abba yake fada musu abinda
Likitan ya ce game da farkawa in tayi.
Koda bude
bakin tsohuwa sai cewa ta yi ai ko dai ba a bar
mai sunan Malam ba, tunda an ce wanda suke
shiri, don in taga mai sunan Malam karasawa
zata yi. * 22.
Duk da ana cikin wani hali sai da
su Alhaji suka murmusa.
Abba kam daure fuska
yayi yana kallon Tsohuwa, Umma ta ce, "Ai da ne
Tsohuwa.
Yanzun shiri suke tunda ta daina rashin
jinta".
Likitan ya shigo ya sake musu bayani
kamar yadda ya yi ma Abba, sannan ya ce su
bata guri kada zantukansu ya farkar da ita a
samu matsala.
Suka fito, Umma ta ce da Abba ya
tafi gurin aikinsa, su Alhaji ma suka fita tare da
Abba.
Fati ta je gidansu Sahabi dan uwansa yana
kankarar rake a kofar gida, inda yake saidawa ta
tambayi Sahabi.
Yaron ya ce mata ya ffita, ta ce
To in yazo kaa ce masa Ummi tana asibiti ba
lafiya, an bata gado.
Karfe uku ya iso asibitin
hankali a tashe, sun gaisa da Umma ta raka shi
dakin, hankalinshi ya tashi da ganin Amaryarshi
kwance a gadon.
Abba kam yana gurin aikinshi
amma hankalinshi na Asibiti, su Alhaji ma duk
nan suka nufo, Abba sai da yayi magriba sannan
ya shigo asibitin.
Jikinshi babu karfi, bai matsa
sai yaga farkawar Ummi ba ne saboda yasan da
gaske ba shi ne ya dace idanunta su soma arba
da shi ba, ya samu su Umma da su Alhaji.
Sahabi da abokansa duk suna gurin, ya gaida su
tare da tambayar ko ta farka?
Umma ta ce har
yanzun dai shiru.
Ya nufi cikin gurin Likitan suka
gaisa, ya ce Likita har yanzu ba ta farka ba.
Suka
jera zuwa dakin, Likiran yana cewa cikin wannan
dan takin zata farka, In sha Allahu.
Sun shiga
takin tana dan motsi suka nufi gadon Abba ya ce
Ummi.
Likitan ya daga mishi hannu alamar yayi
shiru ita kam daidai lokacin mafarkin Abba take
wai suna tafiya ya rike mata hannu sai ga
Sahabi.
Yana zuwa ya kama hannunta tana
tirjrewa, sai janta yake zai fita da ita, Abba yana
tsaye yana kallonsu.
Ita kuma sai kiran "Ya Abba!
Ya Abba!!
Take yi.
Likitan ya kara kunne gurin
bakinta ya dagowa yayi ya dube shi.
"Waye Yaya
Abba?" Abba ya ce ni ne.
Liitan ya ce, matsa
kusa, ya kama hannunta.
Ummi.
A hankali ta
bude ido.
Ya Abba!
Ya abba, zan sha ruwa, ya ce
to ya kalli likitan za ta sha ruwa, Likitan ya ce,
"A'a bari ta dan kara warwarewa tukunna.
Likitan
ya kama kafafunta ya dan matsa, sannu ko.
Ta
kalle shi, kin ji zafi?
Bata yi magana ba ya dauki
allira ya 6are ya dan soka mata a tafin kafa ta ja
kafafunta alamun taji zafi.
Ta yunkura zata tashi,
Ya abba zan tashi, ya tayar da ita zaune.
"Likitan
ya ce Alhamdulillah, Abba ya kalli likitan, ba
matsala kenan?
Ya ce, Ina zaton haka insha
Allah, Abba ya ce "Alhamdulillahi, ya jinginata da
jikinshi, sannu Ummina. 41....
Alhaji ya shigo
yana cewa, "Ina Abba ne?" ya ganta zaune a'a ta
farka ne? ya kama hannunta sannu uwata.
Ta
kalle shi.
"Ina Ummata?" ya ce, "Bari in kira miki
ita".
Yaje ya sanar da su, sun shigo da murna.
Sahabi ya iso gaban gadon.
"Sannu Ummi".
Ta
kalle shi sai ta kwantar da kanta a kafadar Abba,
"Ya Abba ina son in wanke bakina".
Ya ce, "To
bari in siyo miki Maclean din".
Ta ce, "A'a kada
kaje".
Ya gyara zama "To shi kenan." Umma ta
ce, "Me ta ke so?" Abba ya ce "Baki zata wanke".
Umma ta ce "Ai nazo mata da maclean da
burushin nata, don nasan ita gwanar wanke baki
ce".
Nurse ta kawo wani dan kwano na silba
Ummi ta wanke baki da taimakon Abba.
Likitan
ya ce, a bata tea mara zafi sosai, sannan a bata
magani.
Takaici dan'kam a zuciyar Sahabi, irin
wannan shigewa da Abba ke matar da zai aura
tayi yawa.
Kai shi fa wannan Yaya Abban bai
masa ba ma, don yana daure mishi fuska ko
gaida shi yayi d kyar yake amsawa.
Shi fa tun
ranar da a ka ce mishi Ummi ba cikinsu daya da
Abba ba ya ji ya tsane shi.
Umma ta ce, "Abba
an kira Isha'i.
Sahabi kaje kai ma ka huta yaran
nan tun tuni ya ke nan".
Abba ya kalle shi, "Ya
kamata ka tafi haka ko?" ya kalli Ummi sannan
ya dan rusuna "Sannu Ummi".
Ta ce, "Yauwa"
"Innata ta ce in gaida ki da jiki, ni zan tafi sai da
safe.
Me zan kawo miki?" Abba ya dube shi a
kule., "Don Allah Malam kaje ba za ta iya cin
wani abu yanzun ba".
Umma ta ce, "Abba".
Ya
kale ta, sai ta girgiza mishi kai alamun ya bari.
Sahabi jiki a sanyaye ya fice tare da cewa "Umma
sai da safe".
Ta ce, "To Sahabi, ka gaida Innar
taka".
Da ya fita ta kalli Abba "Wannan ba
halinka ba ne kada in kuma gani".
Ya ce "To
Umma". 23.
Su Alhaji sun yanke shawarar daga
auran Ummi a darua na Fati kawai, ita sati biyu
masu zuwa sannan ta murmure sai a daura nata.