← Book details Zurfin Ciki Part 1 - 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 63

Sashe 54

Zurfin Ciki Part 1 - 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yace akwai wani leshi
dan sai maku yana shago, Tun wancan satin
naso In zauna In dinkashi da kaina don mai tsada
ne.

Tace nawa ka siyeshi, yace dubu biyar ko
wane daya, bishira ta tabe baki.

Na zaci zakace
sha biyar wai dubu biyar, yace matsalata da ke
rainuwa yace bari zansa a dinka maku gobe ashe
sunan har yazo?

Tace a'a jiya pha ta haihu, ya
sake kallonta jiya?

Shine zaku tafi jibi?

Tace eh
mummy ce tace mu tafi jibi.

Yace a'a kibari sai
ana gobe suna kije.

Kafin lokacin ma na samu
wasu kudi da nike sa rai.

Sai na sai maki kayan
barka zanen maman da kayan baby.

Bishira ta ce
gaskia gobe zamu tafi, In ka sayi kayan barkar ka
aika dasu can wurin mummy yan tafiya Ranar
suna su kai mata.

Abba yace nifa ban amince da
tafiyar nan gobe ba.

Ban yarda ba.

Bishira ta ce
ba wai ina neman yardarka bane, ina fada maka
umurnin da mummy ta bani ne, ko ka mance
mahaifiyata ce?

Mamakinta ya cika abba, yace
mahaifiyarki ita zata baki izinin tafiya ko ni?

Umurnina da nata yanzu wanene...?

Bishira ta
katseshi kada kayi ganganci hada kanka da
mahaifiyata, ita ta haifeni ta raineni har ka ganni
kace kana sona Sannan ka dinga kokarin
kwatanta kanka da ita?

An fada maka kowa
baisan darajar mahaifiyarsa ba irinka?

Abba ya
mike ni ne bansan darajar mahaifiyata ba?

Tayi
shiru yace nagode Kuma suna na hanashi ma
gaba daya.

Zan gani Kuma Bishira ta ce zako ka
gani.ls / ZURFIN CIKI book 4 part 19
ZURFIN CIKI book 4 part 19
Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 14:14
Duk ummi tana jiyo su amman bata fito ba, tana
ta mamakin yarda bishira batasan darajar
aurenta ba, bare tasan girman miji.

Ranar da
zasu tafi kuwa ko a jikinta ta dibi tsummanta ta
nufi gidan su, Duk ta fadama mummy yarda
sukayi.

Mummy tace kinman dai dai talakan
banza shine zai hada kanshi dani, tafiya zakiyi in
yaso in kika dawo ya ce baya auren.

Abba ya
dawo ya samu dakinta a rufe, ummi na daka
sakwara a kofar dakinta yace ina bishira?

Ummi
tace ina ga ta fita, don ina daki bansan fitarta ba.

Ya daga waya ya kira aunty yace bishira tazo?

Aunty tace bata fada maka zasu tafi abuja bane,
Abba yace ta fadaman amman nace a'a sai ana
gobe suna zataje, ya kwashe komai ya fadama
aunty.

Aunty tace kayi hnkr don allah idan ta
dawo da kaina zan hadata da daddyn mu, Abba
yace kiyi hnkr aunty na gaji da halin bishira inga
wannan karo gwara kowa ya huta ni da ita.

Aunty
tace kayi hnkr Abba yace sai anjima ya kashe
wayarsa.

Zama yayi kan kujera dakin ummi yace
gaskia wannan karo bazai fadawa kowa ba ya
gama auren bishira.

In bai nuna mata kurenta ba
nan gaba zata masa abunda yafi wannan don
Haka yabar komai sai ta dawo.

Ummi kam
batason ya rabu da matarsa, amman kam saida
taga tarairaya cikin kwanu kan nan matsalarsu
daya, Abba yace ummi kodai asibiti zamuje ne,
ummi tace muce masu mi?

Yace muyi masu
bayani mana, ummi tace a'a.

Yace to muje mu
fadawa umma, ummi ta zare ido yanxu sai kama
umma wannan zancen?

Yayi murmushi.

Ai da zan
iya mata wannan maganar da tuni na mata,
asibiti ma abunda yasa banson zuwa sai likita ya
bukaci ganin wurin.

Ni kuma ina kishin wani
namiji ya kallan mi al'aurarki, ummi tace nima ai
shine, ya sake janyota jikinshi.

Yanzun Haka
zamu zauna?

Shine nakeson in fada maka naji
kana ka gaji da aunty bishira kila zaka saketa ne.

Toh don allah ka rabu da ita tunda ko ka saketa
sai ka auri wata.

Tunda nasan zama Haka bazai
yiwu ba.

Ta soma hawaye ya shiga lallashinta
yace Allah zai yaye masu.

Haka sukaci gaba da
rayuwa cikin kwanakin da bishira bata nan, ummi
tanason kalolin wasanin da Abba ke mata,
amman da yaso kwatantawa ko allah ya amshi
addu'a su ta warke saita kwace jikinta ya hau
bari tayi ta kuka.

Don Haka sai ya hnkr da
bukatarsa amman ya takura sosai, kuma yana
ganin dole yabar batun bishira yanxu don Haka
ya jaye batun saki amman sai dole ya nuna mata
kurenta.

Ranar data dawo kwananta takwas
Ranar ma bata da niyar dawowa sai da aunty ta
kira mahaifinsu ta sanar dashi, ya kirasu a waya
ya zagesu tas gaban mahaifiyarsu harda mai
jego.

Tace bishira ta dawo shine ya kira Abba da
waya ya bashi hnkr yace Duk irin wannan ta faru
ya kirashi ya sanar dashi.

Abba ya shigo da T.

V
guda 2 daya ya kai dakin ummi, daya ya kai falon
bishira wanda ya yanke kwadon.

Ummi tayi ta
murna bishira kuma ta daki Duk rashin kunyarta
gabanta sai faduwa yake, batasan ya zasu
kwashe ba.

Sai da taga baiko kalleta ba daga ita
har yar sannan ta dan saki jikinta, tasan ba zai
tsaya a fushi ne in taci sa'a.

An dauki sati guda
Abba baya ko kallon inda bishira ta ke ko Ranar
girkinta sai dai yayi kwanciyarsa a falonta.

Duk
da yana bukatarta Haka kuma ya janye yan
wasanin da yake da ummi don wahalce yake
bacci, ita kuma sai ta damu don ya saba mata
sai tayi tunanin ko laifin tayi masa ne.

Ita kam
bishira ganin zura ido ba zai kaita ba, don Haka
ta sauke zafin kai ta iske Abba a falonta wani
dare harda kukanta take bashi hnkr.

Wai sherin
shedan ne ba zata sake ba, Abba ya dubeta mi
kikayi?

Tace nidai ka yafeman, yace ashe kinsan
kinyi ba dai dai ba?

Ai inda ke ce saikin kara,
amman bari kiji na rantse maki duk kika kara
zuwa wani wurin bada izinina ba wllhi sai kinsha
mamaki.

Tace na yarda, abun mata da miji nan
dai suka sasanta, hakan nan dakin ta ya kwana,
suna shiri cikin satin don bishira ta fahimci mijnta
ita kadai a matarsa, yarda yake rawar jiki lokacin
kwanciyarsu. ***ummi na zaune idonta kan tv
Abba take kallo yarda yake watso turanci cikin
kwarewa.

Kullum kara sonshi take, ta kwantar da
kanta a hannun kujera, kusan sati guda kenan
tana lura da Abba.

Baya son ko taba hannunta
sannan ga wani shiri da yake da matarsa, sai dai
yazo yaci abinci ya dauki laptop dinsa ya raba
dare.

Inko yazo kwanciya saidai ya juya mata
baya sabanin kwanaki da yake mata makwanci da
hakarkarinsa, lokacin tasan babu inda keda dadin
kwanciya ga matar aure irin hakarkarin mijinta,
sam bata iya bacci sai tunanin abunda tayi masa,
amman yau din nan zata tmbysa ko laifi tayi
masa, Bayan yaci abinci yayi wanka ta dauko mai
zata shafa masa ya amsa da murmushi yace
barshi kawai nagode, ta dawo ta zauna, zaya fita
tace ina zaka ya Abba, yace aski zani, ko zaki
rakkani tace eh yace taso muje.

Suna tafe suna
hirar aikin shi, yace An koma kirkirar wani filin
kuma An saka shi ciki, yanxu abubuwa zasu kara
mashi yawa.

Sun isa babu layi An suma mashi ya
mika mata wayoyinsa guda biyu tana danne
danne kira ya shigo.

Nan take ta hade rai ganin
sunan dake jiki zainab dina, ya tmbyta da ido
waya kira ta sake hade rai, sannan ta mika masa.

Ya kalli sunan zainab sannan ya daga cike da son
ya zolayi ummi yace zainabuna.

Can bangaren
Duk da kallaman Sun mata dadi tace da ba
amman yanxu ta wani ce.

Yaya salis ya kawo
maka katin aurena?

Yace eh yabani tace ya
amarya?

Yace gata bari in bata ku gaisa, ummi ta
kauda kai tare da jan tsaki, yayi dan murmushi
yanason yanda ummi ke nuna kishinsa, salon da
take wurin kishinta daban ne.

Yace zainab Wai
tana gaisheki, zainab tace to ina amsawa.

Ka
gaida umma sannan ka sai masu anko kalla biyu
ne.

Abba ya naji ko kalla goma ne zan saya tace
to gobe kazo gidan mu nan ake sai dawa.

Ya kalli
ummi yasan kadan ya rage ya kaita bango.

Ya
danne dariyar da ta taso masa yace gobe kikeso
nazo gidanku zainab?

Tace eh don gobe za'a
kawo wasu kayan, yace to zanzo, ummi ta zaro
ido ta mika tsaye dai dai lokacin da aka gama
askin.

Yayi sallama da zainab din sannan ya
shiga karkabe jikinsa.

Ummi kam tuni ta kai bakin
kofa.

Ya sallami mai askin ya isketa Sun jera
yanxu ba kamar daxun da suke fira ba.

Sun kusa
layinsu yace muje mu gaida su umma tace ni
bacci nakeji baice komai ba, Sun iso hijabi kawai
ta cire ta kwanta, yace Wai lafia don zainab ta
kirani tun dazun kin kasa sukuni?URFIN CIKI book 4 part 20
ZURFIN CIKI book 4 part 20
Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 14:17
Ummi ta taba baki, Allah yakawo ta lpy.

Ya ce ni
ban soba gsky.

Sbd ke ummi tadafa kirji, sbd ni?

Ni ya abba, kada kasa duniya ta zage ni, Tare fa
nasameku?

Yace to ni dai kada kiga kamar da
son raina, tace don Allah ya Abba kabar zancen
nan.

Kaje kagyar mata dakunanta don su kamal
bazasu iya ba, yanufi gurinsu ganin kamar ya
damu yasa itama taje tasa musu hannu don dai
ya saki ranshi, sun gyara tsaf ummi ta goge
sannan ta rufe dakin.

Har magriba bishira bata ji
an ce za'a maida taba, sai ta dauki wayar
kanwarta ta kira shi wai yazo don Allah
yadauketa.

Tsakanin mata da miji sai Allah, nan
ya tausaya mata yace zaizo, kafin ya isa sai daya
sai mata waya irin dai ta hannun ummi.

Har cikin
gidan ya shiga suka gaisa da babanta, yayi
murna sosai yayi tawa Abba godiya, tare da ba
shi hakuri yace yasan yanda ta horu zai gata
canza da yardar Allah.

Yasa aka turo ta yayi
mata nasiha, sannan ya gargadeta da cewa inhar
ta bari mijinta yakawa kararta zatayi mamakin
abinda zai mata.
Chapter 54 · 0% Book details