← Book details Zurfin Ciki Part 1 - 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 63

Sashe 11

Zurfin Ciki Part 1 - 4 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ummi party
xatayi na murnan barin gidan shi.ahj ya ba umma
wayarshi kamar yadda ya fada mata,ya ba abba
ya suya mata layin mtn kamar yadda ya fada
mata.ummi tafi kowa murna da wannan
wayan,domin in umma ta aje takan dauka tayi ta
latse latse,har dai ta iya abubuwa a wayan
saboda ta iya karatu.kwanci tashi bikin abba ya
rage saura yan kwanaki.duk gida biyun sai shirya
shirye suke,mu samman gidan amare saboda yan
mata biyu xasu auran.gidansu abba tuni ahj yasa
an masu fantin gidan biyun,gidan ango kuwa ya
sha gyara da fenti.ahj ya sabunta mishi qofofi da
wundunan gidan, batun lefe kam dama tuni ya ke
sayen xannuwanshi da kadan da kadan yana
kawo ma umma tana adanawa.dan haka ahj
karami yana kawo akwatuna umma ta fito da
kayan dan tasan me xa a qaro.sannan ya yaba
da hankalin abba.wannan ya nuna mishi cewa
abba xai iya riqe gidanshi.lalle sana'an hannu
tana da amfanh ga yayanmu a wannan xamanin
namu.umma tai mashi lissafin sauran abubuwan
da xannuwa da leshi xuwa shadda,tace ahj dan
allah adubo mana masu tsada, Ahj yace suwaiba
xan yi daidai qarfina,ba xan yi qarya ba dan sun
san cewa dana talaka ne,kuma suka ba shi.umma
tace,sai batun abin da xa a ci.yace suwaiba
kenan,saunawa xakimin lissafin kayan abincin?na
xata ma xakice kayan sawanku?umma tace suma
a kawo mana da wuri dan mu dhnka da wuri,ba
abba xan ba c saboda harkokin sun masa
yawa.saura sati uku biki aka kai lefe.hjy xainu dai
unguwa ma ta tafi a ranar,danginta na maigidan
su ne suka amsa.sai yatsina suke tare da raina
kayan da suka duba ma sai um da um suke
cewa,wata tace to an gode fa,tunda taji ta gani
mu menene namu?suka ba da tukuici, nan dai
yan kai lefe suka dawo jiki babu qarfi.koda suka
dawo suka sanar da umma sai tace ku qyale
su.mu dai mun yi daidai qarfinmu.umman bashir
kuwa da qannanta suka kai mata labari cewa,tayi
ina ko xa suyi maraba da kaya?suwaiba ta karbe
mishi kudi bada xuba kayan kirki ba,banga
laifinsu ba.ummi kam sai dibar ma umma kayan
abinci take a boye tana kaiwa gidan maman iman
maqotansu ne,matan suna shiri da ummi, don ita
rayuwar ummi dariya take bata,ta gwado shinkafa
ta kawo,taliya,ta tsiyayo mai,ta ce sauran kayan
miya da magi,har nama debowa zanyi. maman
imam ta ce lallai kawayenki zasu sha party.
ummi ta ce tab ai dole inyi party zan rabu da
alakakai sarkin mugancin duniya. maman imam
ta saka dariya,ummi ta kuma fita da gudu tana
fadina na tuna inda gishiri da maggi suke. daga
gidan amare anzo anga gidan amarya,nan ma sun
tafi suna mita,fadi suke "bishira batayi sa'ar miji
ba,wata ta ce ya aureta ne don kudin ubanta.
koda suka je suka fada ma hajiya zainu fasalin
gidan,daki uku ne duka falle dai dai sai kicin da
bayi a tsakar gida. kanwar zainu ta ce,"kai
gaskiya bishira bata yi dabara ba.hashimu dan
gidan Alhaji mansur ya jima da sanar dani ya
kamun bishira." hajiya zainu ta ce,"shi kadai?ko
yayan abokan babansu nawa ke sonta?tunda taki
tsayawa tayi karatu ta zabi ta auri tela,ba shi
kenan ba?dubi gidan ubanta amma ta zabi zama
a wani gida dakuna jere sai ka ce ajin
primary."lol. suka ce,"kwarai kuwa kamar ajin
makarantar gwamnati."ta ce,"shi kenan ai kaya
dai asai mata daidai tsarin gidanta ba iri daya za
a sai musu da Aisha ba." sun siyo sunje sun jera
komai ras,yanzun kam sai daura aure ya
rage,Abba da abokanansa walima kadai ya shirya.
can gidan ne suke ta bukukuwansu irin ma masu
hali.shi kam dai yasan yan'uwanta ba sonshi
suke ba. sam be je gurin shagalinsu ba. ranar
lahadi aka daura aure,misalin karfe goma na
safe,unguwar kam ta cika da mutane da motoci.

Abba da zugar abokananshi salisu yayan amare
yayi musu jagora cikin gidan. sun gaisa da
mutane sannan suka fito kowa fadi yake."kai
amma angon bishira zankadede dashi
tubarkalla."gashi Abba da iya daukar
wanka,tsafta ce dashi ga son kamshi.

KAI MATA
IYAYEN GULMA.

Can gidan ango ma anata
shagalin cin abinci, jama'a dangi da makota sa
gudunmawa suke ba umma tana a'a amma sai
ace ta rike sabida ita mutum ce mai kyauta.
umman bashir kam sai takaici take ji,kowa ya
shigo sai dai ya ce mata."Allah ya sanya
alkairi"kawai musamman ta shigo gidan don taga
ko ana ba umman Abba ne.

Nan fa na fita ta
koma gida babu ko kunya tana ta masifa, fadi
take "lallai suwaiba,gudunmawar auran dana duk
ita ce ke karbewa? gaskiya naga sai dai amin
Allah sanya alheri a wuce,to da sake,ni na haifi
abuna ta bari sai ta tashi auran wannan
figaggyar yar tata sannan ta amshi bikin." ta
gama fadanta ta matsa,danginta suka soma yi da
ita,suka ce wa zai baki wani abu ke da ko dan
uwanki baki san ki bashi gudunmawa ba bare
kyauta.tsinanni yar rowarki ce taja miki."
kanwarta ta ce,"sahura sai dai ta ci na wani ba
dai aci nata ba,dama irinsu sun cika son banza."
ummi kam anci kwalliya an gayyato kawaye
anata party a gidan maman iman,an kunna rediyo
sai rawa suke yi,kafin a gama partyn an bige da
fada da dambe,da kyar aka rabasu,nan taro ya
watse. da misalin karfe takwas na dare,ango da
abokanshi sun taso sallar isha'i Ahmad ya ce don
Allah ango muje mu rakaka. ya ce,"Allah sai nayi
wanka."mukhtara ya ce,"gidan cunkus da jama'a
zakayi wanka?" Aminu ya ce,"don Allah malam
kazo mu tafi,in ma kifi zaka zama a gidanka."
Abba ya ce,"bari dai ku gani." a zaure suka ci
karo da ummi,ya ce,"ke jeki ki wanke bayi ki kai
mun ruwan wanka." ta sobare baki ta koma ciki
tana fadin. na dai kusan hutawa, masifaff. ta
wanke bayin sannan takai ruwan,yana shiga gidan
dangi sukayo kanshi,ga ango! ga ango!! abokan
wasa suka za na can zamfara suna tayi masa
tsiya. dan gidan ummanshi yau dai za a kwana
wani gidan ba na umman tashi ba.ya dai samu
ya shige wanka. bayan ya fito ya bude
dakinshi,ya shirya cikin wata shadda
mirror,lokacin su ake yayi.ruwan kasa mai duhu.
yasha hula mu hadu a banki ita ma kalar
shaddar,ya feshe jikinshi da kalolin turaruka.ya
shigo cikin gidan yaje kofar dakin umma. ya ce
umman tana nan.aka ce mishi tana dakin
Alhaji,yayi sallama a kofar falon Alhajin basu ji
ba,suna ta hira tsit ya yi lokacin da yaji umman
tana cewa Allah dai ya basu zaman lafiya da
zuri'a tagari.

Amma har ga Allah naso Abba ya
auri..... ringing din wayar shi ce ta hana jin kowa
ummanshi ta ce,sai dai muryar Alhajin ya ce
wallahi suwaiba nima tsarina kenan. ahj yace ta
allah ya riga ya shirya ba ita ce matarshi ba.ya
daga wayar,ahmad ina xuwa mana. ba tare da
yaji abinda ahmad din xai fada ba ya katse
kiran,dan yaji haushi.yaso jin wacece iyayansa
suka so ya aura?ya sake doka sallama,suka
amsa.ya shiga ya xauna ya gaishesu,sannanya
dubi umma.dama naxo miki sai da safe ne.ahj da
umma suka yi yar dariya,umma tace to
abba,yanxu dai ka girma,dan allah kyawawan
halayenka dinnan kaci gaba da su.yace na
gode.ahj ma yayi masa nasiha,daga nan ya fita
jikinshi a sanyaye.da muwarsa me yasa umma
bata sanar da shi yarinyar da taso mishi ba
tuntuni?haka dai suka rankaya da abokanansa
dan xuwa dakin amarya. gidan kam tun daga
tsakar gida qamshi ke tashi.sun taradda
qawayenta biyu,ita kam tana lullube kan
gado.nan dai suka sayi baki akayi yan shaqiyanci
tare da barkwanci,sannan qawaye suka yi mata
sallama suka tafi,shima ya raka abokansa. ya
dawo ya xauna bakin gadan yana dubanta, itama
kallonshi take cike da so. sukayi ma juna
murmushi,ya janyo ledan kaxan da suka shigo da
ita.

Ya warware takardar,y yago cinya ya mika
mata a baki,"ci,nasan yau kin wuni da yunwa
ko?" ta ce,"na koshi bana jin yunwa ma,ni kam
duk yau banji yunwa ba." ya ce,"ni ma haka,dama
yau bai da ce muci abinci ba."ta dube shi da
alamar tambaya a kwayar idanunta.ya ware
idanunshi.

"taron da muka tara ko ina cike da
jama'a." yayi yar dariya sannnan ta bude baki ya
saka mata kazar.ta dan figa.haka yayi ta bata
tare da zuba mata juice a kofi shima yana bata.
ta ce,"to kaima ka ci." ya ce,nima ke zaki
bani."ta sunkuyar da kai don kunya sannan ta
dauka ita ma ta soma bashi. sai da suka yi
dam.sannan ya ce mata kije kiyi alwala kizo muyi
sallah. ta ce ai tun dazun nayi sallah.ya ce
wannan ta ma'aurata ce,zamu gode wa Allah
taare da rokonshi zuri'a tagari,da kuma fatan ya
tsare mu daga sharrin shaidan dama duk abin ki.

Ta fita ta dauro alwala,shi kuma ya kuskure
baki.shine yaja su sallar,raka'a biu sannan sukayi
ta addu'a,shi ne ma yake addu'ar ita kuma tana
cewa amin. bayan sun idar da sallah idar da
sallar,ya yi mata tambayoyi game da addini ta
sanar da shi,yayi mata yan gyare-gyare sannan
suka kwanta. sam Abba be daga kafa ba,a ranar
ya angwance abin shi.don haka yayi kwanan farin
ciki. da asubahi ya dawo masallaci,har lokacin
amarya tana ta shirga bacci ya zauna bakin
gadon yana kallonta.yasa hannunshi a gefen
kumatunta.
Chapter 11 · 0% Book details