← Book details Zurfin Ciki Part 1 - 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 63

Sashe 60

Zurfin Ciki Part 1 - 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kumatun shi ta shafa
nima yau kamin kyau, koda yake dama kai me
kyaune, ina sonka ya abba sosai.

Cikin jin dadi
ya mannota a jikinshi, nima ina sonki, ina manta
kowa da komai in muna tare, tace ina tsoron kada
wata rana ka juya min baya.

Ya saqalo
hunnuwansa cikin nata ina fata in mutu kafin
lokacin.

Ummi tasomayi masa wasu irin darussa
wadanda tasan yana saurin tada sha'awarshi
nanda nan kuwa tasa shi fita hayyacinsa yakama
surutai.

Ummi ta tabbata bishira tana wurin ta
labe, don haka tai murmushi ta bishi suka tafi
duniyar ma'aurata.

Bishira tamkar tayi hauka sai
kawai ta fado dakin tana fadin, maciya amana,
har yanzun ba afita daga lokacin girkina ba
munafiki.

Abba ya tashi sannan yaja riga yasaka,
ok dama kina labewa ne kiji sirrinmu?

Da taga ya
sauko da zafin rai saita gudu dakinta.

Yabita
yamata tatas, kuma ya fada mata cewa tazo ta
shiga dakin ta zauna ba labe ba, yanzun zai
komane yaci gaba daga inda ya tsaya.

Tayi ta
kuka gashi ba damar zuwa gurin umman bashir
dole ta tafi gidansu.

Shi kam abba shareta ya yi
kosu umma bai fadawa ba.

Sabuwar soyayya ma
ya balle agidan, su ci abinci tare, wanka tare, su
fita yawonsu a qafa ko amota.

In yana gurin aiki
bini- bini ya kira waya, ita kuma ko yaushe cikin
kirkirar girki da kwalliya tare da dadadan kalaman
dazata fada masa take.

Duk lokacin datayi masa
zancen bishira sai ya ce, don Allah ta bar ta ta
huta, ummanshi kuwa 'yar bin qwaqqwafi sai da
tabi ta gano bishira bata nan.

Don haka koda ya
shiga gaisheta sai tace kada ya yarda yaje yama
bata takardarta.

Ita ko tana can uwarta tace ma
mahaifinta abba sakinta yayi, shi kuma yace to
sai tazauna tunda zaman gidan take so.

Amma
su sani daga abinci sai ruwan gidanshi ya amince
tayi amfani dasu sai ko gurin kwana, amma bnda
wannan ko makilin dinshi ta taba bai yafe mata
ba, wannan hukunci yayi musu tsauri.

Ko wata
bata rufa ba taji gidan ya isheta don hajiya zainu
taso maidata makaranta amma yace tagama
boko.

Bishira na zaune ta zuba tagumi hajiya
zainu ta shigo dakiki tace tagumin menene kuma?

Tace, su sumayyah ne wai nace suyi ma muhibba
wanka sukace Allah yakiyaye.

Wai tunda nazo
dakinsu ya lalace da kazanta, hajiya zainu tace
aiba karya suka yiba, don haka ma maida
yarinyar nan za ayi ke kuma ki koma gidan
antynku ko ki tafi abuja gidan aisha.

Tace
baxanje gidan aisha ba, don itama bama shiri,
gara gidan antyn amma gsky ni abarmin 'yata
kuma fakinsan bai sakeni ba.

Tace, inda ubanki
yasan ba saki bne da tuni bai kora kiba?

Don
haka mubarshi haka amma batun 'ya nice zan
maidata.

Ranar da ummi takira ummansu tafada
mata cewa bishirafa tuntuni tayi yaji amma Abba
yaqi zuwa, umma ta kira shi tace inya dawo gurin
aiki tana son ganinshi.

To kafin yadawo ma saiga
hajiya zainu da direba tazo gidan su umma tadire
musu 'yar, sannan tashiga gidan umman bashir
tace, in kin haifi danki na halas ne ba shege ba to
kisa shi ya aiko wa 'yata saki.

Umman tace zoko
kiga dan halas ne in yaso kuje ku nemi arne mara
sallah dan uwanta kazami kubashi.

Nan fa zage-
zage ya tashi har su umma dasauran makota
suka shigo.

Dakyar aka tura hajiya ta tafi, tace
kuma saita kira 'yan sanda anzo antafi da umman
bashir.

Alhji qarami ma cewa yayi maza abba
Abba yarubuta takarda ya aika ma bishira.ZURFIN CIKI book 4 part 32
ZURFIN CIKI book 4 part 32
Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 14:37
Shiko alhji babba da umma suka ce a'a abari
qura ta lafa sannan aje.

Koda aka kwana 2 abba
kin bin alhaji yayi sai wani abokinshi alhaji
yasamu suka tafi tare.

Mahaifin bishira yaji
mamaki cewa ba sakinta abba yayi ba.

Kuma bai
san sun maida 'ya ba, tadai ce mishi kunzo kun
amshi 'yarku, to yanzun tunda haka ne kunga
kenan bishira da uwarta basa son takoma gidan
mijinta ko?

Su alhaji suka ce eh, yace to ku sa
shi ya rubuto takardarta ku kawo min, su alhaji
sukace ba za'ayi haka ba.

Yace, to kuje ku barta
zata gane gidan ubanta bananne yadace tazauna
ba.

Sukai godiya suka tafi.

Harta koma gidan
anty farida mahaifinsu yace tadawo nan gidanshi
badashi take takama ba?

Wato ta kashe auranta
zata je ta kashe na yarta dole ta dawo, tsohuwar
dake musu aiki yace ta koma gida tahuta amma
duk wata tazo ta amshi albashinta.

Sannan yace
bishira itace zata dinga wannan aikin duka ita
kadai, lamarin yayi wa bishira tsauri da yawa,
gashi ba fita duk ta rame ta lalace ga tunanin
'yarta.

Muhibba kuwa tana gurin umma, ummi
ma takan daukota sannan ummi tasamu nasarar
rufe bakin umman bashir, ta hanyar yi mata
kyautuka ko me sukace sai ta aika mata.

Tasa
Abba ya canja mata gado don nata ya lallace,
sannan da fati ta haihu tasa Abba ya sai mata
garar abinci, ita kuma tasa zani da rigunan yara.

Nan fa sai ga sahura babu ko kunya tana shima
ummi albarka, ko bashir ne yakawo gulmarsu
ummi sai tace ai ita bata yo halin uwarta ba.

Tafi-tafi ma in ya kawo sai tace ai su umma da
ummi sun gane kuransu.

Haba sahura kodai ki
gane kuranki?

Abba yasoma damun ummi da
batun ciki, wai shifa yana tsoro kada su gaji su
umma, ummi tace su dai yi addu'a sunje asibiti
ba wata matsala, likita yace in rabonsu yazo zasu
haihu.

Da kyar ummi ta shawo kan Abba ya
amince ta zana (JAMB) don ci gaba da karatu,
sannan ta shiga islamiya.

Abba yayi kyau yayi
kiba ya kara gogewa, haka nan ummi duk wanda
yaganta saita birge shi, daka ganta kaga wayayya
wadda mijinta yasan da ita.

Taci nasarar samun
(POLY) saboda bata samu abinda take so don
zuwa (UNIVERSITY) ba, sai dai ba tasha dokoki
kafin ta fara zuwa.

Bayason kawaye baya son
abokai, irin wanda wasu matan keyi sannan
yadinka mata manyan hijabai, kuma banda hawa
acaba, inya samu sarari zai dinga zuwa da kansa
yana daukarta.

Sai kuma gargadi na karshe kuma
da babbar murya, in har ya daina samun kular
datake bashi ta kowane fanni wai saboda karatu,
to kuwa za adaina karatun gaba daya.

Tace,
insha Allah sai abinda yai gaba.

Ya canja mota,
umma tayi ta fada wai tafi son yasai fili yayi dan
gidanshi irin na zamani yace za'azo gurin
ahankali kada ki damu umma.

Bishira ta sulale ta
tafi na'ibawa gidan anty da kukanta wiwi don
Allah ta taimaka mata taba Abba hakuri ya maida
ta, wlh tagane kuskurenta.

Anty tace, nifa bazan
iya kiran Abba ba don kin riga kin bmu kunya, sai
dai in ke ce zaki kira shi ga waya can.

Ta dauko
ta kira, shikuma ganin kiran anty sai yayi parking
yadauko ummi daga makaranta, ya daga sai yaji
muryar bishira.

Cikin kuka tana cewa, don Allah
abba nice, kayi hakuri indawo dakina, wallh zan
canza, yace ok baki riga kin canza din ba, to bari
inkin canza din sai muyi magana.

Yakashe haka
tayi ta kuka tagama anty tabata wasu kayan
sawanta sannan ta tafi.

In lokacin labarai yayi
haka take zuwa ta tasa TV tayi ta kallonshi tana
kuka, kullum kara sonshi take gashi yayi kyau
idanunshi sun qara haske.

Wata ranar jumma'a
wuraran karfe sha daya ta saci jiki tanufi gurin
aikin Abba, yana fitowa dakin daukar labarai
akace wata tana nemanshi.

Baiji wani mamaki ba
don mata kanzo neman shi wasu suce suna
sonshi wasu suce ganinshi kurum zasuyi don
yana birge su.

Yana zuwa sai yaga bishira, nan
take ya daure fuska tamkar bai taba dariya ba,
duk da cewa acan kasan zuciyarshi yatausaya
mata.

Ta tsugunna gwuiwa 2 tana rokonsa, yace
ke tashi kada ki janyo min mutane, jeki zanzo.

Koda ta tafi cikin murna shi ko harkokinsa
yakama.

Shiru-shiru tana saka rai bashi ba
alamarsa.

Nan kuma tashiga daukar waya
kannanta tana kiranshi, harma yadaina dagawa.

Wataran taje tasamu ahmad tana kuka, ahmad
yace taje zai ganshi.

Rannan kuwa har gida
ahmad yiyi sallama da abba yashiga rokon Abba
ya maidota.

Abba yace taje taroqi mahaifiyarsa
dasu umma insun yarda shikenan.

Har gida
ahmad yaje ya fada mata, bata yi sanyi ba tanufi
gurin umman bashir.

Umman tana zaune da
'ya'yanta suna shan farfesun kifin da ummi ta
aiko musu dashi, tana ganin bishira ta hade rai.

Tace, lapiya?

Bishira tace lpy lau umma zuwa
nayi in roqi gafararki.

Tace nime kika min?

Tace
don Allah dai ki yafe ni, ina son indawo dakina
Abba yace sai kin hakura, tace oho, yanzun kin
yarda ina da kima agurinsa?

To bari kiji bazaki
dawo ba, mai baqar rowa kince nimai kwadayi ke
kuma mai rowa ko?

To kin gani wannan ummi ce
ta dafo mana ta nuna mata kular kifi, sanda
kinanan bana cin komai bansan dana yana samu
ko baya samu ba.

Yanzun abin arziki iri-iri
kidawo ki toshemana kofar samu?

Tace, wlh
bazan toshe ba, umman bashir tace dukda haka
dai bazaki dawo ba.

Tayi takuka sannan tafita,
har zata wuce gidan su ummanshi sai ta tuna
kada suyi mata dariya sai tace baridai ta shiga.

Kyakkyawar karba umma tayi mata suka gaisa,
tazauna umma ta kawo mata ruwa ta amsa
tasha.

Muhibba tana ta tsalle tsallenta kan kujera
zuwa jikin umma, umma tace ji hibba ki gaida
mamanki, ga mamakin bishira sai yarinyar ta
kalleta tace.

Umma niba wannan bace ba
momina, momina sun tafi da babana zaya kaita
makaranta.

Umma tace, wannan ma ummarki ce
yarinyar taruga dakin tsohuwa tana cewa, ita ba
ummarta bace.

Bishira ta bita dakallo, yarinyar
tayi bulbul gata cikin shiga mai kyau da tsafta
kanta yaji kitso da 'yan duwatsu.

Saita soma
kuka tana fadin mahaifiyata ta cuce ni, umma
tace a'a kece kika cuci kanki, inbaki dauki
damuwarki kin kai mata ba yaushe zatasan anyi?

To ynzun dai dubi 'yarki tana gudunki sbd bata
sanki ba, ina amfanin wannan?

Tsohuwa tace
kukan wanikeji ta shigo tana kallon bishira cikin
mamaki tace.
Chapter 60 · 0% Book details