← Book details Zurfin Ciki Part 1 - 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 63

Sashe 57

Zurfin Ciki Part 1 - 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yanzu kai ya
waye wanzamai ba duka suke dafa kayan aikinsu
ba, haka kawai taje ta hadu da wata cutar?

Alhaji
yayi murmushi yasan kishi ne ke damun Abba, ya
ce Babana kada ka damu, goben sai kuje asibitin,
in sun ce ba su san shi ba to sai a zo a yi na
wanzam ko ?

Kunya ta kama Abba, Sam ya
manta Alhaji yana gurin ya ce to Tsohuwa ta ce
kuje in kun je ma dawowa za Ku yi dan me taurin
kan tsiya.

Abba ya ce naji kin ji ummi taso muje
gda Tsohuwa ta ce oho dai, kuyi ta tafiya in dai
akayi mata aikin ai dole ka barta ta warke .

Alhaji
da umma dai dariya sukayi ta yi musu, shi kuma
yayi musu sallama, ummi kam kasa magana tayi
don duk ta tsorata.

Suna fita ta rike hannun Abba
gam tana cewa.

Don Allah ya Abba kada kabari
wanzam yayi mini aikin nan, zan ji zafi.

Ya
rungumota, Ba zan amince ba wani ya ganmin
al'aurar mata, likita ma mace zan nema ko nawa
zan kashe .

Ummi ta ce, to zan ji zafi ya Abba?

Ya ce, made ki damu, in asibiti ne kila suyi miki
allurar kashe zafi amma in wanzami ne ina za ya
ga wata allura yayi mini.

Ummi sarkin tsoro ranar
kwana tayi cikin damuwa, washegari kuwa tun
bakwai suna asibiti.

Babban asibiti suka je sun
yanki kati likita me kula da fannin mata aka tura
su.

Mata dayawa suna ta kallon su ummi
musamman yanda Abba ke nan-nan da ita,
sannan wasu sungane shi kasan cewar shi dan
jarida mai farin mini.

Wasu mazan kuwa sai zuwa
suke suna gaida shi.

An kirata dakin ganin likitan,
ta mike zata Shiga Abba shima ya mike, wata
Nurse ta ce, malam jira mana, ya ce ai duk Mu
biyu ne bamu da lfy, ya shige likitan namiji ne ba
yanda ya iya dole ya yi masa bayani likitan yayi
ma ummi tambayoyi in da duk ta bashi amsa/ ZURFIN CIKI book 4 part 26
ZURFIN CIKI book 4 part 26
Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 14:27
Sannan ya bukaci ta kwanta kan gado ya saka
safar hannu, juya kai abba yayi don gaskia ranshi
ya baci, lallai ya kamata mata musulmai su dage
suyi karatun likitanci don su taimaki yan uwansu
mata.

Sai da likita ya gama dubata sannan ya iya
dubansa, likita yayi wani rubutu ya mika abba
tare da cewa, an baku gado zayi mata aiki gobe
ko jibi.

Abba yace likita zan iya sanin wane ciwo
ne wannan?

Likita yace tsirone dake fitoma mata
dai daiku.

Sam abba bai fahimta ba don haka yayi
mashi sallama.

Umma ce a wurin ummi tana
shan magani kafin ranar aiki inda abba
hankalinshi ya rabu biyu rabi gurin aiki rabi garin
ummi.

Don ma umma ta koreshi da so yayi ya
rika kwana, addu'a kam yana yinta.

Ranar da
za'ayi aiki abba hankalinshi duk tashe.

Yana
zaune bakin gadon da take kwance ita kuma tana
can ana aikin.

Wayar umma ce a hannunshi yana
ta danne danne, ba don nishadi ba don kawai ya
rasa me zaiyi.

Dript ya shiga yana ta bin abinda
ke ciki, mamaki ya cikashi lokacin da yaga irin
text din da ummi tasha rubuta mashi don ta tura
ma abba, sai kuma ta fasa.

Tamkar cikin mafarki
abba ya rika karanta sakwanin dama ummi tana
sonshi zurfin ciki ne tayi?

Ya sake bude wani
rubutu cewa, Ya Abba ina sonka, ina kaunarka
duk wani motsi na numfashina kara sonka nake,
ka tausaya mun sonka zai zama ajalina, duk
ciwon da nakeyi na sonka ne.

Ko na rantse ba
zanyi kaffara ba, in kaji haushin kalamaina ka
yafeni, nasan ni ba ajinka bace, amman ka daure
kace kana sona koda bada gaske bane.

Gama
karanta sakon yayi dai dai da dawowa da ummi
dakin, da sauri suka nufeta idonta biyu saidai
daga gani tasha azaba.

Tayi wujiga wujiga.

Abba
ya kama hannunta cikin matsanancin sonta da
tausayi.

Sannu suka dinga yimata, nurse tabasu
magungunan da za'a rika bata, umma kuma ta
dauki wayarta don sanar da alhaji an gama aikin.

Abba yasa bakinshi dai dai kunnenta yace ina
sonki ummi, ina matukar sonki.

Duk da tana cikin
wani hali taji kalaman nasa har a tafin kafarta.

Ta bude jajayen idonta ta dubeshi, ya sakale
hannunshi cikin tafin hannunta ya hade su.

Ta
girgiza kai dai dai lokacin da nurse din ta sake
shigowa tace ga kayanta, ya amsa zaninta ne da
siket da sauransu.

Tace ka barta tayi bacci kafin
ta tashi zafin gurin ya ragu, kila zuwa dare a
sallame ku.

Umma tace to mungode.

Nurse tace
yarinyarki nada dauriya, anyi mata allurar kashe
zafi bata kama jikinta ba amman bata yimuna ihu
ba.

Likita ma ya yabata da kokarie ta, Abba ya
kalli ummi cikin tausayi.

Sai gurin karfe ukku ta
farka wurin kam ya dan lafa da radadin, abba ne
yaje gida ya dafo masu abinci sannan ya nufi
wurin aikin shi.

Don ranar bada wuri zashi ba.

Tunda ummi ta farka take ta kokarie tunowa shin
kalaman da taji cikin mafarki ne ko kuwa ido biyu
ne?

Bakwai na dare likita ya shigo ya kara duba
ummi sannan yace suna iya tafia gida.

Ya basu
maganin sha sannan yace ta rika shiga ruwan
zafi da dettol.

Umma ta kira abba ta fada masu
batun sallama.

Yace su jirashi yana zuwa.

Ummi
tace da ummansu su alhaji pha?

Tace sunxo kina
bacci harda ummanku sahura.els / ZURFIN CIKI book 4 part 28
ZURFIN CIKI book 4 part 28
Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 14:30
Bansan lokacin dana dauka ina rigimniya da sonki
danqare a zuciyata.Ummi da ban sameki ba da
tuni bana garin Kano domin lokacin yanke
shawara nayi in nemi canjin aiki zuwa wata jihar
har yau ban daina yiwa Salisu addua ba wanda
shine mutum na farko da ya soma tsegunta min
kin zama mata gareni So, Ummi baya raina
abinda yake so da nayi zaton zubar da kima ne in
furta maki kalmar so musammam in na tuna ke
baki soma, zurfin a so bashida wani amfani don
na sha wahala.Ba zan Qara boye dimbin son da
nike maki ba Ummi ko gaban wa zan nuna kina
jina matsala?

Ummi wadda ke zaton mafarki take
sai taji bakinta yana furta wayyo dadi Ya Allah
kada ka farkar dani in har bacci nike Abba yace
ciji yatsanki zakiji zafi Ummi nine Abban ki mai
sonki wanda ya reneki tun kina zanen gobe.

Hawaye suka soma zubo mata cikin muryar kuka
tace Ya Abba da gaske kana sona?

Naf
i zaton
tausayina yasa ka furta haka, Amma koba gaske
ba ne na gode kuma naji dadi Amma ka sani Ya
Abba ina sonka mai tsanani sai tasa kuka.

Yace
ummi yi shiru, in kukan takaici ne kukan ya kare.

Nima na jima ina sonki jiya naga sakonki a wayar
umma da kike rubutawa mai dauke da nuna sonki
gareni.

Sai zurfin ciki ya hanaki, don allah ummi
kada ki koma zurfin ciki a sona, ki zazzage min
duk irin sonki gareni.

Ummi tace yau kam ji nake
kamar a mafarki.

Sun nutsa a cikin hirar so suna
ta baiwa juna labarin halin da suke shiga a baya,
a lokacin daya ganta da wani namiji yace
hankalinsa yayi mugun tashi.

Sai lokacin daya
fuskanci bashir na sonta, ita kuma Tace ta tsani
koh mace ta kira layin shi, zainab kuwa data
samu labarin ta kamar ta mutu.

Tace ko bishira
bata kishi kamar yarda take kishin zainab, sunyi
nisa basu san sun kwana zance ba, sai da ummi
taji kiran sallah.

Tace ya abba kaji abunda naji,
yace sallah ake kira naji, kin sani kwana zance.

Ban gaji dajin muryarki ba amarya tah.

Ummi
tace gari yayi saurin wayewa kaje kayi muna
godia ga allah ta hanyar nafita, yace to matata.

Hamdala ta rikayi har bacci ya dauketa, muryar
umma taji tana cewa ummi ki tashi kiyi wanka ki
gasa jikinki.

Tana zaune cikin baho wanda umma
ta zuba ruwan dimi da dettol, tsohuwa ta shigo
cikin bandakin.

Ummi tace don allah tsohuwa fita,
tace don allah ja can anki a fita din, ta saka
hannu cikin ruwan wankan ummi dake gefe a
bokiti.

Tace ina suwaiba?

Ai karo mata ruwan
zafi, wannan ruwa yaushe zata gasa jikinta, idan
da dan tawul dauko in danna mata jikin.

Ummi
tace nidai tsohuwa ki barshi don allah, sai kace
wata mai jego?

Tsohuwa tace tafi can kuda baku
san darajar jikinku ba.

Wannan rawar kan da mai
sunan malam keyi idan ba'a gyara kiba saiki ba
sai zance ya dawo baya, idan anyi magana ku
yan zamani kuce bamu waye ba.

Alhali ku
wayewarku itace kwalliya amman jiki ba'a san a
gyara ba, umma tazo ta kara mata ruwan zafi a
cikin bokiti.

Tsohuwa tace yau a sawo bagaruwa
a tafasa ruwan shigar tata da ita don tayi saurin
warkewa.

Kuma ko ina zai hade, in kin koma
gidanki kin kwana biyu ki dinga hada bagaruwa
da alim kina tafasa su kina shiga.IKI novels / ZURFIN CIKI book 4 part 29
ZURFIN CIKI book 4 part 29
Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 14:31
Umma Tace xa'asiyo tafita tabar su ummi
nacewa to tsohowa kije mana tace bantafiya sai
naga yanda xakiyi ganin ummi tabata lokaci nan
tsohuwa ta dauki tawul din tashiga nadar ruwa
tana dannama Ummi, Ummi tanacewa itadai
abata tayi da kanta.

Tsohuwa tace gaddamace
daku ya'yan yau kinga duk macce dake rufe
jikinta tafita daban damasu tallar jiki.

Ita macce
anfison a sameta ko yaushe da dumi a jikinta,
yawo babu takalmi ko a tsakargidane yana
ragewa mace dumi sbd sanyinda ke ratsa tafin
kafarta har ni'ima yana ragemata.

Sannan zama
atantagaryar suminti shima yana rage mace, da a
ace zaku gane kunga masu saka hijabinnan da
safa? bakaramin wayo suke yimukuba.

Inda za'a
banbance za a samu sunfiku ni'ima da kyau fata,
don haka sai kin dage Ummi dai tayi shiru, amma
aranta cewa take wannan tsohowa ko ina tasan
wannan duk bayanin?
Chapter 57 · 0% Book details