← Book details Zurfin Ciki Part 1 - 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 63

Sashe 10

Zurfin Ciki Part 1 - 4 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Amina ta ce ummi dubi har malamin(social
studies)din ya shigo. ummi ta ce,"ina ruwana,ko
wanene ma ni shiga zanyi abuna."Amina ta ce,"in
dai tica hassan ne gara mun juya don sai ya zane
mu." ummi ta ce,"tab ai gara dukanshi da in tafi
gida yanxun wannan mugun yaya Abban ya ci
zalina." sam ummi bata kalli malamin ba,sanda
take takai kujerarta,yayinda Amina ta labe ta
kasa shigowa,kamar cikin mafarki taji muryarshi y
ce,"ke daga ina ki ke?" ta dubi gurin da
sauri,"yaya Abba ne ya hade rai,fuskar nan tashi
babu annuri sai kace mai bada mugun labari. ta
tsorata matuka,ya ce" zo nan kiyi 'kneel down'."
jiki na bari ummi taje ta zube gaban allon.nan
take yayi mata bulala guda goma masu kyau.
take yan ajin suka shiga taitayinsu,don sunga
ummi tsiga tana kuka irin wanda bata taba yinsa
ba.don ko an duketa daurewa takeyi ta kuma
shanye dukan. sannan sabon malami dan bautar
kasa kamar yadda ya gabatar musu da Kansa
daga zuwa yayi wannan duka.lalle dole su
tsorata. ya ce,wuce ki zauna dakikiya mai idon
jaki.wannan kalma ta daga hankalin ummi,domin
taga yan ajin sun guntse dariya. ummi ta koma
kamar ruwa ya cinyeta a cikin ajin duk tsokanarta
ta tsiya,tsunguli wancan,shuri wancan,duk an
samu saukinta. taimako daya Allah yayi mata,duk
da halinta ta da kan daukar karatu.a zaton Abba
bata iya komai ba,tun da basa shiri. don haka
baya ko duba takardunta,islamiya ne yafi tsarata
don tashi hikimar fannin addininta ne dole a
matsa mata ta sani,boko kuma in bata yi ba ta
yiwa kanta. duk rubutun da Abba yayi ummi yake
ta dawowa ya ce ta karanta shi in ko ta mike sai
ta karanta shi tsaf.in da ta dan samu saukin shi
kenan. tun daga wannan ranar ummi alkadarinta
ya soma karyewa gurin yan ajin,domin in suna
fada shh da yazo ba bin ba'asi ita yake horawa.
sannan in ta duki wani kafin ya shigo.daya shigo
za'a fada mishi,don shine ya basu damar cewa
duk wanda ta taba in yazo a fada mishi. duk da
sun gano kanwar shi ce,gashi kuma wani lokaci
tsokanarta suke tunda ya ce mata ummi mai idon
jaki. sam bataji dadin zuwan Abba ba amma
tasha alwashin itama sai ta mishi abinda zaiji
bakin ciki kwatankwacin yadda taji. wata rana
Abba ya siyo wayar sadarwa, lokacin tana farkon
fitowa,yazo da ita gidan yana nuna ma su umma.
nan akayi ta mishi murna umma ta ce,"kai
Abba,kai da zancen aurenka ke karatowa ina kai
ina siyan wannan abar har kusan dubu ashirin ka
ce?" Yace umma amfani kai,kema xan sai miki ai
tunda nan gaba kadan xata sakko.ahj babba dai
yace xaya bani kudi in sayo musu shida ahj
qarami.ummi na wanke wanke tana kallan
su,wayar ta birgeta,irin wanda suke gani a cikin
fina finan indiya, ta xata yan sanda ne kawai
suke riqe irin wannan wayoyin.kai ko na bakin
titin nan da take ganin mutane na bugawa birgeta
yake yi,har ta tuna ranan da sukayi doguwan
tafiya sukaje phone book.suna xuwa suka tarad
ana layi,haka suka koma gyefe saida kowa ya
gama sannan suka shiga sunata latsa latsan
nanbobi suna karawa a kunne.saida wani mutun
yaxo ya kore su,bayan ya dundungure masu kai.
tayi murmushi, sannantace a ranta, allah yasa ya
sai ma umman su,ita ko ta samu abin latsawa.
daya nunama tsohuwa wayan tace shirman
banxa,inba qarya ba da wannan xaka kira wani
daga nesa?yace kn da a saudiyya kike xan kira
ki.ta ja tsaki tayi daki shiko ya fice nana
dariya.cikin satin ahj babba ya ba abba ya hada
masu waya da layi,ahj babba yafi kowa murna da
wayan, saboda shi mata fiyine.

Wata safiya abba
ya shiga wanka, umma na kicin tana soya masu
dankalin hausa. zirif ta shige dakin abba tanata
danna danne,da taji motsin bayi sai ta aje ta yi
waje da gudu.saida ta tabbata ya shiga daki sai
tayi xirif da shige gida.lkc da taxo kawo mai abin
kari tasame shi yanata danna wayan,ya dubeta
kinxo kin tabamin waya ko?da sauri tace a,a.yace
munafuka,kece gashi kinyi min delete din duk
numbers din dake cikin wayan, muguwa. tace to
ni na shigone?ya harare ta yace fita, da ace ban
rubuta lambobin na aje ba da yanxun kin min
asara, muguwa kawai. ummi ta fita tana dariyan
mugunta,domin in da abin da tafi so bai wuce
taga bacin ran abba ba,kamar yadda tayi imani
shima burinsa kenan. umma ta lakato man xafi
tana shafama ahj a qafa tana murxawa.yace
yauwa suwaiba kamar kinsan tun daxu yakemin
kwankwatsa.daxidariya tace in dan tamu ne
kariqa ware ranaku biyu a sati kana hutawa.yayi
yar dariya,ina wani hutu da xanyi a gidan
nan,matsalar ummina kadai ta ishe ni.umma tayi
dariya,sannan tace ai ummi sai addu;a Ta canya
xancan da cewa,af na manta niko yanxu auran
abba yayi wata hudu nangaba?ya ce hudu ne da
yan kwanaki.tace tofa!gashi ni uwarsa banida ko
kobo,bari naxo na kama sana'a. ya tuntsure da
dariya,sannan yace sai yanxu kika san da
sana'a?itama dariyan tayi tace, in ba haka ba ahj
ranar biki ko an kirani bana amsa ba.yace gashi
kuma ke xaki mishi lefe.tace,to na shiga
aljihunka,in yaso in an soma sana'a sai in biya
ka.yasa hannu ya dago fuskanta yace sannu
sarkin wayau.suka sa dariya.yace in san muje
yaga gidajen nan na layin gabanmu,sai ya xaba
guda daya a baiwa masu hayar notice sai a gyara
shi.tace ya xabi na farkon layin dan yafi
kxau.yace amma bashida girma.tace ya ishe shi
daga shi sai matarsa fa?wanda ke cikin gidan ba
mata bixu ne dashi ba?yace to xamuje dai ya
xaba.sannan akoma kan lefe,tace allah ya saka
da alkairi,allah ya kaimu.yace amin.wayanshi
dake caji ta soma ruri,yace dauko min wayar
can.ta miqe tana cewa har naji tsoro,na kasa
sabawa da wayan nan.yace kuma gashi na kusa
bar maki ita. tayi dariyan jin dadi,tana
kallanshi.to ni wama xai dinga kirana?yace ni
mana,bana iya yi miki wata magana in na kira
abba na ce ya kawo maki,sai inga kamar yana
tsaye,inko taki ce dana kira sai ki kebe daga
jama'a muyi hiranmu. tayi dariya, daidai lkcn da
kiran ya sake shigowa,ya daga. ahj buhari ne
wanda ke sarin kaya gun shi daga kaduna.suka
gaisa yace ahj ka kira kan in dauka ta katse.ahj
buhari yace,dama ina san ince maka ne dan allah
gobe xan shigo,kasa ahada min kayan nan da
wuri.yace ba komai xa a hada.bayan sunyi
sallama umma tace ni abin da yake bani al'ajabi
da wayan nan, har kullum yanda xaka kira wani
daga nisan duniya,kuma kuyi xance radau.ahj
yace ci gaba kenan,wata rana ma sai kinga
fasahan data ninka wannan.tace haka ne.abba
yana xaune gaban ahj da safe bayan sun
gaisai,sai ahj yace abba ina ganin da yamma ko
xuwa dare kaje ka duba gidajen nan ka xabi
guda,saboda a ba su notice dan a gyara
didan.yace ahj ba sai naje ba duk wanda aka bani
yayi.ahj yace ummanka tace ka xabi na farkon
layin. cikin murmushi abba yace,ta shi
kenan,nima shina xaba domin duk abinda umma
ta xaba min shine xabina. tuni sahura ta fito da
anko,xaqewanta da nuna isarta akan bikin sai
kace ba dan fari ba. duk dangi sai surutunta ake
yi,har danginta.umma kan cewa tayi anko ba
shine damuwanta ba,dan haka sam bata bi ta
kansu ba.abba a cikin ajin da yake koyarwa,ummi
tana 2n gefe in da yayi mata maxauni a qasa,can
in da ba knwa sakamakon ganowa da yayi in tana
ajin ba a xaman lafiya,sannan babu me ikon xama
a kujeranta.yace,in ma ya sake ganinta ko a wace
kujera ce bas,xai ballata.rubutunda yayi take yi
ranta bace.ya kalli gun datake yace ke!ta dago ta
dube shi,yace xo nan.taje yace,amso min bulala
acan ajin.kafin ta dawo sai da ta duke wata
yarinya ta rugo.nan kuwa yarinyan ta biyo ta har
aji,abba kam daya amshi bulalar saida ya xaneta
tas.sam abba ya sama uni ido ko ta ina,ba
makaranta ba, ba gida ba.dan haka ta matsu yayi
aure ya bar gidan sannan ya gama service dan
shi ya qara gaba. tabbas lkcn auran sa xata yi
party.RFIN CIKI book 1 part 6
ZURFIN CIKI book 1 part 6
Posted by Bashir Sani Fesan on 14 Dec 2016 - 21:56
Tabbas lkcn auran sa xata yi party.
Chapter 10 · 0% Book details