← Book details Zurfin Ciki Part 1 - 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 63

Sashe 58

Zurfin Ciki Part 1 - 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Filo aka ajewa Ummi ta
zauna tana karin kumallo, duk takosa taga
abbanta, koda ta tsinkayi sallamarsa tamkar
tamike ta taroshi.

Amma dole yaje yagaida su
alhaji, tsohuwa tace aefa mu kuma bana munga
takanmu don nan zaka dinga likemana.

Yace
dadin abundai nima nan gidan ubanane, da
uwata.

Umma tana kicin tanamasu dariya.

Tunda
ya zama idanunsu sunsarke da juna sun kasa ko
magana Ummi ce tayi karfin halin lumshe ido
sannan tabude tace sannu daxuwa.

Tasowa yayi
ya tsugunna kusa da 'its, yajikin babyna?sunan
yamata dadi, naji sauki bari in kawomaka abun
karinka. yamika mata tafin hannunsa tasaka nata
yahadasu ya yasarke, murya kasa kasa yace
barshi na' amso.

Ta kula abba mutum ne maison
wasa da tafin hannu.

Ita kanta tanason hakan da
akwai wani sako da tafin hannu ke isarwa acikin
duniyar ma'abota so, kila wannan dalilin ne yasa
abba ke kashema tafin hannusa kudi da mayukan
da ke saka laushin hannu har ita mah ya
saimata.

Koda umma ta shigo Ummi tayi kokarie
amshe hannunta amman abba yaki saki, kuma a
hakan ya karya.

Umma kasa zaman dakin tayi
domin a baki abba yake ba Ummi abinci, umma
nafita taceels / ZURFIN CIKI book 4 part 30
ZURFIN CIKI book 4 part 30
Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 14:33
Daren ranar duk suna kan kujera doguwa a dakin
umma ya bude mata laptop wai yana koya mata
kanta kwance a cinyarsa, umma ta shigo dakin
tsohuwa tace tsohuwa zaifi kyau mu sallami
yaran nan na gaji da ganin wannan aiki nasu ai
tasamu sauki.

Tsohuwa tace suwaiba ina laifin ta
kwan goma ma, umma tace anya zasu kwan
goma nan?

Gobe bakwai guda ta koma dakin ta,
tsohuwa tace shine nan.

Abba yace Ummi kinfa
samu sauki ba zakizo mu koma gidan mu ba?

Tace su umma ne zasu maidani ai nima ya abba
inason in koma yace yau nan zan kwana in sunga
haka sun kuramu, Ummi tace ya abba kayi hnkr
kada ka kwana, shine yace kin yarda goma inxo
mutafi ko ba sanin su umma?

Tasa dariya tace
taf inajin kunya bazan iya binka ba yace to kuwa
zan kwana a nan.

Suna cikin haka umma ta leko
tace abba bazakaje gida ba yanxo fa sha biyu
saura, yace umma nima nan zan kwana.

Ta rike
haba nan din lafia?

Yace to umma nima ba gidan
mu bane?

Ummi tace dama yafi umma kada yaje
wani abu ya rudashi, umma tace a'a abba tashi
ka tafi insha allah gobe Ummi zata koma yayi
murmushi tare da cewa nagode umma.nan dai ya
tattara yanashi yanashi ya tafi gida cike da
kewar matarshi, itama Ummi lamo tayi a gado.

Bayan umma ta gama yimata fada ta bari ta
warke taki ko, sai cewa tayi umma ni fa na
warke.

Umma ta kalli Ummi cike da mamaki tace
yaran yazo saidai a barsu.

Shiyasa akace idan
macce ta isa aure ayi mata a huta.

Ita kam Ummi
tana ganin a barta tabi mijinta ta faranta mashi
shine abinda yafi dacewa don yanxu ba inda ya
kai mata dakinta dadi bacci.

Duk da kashedin da
tsohuwa tasa abba dakinta tayi mashi na cewa
ya bar Ummi sai ta kara sati kafin yace zai
kulata da sunan auratayya, bai sa abba jin zai iya
ba.

Don haka koda ta fada mashi cewa yayi kadai
da huruminki da wanda ba naki ba duk sai kin
shiga?

To nidai ki lafa man haka.

Ya fice a dakin.

Ita kuma tana ta fadanta tana cewa "Na shiga din
dan neman yaro, da kyar ya barta ta kara kwana
biyu ya afka mata don shi hkr sa ya kare, ta
nuna mashi ita fa tsoro take ji kada ta wahala, ya
lallasheta yace ba wani wahala.

Ummi tana son
faranta ran mijinta.

Don haka ta jure duk da
yarda yazo mata ba sauki, sai dai tasha albarka
kuma ta kara samun wani matsayi na
musammam a gunsa.

Cikin satin ta zama yar
lelenshin kafin sati biyu ta hardace duk wani
darasi da abba yake koya mata, abba jinsa yake
kamar wannan lokacin ne ya fara rayuwar
angoncinsa.

Sam ya manta yana da wata mata
uwa duniya saida Aunty ta kirashi tace lafia baya
kiran matarsa sai ga abba da girman shi ya girba
karya.

Wai ya kira ya kasa samunsu Aunty ta
yanda tunda farkon tafiyarsu yana kiransu sun
gaisa da bishira tana tmbyrshi ina hibbarta?

Sai
lokacin ya tuna kwana biyu bai ganta don tana
gidansu umman bashir, amman sai yace tana
lafia in yaje zai kirata taji gwarancin yar tata.

La'asar sur suka jero ita da abba don su dan
zaga kurum.

Sun shigo gidan ahmad da muktar
duk basu rabu ba saida sukaji sun saba da ummi.

Don ita haka take yana da wuya kayi zaman awa
guda da ita bakaji ta kwanta maka a rai ba.

Abba
yaji dadi yarda Ummi ta nuna kauna ga matan
abokanin nasa, yasan bada jimawa ba matansu
zasu zama kawaye kamar yarda yaso da bishira
amman taki.

Daga can suka nufi layin su gidan
su umman bashir Ummi tace su fara shiga su
dauki muhibba abba yace bazata yarda dake ba.

Ummi tace zata yarda muje a ran abba tsoro
yake gada umman bashir ta gwasaleta Ummi, sun
sameta tana shara da sauri Ummi ta amsa ta
soma sharewa hakan ya faranta ran abba sai dai
da ya kalli umman bashir yaga tana hararar
Ummi, saida ta gama taxo ta zauna suka gaisa
abba na rike da hibba tayi kaca kaca da kunu
gashi duk ya dunkule dama ko lokacin da bishira
tana nan haka zakaga yar duk kazanta.

Ummi ta
bude post dinta ta cire dari biyu guda biyu ta
mikawa umman bashir gashi umma kin sai goro
saida ta tabe baki ta amsa babu ko godia, sai dai
abba cikin jin dadi yace angode, da hibba taki
binsu Ummi tace kamal xo ka siyo wa hibba
alawa, kinga baba kamal baya nan xo muje in
sayo maki.

Cikin sa'a sai taxo zasu fita sai ga
bashir dauke kai yayi tare da jan tsaki daya shiga
gidan sai ya hau umma da fada Wai ta daina
barin Ummi da wannan abba suna zuwa in ba
haka ba zasu kawo mata wani asiri.

Umman
bashir tace suta zuwa ma indan ta nine mi jiya
tayi bare yau, ka gansu dari hudu yanxu ta bani
don haka bazan hana zuwa ba amma fa ina nan
yarda nake bazan canza ba, suna shiga gidan su
umma kicin ta wuce ruwan zafi ta zubu ta cude
muhibba tas, ta wanke mata kai ta chajeshi ta
shafeta da mai nan ma basu jima ba suka nufi
gida zanen umma ta ansa ta goye muhibba, shine
ya bude dakin bishira duk kayan yarinyar sun rine
da datti, Ummi dai ta zazzaba yace .ba maidata
za'ayi ba, Ummi tace ta dan kwana biyu mana.

Yace tana fitsari fa.

Ummi tace kasawo muna
pampers Yace shikenan duk da ya nuna bayaso
yarinyar ta zauna gurinsu amman yaji dadi sai
lokacin bacci daya shigo ya shigo da pampers din
ta saka mata Sannan ta kwantar da ita can gefe
ta azama mata pillo guda haba guda baya, su
kuma suka kwanta a nasu makwancin suka
cigaba da soyewa. novels / ZURFIN CIKI book 4 part 31
ZURFIN CIKI book 4 part 31
Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 14:36
Ummi tana son yara don haka hibba ta dinga
samun gata, satinta guda umman bashir ta dinga
jaraba sai an dawo da ita.

Wai kwadayi ne don in
bishira tadawo ta bata tsaraba, amma koda ta
tafi da hibban yarinyar sai taqi sai kuka har dasu
amai.

Dole aka dawo da ita, don alhaji karami
cewa yayi atattara mata kayanta duka inyasake
samun an maido da ita sai ya saba ma umman
bashir.

Hakan da babbar sallah abba yakashe
musu kudi ita da hibba, sai dai duk abinda yasai
ma ummi to ya aje ma bishira nata.

Ita kam tana
can duk addu'arta akan ummi ne, kafin ta dawo
ummi tafita, don haka data dawo da kwarin
gwuiwarta ce wa bazata samu ummi agidan ba.

La'asar sakaliya, direban gidansu ya iso da ita
gidan kamar yanda mahaifinsu ya umarce shi
cewa in ya dauko su kada yaso dasunan, ya dire
kowa agidanta.

Kasancewar unguwa uku suka
soma zuwa sai anty ta taya bishira diban kaya
su shiga.

Daidai kofar dakin bishiran abba na
kwance rigingine, 'yar T-shirt ajikinshi fara kar.

Dawandon jeans gajere iyaka gwuiwa.

Ummi
kuma dogon wando ne irin mai kama jikin nan
dariga mai kamar singileti kanta yasha kana nan
kitso, tayi filo da kirjinshi yana bata labarin wata
mota da yake son yabada tashi yayi ciko.

Ita
kuma tana ce masa ya dai je ya shawarci umma,
muhibba kuwa tana ta faman wasa da sabbin
kayan wasanta da ummi tasai mata.

Ita ma cikin
'yar shimi mai kyau, kanta kuwa ummi tayi mata
kitson (3 in 1).

Sororo bishira ta tsaya tana
kallonsu, sam bata tsammaci a irin addu'ar
datayi zata dawo ta samu ummi agidan ba.

Basu
ganta ba saida anty tayi sallama tare da cewa, ya
naga kin tsaya? da sauri suka waiwayo duk suka
mike.

Gaban ummi yayi wata muguwar faduwa,
amma duk dahaka cikin fara'a ta nufe su, bishira
ta hade rai matuqa sannan taqi ko kallon ummi
ta nufi 'yarta.

Anty kam cikin fara'a suka gaisa da
ummi harta zage jakarta dake kafadarta tabawa
ummi wani dan agogo mai kyau.

Nan dai ummi
tayi ta godiya shima abba ya mata godiya.

Abban
ne ya shigar mata da kayan daki, ummi tana
cewa anty kin mana dawowar bazata, dakin fada
da an share miki dakin.

Nan ma bata tanka ba,
ummi dai data gaji dayi mata sannu bata amsa
ba sai kurum ta nufi dakinta, zuciyarta babu dadi,
tasan yanzun ya Abba zai raba jin da yake da ita
zuwa su biyu.

Bishira tayi kyam tana ta qamshi
don anty baza su barta tazauna masu da qazanta
ba, ga haqorin makka an sako ana ta qwambo.
Chapter 58 · 0% Book details