← Book details Zurfin Ciki Part 1 - 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 63

Sashe 61

Zurfin Ciki Part 1 - 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

'yar nan kece haka?

Ciwo kikayi ko
ko duniya ce ta juya miki baya?

Kai jama'a dubi
yanda kika kare kikayi bikinkirin.

Ita da tadukar
dakai tare da cewa bnyi ciwo ba nidai nazo ku
yafe ni, sannan ku roqa min abba ya yafe min in
dawo dakina.

Yace, bazan dawo ba har sai kun
yafe min, amma naje gurin umman bashir ta kore
ni tace bazata bari in dawo ba.

Kuma gidanmu
wuya nake sha, kusan rabin aikin gidan nikeyi ga
qannaina duk sun raina ni.

Umma tace, yi shiru
share hawayenki bari zaki koma.

Tsohuwa tace,
ke dai kin cika sa kai a uku suwaiba, gashi abin
kirki bai karbe kiba.

Kina yi ana zaginki ana zagin
'yarki, bishira ta ce wlh duk na daina, yanzu na
gane kune masu sona, umma tace ba komai.

Tadaga waya ta kira alhaji ta fada masa komai
yace to yana zuwa donshi ya qosa asulhunta
yarinyar ta koma dakinta saboda darajar
tsohonta.

Yana zuwa yaji komai nan ya daga
waya yakira Abba, yace yana zuwa yana hanya
ne yace to ya same su gida.

Abba yana shigowa
ganin bishira yahade rai ya zauna nan dai alhaji
ya hada su yayi musu fada da nasiha, sannan
yace baya son abba yace komai komai kuma ko
sun koma gida banda tashin tashina.

Bishira tayi
ta godiya alhaji babba yace su tashi ashiga gurin
umman bashir din tana ganinsu tahau cewa alhaji
dakanka?

Maimakon ace in zo?

Umma tace, a'a
keda zamu zo baki hakuri ai mu ya dace mu
shigo.

Nai dai alhaji yayi bata hakuri tace taci
albarkacinta na hakura, amma da sharadi inta
sake maimaita halin da tayi abaya ko taje ta
takurawa ummi tofa saita tabar gidan.

Bishira
cikin kuka tace ta daina insha Allahu, nan itama
umman bashir din tace dasu umma su yafe mata
sharrin shaidan ne da qaryar barayin imani wato
bokaye da 'yan tsibbu suka ce ba komai.

Nan
alhaji yace da abba yakai bishira gida, ba don son
ranshi ba yadauke tazuwa gida, sam bata damu
da daure fuskarshi ba, dadi da murna fal ranta.

Yana sauke tazai wuce tace, don Allah ka yafe
min sannan ka gaida min ummi, yace zataji.

Tace
to yaushe zan dawo?

Yace, duk lokacin dasu
alhaji suka zo gurin dadynku.

Nan yatafi, ita
kuma ta shiga gida, hajiya zainu ta tsareta wai
sai ta fadi inda taje, tunda ta kira anty tace, bata
can.

Bishira tace naje ba mijina da surukaina
hakuri ne, hajiya zai
nu tace ni dazai maida ki ai
sai nafi kowa murna.

Na gaji da zamanki da
qazantarki, tunda babanku yaqi ki koma
makaranta yakashe miki kudi ki goge ko kya
samu mai kudin dazai aure ki, to gara kin koma
can kin qarata.

Abba kam shi tunaninshi ta ina
zai soma sanar da ummi dawowar bishira?

Don
baya son ko kusa hankalinta yatashi, baya son
wani abu yayi musu katsalandan a cikin
daddadan zamansu, don haka ya share bai fada
mata ba.

Da dare alhaji da umma suka je, an
sasanta sannan suka taho da alkawarin cewa
gobe zata dawo dakinta.

Washegari umma ta kira
Abba tace ya share ma bishira daki yau zata
dawo, yace umma nifa gsky dabata hankalina yafi
kwanciya.

Sannan ina ta tunanin yanda zan
tunkari ummi da wannan zancen, umma ta riqe
baki tare da rafka salati, yace ynzun tsoron
ummin ka koma ne?

Yace, a'a umma kin gata
sakankance ynzun hankalinta yakwanta sai kuma
taji nazo mata da zance dawowar bishira?

Tace,
shi kenan nina fada mata.

Awaya ta kira ummi
tafada mata cewa bishira zata dawo, duk datasan
cewa matar mijinta ce dama, amma sai da
gabanta yafadi.

Umma taja mata kunne da cewa
kada taji kada tagani, abba ranar sai kusan sha
biyu zaije gurin aiki.

Don haka yace kannanshi
suje su soma fito da kayan kafin yazo sunzo sun
fada ma ummi, ita ce ta bude musu dakunan don
abba ya canza makulli bayan tafiyar bishira.

Abba
ya shigo tana zaune kan kujera sai tunani take yi
na irin zaman dazasu yi in bishira tadawo.

Yazauna tare dariko hannunta, tunanin me ki ke
yi?

Takalle shi, halin rayuwa nake tunani, yace
yanzun umma ta kira ni jiya sun je gidan su
bishira wai yau zata dawo.

Ummi ta taba baki,
Allah yakawo ta lpy.

Ya ce ni ban soba gsky.

Sbd
ke ummi tadafa kirji, sbd ni?

Ni ya abba, kada
kasa duniya ta zage ni, Tare fa nasameku?

Yace
to ni dai kada kiga kamar da son raina, tace don
Allah ya Abba kabar zancen nan.

Kaje kagyar
mata dakunanta don su kamal bazasu iya ba,
yanufi gurinsu ganin kamar ya damu yasa itama
taje tasa musu hannu don dai ya saki ranshi, sun
gyara tsaf ummi ta goge sannan ta rufe dakin.

Har magriba bishira bata ji an ce za'a maida
taba, sai ta dauki wayar kanwarta ta kira shi wai
yazo don Allah yadauketa.

Tsakanin mata da miji
sai Allah, nan ya tausaya mata yace zaizo, kafin
ya isa sai daya sai mata waya irin dai ta hannun
ummi.

Har cikin gidan ya shiga suka gaisa da
babanta, yayi murna sosai yayi tawa Abba
godiya, tare da ba shi hakuri yace yasan yanda ta
horu zai gata canza da yardar Allah.

Yasa aka
turo ta yayi mata nasiha, sannan ya gargadeta da
cewa inhar ta bari mijinta yakawa kararta zatayi
mamakin abinda zai mata.

Tace, insha Allahu
baza ta kara ba, yakawo kudi yaba Abba, da kyar
ya amsa ita kuma ya bata wasu zannuwa acikin
leda, yace su raba da abokiya zamanta.

Taje tayi
wa hajiya zainu sallama suka tafi, tamkar
baquwa haka ta koma, sai kace basu taba zaman
aure da Abba ba, nauyinsa take ji.

Suna tafe ya
ciro waya ya miqa mata, tasa hannu ta amsa
yace taki ce, tayi ta godiya yace ba komai.

Sallamarsu tasa gaban ummi faduwa, ta dake ta
fito ta amsa, wani kishi ya tasho mata amma
saita danne.

Ta kalli bishira tare dayi mata sannu
dazuwa, ta amsa tana kallon ummi tayi kyau
tagoge daga ka ganta kaga wayayya 'yar gatan
miji.

Ta dauko makullin dakin ta ba bishira, abba
kuma ya nufi dakin ummi.

Bishira ta dinga kallon
yanda abba ya gyara gidan yaja gini ta gefen
ummi yayi mata falo da kicin, sannan tsakar
gidan an gyare shi da tiles.

Haka bandakin su
yagyara shi, nan dai bishira ta shiga dakinta ta
zauna bakin gado tana yi wa allah godiya tare
dayi wa kanta alkawarin har abada bazata ta
kara yin yaji ko ta janyo abinda zaisa mijinta ya
sake ta ba.

Ummi tana kan gado tana karanta
wani littafi yazo ya zauna bakin gadon bata ko
kalle shi ba don haushi take ji.

Sai take ganin
kamar rawar kai yake yi da dawowar bishiran,
kuma tuntuni yana zuwa gurin ta ya boye mata.

Yace madam ina son in yi magana da ku ne ke da
bishira, ummi tace ina jin ka, yace can zaki zo
muje.

Tace, gsky nagaji, kayi maganar da safe.

Yagama gano kishi ne ke damunta, don haka yayi
murmushi yace yanda kikace hakan za'ayi.

Ya
fita kamar minti 30 yasake shigowa ya aje mata
leda tare da cewa saida safe aciki tace Allah
yabamu alheri.

Yana tafiya taje ta banko kofarta,
yau kam bacci ya qi idanun ummi sbd tayi sabon
bacci a haqarqarin Abba.

Dukkan filolinta ta rasa
wanda zai maye mata madadin haqarqarin
mijinta, ynzun yancan da wata tasan yanda yake
wannan rawar jikin ynzun ya manta da batunta.

Tarasa me yake mata dadi, littafin datake
karantawa kuwa sam bata fahimtar abinda ke
ciki.

Hka ta dinga zubda hawaye har nisan dare,
ganin bata da wata mafita, tashi tayi ta bude kofa
lokacin 2 saura taje tayo alwala tazo ta kama
nafila.

Abba jin bude kofarta ne yasa shi leqowa
ta window aranshi yaji tausayinta don yasan bata
iya bacci sai ajikinshi, ita bata san ya leqo ba
don ko hanyar dakin bata ishe ta kallo ba.

Yakalli
bishira wadda bacci yayi gaba da ita ya tausaya
mata sosai yanda tayi tarawar jiki alokacin
auratayyarsu dazun.

Yadauko wayarshi yarubuta
ma ummi sako.

KI KWANTA KIYI BACCI BABY,
TARE DA QISIMA CEWA KINA LAFE
AMAKWANCINKI (WATO JIKINA) INA CIKE DA
KEWAR LEBUNANKI.

Tana sallah taji shigowar
saqo amma bata yi ko marmarin dubawa ba, haka
tai sallah har zuwa lokacin da bacci yasoma
fizgarta.

Tayi adduo'o'i sannan ta kwanta, saida
asubahi ne datayi sallah sannan ta karanta, dan
tsaki taja tare da cewa, Karya kawai, kishi yasa
ta fadin haka don tasan Abba sosai baya boye
mata komai ynzun.

Sai dai abinda yasake qular
da ita da asubahin nan yanda tana fita shi kuma
ya fito wanka, duk da tasan dole wani abu yafaru
tsakaninshi damatarsa, amma sai taga tamkar da
gayya ya tsaya don tafito taganshi.

Tna idar da
sallah ta dora ruwa akicin dinta, tadafa ruwan tea
taje kicin din bishira tadauko flask tazo ta wanke
ta zuba musu ruwan zafi taje kofar bishira tayi
sallama bishiran ce ta bude ummi tamiqa mata
tare da cewa an tashi lpy?

Cikin sakin fuska tace,
lpy lau, nagode.

Ummi ta ce ba komai takoma
dakinta ta kulle kofarta don yau bata da darasin
safe.

Abba ma yau bada wuri zai fita ba, don
haka yadan samu baccin safe sai 8 yayi wanka
ya karya, sannan yanufi dakin ummi.

Kofarta tana
rufe, ya kwankwasa ta share sai can dai dataji
yaqi tafiya sannan tazo tabude.

Takalle shiya yi
kyau cikin kananan kaya, ta kauda kai tare da
cewa, an tashi lpy?

Yace lpy lau, kin karya?

Tace,
um'um sai anjima, zata rufe kofar yace,
makaranta fa?

Tace sai karfe 2 nake da darasi.

Ta maida kofar ta rufe, yayi dan murmushin
takaici sannan yafita.

Kwananshi 2 dakin bishira
yayi niyyar dawowa dakin ummi, don ya kosa
yadawo ya lallasheta bazai iya daukar wannan
shariyar da take mishiba.
Chapter 61 · 0% Book details