← Book details Zurfin Ciki Part 1 - 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 63

Sashe 18

Zurfin Ciki Part 1 - 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"yanzun menene mafita?"ya tambayi
kansa,wata zuciyar ta ce, "kayi shiru tamkar baka
ga wannan takarda ba,tunda ba wanda yasan ka
gani." a fili ya ce,"haka ne." ya ci gaba da
tunanin kila ma yanxun ya janye kudirinshi,tunda
yaga ummin bata da kan gado. don yaga rubutun
yayi shi ne tun ranar da aka haifi ummi,ko kuma
ranar sunanta. tunda gashi har da sunan ummi a
jiki.mafita kenan yayi shiru.wata zuciyar ta ce,"in
ko kayi haka kayiwa Alhaji da ummanka adalci?
koda yar su ba yar adam ba ce bai kamata ka
gujeta ba.ko don albarkacin son da suka nuna
maka. shin da ummi ta kasance mai jin magana
da nutsuwa,kuma mai tsananin kyau zaka
gujeta?

Kada kayi zaton Alhaji yayi kudurin aura
maka yarsa ne don yasan zata zama mara ji,kayi
nazari. haka Abba yayi ta tunani har asubah
tayi,amma hukuncin da ya yanke shine yayi shiru.
sai dai ya janye batun rabuwa da matar shi,don
yasan yana sakinta zai zama mijin ummi,kai
batun nan hadiye ma cikinshi shine mafi dacewa.
dunkuna masu kyau yayi wa matarshi saboda cin
suna.haka yayi wa dan siyayya daidai karfinshi,ya
kawo ma umma.

Taji dadi sosai nan ahj ya iske
su, shima ya shiga dakin umman ya xauna ya ce
a dauko masa abinci nan xai ci yau.ya dubi abba,
babana nayi sautun raguna xuwa qauye nace xa
a siyo nmanya.abba ya ce biyu?umma tace
hakan yayi.abba ai tuwan girma miyarsa nama,
aja rago daya xiqal a shiga wannan gida da shi?
abba yace,me xai hana tunda ban musu qaryar
arxiki ba sun san mu talakawa ne.ahj yace
xancanka dutse bacna,amma maganar ummanka
ita xa a bi, sannan xa a sai buhun shinkafa da
cefane a kai musu.ana gobe suna abba da
abokansa suka dira gidan da ragunan da kayan
mai jego da na yaro sannan ga kayan abinci. sun
samu anty a gidan,ta musu tarbar mutunci.da
yake abba xana waya da ita,ya fada mata komai
ta sani.hjy zainu da taji kukan raguna ta fito,anty
tace dan Allah momy kada ki musu magana,kin
ga shi da abokansa ne.da qar ta samu ta turata
sashin ahj,shi kuma murna yayi yace aje a daure
su.zainu tace ahj menene na numa farin ciki sai
kace ba ma cin nama?can ba xa a ka kada ba
dan kawai shagalin sunan, sannan tace harda
shinkafa suka kawo sai kace muna yunwa? nana
take ya hade rai tare da cewa,zainu kada dai ki ce
min kin sa an dawo da yarinyar nan gidan ne dan
ki kashe mata aure?tace haba dai. ya ce to hir
dinki dan bansan in kuma jin irin xantukan nan
yayi ma matarsa daidai arxikinsa. mu kuma mu
ma yarmu da jikanmu gwargwadan arxikinmu,in
ya fito daga gun mai jegon ki turo min shi,sbd mu
ji in da xa a yi sa sunan.tace ina xa ayi in ba nan
ba?ya dube ta an taba haka?ki dai turo minshi.ta
taba baki sannan ta wuce.lkcn da ta leqa dakin
abba da abokansa suna xaune,abba yana ta fama
da danne dannen waya,domin tun da suka shiga
ya qi ko kallan inda bishira take bare danta.tace
bishira ki eada musu in sun fito ahj na san
magana da su.ta wuce ba tare da jiran jin amsa
ba,ko amsa gaisuwan da abokan abba suke mata
bata yiba.bishira ta kalli abba wanda tana
hankalce da shariyan da yayi mata,tace kaji abin
da momy tace?sai lkcn ya dubeta me tace? yayi
maganar ne cikin tsare gida.dadynmu yana san
ganin ku. bai amsa ba,sai kurun ya tura mata
jakar kayanta,ki duba,ta xaxxage dinkuna ne na
gani na fada masu kyau,duk da xannuwan ba
masu tsada ba ne kala uku atamfa daya shaea
daya sai kuma leshi.sai ko kayan yaron.ta dube
shh an riga an sai mana kayan fitar
sunanmu.ahmad ya dube ta wannan din baki so?
tace ni bance ba.abba yace ku tashi muje.tace
ina san magana da kai.ya ce kiyi
maganarki.muktar yace kuxo mu fita ta dauki
yaran tare da miqa mashi ta ce ina lura da kai
rabon da ka dauke shi tun randa aka
haifeshi,alhalin mu kuma yana nan yana hana mu
baccin dare.kai kana can kana baccin ka.ta fadi
haka ne cikin sanyin murya.ya amshi dan tare da
cewa ai gara ya hanaku bacci tunda kunqi ku
kaishi gurin babanshi.ya tsura ma yaran ido,wata
qaunan dan ce take shigarsa.ta matso
jikinshi.abba ya kalli furkarta,ita ma kallansa
take,ta ce yanxu ko dan murmushin ka bana
gani.yace,in da kina san gani da baki dawo ghda
ba.yaci gaba da cewa na sha mamakinki
bishira,da har xa ki yarda ki dawo gidanku ba da
ixinina ba. kuma tun kafin ki haihu sai da na fada
miki ba za ki zo gida ba.Ta ce To Abba mony ce
ta ce sai an zo.

Ya ce shi kenan ku zauna. ya
mike mata yaron ta amshe shi ta kwantar ta
kama mishi hannu.

Abba wane suna ka sa masa?
ya ce Sunan Alhj babba.

Da sauri ta saki
Hannushi .

Sunan 'yan da? ya kalle ta Na zaci
zaki ce suna mara ma'ana,tund da ne da sauki.
ya fice.

Haushin hali irin na Bishira ya ke ji.dn
son shi yasan tana matukar sonshi,amma bata
son yin biyayya ga abn d yake so.

Ya samu su
Mktr sannan suka shiga gurin Alhj ya tambaye su
in d za a sa sunan,Abba ya ce a masallaci kusa d
gidn babnshi ne za a yi addu a.

Amma tuni an sa
wa yaro suna Sulaiman.sunan babana.

Alhj ya ce
Madalla Allah ya raya mana shi, ba sai mun zo
ba dn yanayin sanyi ne.

Nan dai Abba d
abokansa suka tafi suna yabn Alhjn.

An ci sunan
shima Abba shi d abokansa sun yi walima da
Azahar. matar abokinshi Bala ita ce suka bai wa
girkin ta yi masu.

Mai jego taci gaba d wnk.

Abba
kan leka su lkc zuwa lkc,kusan dk lkcn d yaje ba
su cika rabuwa d dadi ba sbd mgnr d hjy zainu kn
datsa mishi.

Umma shi ma bata yi fushi ba tana
leka su dk d rashin sakar mata fuska d mai jegon
tare d mahaifiyar keyi.

Ummi tana tafe tana 'yan
tsince-tsincenta,kmr yadda ta saba,sai ko taga
sim,take ta yarda dk wani abu d t samu t dauki
Sim din.

Gefen zaninta t samu ta kulle,sannan ta
tafi,cikin jakr mkrntrta t saka.wata rana ta dauki
wayar umma ta shige daki,ta bude wayar ta cire
sim din ta saka wanda ta tsinto a cikin zani ta
soke wayar ta fito soro.Jikin dakin yaya Abba a
bakin kofar ta dauki lamar Abba da ya rbt sbd
masu zuwa nemanshi tana kira taji wayr tana
ringing.

Ta kashe tana ta dry,hk tayi ta yi wa
Abba Flashing dg nan tayi gidn du Amina
kawarta,tana ba wa Amina lbrn abn d ta ke wa
Abba.

Ta ce Amina nsn yanzun hk yana cn yana
jin haushi,shi yasa ki ka ga ina murna.Ta ce in ya
gane fa?Ummi ta ce Ai tsintar sim din nayi,Umma
kuwa ba za ta san na dauki wayarta ba,domin
yaya Abba da Alhjnmu kawai suke kiranta.

Amina
ta ce Yadda za a yi ki kira shi ne in ya dauka sai
ki make murya ki canza suna.

Ummi ta ce Tab,dn
in ci duka.

Amina ta ce Dalla cn gane ki zai yi?
suka kira ya daga ummi ta sirantr d muryarta
tana fadin "Hello!

Abba ya ce Ke wace ce ki ke
kiran layina?

Ta ce Sunana '"Suhaila. ya ce
Menene ki ke kirana?Ina ma ki ka samu lambata?

Ta ce Gani nayi ni ma a cikin wayr.

Tsaki yaja
Sannan ya kashe.Suka dinga tsuntsira dry.

Amina
ta ce Sake kiranshi ki ce ma ke a kaduna ki ke.

Ummi ta ce Kai yin waya akwai dadi ni ina son
buga waya.

Ta sake kira cikin Zafin rai ya ce Ke
lfy??kin dame ni fa!Ummi ta ce To tsaya mana
kaji ina son mu gaisa ne ni ina kaduna ne.

Ya ce
To na gode.

Sai ma ya kashe wayar gaba daya
suka yi ta kira a kashe.

Tun daga ranar Ummi ta
samu in umma tana aiki ko tana bacci sai ta sace
wayar ta cire sim tasa nata ta kira Abba.

Tun
yana kyararta hr ya daina ya koma rokon ta
daina kiranshi,dk a banza.

Daga baya sai Abba ya
soma sauraronta, ranar kuma ta kira shi ne
misalin dayan dare,ranar taki zuwa dakin
Tsohuwa ta kwanta a dakin umma. umma kuma
dama dakin Alhj take kwana.

A dai-dai lkcn ya
kwanta kadaici ya dame shi,ga garin yanayin
sanyi. wayar ta katse tunaninshi d yake yi na
matarshi zuwa yanzu ya haddace lambar Suhaila.

Ya daga ya ce "Hello ya ce Ke wai me ya hana ki
bacci?Ta ce Ni ba sunana ke ba,Ni sunana
Suhaila,kai fada min sunanka.

Ya ce Abba Ta
danne dryr d taso kwace mata ta ce Abba ba
suna bane,Fada mn sunanka n gsky.

Ya ce "Idris
Yadda ya fadi sunan sai da ta dage kwarai
sannan ta maida dryrta.

Ya katseta d cewa Ina
ku ke a kaduna?tayi dim,dn dai bata san ko ina
ba a garin kaduna ba,ba ta ma ta6a zuwa ba.

Take ta tuno Amina sun ta6a zuwa unguwar
Sarki,dn hk ta ce "Unguwar Sarki.

Ya ce, wai
shekaranki nawa?

Ta ce Sha takwas.

Ta sheka
masa karya.Ya ce Amma shi ne a ka ba kiwaya?
ta ce ta ka san wanene Babana?

Ya ce A"a ta ce,
To shi ne mai bawa Gwamna shawara a jihar
kaduna.

Abba ya ce Lallai, ki ce in nazo kawo
miki ziyara ba zan samun ganinki ba?

Ta ce za
ka ganni mana.

Ya ce To zan zo.

Ta ce To, Ya
ce,Amma fa ina d mata ta haihu ne ta tafi
wankan gida. .

Ummi ta ce Lallai to sai da safe.

Ya ce, Wa ke zuba miki kudi ne cikin waya?Ta ce
Babana mana. ita sai lkcn ne ma ta tuna cewa
ana saka kudi tunda ta ke kira bai taba kin zuwa
ba,aranta ta ce kila wannan ba a sa kudi.

Sunyi
Sallama babu dadewa,wayar ta sake daukar
tsuwwa.

Ga zaton Ummi Abba ne sai da ta daga
sannan taji muryar wani.
Chapter 18 · 0% Book details