← Book details Zurfin Ciki Part 1 - 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 63

Sashe 25

Zurfin Ciki Part 1 - 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Su
Safiyya suna mmkn yadda Habiba take da
matsanancin nacin gida. ******** Abba ya shigo
gidanshi dauke da ledajin kayan miya,da sauri ya
dire su kofar kicin ya nufi Bishira da ke kofar
bandaki tana shara amai.

Ya kama ta,"lafiya?Me
ki ka ce?

Sai da ta gama aman sannan ya karasa
da ita ta wanke baki da fuska a cikin bayin.

Ya
ce,Ba ki d lfy ne?Ta soma Hawaye, Ka gani ko
Babn Walid,kila fa ciki ne da ni.Tun wancan Satin
ya kamata in ga al'aldata amma shiru.

Ya ce, To
menene na kuka?

Yi shiru,Allah ya inganta.Ta
harare shi Dana fa bai shekara ba.Ya ce,To dole
ne sai danki ya shekara sannan Allah zai baki
wata kyautar?

Ta soma kuka,Ni dai zan je a
ciremin ne. ya hade fuska,Ban yarda da haka ba.

Ganin ta tada hnklnta tana cewa "Dama Hjyrsu ta
ce mata tabi a hankalu ta ki ji gashi nan yanzun
tana da wani ciki.

Ya ce To kada ki damu kin ji?

Zamu je asibtin dn a tabbatar da cikin kafin a san
abnyi.

Da za suje asibiti shi ne ya dage sai da
tayi wanka,dn d farko kaca-kaca ta dauko
mayafi, ya ce sai tayi wanka ta canza tufafi.

Gwajin farko ya tabbata tana da ciki,nan ta shiga
kuka. shi kanshi ya damu domin bai so ciki
yanzun ba.A son ranahi sai an yaye yaron kafin
wani cikin.

Amma ba shi da ra'ayin
zubarwa,nashi ganin kyautar Allah ce,dn haka ya
amsa ya kuma gode.

Ya lallashe ta da cewa,ta yi
hkr su amshi kyautar Allah dn haka wani na nema
da kudi bai samu ba. likita ya ce,Kada ta
damu,taci gaba da bai wa danta abnci tana hada
mishi da nonon,a hnkli zata yaye shi bana farat
daya ba.

Bayan ya kaita gida ya kuma
lallashenta,saiya nufi gurin Umma.

Bayan sun
gaisa,ta tambayi iyalanshi ya ce "Daga asibiti ma
muke da Bishira." Umma ta dube shi da
sauri,Waye ba lfy? ya ce, Ita ce.Sai kuka ma take
yi wai dn an ce tana da ciki.

Umma ta ce, Ikon
Allah, to Allah ya inganta.Sai dai kuma kada
Walid ya sha ciki.

Abba ya ce,likiya ma ya yi
mata bayanin yadda za ta yi masa,hr ta janye shi
daga nono cikin hikima.Umma ta ce, Da za ta
yarda ma an kawo mana shi nan. ya ce,Ai dama
nan zan kawo shi da zarar an yaye shi Umma.

Sam bai fada ma Bishira nufinshi na baiwa Umma
Walid ba,dn yasan ba zata ta6a laminta ba.Sai
dai itama tasan dole hakan zai yi.

Don haka ta
garzaya gurin Umman Bashir ta shaida mata
cewa sunje asibiti,dk ta fada mata komai,sannan
ta ce ita danta take tunani kada ya dauka ya
kawo wa Ummarshi ita ma a mallake mata yaro.

Umman Bashir Ta ce Wannan a zaune take,sai
dai in ko ba a kai shi ba.Amma ki bari daga kin
kula ya daina damuwa da nonon ki janye shi,zan
zo in taho da shi wurina.

Bishira taji dadi tare da
cewa, Hakan dai yafi.

Sabuwar kazanta ta
samu,Bishira dk abn bi bangon daki an tofe da
yawu.Rashin wanka sabo,kai abn nata sai
addu'a.

Ibada kuwa ba a mgn,domin dai tuni ta
aje Sallah a gefe,Azumi dai tana yi amma in ta
sha bata ramawa.Allah ya shirye wanda ya 6ata.

Abba ya dai yanzun tuni ya yafe abincin
gidansa,matsawar ba shi da kanshi ya girka
ba,don kuwa dama can shi mutum ne mai
kyankyani.

In zata fita takan wanke kafafunta ta
dauki kaya ta saka,sai ka rantse tayi
wanka.Amma da zata matso kusa da kai,nan za
ka ji kauri na tashu da karni da kuma wari.

Dole
ya hkr da laluranshi ta aure a gurinta,domin in
yaje shimfidarta ba zata ki ba,amma wari da
zarni suna hana shi yin komai cikin nutsuwa.

In
kuma dakinshi ya kirata ko bata kwana ciki ba
har gari ya waye yana jin warin jikinta a
shimfidarshi don haka lokuta da yawa yake
hakura da ita. *********** .

Ummi tana kwance
kan gadonta,yayin da Khadija da Safiyya suke
zaune bakin gadon Safiyyan wadda ke kallon
Ummi.

Hirar masoyinta take basu,Safiyya bata ko
gajiya da zancensshi.

Khadija ta ce,ita ma da
zata taho har kuka nata Saurayin ya yi.

Sai lkcn
Ummi ta dube su,"kuka Khadija?Khadijata
ce,"Riris Kuwa.

Ummi ta ce, Hu'um ba namijin shi
yasa nike da za6i a kan irin mijin da zan aura.

Safiyya ta ce,"ke banza,dk cikin so ne.

Ummi ta
ce Ban damu da sai namiji yaso ni ba,in dai ya
tara abubuwan da nake so ga namiji to zan yi
amfani da kasantuwata 'ya mace in koya mishi
Sona.

Khadija ta tashi ta dawo kusa da Ummi,Kin
san me ki ke fada?Koda yake sanar damu yadda
ki ke son mijinki ya kasance?

Ummi ta ce "Na
farko mai son Addini,Mai Ilimi duka 2,mai hakuru
,sannan yana da saurin fushi,mai kuzari da
kwarjini.

Ma"abocin tsafta da tsantseni,wandadk
tufafin da yasa sai sun kar6e shi,mai biyayya ga
iyayensa,sannanmai kula da gidansa,baki mai
tsare gida,ga yawan Ibada, Safiyya da khadija
suka kwashe d dry,Khadija ta ce, Ina za ki samu
dk mai wadannan lissafin da ki ka yi???

Safiyya
ta ce, Kuma fa bata gama lissafin ba ke ba ki ji
ana cewa dan Adam tara yake bai cika goma ba?

Ummi ta ce,Akwai shi,Ya Abbanmu haka
Halayansa suke.

Yanzu ma da ni ke lissafin shi
na ke kallo a idona.Khadija ta ce,To ba dan
uwanki ba ne da shi kenan kin samu a gida.Ummi
ta ce,Wuu fitina Road,wannan ya mugun tsanata,
ina son dai me irin halayarshi ds
dabi'unsa.Khadija ta ce,Har da kamaninsa?

Ummi
ta ce,sosai ma.

Saitaga sun sa dry.Safiyya ta ce,
Malma shi ki ke so,kuma dk yanda a ka yi ba
shakikin ki ba ne,da aure a tsananinku.

Umma
tayi Shiru tana kallonsu,Khadija ta ce,Habiba
kenan,wai har saurin fushinshi tana so.

Ummi ta
6ata rai tare da cewa,Tunda kun kasa fahimtata
shi kenan.Ya zan yi in ce ina son Ya Abba yana
da matarsa?

SAfiyya ta ce,ke dai in da aure
Tsakaninku kada ki tsaya "ZURFIN CIKI, kizo a
karshe kina da kin sani.

Ummi ta ce,A bar
zancen. 32...

Sai dai kuma a daran ranar ta
tsinduma duniyar tunani.Tabbas zuciyarta da
shisshiga take,tunda ta rasa wanda zata so sai
Ya Abba.

Wanda ya yi mata muguwar tsana.Afili
ta ce,Duk kauce-kauce da kewaye-kewaye ba za
su kai ni ba,Ya Abba nake so.

Hawaye Suka
soma sintiri daga idanunta.

Wannan lkcn ziyarar
da yazo Abba da Umma d Tsohuwa da Alhj
Karami dk suka zo.

Dadi ya kashe Ummi,ta rasa
jikin wanda zata fara fadawa don dadi.

Alhj
karami ta soma kamkamewa sannan
Umma,Tsohuwa kam ai tana manne jikinta hr
suka zo tafiya.Shi ko Ya Abba yanzun kunyarshi
take ji,dn haka tunda suka gaisa mgn bata kara
hada su ba.

Sai dai jife-jife suna satar kallon
juna,in sun hada ido sai ya dan daure
fuska.Safiyya da khadija sun gaisa da su sannan
sun yaba da yadda a ke ji da Ummi.

Da za su tafi
kuwa Ummi kuka Tsohuwa kuka,sai da Abba ya
ce ba za a sake zuwa da su ba,Sannan Ummi tayi
shiru.Sun tafi sun barta d kewarsu,Kamar yadda
suma suka tafi suna kewarta. ********** .

Bishira
da kanta ta dauki Walid ta kai ma Umman
Bashir,domin ta san zai kai ma Ummanshi ne.

Abba ya rufe ta da fada lkcn d y tambayi dan ta
ce ta yaye shi ta kai ma Umman Bashir.

Ya ce To
je ki dauko mn yarona,dn ba can nayi niyyar kai
shi ba,Ta rike kugu,kaje mana da kanka,tunda ba
ka son zamn danka hannun mahaifiyarka to ni ba
zan yi saken da Mahaifiyarka tayi ba a ka raba ta
da danta ina fata ka fahimci karatuna?

Kallo
kurum ya bita da shi,sannan yaja tsaki tare da
cewa,Dube ki kmr wata Bauna,jiki sai tsami yake.

Ta ce,Eh dk abn da zaka ce kace.

Ya juya ya fita
rai 6ace.

Umma ya Samu ya fada mata, ta ce, To
menene na bata rai Abba?

Can din da nan ba dk
daya ba ne? ai ba za su cutar da shi ba.

Ya ce, ki
fahimce ni Umma,ba ina nufin zai cutu ba
ne,amma can da yara kanana,nan kuma babu.

Sannan......... ......

Sai kuma ya yi shiru tare d
cewa,Shi kenan.

Umma ta ce,Yauwa bana son
kana daga murya kan abn da bai kai ya kawo ba.

Allah ya raya mana shi ya kuma sauketa lfy.

Abba Ya ce Ameen.

Gidan (T.V)sun kira Abba sun
masa (intervier)da kusan wata 2,dmn ya cire ran
samun akin, ko da yaje suka ce sun dauke shi
aiki.

Abn d yasa suka yi jinkiri daukarshi,suna
canza tsarukan aikin ne sannan sun sake
tantance ma'aikatansu.

Litinin Abba ya soma
zuwa aiki kmr yadda a ka bukata,dakin watsa
labarai a ka kai Abba.

Sam bai samu matsala
ba,dk d shi na mai yawan surutu ba ne,amma a
cikin sati 1 ya goge da aikin,km an yaba da yadda
yake watso labarai.

Yana yi da Hausa minti sha
biyar da turanci minti sha biyar,ana sakawa karfe
7 na yamma.

Abba ya kama aiki cikin sa'a nan
da nam sai farin jini cikin abn d bai fi wata ba ya
nemi izinin a bashi fili koda mint 15 ne don
gabatar da wani fili da ya yi masu don matasa.
filin yana kiran shugabannin matasa na
unguwanni suna hira da su akan halin da matasa
suke ciki na shaye- shaye da sace-sace da kuma
rashin sana'a.

Da turanci a ke shirin,sannan a kan
baiwa sauran matasa na gida su bugo waya su
fadi nasu ra'ayin,game da abin da ya kawo
hakan,da kuma hanyoyin da za a bi don magance
su.

Haka nan ya kan samu lkc ya shiga cikin
matasan musamman ma su shaye-shayen da
marasa sana'a dn jin ra"ayoyinsu,da dalilan
fadawarsu cikin harkar.

Kafin wani lkc filin ya yi
suna kuma kullum yakan tallata filin kan cewa ya
kamata Gwamnati ta dauki nauyi filin don yana
taimakawa mata wurin inganta rayuwar matasa.

Cikin ikon Allah sai gashi Gwamnati ta yaba da
filin,ta dauki nauyin shirin kuma an sa shi hr
fannin Radiyo.
Chapter 25 · 0% Book details