Sashe 40
Zurfin Ciki Part 1 - 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Inna Saratu
ta ce, Kai Ummi da iya shege take, ina kallonta
shi ta fara kare ma kallo sannan ta kalli kowa
amma wai bata ganshi ba.
Su Alhaji dai 'yar
dariya suka yi sannan suka fita, Abba ya bi su
tare da yi wa su Umma sallama. * 31.
Bayan
fitarsu, Umma ta dubi Ummi fuska daure, ina
fatan baki nuna damarar nuna kiyayya ga Abba
ba ne?
Ummi ta sunkuyar da kai, a ranta ta ce,
"Kin ji Umma da wani zance, ai ina zaton nafi
Mahaifiyarshi sonshi ma bare ku.
"Amma a fili sai
ta ce, To Umma shi ma fa Ya Abban bai ce yana
sona ba, Umma ta ce Saratu ji ta da wani shirme.
Ina ce ita ce zata janyo ra'ayinshi gareta?
Inna
Saratu ta ce, Kwarai kuwa, ta hanyar ladabi,
biyayya da girmamashi, musamman shi da ke da
matsalar mata.
Ummi ta ce, Kuma ina tsoron
masifar matarsa ba dai guri daya zamu zauna ba
ko?
Umma ta ce ina ruwanki da matarsa?
Sannan in ba ku zauna guri daya ba haya zai
kama?

Kada ma in ji kin kuma zan nan, Ummi dai
tayi shiru.
Da dare Alhaji ya tasa Abba zuwa
gidan su Bishira, zuwan su ne ma Alhajin yasan
'yarshi tayo yaji, cikin 6acin rai ya kira wayar
Hajiya Zainu ya ce su zo ita da Bishira.
Ba tare
da ya jira amsarta ba ya aje wayar, ba tare da
yasan abinda ya faru ba ya shiga ba su hakuri.
Hajiya Zainau taje dakin su Bishira ta kira, suka
nufi sashen Alhajin tana mitar cewa munafukai
sun zo kenan, ai za'ayi ta bari muje mu ji.
Suna
shiga Alhajin ya kalli Bishira, "Me ki ka zo min ki
yi a gida?
Ta ce, Daddy cin amanata ya yi, aure
fa ya yi da yarinyar da suka tsane ni.
Alhajin ya
daukin da ke gabanshi na plastik ya jefe ta da
shi, auren shi ne cin amana don uwaki?
Hajiya
Zainu ta ce, "A'a Alhaji, zan cen gaskiya a duba
hakkinta itama, ya ya za a dau 'yar da bata
kaunarta, iyayenta basa kaunarta a ba shi.
Sannan ta yi magana ya hauta da zagin iyaye?
Ya ce, "Ke yi min shiru ban tambaye ki ba".
Ya
kalli Abba, Ya abin ya faru?
Ban ji ta bakinka ba?
Nan dai Abba ya fadi komai har ta taho, daidai da
cewa tazo ya rage mata haya da abin da ta ce
duka.
Alhajin ya yi tsaki ya dubi Alhaji Babba, irin
wannan ai ba a biyo su, tayi ta tafiya sai dai
nima in ba zata koma gidanta ba, to ba gidana
ba.
Ya zura hannu cikin aljihu ya ciro rafar 'yan
dari bibbiyu, Ga shi Abba, dama nayi maka
alkawarin baka sadaki duk lokacin da ka nemo
aure. 57.....
Abba ya ce, "A'a ka bar su ai an riga
an yi.
Mahaifin Bishira ya ce, "Ni nayi alkawari.
Suka yi godiya.
Ya kalli Bishira, Ko ki bi mijinki,
ko ki bar gidana.
Hajiya Zainu ji take tamkar ta
shake Abba.
Ta ce, "Haba Alhaji, gaskiya ban
yarda da wannann hukuncin..." Ya katse ta da
cewa, Ke!
Da Allah fita anan.
Su Abba suna shiga
mota Bishira na fitowa da kukanta, dole ta zo ta
shiga motar.
Alhaji Babba ke ta bata baki har
suka kai gida, shi kam Abba da suke sauke Alhaji
ya yi nasu gidan, suna shiga ta soma zantuka.
Ba
za ka ta6a samun kwanciyar hankali ba a gidan
nan har abada, ba dai ka matsa an dawo da ni
ba?
Abba ya yi murmushin mugunta, ai ni
wannan yajin naki naji dadinsa, gashi har na
samu gudunmawa, kin ga sai naje kasuwa in
soma darzo wa Amarya zannuwan lefe.
Ya nufi
dakinshi ya barta nan tsaye tana zage- zage,
lefen banza, in ma uban lefe ne kai da ita sai na
koya musu hankali.
Kusan goman dare Ummi
tana kan doguwar kujera, addu'a take yi Allah
yasa Abba yazo ta ganshi kafin tayi bacci.
Can
kasan zuciyarta kuma kishi ne don tasan sun je
gidansu Bishira ne biko ganin Alhaji ya shigo shi
daya sai ta debe tsammani da zuwanshi.
A ranta
take raya cewa yanzun haka suna can suna cin
soyayyarsu, kamshin turaren shi ne ke mata gizo
a hanci.
Amma sai kunnuwanta suka tsinkayi
sallamarshi, a hankali tamkar ba ya son a san ya
shigo.
Umma tana ciki?
Tambayar da ya yi kenan
ba tare da ya jira ta amsa sallamar ba, ta tashi
zaune da sauri a'a tana gurin Alhaji.
Ya shigo ya
zauna ta ce, "Sannu da zuwa".
Ya amsa yana
kalonta, ta sunkuyar da kai, gabanta ke wata irin
faduwa.
Shi kam ji yake tamkar ya manne ta a
jikinshi, sai dai yana jin nauyin hakan tunda ba
suyi wannan sabon da ba rin haka zata faru
tsakaninsu ba.
Dakin yayi shiru, ita tana wasa da
yatsunta shi kuma yana kallonta, can ya ce
"Ummi".
Ta dube shi "Yaushe za ki tare?
Ta ce,
Nima ban sani ba, sai yanda su Umma suka ce.
Ya dauko kwalin wayar da ya sai ma Bishira ta
jefe shi da shi ya ciro wayar ya hadata da batir
din bayan ya 6are sim din ya saka.
Ummi dai
tana ta kallonshi, ya manna chajar a jiki, ya mika
ma Ummi jona min can, ya nuna mata soke din
da ke bayanta.
Ta amsa cike da sha'awar wayar
duk da bata nuna hakan ba sannan ba ta ce kala
ba.
Ya ci gaba da cewa, "Karfe nawa a ke kashe
inji?
Ta ce, har yanzu ba a canza daga yanda ka
ke kashewa ba.
Ya ce, "Sha daya zuwa sha biyu?
Ta ce, "Eh, ya ce in har zuwa wannan lokacin ba
kiyi bacci ba to ki cire in an kashe, ki kunna ko da
yake in dai ke ce ba sai na ce ki kunna ba.
Ta
dago ido ta kalle shi, ya ce, Eh kunnawa za ki yi
ko za ki musa ne?
Don kin fi ni ma sanin kan
waya.
Ta ce, Wayar Umma kadai na iya kunnawa,
sai taka.
Ya ce, Oho, cikin dan murmushi, na za
ci ba za ki fadi tawa ba in tuna miki lokacin da
kika kunna tawa.
Haka nan don tsabar iya sarrafa
wayarki tun kina 'yar karama ki ka tura ni garin
Kaduna. * 58....Haka nan don tsabar iya sarrafa

Kaduna.
Ta zuba fuskarta cikin tafukan
hannayenta, sam bata son Ya Abba yana tada
wannan zancen, Umma ta shigo da sallama tana
cewa, Yuwa Ummi, ina ki ka sa min 'yar kwalbar
turaren nan?
Ummi ta dago fuska, "Cikin jakarki
ta rataye.
Umma ta dubi Abba, "A'a ha, yaushe
ka shigo?
Ya ce Ban jima sosai ba.
Ta zauna ya
gaisheta, sannan ta ce masa dama Alhaji yanzu
yake ce min zaman me Ummi ke yi a gidan nan?
Ya zaci tun daga asibitin zata wuce dakinta,
Ummi ta turo baki.
Umma Alhaji ya gaji da ni
sosai, suka kalle ta, Umma ta ce, Ji wani shirme,
me ya yi na gajiya?
Ta ce To dubi fa daga cewa
an fasa aurena sai da ya matsa ya daura min
aure.
Sannann kuma yanzun wai ya zaci daga
asibiti zan tare?
Abba ya ce, Ai yana daki yi
hanzari ki same shi don shi ya san amsarki ba
Ummata ba.
Umma ta ce, "Wallahi daga nan suka
share Ummi.
Ta kalli Abba ta ce, "To kawai
yanda za a yi gobe ka kwashe kayanka daga
dakinka sai a kai na Ummi din kawai.
In yaso
zuwa yamma ko Saratu da sauran makota sai su
rakota.
Abba ya kalli Umma, ni da so nayi a dan
yi kwaskwarima a gidan kafin sannan na dan
samu na sai ma Ummin Zannuwa.
Umma ta ce,
"Zancen wofi, yanzun tsirara take yawo?
Kawai in
kana da fenti a hannu a goga a kawo ta haka, in
babu ma dai goben nan zata tare don ba zan
amince ran mijina ya 6aci ba.
Abba ya yi
murmushi, to shi kenan Umma da safe kafin na
fita zan nemo masu aiki ina da fenti da siminti
sai ayi 'yar kwaskwarima shi ke nan.
Dama ga
kudi nan da Mahaifin Bishira ya bani, wai dama
ya yi min alkawarin biya min sadaki. . 59...
Umma ta ce, "Yanzun Alhaji ya gama bani labari,
Mahaifin yarinyar nan mutumin kwarai ne, don
Allah Abba ka rike yarinyar nan ko don darajar
mahaifinta.
Ummi ta ta6a baki, kishi ya motsa.
Abba ya ce "In sha Allahu Umma nima abinda
nike dubawa kenan, ni ke hakuri da ita.
Ta ci
gaba da cewa, Sannan kada kaga Ummi yar
uwarka ce ka ce zaka fifitata, sam ba zan yarda
da haka ba.
Kayi adalci a tsakaninsu ka dinga
addu'a Allah ya hada maka kansu.
Ya ce, "In
Allah ya yarda Umma zan kula.
Ta ce, "To maza
ka tashi ka tafi gurin iyalinka.
Sam bai ma dace
ka fito ba, kamata ya yi a ce ka zauna gida ka
kara ba matarka baki, ya cee To Umma.
Ta mike
tana cewa, tashi maza.
Ya mike yana kallon
Ummi, yayin da ita kuma ta juya fuskarta cike da
6acin rai.
Ya ce, Ummi ki fa kunna in an kashe
injin?
Sam ba ta tanka ba don haushi, sai da ya
tafi sannan Umma ta dubi Ummi.
Ki tashi ki
kwanta don gobe ki tashi da wuri, kiyi duk shirin
da ya dace saboda babu daga kafa a tarewarki
gobe.
Ki ta fasha-fishenki ba zamu kuma yarda
da kalace-kalacen ciwonki ba, ta tafi abinta.
A
zaton Umma, Ummi tana fushin ba zata tare ba
ne, ita ko haushinta korar mata miji da Umma
tayi ya tafi gurin kishiyarta.
Koda ta kulle kofar
ba ta shiga uwar dakin ba, nan kan doguwar
kujeta ta mike abinta.
Jira ta ke a kashe Injin ta
kunna waya.