← Book details Zurfin Ciki Part 1 - 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 63

Sashe 55

Zurfin Ciki Part 1 - 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tace, insha Allahu baza ta kara
ba, yakawo kudi yaba Abba, da kyar ya amsa ita
kuma ya bata wasu zannuwa acikin leda, yace su
raba da abokiya zamanta.

Taje tayi wa hajiya
zainu sallama suka tafi, tamkar baquwa haka ta
koma, sai kace basu taba zaman aure da Abba
ba, nauyinsa take ji.

Suna tafe ya ciro waya ya
miqa mata, tasa hannu ta amsa yace taki ce, tayi
ta godiya yace ba komai.

Sallamarsu tasa gaban
ummi faduwa, ta dake ta fito ta amsa, wani kishi
ya tasho mata amma saita danne.

Ta kalli bishira
tare dayi mata sannu dazuwa, ta amsa tana
kallon ummi tayi kyau tagoge daga ka ganta
kaga wayayya 'yar gatan miji.

Ta dauko makullin
dakin ta ba bishira, abba kuma ya nufi dakin
ummi.

Bishira ta dinga kallon yanda abba ya
gyara gidan yaja gini ta gefen ummi yayi mata
falo da kicin, sannan tsakar gidan an gyare shi da
tiles.

Haka bandakin su yagyara shi, nan dai
bishira ta shiga dakinta ta zauna bakin gado tana
yi wa allah godiya tare dayi wa kanta alkawarin
har abada bazata ta kara yin yaji ko ta janyo
abinda zaisa mijinta ya sake ta ba.

Ummi tana
kan gado tana karanta wani littafi yazo ya zauna
bakin gadon bata ko kalle shi ba don haushi take
ji.

Sai take ganin kamar rawar kai yake yi da
dawowar bishiran, kuma tuntuni yana zuwa gurin
ta ya boye mata.

Yace madam ina son in yi
magana da ku ne ke da bishira, ummi tace ina jin
ka, yace can zaki zo muje.

Tace, gsky nagaji, kayi
maganar da safe.

Yagama gano kishi ne ke
damunta, don haka yayi murmushi yace yanda
kikace hakan za'ayi.

Ya fita kamar minti 30
yasake shigowa ya aje mata leda tare da cewa
saida safe aciki tace Allah yabamu alheri.

Yana
tafiya taje ta banko kofarta, yau kam bacci ya qi
idanun ummi sbd tayi sabon bacci a haqarqarin
Abba.

Dukkan filolinta ta rasa wanda zai maye
mata madadin haqarqarin mijinta, ynzun yancan
da wata tasan yanda yake wannan rawar jikin
ynzun ya manta da batunta.

Tarasa me yake
mata dadi, littafin datake karantawa kuwa sam
bata fahimtar abinda ke ciki.

Hka ta dinga zubda
hawaye har nisan dare, ganin bata da wata
mafita, tashi tayi ta bude kofa lokacin 2 saura
taje tayo alwala tazo ta kama nafila.

Abba jin
bude kofarta ne yasa shi leqowa ta window
aranshi yaji tausayinta don yasan bata iya bacci
sai ajikinshi, ita bata san ya leqo ba don ko
hanyar dakin bata ishe ta kallo ba.

Yakalli bishira
wadda bacci yayi gaba da ita ya tausaya mata
sosai yanda tayi tarawar jiki alokacin
auratayyarsu dazun.

Yadauko wayarshi yarubuta
ma ummi sako.

KI KWANTA KIYI BACCI BABY,
TARE DA QISIMA CEWA KINA LAFE
AMAKWANCINKI (WATO JIKINA) INA CIKE DA
KEWAR LEBUNANKI Tana sallah taji shigowar
saqo amma bata yi ko marmarin dubawa ba, haka
tai sallah har zuwa lokacin da bacci yasoma
fizgarta.

Tayi adduo'o'i sannan ta kwanta, saida
asubahi ne datayi sallah sannan ta karanta, dan
tsaki taja tare da cewa, Karya kawai, kishi yasa
ta fadin haka don tasan Abba sosai baya boye
mata komai ynzun.

Sai dai abinda yasake qular
da ita da asubahin nan yanda tana fita shi kuma
ya fito wanka, duk da tasan dole wani abu yafaru
tsakaninshi damatarsa, amma sai taga tamkar da
gayya ya tsaya don tafito taganshi.

Tna idar da
sallah ta dora ruwa akicin dinta, tadafa ruwan tea
taje kicin din bishira tadauko flask tazo ta wanke
ta zuba musu ruwan zafi taje kofar bishira tayi
sallama bishiran ce ta bude ummi tamiqa mata
tare da cewa an tashi lpy?

Cikin sakin fuska tace,
lpy lau, nagode.

Ummi ta ce ba komai takoma
dakinta ta kulle kofarta don yau bata da darasin
safe.

Abba ma yau bada wuri zai fita ba, don
haka yadan samu baccin safe sai 8 yayi wanka
ya karya, sannan yanufi dakin ummi.

Kofarta tana
rufe, ya kwankwasa ta share sai can dai dataji
yaqi tafiya sannan tazo tabude.

Takalle shiya yi
kyau cikin kananan kaya, ta kauda kai tare da
cewa, an tashi lpy?

Yace lpy lau, kin karya?

Tace,
um'um sai anjima, zata rufe kofar yace,
makaranta fa?

Tace sai karfe 2 nake da darasi.

Ta maida kofar ta rufe, yayi dan murmushin
takaici sannan yafita.

Kwananshi 2 dakin bishira
yayi niyyar dawowa dakin ummi, don ya kosa
yadawo ya lallasheta bazai iya daukar wannan
shariyar da take mishiba.

Tsakaninta da bishira
lpy lau amma shi sai tana wani share shi.

Ya
shigo da zumudi zai nufi dakinta, tamiqe cikin
fara'a daga wanke-wanken da take yi ta amshi
ledar hannunsa da jakar laptop ta nufi dakin
bishira.

Shida bishira suka bita da kallo, ganin
zata shiga bishira tace ummi yau ai dakinki yake.

Ummi tace injiwa?

Anty bishara ai kullum ke ce
dashi har sai kin rama duk kwanakin da kika
dauka agida.

Kinga kenan kusan wata goma sha
daya kenan.

Abba cikin sauri yace ke
mahaukaciya ce?

Ina ki kasamo wannan fatawar?

Ta kalle shi, sannan tashiga dakin ta ajiye ta fito
taqara kallonshi gurin malamai, yace to ban
yarda ba, don haka zanci gaba dayi muku kwana
bibbiyunku, ummi tace to ni na yafe mata nawa
kwanakin bishira tace nagode ummi.

Haushi ya
cika Abba, amma shi bazai dauki wannan horon
da ummi take shirin yi masa ba.

Yadawo dakin
bishira a fili yafurta kema saina baki haushi zakiyi
dakin sanin wannan furucin.

Sharewa yayi yaci
gaba da kwana dakin bishira tare da nuna kulawa
ga bishiran.

Ummi ta jure duk da duk daren Allah
sai taci kuka ta gode Allah, sannan tashiga zargin
cewa shi ma ya Abban dama can yana son
tarewa dakin bishira, inba haka bame zaisa yayi
saurin yarda kuma yayi ta nuna mata soyayya?

Ganin ummi tana yi tamkar bata damu ba yasa
shi qa rajin haushi, yadawo da yamma suna
zaune kowa A qofarshi.

Ummi tayi kwalliya cikin
qananan kaya, bishira kuma tana sanye da leshi,
karatun littafi bishiran keyi ita kuma ummi tana
yin gyaran qumbunanta.

Bawai suna wata hira
bane amma suna kula juna sosai musamman
bishira tana son su saba da ummi.

Ummin ce.
bata cika son fitowa ba, bishira ta tashi ta masa
sannu dazuwa tare da amsar kayan hannunsa
don yanzun tana koyi da ummi gurin kyautatawa,
ummi ta kalle shi sannu dazuwa, ya amsa da
yauwa baby.

Yakalli bishira sweety zanyi wanka,
tace to, takai masa ruwa yashiga dakinta, sai
tazo tace masa takai nan k sweety zanyi wanka,
tace to, takai masa ruwa yashiga dakinta, sai
tazo tace masa takai nan kuma yajanyo bishira
jikinshi.

Ba wai yana da bukata bane, amma don
ya shaqar da ummi sai ya banko kofar, qaran
kofar ne yasa ummi kallon gurin dakin.

Ta duqar
dakai taci gaba da abinda take yi, kusan minti
arba'in suka fito, Abba ya matsawa bishira wai
suyi wanka tare, tace ni bazan iya ba akwai ummi
dama da dare ne inajin kunya.

Kuma kada taga
kamar cin fuska ne, yace kenan don kada ki bata
mata rai ni mijinki bazaki faranta min ba ko?

Dole
ta bishi suka shiga bayi.

Baqin ciki yasa ummi
tashi tashige daki, kuka sosai tayi daga nan bata
fito ba sai magriba, tanayin alwala tarufo kofa,
washegari ma qin bude qofar tayi daga alwalar
asubahi.

Abba yayi ta raba ido ya ganta amma
bata fito ba, yasan fushi take, ya kira wayarta
taqi dagowa yayi mata saqo cewa in zata
makaranta tafito inkuma sai darana ta bude ta
amshi kudin mota.

Tana gama karantawa tayi
wuri da wayar ba tare data bashi amsa ba, haka
ya tafi.

Bishira ta qwanqwasa ma ummi ta bude
suka gaisa, tace naga baki fito bane ina fata lpy?

Tace lpy lau bacci ne, tace yau baza kije
makaranta bane?

Ummi tace, zanje sai sha biyu.

Bishira tace kinji dadinki ni gashi nan ina tayi
masa zancen karatun amma ya share ni, ummi
tace inkin matsa zai yarda, tace ko za ki dan sa
min baki?

Ummi ta riqe baki, ni a wa?

Ke da yake
hannunki ai ke ce zai saurara, ni kin zo ne ma ki
zage ni.

Bishira tace wane irin zagi?

Ni dama ki
amshi mijinki ummi don gangar jikinshi ce kawai
agurina, amma ruhinsa yana gurinki.

Ummi ta ce,
ngd da zagi, bishira ta ce zancan gsky ne ba
wani zagi.

Haka suka yi ta rayuwa cikin kwanakin
ummi kam har rama tayi shima Abba ya rage
walwala don wanda yasan kan kula da shi
kamarta.

Yayi missing din abincinta.

Amma ya
gaji bazai jure ba.

Ya tuna bishira tace masa zata
ta yini gidan ummanshi.

Don haka yana gama
muhimman abubuwan da zai yi agurin aikin
yanufi gida.

Ummi tana shirin tafiya makaranta ta
dauko jakarta sai kurum taga mutum kamar an
jeho shi.

Ta daure fuska tamkar bata taba dariya
ba, yace ummi nagaji kin ji ko, na gaji da wannan
horon naki.

Laifin me nayi miki?

In don na dawo
da bishira ne sai in saketa, duk ba kece kika
takura min sai na dawo da ita ba?

Ummi tace, ni
karka doran jakar tsaba kasa kaji su bini, ka saki
matarka sbd ni?

Ba ruwana.

Yace, to ki dawo
yanda kike, kuma ki janye batunki na wai kin
haqura dani, niban haqura ba.

Ke ma kuma nasan
dole ki kasa kanki, ummi ta ce ni ban damu ba,
ya ce qarya ne gashi nan duk kin rame?

Ya
canza daga fada zuwa lallashi, ummi don Allah
na roqeki mu koma kamar da, haba bebyna.

Ya
lalubo hannunta ta qwace, don Allah ka tafi kada
bishira ta dawo ta same ka anan ta zargi wani
abu.

Haushi yakamashi sosai, ya daga murya da
qarfi, kin san Allah ummi zan hadaki da umma, ta
nufi hanya fita, nikaga kada kasa ni yi latti don
lokaci yayi nisa.

Ya ficiko ta ta dawo ba zaki
makarantar ba, ke an ma daina karatun tunda yafi
ni.

Ta zubar da jakar da hijabi ta nufi gado shi
kuma ya fita cikin zafin rai, gidan su umma yaje.
Chapter 55 · 0% Book details