← Book details Zurfin Ciki Part 1 - 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 63

Sashe 20

Zurfin Ciki Part 1 - 4 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Umma tace in sha Allah
gobennan xai dawo gida. ummi tace to,umma
tace kinga wayata? gaban ummi ya fadi ta tashi
da sauri ta shiga neman waya,taci sa'ar ganin
wayar,sai dai bata san inda ta saka sim din ba
sai wanda ta tsinto ne a ciki.ummi dai tayi shiru
ta miqa ma umma waya. kusan qarfe goma sha
daya wayar abba da umma ta taho da ita ta
soma qara,umma ta dauka.alhj ne ya ce ina
wayarki ina ta kira ana cemin a kashe?una tace,
a ku6e take gata ma a hannuna.yace to inata
kira.tace qila faduwan da tayi daxu ne ta samu
matsala.yace to dama zance ne ki dafa masa
ruwan xafi a xuba a flask dan uwan matansa xai
kawo mu yanxun a mota xai amsa ya kai.ta ce to
alhj wayn xai kwana gunsa?yace bashir na nan
kuma matarsa anyi anyi ta qi tafiya shi yasa na
haqura xan dawo dan ba na xauna gun su ba ko?
umma tace amma yaya jikin nashi?ya ce da sauqi
yanxu ma yana son shan tea ne.tace to xan hada
harda wayar tasa inya so ma dunga kiran shi
kafin gari ya waye.ya ce yauwa ki
bada.Alhamdulillah abba jiki ba matsala.

Don hk a
ka sallamo shi zuwa gd.kai tsaye gdn su umma a
ka wuce d shi.

A salin dakinsa a ka gyara a cikin
kwana nan 3 ya yi ras sannan ya koma shago.

Bishira kuwa lkcn mahaifinta ya ce maza ta koma
dakinta,tunda ga abn d ya samu mijinta.Sun
dawo hr da tafkeken injin Janareto wai yaron ba
ya son duhu.

Sannan ga kayan kallo d
saraunsu.TabbasAbba ya ji dadin dawowar
iyalanshi,dn dama yana cike d bukatarsu.

Ranar
yini suka yi gyaran gd ita da 'yan uwanta,sai byn
magrib sannan ya shigo d tsarabobi.madara
tatacciya da kaji.

Ya dauki dansa cikin jin dadi
yana kallonta cike da so da kauna,Nayi missing
din ku da yawa.URFIN CIKI book 2 part 3
ZURFIN CIKI book 2 part 3
Posted by Bashir Sani Fesan on 14 Dec 2016 - 22:08
Ai bama shiri. shi ne fa ya kawo ni mkrntr kwana
dn kawai baya son ganina.

Suka yi ta mamaki.

Can jimawa ya dawo, sun fito rakiyar 'yan
uwansu Safiyya da na Khadija, suka ganshi tsaye
yana danne- dannen waya.

Ya taho ya gaida
iyayensu duka,sannan suka koma gefe d ummi,
ya ce Ni ma zan tafi.

Ta ce, Ya Abba ko fa
gaisawa ba mu yi ba.

Ta karkatar da kai,Cikin
raunin murya tamkar mai shawagaba,ta ci ga ba
da cewa Ya Abba su Umma ba wanda ya ce a
gaishe ni?

Sai hawaye suka soma zuba.

Hankicinshi da ke hannunta tasa tana sharar
kwalla.Abba yana da matukar tausayin mace.

Don
haka duk da tsanar da ya yi wa Ummi sai da ya
tausaya mata.Ya tausasa Murya.

Sun ce in
gaishe ki sosai, za ki ga gyada mai gishiri,
Tsohuwa ta ce a ba ki.Umma ta miki miya, ta
kuma daka miki yaji.

Ta ce Na gode, Alhj me
yasai min?ya ce kayan tea ne da lemun kwali.

Ta
ce Na gode.

Tana ci gaba da share hawaye.

Ya
mike Zan tafi. yasa hannu cikin aljihu ya ciro kudi
ya mika mata, ta ce A'a ya Abba ka bar kudinka.

Ya ce Ba ni ne na baki ba,Alhj Karami ne ya ce in
ba ki.

Ta sa hannu 2 ta amsa tare d godiya.Sun
raka shi kusa da Gate ita da su khadija,sai kuka
Ummi ke yi.

Bayan sun dawo dakinsu ne ta zauna
tana duba kayan da ya lissafo mata,duk ta gani.

Sai kuma saitin sabulun wanka da manshi da
turaransa da hodarsa duk na (Aloe vera.) Shi
kuma bai fada mata ko daga wa ba,ko ba komai
ta dai yi murna sobada tana da 'yan kuraje a
fuska,tasan kuma za su mutu.

Sai kuma audagar
mata,tayi dan murmushi. .

Tunda Umma taji
sallamar Abba ya shigo dakin ta bar komai tazo
ta zauna tana son jin lbrn Ummi.

Abba ya fahimci
Haka,dn haka sai ya boye mata cewa, Ummi na
kuka hr yanzun.

Ya nuna mata ai Ummi ta
kwantar da Hankalinta,km tayi hnkl dn ya bincika
ya ji ana ta yabonta.

Umma taji dadi Sosai,Sai da
ya fara zuwa gurin Ummu,sannan ya je gida.Ya
samu Bishira tana zaune tana aikin nata,wato
Kallo.

Tun da ta dawo daga wankan gida tazo da
janareto da kayan kallo,shi kenan ta sanu abn
yi.Kullum tana gabn (TV)da ta shi da safe in ta
kokarta shi ne ta dafa ruwan tea ko wanka ba za
ta yi wa dan ba,sai lkcn d man injin ya kare.

Ya
nufi gurin injin ya kashe,dif din da ta ji komai ya
tsaya shi ne yasa ta zabura ta mike tana fadin
Ba dai har man nan ya kare ba?

Ta fito da niyar
dubawa.Abba ta gani tsaye gabn injin yana bn
tsakar gidan da kallo cikin takaici.

Ta ce Baban
Walid kashe min injin kayi??Ya ce Eh na kashe dn
Allah dubi gidanki?kalli wanke-wanke kuda na bi
dubi tulin wankin kayan Fitsarin yaronki.

Dubi
kicin dinki,kuma ko da bn shiga dakinki da
wannan falon da ki ke kallo ba.na tabbata da
wanda ki ka dauke ko tsinkw a cikin sa.Kila ma
ba ki yi Sallah ba.

Ta ce Dan karashe ne fa ya
rage min in gama kallon in zo in yi aikin.Haushi
ya sake kana shi,Sai kurum ya shige daki.

Tsakuwar da ya dora kafa a kai tasa tsigar
jikinshi tashi,sam ya tsani ya shiga daki ya dora
kafa kan datti.

Ya dawo yasa takalmanshi ya
shiga da su,Walid yana kwance tun kayan da ya
bar shi da su da safe sune a jikinshi yana ta
bacci cikin fitsarin da ya shafka wanda ba wata
leda da zata hana katifar ta jike.

Ko wankan safe
ma ba a mishi ba kenan.A fili ya ce,",Inna lillahi
wa'inna ilaihinr raji'un. ya juya ya nufi shagi.

Ita
kam sai ta kunna injinta ta karasa kallonta,
sannanta tashi ta dora girki.sai lkcn ta ma Walid
wanka.

Ta dan dauraye kwanukan da za su ci
abnci,wai ta gaji sauran wanke-wanken sai gobe.

Fati ta shigo,Bishira ta ce Yauwa Fatima naji
dadin zuwanki.shuga dakina ki gyara min gado,ki
dan yo min shara.

Fati ta ce To.

Ta shiga ita ma
duk shegiyar darin ce gurin kuiyar aikin,dn haka
ta dan birbira ta fito ta ce ta gama.

Bishira ta ce
Yauwa dan dauraye min kaya can na Walid.

Nan
ma tasan sama ta shanya.

Bishira ta ce Yauwa
ta ga abnci nan kici.sai ki dauki na Ummarku ki
kai mata.

Har Fati ta kai waje,Bishira ta kwala
mata kira. ta ce,Zo ki tafi da wannan galan din
na man fetir kije shagon Babn Walid kice ya taho
mana da shi,dn man ya kare.

Koda Fati ta same
shi da galan ta fada mishi sako ya ce Ba zan siya
ba,Maida mata galan din.

Ta tafi,Shi kuma ya ci
gaba da mita a zcyrshi.

Yana fadin Na daina
sayan man tunda ba za a bari sai dare a kunnan
ba.Gidan Ummanshi yaje,ba ta nan ma taje
barkar Haihuwa.

Ko dakin Tsohuwa bai shiga
ba,ya zauna nan falonta.Ya za kula ya zuba
abncinshi ya ci.sannan ya dan huta sai ya fita
zuwa gidan su Ahmad.

Cam ya samu wasu daga
cikin abokanshi suka shiga hira.

Ranar dai Abba
bai je gida ba sai misalin sha daya ko daya shiga
bai nemi matar gidan ba,ya dibi ruwa ya yi wanka
sannan ya shiga dakin.

Ya lalibo makunnan wuta
ya kunna,dn Nefa sun kawo wuta.

Tana kwance
irn banzan kwanciyarta da ta iya,dakin sai tashin
wani irin wari yake kamar na ruma,kamar na
fitsari ko na datti.Ya kalli ko'ina kullin kaya ne na
wanki ne,na gaga ne ciki da guri.Ranshi ya
baci,Ya kuma dubanta ga wata kiba da ta tafka.

Tun da ta haihu ta zama rusheshiya,gashi bata
son kama jikinta.Tsaki yaja,sannan ya dauki fiko
ya fita. kan doguwar kujera ya jefa filo,ya kwanta
a gajiye.Amma me?sai ya ji dora gadon bayansa
acikin lema.Da sauri ya mike ya kunna wuta.Duk
fitsarin yaron ne a kan kujerun dakin,dn haka sai
ya nufi dakin da takw aje tarkace ya kunna
wuta,shi ma dai duk shirgi. .

Ya share Ya
shimfida ta barma ya kwanta,a ranar ya dauri
aniyar maida dakin ya zama nashi din-din-dn.

Don haka washegari yasa a ka zo a kayi masa
fenti,ya siyo kati fa ya yar da zanin gado,dk wani
abu nashi sai da ya kwashe su.

Kafin wata guda
ya maida dakinshi cikakken daki,ya zuba dk wani
abu da yake bukata. kafin ya fita kullum sai ya
gyara dakinsa fes. ita kuma sam bata zuwa
dakin,sai dai in yana da lalura yaje can ya sauke
ya dawo. kazantarta kam ta kai in da ta kai,tunda
hr kayan kashi tana zube su a cikin daki.

Ya gaji
yaje ya samu Anty ya fada mata,hr gidan Anty
tazo ta zazzageta,ta tasata suka gyara gidan,
amma ko a jikinta.Washegari ta ci gaba da in da
ta tsaya.

Sam babu wanda zai ganta ya ce
haihuwarta daya.

UMMI yau
ba wanda ya kaita murna,domin yau dai an basu
hutu..Sai dai tunaninta zata ko iya kai kanta
gida?
Chapter 20 · 0% Book details