← Book details Zurfin Ciki Part 1 - 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 63

Sashe 16

Zurfin Ciki Part 1 - 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yaya-yayi ta
ki,shi km gsky ta zo tayi mata fada,dn ba ya so
su momy suga laifinshi., Don ko d suka je
gaisuwar surukai sai d ta ce "Kada a katsewa
'yarta krt"Anti ta ce za ta zo. .

Ai kuwa ranar d
Anty tazo taga ta kaici gidn Bishira,ko ina
datti,Falon d ta leka dk kura d yanar gizo-gzo.

Cikin dakin baccinsu kuwa ko ina yamutse d
kaya,bngo dk t tofe shi d miyau,sannan g wani
gwangwa
ni madara gefenta ta kusan cika shi d
miyau.

Gashin kanta rabi an tsefe shi rabi ba a
tsefe ba.jikinta fari sol tamkar bai ta6a ganin
ruwa ba.

Anty t doka salati tare d cewa Bishira
me zan gani hk?Dan ubnki hk ki k dawo?

Dubi
gdnk?dubu kanki?

A kanki a ka soma ciki?nan t
zauna ta zageta tas, sannan ta taya t suka gyara
gidn suna yi tana fada.

Ta ce Hk ki ka ga ina yi a
gidana?Ko sauran jama'a hk suke yi?

Za ki sa a
zagi uwarmu a ce an sangarta ki alhalin aikin
gida dk a na sa ku.Sannan kin ki mkrnt,to ki sani
kanki zaki cuta dn kuwa dk ranar d mijinki y
zama wani abu 'yar boko zaya nema ya tafi d ita
cikin lamuranshi. .

Zan km hada ki d momy.byn
sun gyara gidn t sata tayi wanka t dauki kaya
masu kyau t saka.

Gwangwanin miyau tasa t tayi
jifa dashi,ta ce ki dinga saka sweet ko goro a
bakinki zanje nan d sati 1 zan dauko momy muzo
tare. kin san dai me zai biyo baya.

Abba da ya
shigo gdn byn Isha'i dk d cewa dare ne sai d y
gane an tsaftace gdn,Domin kamshi tare d iskar
da ke kadawa a gdn sun bayyana hk.

Dakin ta da
ya yi wa kaura yau kam hr bakin gado,ganin t
cikin kwalliya yasa shi cikin wani yanayi wanda
ya kwana 2 bai shiga ba.

Ko abncin bai nema
ba,ya shiga caftar Syy,wnd ita ma dk d tana
laulayi tana ra'ayin hkn,don hk sai suka rankaya.

Kwana 2 ya dan samu sauki kazantar dn tana
tsoron momynsu tazo ta gani,sannan tana zuwa
mkrnt.

Amma d momyn tazo tayi mata fada t
tafi,shi kenan sai ta koma gdn jiya,dama
Hausawa sun ce mai hali ba ya fasa Halinsa.

Haka dai hr cikin ya tsufa Umma tasa shi ya sayi
dk wani abu da mai jego da jaririnta za su
bukata. .

Ita km ta daka yajin mai jego ta tanadi
sabulun salo zuwa Kwallin da za a sa ma jariri.

Wani dare Abba y kira Umma,Alhj ne y daga nan
y sanr d su bishira bata d lfy,yana ganin haiuwa
ce.

Alhj d kns y raka umma hr gidn suka buga
Abba ya bude,suka shiga.Ranar Alhj y yi burin
mota,dmn d yana d mota yanzun sai su tafi
assibiti.

Bishira bata d juriya,dn hk sai raki take
yi,tana fadin a kaita assibiti.

A daddafe suka kai 4
dare Ahlj ya je ya taso abokinshi suka kaita
assibiti tare d su umma,karfe 8 na safe ta haifi
danta namiji. .

Umman Bashir d taji sai ta hau
fadan me ya sa ba a sanr d ita ba?Alhj karami ya
rufeta d fadan cewa,ita wace irin mutum ce?

Sam
ita bata son Alkairi ba,sannan ya fita ya yi wa
Alhj babba barka,dg assibti gdnsu iyayenta suka
wuce d ita ba tare d sun nemi shawarar mijinta
ba ko ta iyayenshi.

Hjy ce ta bada wannan
umurnin,rai 6ace Abba ya zo gurin umma dn ita
ta baro gurin ne d iyayenta suka iso.

Ya
ce,"dama umma umma haka akeyi sai a daukar
wa mu2m mata a tafi da ita ba tare da neman
izini ba?to gaskiya bazan yarda ba." umma ta
ce,"ka kyalesu, Allah ya raya.shi kenan, tafiya da
ita ba laifi bane tunda ita kadai ce a gidan ba mai
kula da ita matsalar dai da basu nemi izininka
ba." ya ce,"sai ka ce ba zamana take ba?
wankan gidan addini ne?dama fa niyyata in kawo
ta nan gidan ki lura da ita." umma ta ce,"to
yanxu dai hakuri kawai zan baka,ka bar
maganar." tayi ta lallashinsa har dai ya
hakura,amma shifa ya dau alwashin sai ya nuna
musu nasa ikon. umma ta hada abubuwan data
tanada suka tafi da makota.bayan sun shiga
gidan aka kai su gefen da maijego take. sun sami
dakin tamkam da jama'a nan dai suka zauna aka
gaisa,sa wani gani-gani ake musu ga talakawa.
umma ta ce,bishira ina ummar taku mu gaisa?sai
da ta yatsin fuska sannan ta kalli
kanwarta"sumayy a kije ki cewa momy ga
baki,koda yake kice mata yan gidan su Abba ne."
Hajiya zainu tana zaune da kawayenta da suka zo
barka, tana labarta musu rashin mutuncin dangin
mijin bishira dashi kanshi mijin. ta ce,"yau
kwananta uku tunda tazo gidan nan bashi ba
danginshi,kuma yanda bishiran take fada mana
laifin masu rikonshi wato wan ubansa da
matarsa. sun mallake yaron sai abinda suka
ce,hajiya nafi ta ce,"ku nuna musu kuskurensu ne
yanzu haka tunda kika ga sun mallake shi kila
shine mai dan samun gunshi suke ci." Hajiya
sabuwa ta ce"shi yasa auran talaka ko tsiya,yar
wajena Amina da tazo min da wani wai sun hadu
a ummara,koda na bincika sai na tarar likita
ne.karamin likita ubanshi dashi ya dogara na ce
ba dani ba." Hajiya zainu ta ce"ai gara shi
wannan fa tela ne." "TELA?" kawayen suka hada
baki, ta ce"au dama ku duk fadan da nayi lokacin
biki baku ji ba? tabi ta nace sai shi gashi nan
yanzun ya wulakanta mu." Ta dube su d
wulanqacin da ya fi Ki haihu kwana 3 tun dg
asibiti miji bai kuma bi ta kanki ba?

Hjy Nafi ta
ce in bai zo don kowa ba ma yazo dn dansa.

Zainu ta ce Ina nan ina jira ko shi ko danginshi
domin........

Sumayya ce ta katse su da sallama.

Sannan tace momy wai kizo ga yan gidan su
Abba sun zo. su duka suka mike ita d kawaynta
suka nufi gurin su Umma.

Hjy Zainu ta kalli gurin
d su umma suke,sannan ta kalli Bishira,
wadannan sune 'yan gdn Su Abban?

Bishira ta ce
Eh ummar tasa ce gata nan. ta nuna umma Hjy
zainu suka kalli juna d kawayenta sannan suka yi
'yar dry wanda hkn ya kashe jikin umman.

Tasan
cewa akwai wani tanadi d a ka yi mata.

Hjy
Zainu ta ce d kawayenta ku mu zauna,aikin
zaune yafi na tsaye.

Suka zauna.

Ta kalli umma
Dama ko ina son ganinki,ke ce uwar goyon tasa
ko? ta ci gaba To gsky ba ki yi wa dnki tarbiyya
ba,sbd rashin mutunci a yi maka haihuwa amma
kwana 3 ba zuwa ba aike?

Kuma sai yau za ku
kwaso kafa kuzo in 'yarki ce zaki so hk?umma
tayi shirun tana tunani, ta kuma rasa me zata ce
dn tund take ba a ta6a ci mata mutunci ba irin
wannan ba.

Amma ita bata iya fada ba,dn hk sai
ta ce, To Hjy a yi hkr, bn san cewa Abba bai zo
ba,Amma zan tsawata mishi,dn kuwa bai kyauta
ba.

Sai dai km shi ma bai so yadda a ka dauko
masa mata ba izininshi ba,dn ya same ni d
fushinsa ya ce min shi ba ya son wankan gidan
nan,sannan ba a yi shawara da shi ba a ka taho
d ita nan. kin ga km hkn bai dace ba..........

"Dakata min Hjy zainu ta katse ta Shi ne ya
haifar min 'yar d hr zan tsaya neman izininsa?
shi kuma a wa?

Ramatu mokociyarsu ta ce "Miji
km hjy ai ba abn wasa ba ne. hjy nafi ta ce ko?to
ke kinji hjy Zainu tabdi!Tun farko kuskuran naki
ne da ki ka bar 'yarki tayi irin wannan auran na
rainin d tsiya.

Umma ta ce d abokan tafiyarta
wadanda ko dan (ba) ba su ce ba, ta ce kuzo
muje"Ta dubi hjyr "Allah ya baku hkr.Hjy zainu ta
ce Ai ban ga gama maganata ba. umma ta ce,To
fadi ina jinki.

Hjy zainu ta ce Sako ne zuwa ga
danki ki fada masa ba komai muke nema dg gare
shi ba,abn d ya siya ma na yaron dk mun canza
wasu sdb dk 'yan gida ne.

Bukatarmu ya zo ya yi
wa yaronsa huduba,in km ya kai gobe za mu yi
masa d kanmu. umma ta ce Abba ya yi wa dansa
huduba,tn lkcn d a ka haife shi.

Hjy Zainu ta
ce,To ai bai yi shawara d uwar yaron ba,ko d ya
ke ga ki dawa zaiyi shawara?

Uwar d ta haife shi
ma bata zama komai ba, a dai ji tsoron Allah.
umma jiki ba karfi ta fito.

Su Ramatu suka biyo
ta hr kuka sai d umma tayi dn takaici. koda taje
gida sam bata fada ma kowa komai ba,illa dai dk
wanda ke gidn yasan yau umma tana cikin 6acin
rai.

Hatta ummi da bata d kn gado sai d tayi ta
tambayrta,umma baki d lfy ne?ta ce Eh,kaine ke
ciwo.

Da ta zauna sai ta shiga tunani so take
lallai sai ta gane aibnta,ko kasawarta akn Abba.

Ta kasa fahimtar mallakr d a ke fadin tayi wa
Abba.

Tana ganin nuna tsanarta ga Abba shi ne
mafitarta.

Abba ne ya katse mata tunani d cewa
Ummana ina t zuwa ba kya nan.

Ta dube shi g
mmknta ba ta iya bayya tsanarta g Abban,
maimakon hk ma sai ta samu kanta da cewa
Naje ganin jariri ne.

Ya shiga ya zauna kusa d ita
t dube shi Yanzu Abba dm bn isa in fada maka
mgn ka ji ba?Dama kin zuwa kayi ka duba
matarka da danka?

Ya shafa kai,Umma anjima d
dare zamu da su Ahmad ni haushi sukai bani.

Ta
ce to ka tabbata yau din kaje,Sannan ko sun
nuna ma fushinsu naka kawai ka ba su hkr,Ya ce
to umma ta ce Na sanka d zcy ne.

Ya ce to zan
kiyaye Umma.

Ya kuma dabn ta ummata yau na
ganki a yanayi mara dadin gani. ta dube shi kaina
ke ciwo Abba na kuma sha magani.

Da gaske
ciwo kanta ya dinga yi dn damuwa.

Yace Allah y
kara sauki.

Ya fita.
Chapter 16 · 0% Book details