Sashe 5
Zurfin Ciki Part 1 - 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya tura masu kayansu suka duba sunata murna dan ya masu wadda sukeso. aisha ta aje masa cikon kudinsa kan table. har sun fita yagadai baxai iya hakuri ba, yace bushura xo gashi. ta juyo tana dariya taxo. yace bushura inasan na fada maki wata magana gashi kuna sauri ko? ta kalli motan tace fada min. yace kina sona? ta xare ido sannan ta ruga da gudu. gabanshi na faduwa, bata tsaya ba sai mota. ya kwantan da kanshi akan keken yace menene maanan gudun da yarinyannan tayi? ya tambayi kansa, qarfe uku sunada lecture, amma baya xatan xashi makarantan. ahmad ya dubi abba wanda daga ka dube shi xakasan yana kin damuwa. yace wai banaga sunxo ba? ko ba motan su bane? shiya bandawo ba nakuma hana yaran dawowa dan ku sasanta. abba yace um, inaga yarinyannan gara na haqura, dan bana san insa kaina cikin tunani. ahmad yace ban gane ba, abba yace, to naga daga tambaya tana sona, saita kwasa da gudu ta shige mota. ahmad yayi yar dariya sannan yace ,amsan ta baka. tana nufin tana sonka. abba ya harare shi kada ka maidani dan iska, ina ta magana ta xabga da gudune shine tana sona? yace jeka tambayi manya .yaci gaba da cewa kaine baka mata magana da hikimaba, ka fito mata kai tsaye baka sakaya ba. abba yace, kai nifa ka sanni ba ruwana da wata kwana kwana, idan abu yayi min bana kwana, inko bai min bama haka, ni ba ruwana.
Ahmad yace sai xurfin kici ko? da ya aka shawo kanka ka fada mata,abba ya mike tare da kallan agogo, yace inada lecture. gida ya nufa dan shirin xuwa makaranta, har yayi kamar ya tambayi ummanshi cewa in ka ce ma mace kana sonta taji kunya ta gudu wai alamun so ne? sai kuma ya kasa, yana jin nauyi amma in bai samu wata manufa ba dole yaxo ya tanbaye ta dan baya boye mata komai.bushura yar ahj sale ce kwamishinan gona na wannan xamani, gidansu yana karkasara. danqareran gida ne ginin xamani, sun san abba ne sanadin dinki da yayi wa wata qawansu jamila.dinkin yayi matuqan birge su dan haka suka fara kawo masa dinki, tun ranan da ya fara ganin su bushura ta kwanta mashi a rai. to ashe ita ma yamata.shiyasa yau daya furta mata take ganin kamar anmata gafara da aljanna.wata xuciyar tace ,to yanxu da kika gudu in ya xaci baki sansane fa, nan take hankalinta ya tashi har tana rayawa ga abba can da wata.dan haka taga dolene ta koma gun sa inhar tana sansa. dan tasha ganin mata na masa tayin kansu in sunxo kawo dinki.nan ta soma tunanin wace dabara ce xatayi ta fita?saiko ta warware daya siket din kayanta cikin dare.da safe ta nunama momynsu tace mata telan ya manta bai hada wannanba,dama yace xai gwada nine kafin ya hada.momy tace direba ne xai kai mashi.bushura tace momx xaifa gwadani ne muje dai xa kaini.tace to kuje, bushura ta danyi gayunta suka tafi.saidai kash! bata samu abba ba ance mata yana gida. tace gidan da nisane, aka ce mata babu nisa,dan haka ta sa aka rakata.tacema direbansu tana xuwa telan na gida.gidan ba nisa.
A qofar gidan su abba ta tsaya, sai ga ummi ta sheqo da gudu tana dawowa daga aike.ta tsaya tana kallan bushura, sannan tace lafiya?bushura ta dubeta. yauwa abba yana nan?budan bakin ummi sai tace yaje kashi ya fada a masai.bushura ta dafe qirji, yaushe? ummi tace oho.sai ga abba ya futo sanye cikin shadda bulu mai duhu yana ta qamshin turare.shawara ya yanke lkcn da yake xaune a shago kan cewa yaje gidan su bushura,tunda gidan kwamishina ba boyayye bane,suka hada ido da bushura,ta saki faraa sannan ta dubi ummi,kince ya fada ina? ummi tayi ciki da gudu.ya bita da kallo sannan ya kalla bishira,me tace maki?bishira tace, ba komai.saidai dariya da maganan ummin tabata.yace tunda baxaki fada min ba xomuje ki gaida ummana.cikin muryan jan hankali tace ina jin kunya.ta bude jakanta tace kamanta baka dinke wannan siket dinba.yace mugani,yaga yadda aka warware shi aka cire xaran da kyau. murmushi yayi dan yasan ya dinka siket din,kusan shinema na farkon dinki.ya gane yaran nata qila san ganinshi take san yi.
Ya dinke siket din yana cewa"to amma sai dai ayi min izini inzo gida in kawo da kaina in na gama." tace haba dai,ya za ayi in taso ka?"ya ce,"ba komai,in dai anyi min izini sai inzo," ta ce,"to in maka kwatance?" ya ce,"a'a huta kada ki bata bakinki,nasan gidanku zanzo anjima bayan tarawih." ta ce,"to." sai mun zo" tace"ku dawa? ya ce,"abokina mana,kinga zo muje gurin ummana ku gaisa." Bishira ta bishi cikin jin kunya.tun kafin su shigo daman ummi ta shiga gurin umman da gudu tace mata"umma ga budurwar yaya Abba." Umma tace budurwa kuma? tace eh ai zama su shigo.daga nan ta kara kyallawa dakin tsohuwa tana fada mata.
Umma dai jim tayi dan bata da wani burin da ya wuce ta baiwa Abba ummi,kuma da tasan har zai ga wata can da wuri haka data fada masa kudurinta,sa tay 'ZURFIN CIKI' gami da nauyin baki....... sallamar Abba ce ta katse ta ta ce,"shigo Abba." ya ce Umma bakuwa ce taxo gaisheki.Umma ta fadada fara'arta tace to shigo,ba dai surukar tawa bace?" ya ce,"ai ita ce kam" Bishira ta shigo tana sunne kai,ta gaida umma Umma ta ce,"masha Allah,Allah yasa rabon muce."Abba yana dariya ya ce,amin ummana."ya dubeta,"tashi ki gaida kakata." suka nufi dakin tsohuwa,umma ta jinjina kai .tabbas Abba nason yarinyar,in ta dubi yanda yake fara'a da zumudi. a fili ta ce,"Allah yayi mana zabin alkairi."ummi na kwance kanta na cinyar tsohuwa,sai ta kalli bishira ta tuntsure da dariya,lokacin da suke gaisawa da tsohuwa.
Abba ya ce,"dariyar uban me kike yi?" sai ko ummi ta sake shekewa da dariya. ya nufota ya suri kafafunta,tsohuwa ta ce haba mai sunan malam yanxu in bata yi dariya ba kuka zatayi?" ya ce,Bishira tashi muje" Tsohuwa tace to yanmata mun gode ki gaida magabatan naki,sannan kiyi ta hakuri da halin wannan miskilin." Umma ta ce,"tsohuwa kodai kishi ne?suka yi sallama,ummi wadda tunda ya shureta ta rigasu fita sai ta dauki takalmi Bishiran guda daya takai soro (zaure). don haka da suka fito suka shiga nema ummi ta kule uwar dakin umma tana ta dariya tana lekensu.
Abba ya ce,"ummi! ummi!!" taki amsawa ya nufi waje da niyar dubota don yasan ita ce zata dauki takalmin,sai ga takalmi a kofar shi.
Don haka ya dauko kawai ya dawo ya bata umma ta ce,"ka kaita su gaisa da umman Bashir." Abba ya ce,"a'a ba yau ba."ya rakata wurin direbansu,kusa da shagonshi sukayi sallama da alkawarin zai zo washegari. yaje kuma bishira ta fada masa lallai tana sonsa sai dai tana tunanin iyayenta ko zasu amince? ya ce,to shi dai zai turo magabatansa su nemar masa izinin zuwa zance kamar yanda yake a shari'a Bishira tace a'a ya bari tunda yanxu shekarar farko take a babbar sakandare(s.s.1)ba za a bari ya dinga zuwa ba,amma zasu dinga haduwa gidan yarta dake na'ibawa.
Abba baida zabin da ya wuce ya yarda da hakan tunda tace baza a barta yin tadin ba.sai dai fargabar shi kada nan gaba sunyi zurfi cikin soyayya ace ba za'a bashi ba. ta ce,"Babana bashi da matsala,amma momy dinmu ce abin tunani."Abba ya ce,"shikenan Allah ya shige mana gaba." soyayya ce mai karfi ta kullu tsakanin Abba da bishira,wanda har ummanshi da kanta tasan cewa Abba yana son yarinyar.
Domin duk lokacin da zaije gurinta tana lura da zumudin da yakeyi,kazalikain tace ka gaida surukar tawa, bakinsa baya rufuwa.
Don haka sai ta tattara batun ummi ta aje a gefe addu'a ce kadai bata daina ba.ana sauran kwana uku sallah.Abba ya siyo fenti yazo da mai fentin nana ak fente gidansu ciki da bai.
Da yamma kuma ya kawo dinkunan su ummi da fati,ummi tasa ihu,sam irin dinkin da ta aro gurin kawarta Amina ba shi yayi mata ba,ya zai mata dink iri daya da fati? ya ce,"kin isa ki sani in miki dinkin da kike so?ta ce to ni dai bazan sa ba umma ta rafka salati tana kallon ummi ta ce,"ummi kina da hankali kuwa? kudi kika biya ko ko Abban sa'anki ne?" tace cikin kuka to ni umma ya zai min iri daya da fati? ya dubeta a fusace,"in kin bari na dauki kayannan wallahi bazaki sasu ba." Umma ta ce,"ni da zaka daukesu ma da naso"tsohuwa ta fito ta ce,"saboda me? akan wane dalili zaka amsar mata kaya?tunda baka mata wanda take so ba sai ka kyaleta." Da hannu Umma tayi mishi alamar yayi shiru,sannan ya fita waje.Abba ya kada kai ya fita. washe gari kuma ya shiga da me fenti har cikin gidan Alhaji karami,sahura tana daki lokacin da yake nuna ma mai fenti guraren da zaya fara.
Ta fito daga daki ganin Abba sai ta hade rai sannan ta ce,"mune kashin baya? ai dama ka bar shi tunda baka mai da mu wani abu ba,mu ne dai baka so din mahaifanka.
Ta dalilinmu zaka shiga aljanna,ba dalilin wasu banzaye ba da sauri ya nufi hanyar fita waje don baya son yaji zagin da zata yiwa Alhaji da Ummanshi. wannan na cikin dalilin dayasa baya son zuwa gidan Alhaji Babba da Umma,sune suka ci kashi da fitsarinsa. suka bashi tarbiya da ilmi,suka ci da shi suka shayar dashi.amma sam basa yi masa abinda umman Bashir ke masa. haihuwarsa ce kadai su Alhaji babba basu yi ba,sahura tana zuwa har shago tayi masa rashin mutunci,sannan ta ce ya bata kudi,ta ce ya ba bashir kudi ko ta aiko fati.
Bai taba kin bata ba,amma duk da haka bai tsira daga zagin rashin mutunci ba.ta ce ya tare a gidan ummanshi komai nashike mata,wai da kuma sam ba haka bane.
Umma bata taba tambayar shi sisi ba,haka nana duk lokacin da ya bata wani abu ko ya sai mata,sai tace ina na umman Bashir? kaje itama ka bata,in ko bashi da yawa ni naci girma ka bata.
Ranar sallar idi kuwa ummi koda tayi wanka kin saka sabon kayanta tayi sai na bara.