← Book details Zurfin Ciki Part 1 - 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 63

Sashe 22

Zurfin Ciki Part 1 - 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya isa igiyar shanya ya
ciri wasu yasa masa,sannan ya fita dashi.Wani
babban kyamis ya tafi da shi,mai kyamis din
likita ne,sai dai ba na yara ba ne,amma kowa
yazo sai ya duba shi.Nan dai ya masa bayani ya
ba su magunguna.

Sha biyu dai dai ya dawo,tana
zaune tana kallo ya ce "A'uzubillahi,wai ke kallon
nan masifa ya zamarmiki ne?to ki sani na kusan
fita da kayan kallon nan.

Ta ce,Tab,ka kaisu ina?
dadinta dai dafa gidan ubana a ka kawo su.

Ya
ce ta za su koma gidan uban naki.

Ta dafe kirji
"Zagina ka ke yi?ya dora mata dan a jiki "An
zage ki,ke din banza,kazama!yazube mata
maganguna ya fita.

Ya jima zaune a kofar
gidanshi dafe da kai,yana tunanin shin wai shi
kadai ne bai yi sa'ar mata ba,ko kuwa duk maza
ne.Ya tuna abokanshi 2 da suka yi aure.

Muktar d
Jamilu,sam ba su da wannan matsalar,duk lkcn
da yaje gidansu tsaf matansu,ga mutunci da
mutanta mutane.

Shi kuma a cikin abokanshi
babu mai zuwa gidan sbd bata gainin kowa da
gashi.

'Yan uwanshi sai wanda ta za6a sannan
zata yi hulda da su.

'Yan garinsu kuwa can
ZAMFARA
In suka zo kiri- kiri take nuna musu
kyama ga rowa,sam bata hulda da matan
abokanshi.

Ya numfasa zai bi shawarar Umma ya
gani, amma gaskiya Bishira ba matar zama ba
ce.

Tun da ya dawo sallarAsubahi dakinta ya
shiga tana ta shirga bacci.

Walid kuma ya yi
faca-faca cikin kashi ya tausasa zuciyarshi ya ce
"Bishira! .

Bishira!!Ya dan duki kafarta,sannan ta
tashi.

Ya ce Ki tashi ki gyara masa jiki kiyi
sallah.Ta ce,Tab, me ya yi?ya ce, "kashi ya
yi.kurum sai ya ji ta ce Tab,wannan akwai dan
iskan yaro.Yanzun dan ubanka kashi ka min?

Sam bai san lkcn da ya watsa mata mari a baki
ba,cikin murya mai karfi ya ce "kada ki kuskura ki
sake ce ma dana dan iska!kar ki sake zagar min
yaro kada ki yi wa dana baki.Ba zan dauki
wannan ba. .

Ta mike daga kan gadon tana kuka
Ni ka daka? wlh sai na rama.

Kasancewar lebe
baya raina duka,sai jini.Nan da nan sai kumburi.

Ta cakumo shi,wlh sai na rama.Ya hankadata kan
gado ya bar gidan.cikin zcyrshi yana fadin
,"Wannan fitina da me tayi kama?

Ita kam ruwa
ta dafa sannan ta wa yaron wanka, cukuikuiye
zanin gadon ta saka shi cikin baho,sannan tayi
kwaskwarima ta sabi danta baki suntum ta nufi
gida tana kuka.

Mahaifinta bai nan yana
Abuja,Hjy Zainu ta kalle ta bayan ta gama kero
karyarta.

Wai don yaro ya yi kashi ta ce yaron
bai kyauta ba shine ya hau ta da duka da zagi.

Hjy Zainu ta ce Amma wannan da muciya ya
dake ki ko?ta ce, Da hannu ne,nushina fa ya
dinga yi.

Hjy Zainu ta ce Ai kin gani ba yadda ba
a yi ba ki tsaya kiyi karatunki kin ki,kin kafe sai
kin aure shi,wannan matsiyacin?

Dama talaka
yana da wannan tsiyar.Yanzun za ki zauna mu
jiraZuwan Alhj,ba za ki koma ba.Ya dai baki
takardarki in yaso ki koma mkrnt.Su kuma su
dauki dan nasu.

Bishira dai tayi shiru,zcyrta tana
jinjina rabuwa da Abba d kuma danata.

Abba kam
gidansu ya nufa.Ummi ya soma cin karo da ita
tana sanye da doguwar rigar bacci,ta dora rigar
sanyu ta sakar ulu, a kai tana wanke baki da
busushi.

Ta dube shi,mmkn ganinshi tayi a
wannan lkcn.Sai da ta dauraye baki sannan ta ce
masa sannu da zuwa,ya amsa a hnkl bai san mai
yasa ya kasa dauke idanunshi daga kanta ba,hr
ta gama alwala tayi addu a ta mike.

Ta dube shi
da niyar yin magana,amma sai ta fasa don tana
tsoron kada ya daka mata tsawa.

Ta daga
labulan dakin Umma zata shiga.

Ya ce, "Ke!' ta
waiwayo cikin hada rai,domin ta tsani kiranta da
yake da ke!Ya ce Ummana fa?ta kalli dakin Alhj
Ba ta fito ba,,Ta shige ta zura hijabi ta tada
Sallah.

Ya shiga dakin ya zauna,yana kallonta
tana Sallah zcyrshi tana nazarin Rayuwar
Ummarshi.

Tun tasowarshi ya ke ganin kulawa da
kyautatawa da take yiwa Alhj Babba ga biyya,
sam bata wasa da dk wani abu nashi daga lkcn
da ya shigo gida ta gama sauraron kowa sai lkcn
da ya fita.

Bai ta6a jin sunyi sa'in-sa ba bare ta
daga murya sama da tasa.Shin sauran matan ba
su fahimci irin wannan ladabi ba ne?Ummi tana
addu'a zcyrta cike da tunanin shi kuma ya Abba
me ya kawo shi da wannan sassafen?

Muryar
Umma suka ji daga waje tana cewa,"Ummi in kin
idae ki fito ki share gidannan,ki wanke bayi,Ummi
ta ce To''.

Sam Umma ba ta san Abba ya shigo
ba,dmn da ta ba Ummi umurni sai ta sake
komawa dakin mijinta, Ummi ta wanke bayi
kansu,sannan ta share ko ina na gidan, ta kunna
risho ta dora ruwan karyawa, sannan ta shiga
firar doya.

Gyangyadi yake daga zaunw, Muryar
Ummanshi ce ta farkar da shi tana cewa, "A'aha!
ya bude ido cike da bacci.ZURFIN CIKI book 2 part 4
ZURFIN CIKI book 2 part 4
Posted by Bashir Sani Fesan on 14 Dec 2016 - 22:10
"A'aha! ya bude ido cike da bacci.

Ya kalle ta tare
da yin mika,ta ce "Lafiya"?

Ya ce,Umma lfyr
kenan.Ta zauna da sauri Me ya faru Kuma?

Yayi
dan tsaki,umma na gaji da auran nan ina ga
wannan karan xan yar da qwallon mangwaro in
huta ta quda. umma ta ce abba! abba!! me yasa
baka da haquri? ban xace ka haka ba abba,ina ce
jiyannan ka min alqawarin kawo qarshen duk
wata matsala tsakaninka da matanka?shin ban
fada maka hanyoyin da xaka bi ka xauna da
matarka lfy ba?ya kamo hannun ta,umma ba na
san bata ranki, ban san yadda xanyi da halin
yarinyan nan ba ne. jiya fa ina kwance taxo tace
min yarona amai naje kai shi kyamis,ina dawowa
na samu ta xauna tana kallon,ina mata magana
ta hayayyaqo min da asuba na tashe ta
sallah,wai dan yayi kashi shine ta hau xagin
yaron nan,wai dan iska. ni ko na bige mata baki
har da cukume ni da dambe fa.umma tace kaine
harda duka abba? dukan mace?ta xuba tagumi
tana kallon shi,ya ce umma xaginshi fa tayi,kuma
kin san dai ba kyau uwa ta dinga xagin danta.dan
ba haka kikai min tarbiyya ba.kalli rashin ji irin na
ummi, amma ban taba jin kin ce mata yar iska
ba.tace to ba sai ka xaunar da ita cikin tsanaki
ba?? .

Yayi shiru a xuciyarshi fadi yake umma ba
xata fahinta ba.tace, tashi kaje ka bata haquri, ka
lallasheta.matafa sai haquri,kasan da qashin
haqarqari aka yi su,dole ka ganta a karka
ce.saidai nasiha da lallashi,da xaran ka ce kan
dole xaka miqar da ita,sai ta karye.nan dai ta yi
ta ma abba fada, har sai da shi kanshi yaga
cewa eh,yayi saurin fushi.dan haka ya miqe ya
nufi gida da nufin bata baki.sai dai kuma kash!
lkcn da yaxo tuni tana gidansu.ya dawo ya sanar
da umma, tace to dole sai alhj yaji kenan.ta shiga
gun alhj yana shirin fita. yace yau dai suwaiba
akwai abin da ya dauke miki hankali daga kaina
ko? tace, me kagani? yace tunda kika fita ban
kuma jin duriyarki ba, hatta karin kumallo yau
uwata ce ta kawo min.ko taya ni shafa mai yau
ban samu ba, tace uhum, abba ne in gaya maka
na gani hankalinshi a duk tashe, matsala ce suka
samu da matarshi,wai ta yi yaji.alhj yace,yaji?
umma tace eh wai a ce kamar abba bai san
yadda xai yi haquri da mace ba, alhj yace ina
abban?ta ce yana daki yana karya wa.

Ya ce kira
min shi.abba ya xauna ya xayyane ma alhj komai
duk abubuwan da ke faruwa wanda take
masa,hatta batun sallah da bata san yi duk ya
fadia.alhj yayi shiru,can ya ce in ko haka ne ba
qaramin haquri kake yi ba, amma kaje xamu je
gidan.abba ya ce, ni dama xa a baita can dana
huta.alhj yace ba xa ayi haka ba haquri dai xa ka
ci gaba da yi.xuwan su alhj biyu gidan amma ba
suyi dace ba ance musu mahaifinta baya nan.
antynta kuwa ta kira shi a waya ya ce yana nan
xuwa gidanta.da dare suka je da ahmad sun
same ta ita da mijnta,anty ta tare su cikin fara'a
aka kawo musu kayan shaye shaye.nan dai abba
ya fada mata komai.ya qara da cewa ban sani ba
ko dan ni talaka ne shi yasa bishira bata ji
maganata? anty tace dame ka gaxa mata?
iskancintane kawai, wai bishira har da rashin
sallah,xa ko taci qaniyarta gun alhj.mijin anty
yace,tabdi lalle kana haquri nan dai suka ci gaba
da hira har mijin antyn yayi mishi alqawarin cewa
ya kawo takardunshi.MD din gidan rediyon
tarayya na jihar kd, amininshi ne.

Amininshi ne
tun da abn da ya karanta kenan za a sama mishi
aiki.Abba ya yi ta godiya.

Bai san da wane baki
zai gode ma mijin anty ba,tun daga nemna auran
Bishira yake taimakoshi, darajar su shi da Anty
da Alhjn su Bishiran yake hkr da halayanta.

Ya zo
ya sanar da su Umman,Sun yi murna hr Alhj ya
ce dole ne in in masa godiya.

Umma ta ce To
Abba ka gani fa,ta dailin matarka gashi zaka
samu aiki,ka yi ta hkr fa.

Abba ya ce Umma ba fa
ta dalilinta ba,in Allah ya rubuto zan samu ta
hanyarshi sai ki gani,ko ban santa ba Allah ya
kawo sila.Ta ce To yanzun dai ita ce Silar,Allah
yasa albarka.Sai dai ba zan ji dadin tafiyarka
garin Kd ka barni nan ba.

Ya ce Umma ko ni
tunda ya ce kd ke kurum ni ke tunan.Umma tayi
Murmushi,Allah ya maka za6i na alkairi,dk in da
za ka je.Amin Ummata.

Mahaifin Bishira ya dawo
kuma Alhj ya tasa Abba sun je in da aka kirata
gata ga shi ga kuma iyayensu.

Abba ya jero duk
laifunkanta bai rage ko daya ba.
Chapter 22 · 0% Book details