← Book details Zurfin Ciki Part 1 - 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 63

Sashe 23

Zurfin Ciki Part 1 - 4 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sannan ya ce,shi
ma yana son ta fadi tsakani ga Allah me yake
mata wanda ba ta So?Nan fa a ka ce ta fadan,
sai ta shiga Kame-kame, Wai in ya shigo gida sai
ya yi ta fadace-fadace sannan ba ya zama a gida
sai tayi bacci,km ga abnci ta dafa amma sai ya
amso na Ummarshi ya c.

Alhjnta ya daka mata
tsawa."Yi min shiru,yaushe ki ka bar musulunci?

Ba kya sallah ko?sannan ki bude baki kina zagar
masa da a gabansa?Ya bige miki baki kin kwaso
kin taho gida,to a miki uban me?ya dubi Abba
"Idiris me yasa ma ka mata duka ba?Ai ke babu
abn da ya dace da ke irin duka.

Maza ki kakkabe
mayafinki ki koma gidanki,bana son in sake
ganinki da sunan yaji a gidana, .

Zan wulakanta
ki.

Kuma game da batun sallah dk lkcn da bata yi
ba ka dakar min ita ni na saka,batun tsafta kuwa
kada tayi,ka nemi mata ka aura ka barta da
tsiyarta. kai dk lkcn da ka samu matar ma zan
biya maka sadakinta ko 'yar wanene.Sai a lkcn
Alhjn Su Abba ya yi magana.

Hakuri za ka yi
ranka ya dade,Allah ya saka da Alkairi bisa
karamcin da a ka yi mana,kuma insha Allah ba za
su sake ba.

Abba ma ya yi godiya,sannan suka
masa sallama.Ita ko Bishira mayafi ta dauko tana
kuka suka tafi.

Hjy Zainu ranta ya 6aci,taso a
kashe auran don dama bata son Abba sam,kafin
zuwan iyayen Abba da shi kansa Abban ta
fadawa mijinta karairayi,kamu ransa ya 6aci.

Ya
kuma daukar wa kansa alkawari in ya bincika ya
tarar haka ne dukanta da zaginta yake ba tare da
ta masa laifin komai ba?sai yasa an raba auran.

Amma da yaji batun Abba gata a gurin bata musu
ba,sai ranshi ya baci da ita, har dai batun sallar
nan.dn haka ya bincike yana da kyau ayi shi,kada
ka yanke hukunci da maganar gefe daya,wannan
shi ne adalci.

Bayan sun dawo Abba ya rakata
gida ya zo gurin Alhj da ya ce ya dawo yana
jiranshi.

Alhaji ya masa fada cewa dk in da tara
tayi to ya kansace a gida.

Sannan fadan da ta ce
yana yi in ya shiga shi ma ya daina,haka ya
dinga zama yana cin abncin.Abba ya ce to.Umma
ma da ya shiga suyi Sallama nan dai ta kara
masa fada tare da nuna mishi hanyoyin da zai bi
ta ce kuma cikin satin nan yayo mata rijistar
Islamiya tunda da ita a kusa.

Ya shiga ya same
ta zaune bakin gado tana ta fushi,ya zo ya zauna
kusa da ita.Yasa hannunshi ya kamo nata,sannan
ya kira sunanta bata amsa ba bata kalle shi ba
ya ci gaba da mgn.

Kin san dai ina sonki ko??ta
dube shi Da ba kafin a zuga ka.Ya ce wa zai zuga
ni? ta ce Wa kuwa in ba Ummar taka ba.

Ya yi
tsam ya ji haushin maganarta sosai,amma sai ya
danne kada ki zargi Ummata tana sonki kin ki
fahimta ne kawai.amma mu bar zancan kiyi hkr
akan abubuwa da nike miki. ki yafe min nima na
yafe miki. .

Ya jawota zuwa jikinshi,hr gobe ina
sonki sosai.Ranta ya yi sanyi don mata na son
wannan kalma daga mazajensu.

Ya kira sunanta
ta dube shi cikin ido suke kallon juna,ya ce kin ya
fe min?ta daga gira,kina sona hr yanzun?Ta kara
mannewa a jikinshi "Ina sonka sosai ma.Ranar
dakin shi suka kwana,kuma ranar ce rana ta
farko da suka soma kwana a dakin nasa.

Washe
gari tunda ya dawo Masallaci ya soma akin share
gida,lungu-lungu ya gama ya wanke bayi kan su
sannan ya yako ta da kyar ta tashi ya ce tayi
sallah ta yiwa yaro wanka.

Tayi Sallar,wankan ta
kuke wai akwai sanyu,sai ranar ta daga.

Ya ce,To
t dafa musu ruwan zafi su karya.Shi kuma ya
fitar da wankinshi yana yi ya gama ya ce ta fito
da duk wankinsu ita da yaron.Tsawaya ya yi yana
kallon tilin kayan,amma gudun kada suyi rigima
sai ya yi shiru ya ci gaba da wanki. .

Ya cire
kayan yaron da zannuwanta hr ma zanin gado
wadanda yaron ya yi kashi ta aje su suka
bushe,,wasu kayan hr da tsutsotsi.

Ya kira ta ya
ce "To kalli kayanki hr da tsutsotsi,wanna n ya
dac fisabilillah?samo leda ki kwashe su,ba zan
iya wanke su ba,in kuma za ki wanke to.

Nan ta
samo bako ta kwashe takai gurin bola,ya ce
Bishira tsafta cikin addini ce,Annabi (S.A.W)ya ce
Babu mai shiga Aljanna sai mai tsafta.

Don Allah
ki dinga kula,ke kanki za ki ji dadi in har ki ka
tsaftace ko'ina na gidanki.Ta tura baki ta wuce.

Ranar haka ya yini wanki kayan yaron dk sun
dafe kaya masu tsada da kyau irin wadanda a ka
sai masa daga gidan iyayenta,ranar dai ko shago
bai je ba.

Cikin satin dai babu laifi suna ta
shiri,kuma tana daurewa tana yin tsaftar
jikinta,haka nan yasa ta wanke kai tayo kitso. sai
dai ita gani take dk an takura mata,amma tana
jin dadin yadda ya sakar mata fuska kamar
farkonauresu.

Mitar da take masa kullum ya
daina dadewa a waje,ita don Allah ya zauna a
gida suyi hira.

Ranar dai saiya gwada zama tun
da ya dawo sallar Isha'i ya shigo gida.

Tana
zaune ba riga ya ce,Wai Bishira kayan kwalliyarki
sun kara ne? ta ce,Me ka gani?ya ce,Rabon da in
ga kwalli a idonki tun kina amarya bare dan jan
baki. .

Taja dan tsaki "kwalliyar me zan yi sai
kace wata budurwa?Da dai nayi.Ya ce kin ji wani
shirme kuma,ban da ke ai matar aure me miji a
hannu ita ce da yin kwalliya.

Ta ce, To ko ma
nayi ba zama ka ke ba.Ya ce "To yau dai gani na
zauna,kuma ina son a sheka min kwalliya.

Ta
dube shi Gsky sanyi ba zan iya yin wanka yanzun
ba.Shiru ya yi yana kallonta,can sai ta zame ta
kwanta,sai kuma bacci.

Ya yi murmushi.Dubi
matar da ta ce wai ba na zama a gida. to yau na
zauna amma kalli yadda ta bingire tana shirgar
bacci.

Ya mike ya fice.cikin takaici korafin banza
kenan take yi tunda ba ta san yadda za ta yi fira
da mijin ta ba. haka dai abba yayi ta hakuri don
baxai yiwu ya ce shi kadai zai dauke mata duk
aikin gidanta ba. sai dai yayi wanda zai iya,amma
duk wanda ya shigo gidan shi ko ba a fada ba
yasan matar gidan kazama ce ta bugawa a
jarida. ummi tana zaune gaban umma,fuska
shabe- shabe da hawaye.ta rikewa ummar
hannu."kinji don Allah umma kice wa ya Abba ya
dawo dani garin nan.wallahi bana son makarantar
kwana,ni dai bazan koma ba."umma ta ce "haba
ummi xuwa yanzu ya ci ace kin saba da
makarantar" ta ce,"umma bazan saba da rashinku
ba....."karaf a kunnen Abba. ya ce,"to sai ko ki
shirya sabawa,don wata rana ma aure zaki yi."
umma ta ce sosai kuwa. tsohuwa dake zaune a
kofarta,tana jinsu ta sako baki da cewa,"ku dai
lallasheta,karatun nan fa da ake ta matsanta
mata bana ganin manzo bane." Abba ya ce
mata,"in ji wa? kin ji ki,to ana neman aljanna da
karatun boko kuma ana neman wuta." ta ce,"kai
ni raba ni da
shegiyar karya tunda bata so a
barta." Abba ya dubi ummi,"kada ma kiyi za ton
maganar tsohuwa za tayi wani tasiri,gara ma ki
shirya komai gobe da wuri zamu wuce." ta dube
shi,"don Allah ya abba." ya mike ki shirya da
yamma zanzo muje (sahad store). ya dubi umma
na tafi. .

Ta ce,"abba bamu ko gaisa ba,ya mutan
gidan?" ya ce,"suna lafiya,sauri nake in karasa
wasu dinkuna,saboda gobe bana nan jibi litinin
zanje interview da gidan radiyo da talabijin na
(c.t.v) ta ce,"a'a ka samu anan din ne?" ya
ce,"eh bana fada miki ba da aka tura takarduna
can sai suka ce gurin da zasu saka ni akwai wani
wanda suke jin dadin aikinshi a gurin? don haka
zasu turo ni kano,suna ganin ana bukatar irina.to
shine mijin anty ya fada min to yanzu sun kirani
ranar litinin zasu min (interview).ummi dai na
jinsu bata ba kukanta ba.abba na ficewa umma
ta ce tashi kije kiyo kitso ummina,kin ji? dakyar
taje ta dawo.umma tana yankan kubewa wayarta
ta shiga ruri,ta dauka Abba ne.ya gaisheta ta
amsa,ya ce ummana ummi fa ta shirya? umma
takai duba cikin daki inda ta hango unmi nade
kan kujera tunda ta fito wanka.
Chapter 23 · 0% Book details