← Book details Zurfin Ciki Part 1 - 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 63

Sashe 37

Zurfin Ciki Part 1 - 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kukan Ummi na tsikararshi, sun yi tafiya mai nisa
sannan ya tsaya a hankali cikin wata irin murya,
ya ce "Ummi ki fada min gaskiya kina son
Sahabi?" Ta dago ta dube shi, "Ni bana son shi".

"To me yasa ki ka fito da shi?" cikin dasasshiyar
murya ta ce, "Ba ni da yanda zan yi ne, saboda in
ban za6i Sahabi ba za a bani Bashir".

Ya ce, "To
ke yanzun fada min wa ki ke so?" Gabanshi ya
shiga faduwa don tsoron kada kunnenshi ya ji
mishi ta ce wani ba shi ba.

Ta kuro shi da ido
tamkar ta ce kai, amma sai take ganin in ta fada
mishi haka dan shirin da suka soma yanzun zai
wargaje, kila ma sai ya hada mata da duka.

Wasu
zafafan hawaye suka gangaro kan kumatunta,
daidai lokacin da yake cewa "Ko dan digo ki ka ji
son ko waye a ranki kada ki rufe min". 45...

Ta
girgiza kai "Ba na son kowa Ya Abba".

Cikin wani
irin yanayi ya dubeta, "Shi kenan, sai ki je ki
hakura da Sahabin a sannun kin so shi".

Cikin
kuka ta ce, "Ya Abba Allah ni bana son shi, kai to
ka hada ni da ko waye mana".

Ranshi 6ace ya
dubeta cikin tsawa ya ce, "Ki rufa min baki tunda
ba ki ta6a son kowa ba ki zauna da wanda ki ka
za6i zama da shi.

In da kina son wani ne to da
sai in cije in tunkari su Alhaji, tunda kuwa babu
sai in ce musu me?" Ya fada mota, ya koma kofar
gidan.

Koda ya tsaya tafi minti uku sannan ta
fito, yana kallonta maimakon ya wuce gida sai
kawai ya nufi gidan Maman Iman makociyarsu da
suke shiri da ita.

Shima kanshi na kan sitiyarin
motar har ttsawon shudewar wasu dakiku,
sannan ya nufi gida. 27.

Misalin karfe tara
Umman Bashir ta rangada sallama a tsakar gidan,
Innar su Sahabi ta amsa tare da fadin "Shigo".

Sahura ta shiga tana tambayar "Ba kowa dai ko?"
Inna ta ce "Shigo mu kadai ne".

Bayan sun gaisa
ta ce "Ba ki sanni ba ko?" Inna ta ce, "Eh."
Sahura ta ce, "To ni dai tsakani ga Allah zuwa
nayi in ba ki shawara bisa ga yarinyar da danki
zai aura.

Tsakani ga Allah yarinyar ba ta da
mutunci, sannan iyayenta za su mallake miki da,
don ni kaina ya faru da ni".

Sahura don makirci ta
soma rishin kuka.

"Dana maigidana ya ba su riko,
ina sheda miki wannan zance 'yar uwa yanzun
tsakanina da shi sai ido, sun makkale shi komai
shi yake musu, ni ko da nayi wahalar ciki da
nakuda sai na tashi a banza.

To da yake an ce
ciwon 'ya mace na 'ya mace ne, shi ne nazo in
sanar da ke.

Amma in kin ji haushi kiyi hakuri".

Ta yunkura zata mike. 46...

Inna ta ce, "Zauna
'yar uwa, na gode.

Nima fa tuni auran nan ya fice
min a rai, dama da naga shi Sahabin ya dage ne
sai kuma suka aiko gobe azo za a daura aure sai
na hakura".

Kafiin Sahura tayi magana sai Sahabi
ya doka sallama, Inna ta ce "Yauwa zo nan".

Ya
nufo ta "Zauna kaji ma kunnenka".

Ya rage
tsawo, Inna ta ce "Baiwar Allah ya ki ka ce?" Nan
Sahura ta soma zuga sharri, ta kara da cewa
"Yaro ina ga ma za ka san dan nawa da suke riko
Abba a ke ce masa".

Cikin saurin baki ya ce, "Na
san shi".

Ta ce, "To dana ne da asiri suka amshe
min shi, sai dai Allah ya isa".

Ya tuna irin halayen
da Abban ke nuna mishi.

Yaa jinjina kai, sannan
ya dubi mahaifiyarshi "Inna to da Kawu yayo
binciken halayan iyayenta ai ana ta yabon
halinsu".

Inna ta ce, "Kin ji shi ko?

To bari kaji,
kwanaki ma Tasalla da ke bayan layin nan tazo
ta fadan irin wannan matsalar ban kama ba ne
don na asanta da shegiyar karya.

To kuwa an yi
biyu ba zan bari ai na uku ba, don haka a daran
ta tabbatar ma da danta an fasa gobe ya wuce
gurin Badariyya a daura, su kuma in sun ji shiru
sa ba wani can".

Cike da murna Sahura ta koma
gida. * Maman Iman tayi lallashin duniya amma
Ummi ta ki yin shiru, ga zazza6i tamkar wuta a
jikinta.

Sai kusan sha dayan dare sannan Maman
Iman ta rako ta gida, lokacin Umma tana ta
neman layin Abba a kashe.

Ta ce, "A'a sun dawo
ne yanzun ni ke neman Abba in ji suna ina ne?"
Maman Iman ta ce, "Tun dazu tana gidanmu
zazza6i da ya rufe Ummin, na bata magani ta 'ki
sha". 47...

Umma ta ce "Rabu da ita kar Allah
yasa tasha, aure dai gobe babu fashim dubi irin
yanda a ka sa gidan su yaron nan wancan karon
suka kashe kudi gurin yin girki da sauransu ba a
yi bikin nan ba.

Yanzun a kuma dagawa daga
lokacin da muka samu?" Maman Iman ta ce, "Ai
ba zai yiwu ba, sai dai a bi ta da lallashi".

Umma
ta ce, "Mun daina lallashinta tunda ko mun
lallasheta aikin banza ne".

Maman Iman ta ce,
"To Allah ya kaimu gobem bari in shiga gida sai
mun shigo aiki da safe".

Umma ta ce, "To sai da
safe".

Ummi tana shiga dakin Umma taga baki
kwakkwance, ta ce a ranta "Mayu, don kalata sai
da wasu suka dada zuwa".

Tana fushi da
tsohuwa amma duk da haka dakin ta nufa, ta
kwanta a bayanta don ita tuni tayi bacci.

Nishin
kukanta ya farkar da Tsohuwar, kala bata ce
mata ba, sai sauka tayi ta shimfida a kasa ta
kwanta, sannan ta ce "Aniyarki ta biki Takwara".

Wannan dare gurin Ummi da Abba wani dare ne
mai cike da bakin ciki da tashin hankali, ko Sarkin
sata bacci ranar bai samu galaba gare su ba.

Dukkan su a kan kunnansu aka kira sallar farko,
Abba ya mike cikin rangaji, jin jikinshi yake yi
tamkar iska ta dauke shi saboda rashin karfi.

Ruwa ya diba ya watsa, wanka sannan yayo
alwala don yin nafila, addu'a yake Allah yasa
hakan shi ne mafi alkairi a gare shi.

Da ya dawo
Masallaci kwanciya yayi amma baccin ya ki bai
fita ba sai kusan takwas.

Koda yaga Bishira
zaune a tsakar gida tana karatun littafin sam bai
ji haushin rashin zuwanta gidan su Umma ba.

Nashi ganin duk wanda yaje tamkar yana murna
ne da rasa Umminshi da yayi, ita kuwa da gadara
ta fito don ya ji haushi, bata je ba yana son sanin
halin da Ummi take ciki amma ba ya ra'ayin
zuwa gidan su Umma.

Shagonshi ya bude ya
shiga ya dan zauna har zuwa tara, yana kallon
lokacin da Jama'a suka yi ta dafifin shiga layinsu
don halartar daurin auran.

Kurum sai ya samu
kansa da tare dan Aca6a ya hau ba tare da ya
shaida masa inda za su ba.

Koda dan Aca6an ya
tambaye shi ce masa ya yi mu je. 48....

Ita ko
Ummi ranar zaune tayi sallah ta koma ta kwanta,
duk kaikawon ai da 'yan shewe-shewen da jama'a
dangi da makota tana jin su.

Sai dai makoshinta
ya bushe ga zufa da ta rufeta, duk da yanayin ba
na zafi ba ne.

Karfe goma daidai shi ne lokacin
daurin auran, layin ya dinke da jama'a, Alhaji
ranshi a dame don bai ga Abba ba.

Ya kalli Alhaji
Karami, "Ina Abba ne?" Alhaji Karami ya ce,
"Abokan aikinshi ga su can sun zo ba a ganshi ba
son daukan daurin auran".

Alhaji ya ce, "Su dauka
mana nasan yana nan tafe".

Har sha daya ana ta
jiran 'yan gidan Ango shiru, su Alhaji suka tashi
dan aike gidan don a ce ana jiran wakilan ango.

Amma sai a ka dawo musu da sako wai sun fasa,
kalmar da ta rikita Alhaji ta tashi hankalinsa.

Ga
jama'a an tara, Alhaji Karami ya ce wadannan
akwai kananan mutane." Daidai lokacin da muryar
wani Maroki ta ratso dodon kunnuwansu da
cewa, "Alhaji ku hanzarta Jama'a sun gaji da
jira".

Alhaji ya dubi Alhaji Karami, "Aminu a daura
da Bashir".

Alhaji Karami yayi shiru, can ya ce "A
daura da Abba".

Alhaji Babba ya ce, "Ina zuwa".

Ya fito daga dakin Abba na da inda suke yin
shawarar, ya ratsa mutane ya ce a yi masa
magana da Suwaiba.

Umma ta fito daga kicin ta
same shi a dakinsa yana tsaye yana kai-kawo ta
ce lafia?

Ya ce Gidan ango ne shiru, an bisu sun
ce sun fasa.

To shi ne na ce me zai hana a daura
da da Bashir? 49...

Umma ta ce a daura da Abba.

Ya ce, "Haka ma Aminu ya ce.

To ni ban ga
Abban ba ma, amma bari muje Allah yasa hakan
shi ne mafi alkairi".

Take a nan a ka daura auren,
Habiba da Idris Alhaji Babba ya kirgo sadaki ya
mika.

Alhaji Karami Waliyinta ya amsa, mutane
na ta al'ajabin yanda lamarin ya sauya.

Umman
Bashir kuwa Bashir din ne ya shiga gidan hankali
a tashe yana fada mata cewa da Abba a ka
daura.

Nan ko ta hau bala'i da zage- zage.

Ummi
ko tunda ta jiyo guda na alamta mata an daura
aure, sai ta birkice ta shiga kowa da
numfashinta.

Fati da ke kusa da ita tana
lallaminta ita ce ta kwala ihu, ba shiri aka yi
asibiti da Amarya.

Fati ta shiga gidansu da kuka,
nan ta taras Ummansu tana bala'i sai lokacin ta
ji da Abba a ka daura.

Ta ce da Ummar su to
menen ba shi ke nan ba?

Umma ta hau zaginta
tare da cewa, kar ki ga kin yi aure sai in miki
shegen duka, Fati dai ta fice ta bar gidan.

Sam
Umma bata ji dar da ciwon Ummi ba, wannan
karon don haka ma bata bi su Asibiti ba, da
kanwarta Saratu a ka tafi.

Likitan yayi ta fada
lokacin da yake yi mata allurai, a kuma bata gado
Umma ci gaba tayi da kula da bakinta.
Chapter 37 · 0% Book details