Sashe 33
Zurfin Ciki Part 1 - 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yanzun kuma ta wannan sai ki wamu
wani don ni ba zan matsa lamba a kan al'amarin
da Aljanu suka nuna tsoronsu ba, tsaki taja
sannan ta kashe wayar.
Har gari ya waye ba ta
daina tunani ba, haka nan bata yanke matsaya
ba.
Gidan Aminiyarta Attine bishsha ta nufa, sun
tattauna sosai sannan suka bukaci sukai koken
ga wasu Malaman.
Sai dai guri uku zancan iri
daya ne, wato ta bar shi kawai, yayin da guri
biyu suma zancan su iri daya ne, sun ce zata ci
sa'ar kashe shi amma asirinta zai tonu zata rasa
ran 'yarta daya kuma zai yiwu tayi zaman Jarun.
Ta ce, "Wannan akwai shegen yaro, shi yasa da
na ce zan sa Aljanu su dauko shi ya ce min yana
da makaminsu?
Daga karshe ta ce na bar shi
mara rabo".
Attine ta ce da dai yafi shi yasa tun
farko in naga wanda zai ja min aji ni ke watsi da
shi in nemi wani.
Kai jama'a sai kace aikin Allah
menene amfanin zinar ma da har ake shiga
Bokaye dominta?
Allah ka tsare mana Imaninmu,
amin. 12 24....
Ummi tana zaune zata wanke 'yan
kayanta na ciki, ta zubo omon cikin ruwa tana
faman karkadawa, tana 'yar wakar da ke sata
nishadi.
Sam ba ta ji sallamar Abba ba, yana
jingine yana kallonta, tana fadin, Akwai wanda na
ke so, amma kunya naso, ya wanke ni da soso
dan Yayana.
Ta tsoma sikyat dinta da fant da
'yan bireziyoyinta farare ne ta soma cudawa tana
maimaita wannan baitin wakar, shi kadai ta iya.
A jikinta taji cewa ana kallonta, ta waiwaya da
sauri, idanunta tsaf cikin na Abba, sai ta samu
kanta da sunne fuskarta cikin cinyoyi.
Ya ce,
"Kunyata ki ke ji ne Ummi?" Ta dago da dan
murmushi, "Sannu da zuwa Yaya Abba".
Ya ce,
"Yauwa dama kin iya waka?" Tsohuwa daga daki
ta cafke, tun da ta samu wannan wakar sai ka ce
me hadda, kullum Abba ya isa kofar Tsohuwa
suka gaisa.
Ya dawo kofar Umma yana tabayarta.
Ummi ta ce, "Taje Hotoro sunan kanwar Umman
Bashir da ta haihu, ya manta fa matarshi ma ta
na can, Tsohuwa ta fito tana cewa, ai Ummanku
ta juri wulakanci.
Waccan haihuwar da Zilai
kanwar Sahura tayi tas a ka zageta a gidan
sunan, amma yau ta koma.
Abba ya ce, "Ummata
tayi nisa a zumunci, Allah zai bata lada" Tsohuwa
ta ce, "Ai sai tayi ta yi, in dai shisshigi ne ba
kwarjini".
Ta dubi Ummi, wai wankin me ki ke yi
ne har yanzun ina nan ina jira ki yanke min
farce".
Ta hango kayan Ummi na daura ta ce,
"Kai ni wannan zamani naku yana bani mamaki,
ace 'yammata suna saka rigar mama?
Kunya ta
cika Ummi saboda Abba da ke gurin. 25....
Abba
ya ce, "Kin ji tsohuwa, lokacinku da namu daya
ne?
Ku lokacinku kai bai waye ba, ta aje 'yar
kujerarta ta zauna.
Tir da wannan wayewar taku
ta zamani, yarinya ta fadi a gaban iyayenta har
ta shiga sa tara mama bata kama dakin kanta
ba?
Mu kuwa da wata ma ba sai tayi haihuwa
goma ba ma ta sa ran mama ba.
Abba dariya ta
ishe shi yayin da Ummi kunya ta hanata shanya
kayan ta matse ta aje.
Abba ya ce, "Yanzun
Ummi har wani girma tayi, shekara sha takwas
kurum ce fa, bata ma cika ba.
Ta ce "Mu lokacin
sha biyu sha daya yarinya ta kama dakinta.
Ummi ta zanua ta soma yanke ma Tsohuwa
'kumba, tana cewa To dai nima na kusan tafiya in
huta gorinki.
Abba ya matso, "Ummi don Allah in
tambaye ki mana?
Ta tsaya da yanke 'kunbar
tana kallonshi, ya maimaita tambayar da gira ta
bashi amsa ya ce kina ko son wannan Sahabin?
Ta maida kanta ga yankan 'kunbar duk jikinta da
hannunta suna dan rawa, a zuciyarta ta ce, "Kai
ne kadai zuciyata ke so, amma a fili sai ta ce,
Um, ya ce Yaya hausar um?" Tayi kokarin
saisaita hawayenta, sannan ta ce Eh, jikinshi yayi
lakwas, Tsohuwa ta ce, "Zancan banza, in bata
sonshi zaka daga batun auren ne?" Ai ko tana so
ko bata so tunda ta kawo shi zance ya kare, ka ji
mai sunan Malam da zancen wofi.
Ya ce,
"Tsohuwa ni fa ba wani abu na ce ba, kin ga ma
dai bari in tafi abina.
Ummi ina Azimi yau, zan zo
in yi buda baki anjima.
Ta ce, "To." Tsohuwa ta
ce, "Wai kai ba ka da gidan mata ne kullum kana
la'ke a nan?
Tsoron ta ka ke ji ne da zaka kasa
lankwasata ta yi maka girki?" Ya ce, "Na nan
nake son ci Ummi kam tana can duniyar tunani
tana tambayar kanta shi kenan ta rasa Abbanta?
Son da da yayi mata da ca dama ba na aure ba
ne, na 'yan uwantaka ne?
Kai ko dai ta fito ta ce
Abba take so, gaskiya ita fa Sahabi ba sonsa
take ba.
Kusan wata daya kenan rabon da ya
samu biyan bukata daga matarsa, don gaskiya
baya iya zuwa dakinta saboda kazanta da kuma
datti da wari da zarni da 'karni ba za su bar shi
ya samu cikakkiyar biyan bukata ba.
In ta zo
dakinshi ma jikinta tashi yake, a haka yake
maneji, amma in iskancinta ya motsa har yanga
take mishi (Mtsw!
Allah rabamu da kazaman
Mata).
Shi kuma yana da wani hali, duk yanda ya
matsu in har ya nuna mata bukatarshi ta 'ki sai
ya hakura ya roki Allah ya shiryeta, shi kuma ya
kare shi da fadawa sharrin zina. 26....
Bai zaginta
ko ya ce zai nuna mata karfin shi, ko ya ce zai
tsaya rokonta, shi yasa yake yawan yin Azumi.
Ummi ta ce, "Umma ki kawo kudi in siyo kwai in
soya ma Yaya Abba doya, ya ce zai zo shan
ruwa.
Ta ce, "To je ki kasan filo ki dauko, amma
fa sai kin yi azama don an kusa kiran sallah.
Ta
ce, "Ai na dafa ruwan shayi, sannan na masa
kunun tsamiya, doyar ce kawai, ta ce "To sai da
ta gama komai sannan tayi wanka tayi sallah.
Riga da siket na leshi tasa fari tas, bata damu da
yin fenti da dare ba amma yau tayi ta feshe
jikinta da turare wanda shi ne ya sai mata.
Sallamarshi ta jiyo suna gaisawa da su Umma, ta
fito ya bita da kallo, kin yi kyau kanwata, Umma
ta ce yau za ku hoton ne?
Ta ce kila, Abba ya ce
shi yasa ki ka yi kwalliya haka?
Ba ta ce komai
ba sai dai ranta bai so ma maganar da Umman
tayi ba.
Suna hira da Umma ta shirya misi abinci
ta koma kan kujera ta dauki littafi lokaci-lokaci
idanunta suna kan Abba. 13 Suna hira da Umma
ta shirya mishi abinci ta koma kan kujera ta dauki
littafi, lokaci-lokaci idanunta suna kan Abba.
Shi
ma haka ya ce wai ni littafin nan da ku ke nacin
karatunshi dame kuke karuwa?
Umma ta ce, Ai fa
gara ka tambaye ta, don ban ga abinda ta ba
muhimmanci ba irin wannan littafin.
Ummi ta cem
ina karuwa sosai Umma suna koya mana tarbiyya
yyanda zamu tafi da rayuwarmu cikin tsarin
Addini da al'adarmu.
Abba ya ce amma basa
koya tsafta da biyayya, Ummi ta ce suna yi sosai
ma, ya ce Umma ni naga jarabar karatu irin na
Bishira amma kullum mugayen halayenta bayyana
suke yi.
Ummi ta ce ni ko har addu'o'i zuwa girki
kala- kala ina koyo, Umma ba rannan nayi
dafadukan kwakwa ku ka ce ya yi dai ba?" Ta ce,
"To ki dai dinga daukan na kwarai kina yarda na
banza, Abba ya ce in haka ne d agaske zan samu
lokaci in zo ki karanta min in ji, ta ce "To." 27.....
Umma ta yi 'yar dariya ta ce, "Sai ka ce ba ka da
aikin yi?
Ya ce, "Allah Umma da gaske nake yi
don in ji wacce irin koyarwa suke yi, marubutan
ko ko sai shirme?" Kiran sallar Isha'i ne yasa
Abba mikewa, ita kuma Umma ta tafi kicin don
shiryawa su Alhaji Abinci.
Ummi kam sun bar ta
cikin takaicin tafiyar Abba don dai bata gundura
da shi. * Alhaji Ya kalli Umma, wai yau bikin
yaran nan saura wata nawa?
Ta ce, "Wata ko
kwana dai?" Yau saura kwana talatin da shida,
ban ga kana motsi ba?
Alhaji bikin nan zai
mamaye mu, ya ce "Yanzun ya za a yi da batun
kaya?" Ta ce, "Ni da cewa nayi ga Abba sai yaje
ko kuje ku za6a musu kaya masu kyau a siya,
kada a ba kafintoci in ba a yi sa'a ba har lokacin
yayi ba a gama ba".
Ya ce, "To zan sa shi ya tafi
da su kawai su za6a".
Ta ce, "Sai kayan girki na
dai sayi tukwane da risho, sai kuloli".
Ya ce, "Duk
da haka uwata zan sa ta za6i wasu kayan."
Umma tayi dariya tare da cewa, "Allah ya kara
budi, nan dai suka yi ta lissafin kudi.
Da safe
Alhaji ya kira Abba a waya ya sanar da shi cewa
ya dauki su Ummi suje su za6i irin kayan da suke
so, duk da cewa zancan ya doki zuciyarshi amma
ya ce "To." insha Allah zamu je, suka yi sallama.
Sam baya son ya ji batun auran su Ummi, baya
son rasata, kuma yana ji a jikinshi cewa zai same
ta. ** ** 28.....Yammacin ranar Asabar La'asar
lis garin yayi dan sanyi Abba ya nufi gidansu don
daukan su Ummi zuwa kasuwa.
Jikinshi sanye da
farin yadi mai shara-shara, har ana iya hango
fara kar din singiletin da ke ciki ta manne a
jikinshi.
Kamshin turarenshi ya cika dakin Umma
wanda ba shiga yayi ba daga bakin kofa suka
gaisa.
Ya ce, "Ummi su fito don Ummi ce ke
shiryawa tuni Fati ta fito, ya matsa kofar
Tsohuwa suka gaisa, sannan ya ce "Umma sai
mun dawo.
Ya nufi waje yana fadin su Ummi su
mishi sauri.