← Book details Zurfin Ciki Part 1 - 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 63

Sashe 32

Zurfin Ciki Part 1 - 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da jin haka sai ya taho, nan
dakin na kawo shi, sannan na fito mishi da
maitata fir! ya shiga jawo min ayoyi na numa
masa cewa ba zan hakura da abinda zuciyata ke
so ba.

Don ban ta6a 'kin cika mata burinta ba,
shi kuma ya fir ya ki ya nemi ya gudu na bashi
guri ya dan ci abinci na nuna masa mishi kuskure
ne ya ce zai gudu.

Don gidan nan duk masu tsaro
ne har da ma layin gaba daya.

Da sauri za a
kama ka a matsayin dan fashi, sannan in ka yi
kokarin shigo da jami'an tsaro lamarin to, zaka
kwana ciki.

Domin duk a hannunmu suke, amma
Ustazun ya ki shan ko ruwan gidan nan, gashi ya
min shame-shame zai mutu don yunwa.

Ba arziki
na saka aka fita da shi kuma aka kai shi gidan
karuwai a ka ba su na sakar musu kudi suka sa
shi a daki.

Nasa Malamina ya karasa min shi,
sannan na sa karuwan suka kira 'yan sanda kan
cewa ga wani ya zo gurinsu amma kwananshi ya
kare a nan.

To dama iyalanshi suna ta nemanshi
an sace shi nan fa suka dauke shi, na san yanzu
ka gane kowane Malami ne tunda labarin ya yadu
a cikin garin nan da ma wajen shi".

CIKI book 3 part 3
ZURFIN CIKI book 3 part 3
Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 00:24
Abba ya ce "Lokacin da muke cin abinci tare,
Umma ta ce, lokacin da ka ke bata dai, Abba shi
ne ya fara baki abinci a baki. 20.....

Watanki
hudu, da kin hango shi za ki soma daga hannu,
Abba ya ce Umma na fa goya Ummi a bayana.

Lah, goyo?

In ji Ummi.

Umma ta ce, "Goyo sosai
kuwa, suka sa dariya, Umma ta ce, "Shi yasa in
naga yanda ku ke rashin shiri a tsakaninku
yanzun sai in ta mamaki.

Don tun ba ki fita a
tsumma ba Abba ke rainonki, tun ba ki fi wata
hudu ba, ki ka tantance muryarshi.

Haka nan
sunan shi ne ki ka fara iya fadi a duniya.

Abba
yana goya ki kin sha yi masa fitsari da kashi da
tumbudi, wanka da wanki duk Abba ya miki
Ummi.

In ko na aike shi ko zai tafi Makaranta to
sai da wayo da dabara.

Ke har an kai lokacin da
kin yarda in tafi unguwa in bar ki gurin Abba, in
ya dawo Makaranta tun daga soro zai soma miki
wakar da yake miki.

Ummin Abba da Alhaji,
Ummin Umma da Tsohuwa, da kin ji haka za ki
dibi rarrafe ki nufi gurinshi, kuma duk kudin break
dinsa zai debo miki tsaraba.

Umma na bada tarihi
Ummi ta zuba ma Abba idanu cikin wani irin
yanayi da ba zata iya tantance shi ba, shi kuwa
lokacin ne ya dawo mishi, ido ya yi dan murmushi
tare da cewa "Allah sarki da na tuna ranar da aka
yaye Ummi, Umma tayi dariya ta ce, "Ranar tare
kuka kwana kuna min kuka wai in yi hakuri in
baki nono".

Wata sabuwar kauna da so Ummi taji
ya rufe ta na Abba, har kwalla ta cika mata ido,
ta ce "To Ya Abba me yasa ka daina sona?" Ya
ce, "Ummi ban daina sonki ba, kanwata kiriniyarki
ce ta hada mu fada dama, yanzun kuma kin
daina ko?" Ta daga kai alamar eh, Umma ta ce
"Labarin yanda ku ka kaunaci juna mai tsawo ne,
kusan kullum sai mun yi labarin da Alhaji".

Ummi
ta kalli Umma shi ne ba ku ta6a bani labari ba?

Ta ce ba gashi kin ji ba, Tsohuwa tayi sallama,
suka amsa.

Ta ce, "Kai me sunan Malam me ya
faru da kai?

Nan ya warware musu komai, suka
yi ta al'jabi.

Umma ta ce "Ni 'yasu, yanzu haka
mata suka maida aure ba a bakin komai ba?"
Kuma ka ce matar aure ce, Abba ya ce dama z
aki san kowa ce ce za ki ji mamaki fiye da haka,
don dai kurum na rufa mata asiri ne in taci gaba
to can gabanta hadu da mai tona ta.

Su Alhaji
suka shigo da sallama, nan suma aka ci gaba da
jajanta batun, Alhaji Babba ya ce, "Babana ina ga
dai rahoto za mu kai gurin 'yansanda".

Abba ya
ce, "Alhaji tuni manyan shuwagabannin gurin
aikinmu suka shigo da hukuma, in Allah ya yarda
dolenta ta bar ni, Alhaji Karami ya ce, "Addu'a dai
ita ce z aka kara rikewa, Allah ya ja mana gaba".

Suka ce Amin. 21...

Ranar su Alhaji a tsakar gida
suka ci abinci anata hira, Ummi dai kallonsu take
yi amma zuciyarta na can duniyar tunanin labarin
da aka bata.

Ashe har yanzu Ya Abba na sonta,
Allah ya sa haka har yanzun.

Sai kusan sha daya
Alhaji ya matsa wa Abba ya tafi gida.

Abba ya ji
dadin hirar musamman in ya waiwaya idanunshi
suna kallon Ummi ta mai 'kuri da ido, Umma ta
ce, "Ka gaida 'yan gidan".

Ya ce "Za su ji, har ya
kai soro Ummi ta ce Alhaji da an raka shi kada a
kara sace shi fa, duk suka sa dariya".

Abba ya
dawo yana cewa, "Umma kun rage man fetur
kuwa?

Na san yanzu na gidan ya kare tunda ba
shi da yawa, bana son kuma sai na sake daukar
galan na fita".

Alhaji ya ce, "Na shigo da mai
dazu duba nan soro na aje shi, Ummi ta sake
cewa Ya Abba ka ce Alhaji su rakaka gida, yayi
'yar dariya kada ki damu Ummi, ina yin addu'a
Allah zai kare ni.

Yau kam Ummi ta dade bata ga
daren da farin ciki ya hanata bacci ba irin yau.

Haka nan shima Abba zuciyarshi fes Ummi ta
fahimci dama can santa yake, da alamu ba zai
sha wuya gurin shawo kanta kuma cikin
karammin lokaci. 11 HAJIYA NINA Ta kalli
matashin, sannan ta kalli jaridar hannunshi ta ce,
"Me ya'ki kai fa ba jakadan azriki ba ne, a duk
lokacin da na ganka sai gabana ya fadi,
musamman in kazo min da jarida".

Yayi 'yar
dariya "Hajjaju makatu sallah Makka Sallah
Madina, ni dai kin san ba ilimin nan gare ni ba, in
da z aki tsare ni in karanta ban iya ba, ni dan
sako ne.

Muftahu ne mai siyo duk wata jarida da
ya ga ta shafe ki, ta amsa ta bude cikin azama,
hoton Abba ta gani gabanta ya fadi, ta ce dan
jarida shege ne, yaron nan tallatani zai yi?

Ta
soma karanta labarin zufa tana karyo mata, har
ta gama.

Kafa kurum take karkadawa tana
tunanin abin yi, murna daya tayi da bai tona ma
duniya cewa ita ce Hajiya Zabba'u ba.

Amma duk
da haka ba zata bar shi ba, koda yake ta ga
manyan 'yan jarida na kokarin shigowa ciki, ta
kai hannu ta dauko daya daga cikin wayoyinta ta
danna kira. 22....

Jim kadan aka daga ta ce,
"Karamakallu barka da warhaka, ya amsa da
Ranki ya dade lafiya dai ko?" Ta ce, "Malam ba
lau ba, kana ji?

Ina yaron da nake baka labari
dan jarida?

Ya ce, Naji.

Ta ci gaba, Yaron nan
kaga yanda ya yayata ni a duniya?

Sai na koya
mishi hankali, da ni zai ja?" Malam ya ce, ya ma
ki ka ce sunanshi?

Ta ce Idris, ya ce To zan kira
ki anjima, kada ki dauki wani mataki tukunna sai
na gama bincikena duka.

Ta ce an gama.

Sintiri
tayi ta yi tsakanin dargajejen falonta zuwa
barandar shakatawarta, lokacin da taji rurin
wayarta tayi tsammanin Malamin ne, sai data
duba taga Aminiyarta ce Haiya Attine.

Ta daga da
cewa, "Hello Attinen bishasha ya aka yi ne?

Ta
ce, Zabba haka kwallon dan iskan yaron nan zai
miki?

Ta ce, Hum!

Ke dai bari Aminiyata, yanzun
nan na gama karantawa a jarida ban ma san
hukuncin da zan yanke ma yaron nan ba.

Attine
ta ce, sa su Adda su tura shi Jami'ar mi'kakku
mana.

Hajiya Zabba'u ta ce, "Ai kuma na riga na
kira Teacher ya ce in saurare shi".

Attine ta ce,
"Eh to kin yi dabara ma, kya iya sa Teacher din
ma ya tura ba tare da an zargi kowa ba".

Hajiya
Zabba ta ce, "Kin san jami'an tsaro suna cikin
maganar tsundum!

Don haka dole in yi taka tsan-
tsan, guri daya yaron ya yi min kyan kai, da bai
fada ma duniya Zabba'u ita ce Nina ba." Attine ta
ce "Eh yayi wannan adalcin, yanzun bari muji ta
bakin Teacher". 23....

Shikam Malamin duk
lamura sun kasa masa daidai, sai kusan karfe uku
saura, sannan ya kira ta da rawar jiki ta dauka.

Ya ce, Hajiya?

Ta ce, Na'am ya ce ki tattara ta
batun yaron nan ki watsar domin yanda naga
al'amuran to fa in mun matsa ba zamu kai labari
ba.

Haka nan allura zata tono garma game da
damuwar malamin nan, sannan asirinki zai tonu a
gurin maigidanki.

Tsaki taja don maigidana
Malam nasha fada maka ban 'ki ya ji ba, tunda
shi ne sanadin komai, tafiya kullum daga waccan
kasa zuwa waccan, kullum cikin bakin yawon
neman kudi.

Sam baya biya mini bukatata ba
dole in nema ba?

Yarana biyu cal a duniya duk
sun yi aure su ne kawai zan ji kunyar su sani,
don haka in zai yiwu ka sa Aljanu su tsotse min
jinin matsiyaci.

Malam ya ce, "Ba zai yiwu ba, ina
ce tun lokacin da ki ka zo min da batunshi kafin
ma ki sa a dauko miki shi sai d ana fada miki
yaron yana da kariyar da take kare shi daga
Ubangiji.

Yaron ma'abocin kyautata Sallah ne,
tare da yin Azkar, yana da makarin da Aljanu ba
za su iya tunkararshi ba...

Dakata Malam, ta
katse si duk addu'arshi ya kai Malam ne, kuma
muka ci nasara a kanshi?

Ya ce kila shi Malamin
kwananshi ya kare dama ke ce sila shi ko
wannan da sauran shan ruwansa.

Ta ce, "Kai ne
sila dai daina jingina min mutuwarsa, ya ce ko
kin ki dole ki dauki nauyin zunubin mutuwar
Malam".
Chapter 32 · 0% Book details