← Book details Zurfin Ciki Part 1 - 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 63

Sashe 4

Zurfin Ciki Part 1 - 4 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Wata rana abba ya ke cewa, umma da ace lkc
daya kuka haihu da umman bashir, allah cewa
xanyi kunyi canjin yaya. umma ta dube shi dan
me kace haka? yace sbd masifar ummi irinna
umman bashir ne, fati kuma ba ruwanta kamar
ke.dariya kawai take yi. kwanci tashi ummi ta
gama pry, lkcn abba yana shekaranshi ta qarshe
a jamia. yana karantan (mass comm)ne dan yana
san xama dan jarida. umma tasoshi da likita
amma yace baida raayi. tace kaga kai bakada
hayaniya abba aikin jarida na masu maganane.
yayi murmushi yace umma kenan. ummi ta samu
shiga aji daya a qaramar sakandare. maimakon
hankali abin nata sai gaba yakeyi. aduk lkcn da
tai laifi abba ya daketa sai tayi wani abun dan
tabashi haushi, da sunan ta rama. ahj babba ya
bude mai shago, tare da xuba mishi kekuna.
tsohuwa tace dakai wanine mai sunan mlm, saika
tafi da takwarana ta koya. abba yace ko a
kwafan shago na na ganta ba sai na karya mata
qafa ba. ummi ta murguda baki, sai daya tafi
sannan tace allah ya kiyaye inje wannan qaxamin
shagon nashi.

Tsohuwa ta ce,"tafi can kema da
baki son ci gaba, in banda abinki da zaki kwantar
dakai ki koya in an tashi auranki basai a saya
miki keken ba. in kuma shi kika aura kinga
shikenan inya samo dinkin da yawa saiki taya
shi, ta ce"Allah ya kiyaye me xanyi da yaya
Abba,yayi ta cin xalina?ni bana son shi" Umma
dake gefe tana jinsu ta ce,"ke in kin samu kamar
Abban ma ai kinji dadi,shine zai ce mai zaiyi
dake? mara hali irinki." Ummi dai tayi shiru tasan
inta cika surutu kan Abba yanxun nan umma ta
doddoketa,umma tafi son Abba fiye da ita. watan
ramadan ya tsaya,duk daukacin musulmi sun
dauki azumi ranar da akai na uku Abba ya shigo
gida karfe daya saura. daga shago yake zaiyi
wanka yaje makaranta don yanada darasi karfen
biyun rana.

Gidan shiru kowa na bacci,don haka
bai shiga dakin umman shi ba don baya son ya
tasheta ya shige bandaki.

Da ya gama ya fito ya
nufi daki kamar ance ya kalli madafi, ummi ce
tsugunne tana cin abinci. ya tsaya yana kallonta,
dagowan da xatayi suka hada ido, yace ke! karya
axumin kika yi? ta toshe bakinta sannan nace
dan allah yaya kayi haquri. yace fito muje. ya
kaita dakinshi yasata gwale gwale. da xashi
masallaci ya kulleta ta baya. ya ce inyaso ki
tashi kafin na dawo, xan gane. yana fita tahau
binci ken abinda xata lalata mashi. ta ciro bidiyon
da yake kallo xata doka da qasa, sai taga kwalin
wani kaset tana kallon hoton jikin kwali, na
tsiraici ne. ta xare ido kicin mamaki, tace lalle
yaya abba, daman shi dan iskane? to kuwa xan
tona mai asiri. ta turashi cikin xaninta, da taji
motsin shi yana bude qofa sai ta koma inda take.
ya shigo ya kalle ta ya ce nasan kin xauna dan
kinga bananan. ya xauna bakin katifa, sannan ya
dubeta fuska daure. ummi meyasa kika karya
axumi? tace ba komai. yace tunda aka fara axumi
kike karyawa ko? tace yaune kawai yaya abba.
yace kinsan hukuncin wanda ya kasya axumi da
gangan.

Tace eh an fada mana a islamiya, amma
mlm yace sai wadanda axumi ya wajaba akan su.
ya kalle ta cike da mama ki, a xuciyanshi yana
cewa, yanxu har yarinyan nan tasan akwai
wadanda axumi ya wajaba akansu? afili kuma
yace lalle ummi kina buqatan sa ido. dama
saboda bai wajaba akanki ba shiyasa kika karya?
to daga yau xansa maki ido, kuma xan fadama
umma ta sa maki ido. hakanan duk wani abu da
akeyi lkcn axumi an daina qyale ki, xaki ringa
sallar tarawi, ke har tahajjud sai kinyi shi. sannan
bayan axumi saikin rama wannan axumin. ya
xuba mata ranqwashi a tsakiyan kanta ,tare da
cewa tashi ki fita munafuka. daga dakinshi bayi
ta shige ta qara kallon kwalin, sannan ta maida
ta soke shi, tace sai na tona maka asiri. da dare
bayan angama bude baki, abba xai tafi tarawi ya
shigo dakin umma yace ina ummi? umma tace
gatanan kan kujera tayi sharkaf, wai yau taji
axumi. abba ya shiga ciki yana kallanta. yace
umma xaki yaudara ko yar rainin wayau, tafa
karya axumi daxu da rana na ganta tana cin
shinkafa.

Yace shine kika xube wai ke kin sha
wuyan axumi ko? umma ta dube ta tana mamaki,
tace abincin da kike kinba almajirai da ma qarya
ne? ya dubeta yace biyu kenan ga larya axumi ga
qarya, xaki sani. tashi muje salla ko in ballaki.
umma tace allah ya shiryi halinki. abba yayi
dariya tare da cewa, kema dai umma yaxaki
amince da batun wai tac almajirai abinci, su basa
axumi ne, umma tace tunanin haka sam bai xo
min ba. saida ya sakata sahun salla, sannan ya
nufi gun maxa. bayan ya gargadeta da cewa in an
idar ta jira shi, inyaxo batanan sai ta sani. koda
aka idar da yaxo bata nan gurin ya kaure da
dambe da wata yarinya wai da suna sallah tana
bigeta. shine daga idarwa ta cakume yarinyan da
fada. bai tsaya sauraranta ba ya cire ta kalmi ya
shiga dukanta, sannan ya tasata xuwa gida. sai
da t
a shige dakin tsohuwa sanna ya koma nashi
dakin. hakanan suka ta xuwa masallaci har
axumi yakai ashirin.

Ahj ya kawo masu shadda
da leshi da atamfa na sallah ita da umman su
bashir da fati. ya suya masu takalma da mayafai,
abbane xai masu dinki, ran ummi baya son dinkin
abba, domin wanda take so bashi yake mata ba.
ta ce umma dan allah nidai a bani dinkina na
kaima laminde, yaya abba baya min ne kyau.
umma tace kije ki karbo da kanki. tace ai baxai
bani ba ne, xai dakeni. umma tace ai nafi san ya
dake kin, lamindan finshi dinki mai kyau tayi ne?
ummi tace nidai gara ita. tsohuwa tace ai banga
lkcn da mai sunan mlm xai faranta ma takwara
ba, kullun burinshi ya quntata mata. umma tace
tsohuwa ummi fa ba a mata gwaninta, inace dinki
in yayi mata har aro ake xuwa yi? ta dube ta
tace keda shine inya jiki kyayi biyu babu, yaqi
maki dinkin luma ya hana kayan bare kiba
laminde inga ta tsiya. qarfe dayan dare ya tura
dakin tsohuwa tana xaune a kan sallaya tana
addua, abba yayi murmushi. tsohuwannan kina
birgeni dama kina ibadan dare? ya kalla kan
gadonta, ummi taya dai dai tana ta bacci./ ZURFIN CIKI book 1 part 3 ZURFIN CIKI book 1 part 3 Posted by Bashir Sani Fesan on 14 Dec 2016 - 21:42 Ya kalla kan gadonta, ummi taya dai dai tana ta bacci.

Yace, ummi ke! ummi!! tashi. tsohuwa tana yi masa alama da hannu gami da gyaran murya, wai ya bar ummi maimakon haka ma sai ya dauki wani kofi nan gefansa da guntun ruwa a ciki ya watsa mata a fuska. ta farka firgigit, yace taso, da sauri ta tashi yace dauko hija binki maxa. ta dauka suna fita tsohuwa tana sallamewa. tace kai mai sunan mlm ka lafama yarinyan nan haka, wai axumi wajaba akanta yayi da xaka tasheta da tsohon darannan xuwa masallaci? yace kema in xaki, xo muje. ya tasata suna tafiya tana hada hanya suka tafi tahajjud. sai qarfe hudu na asuba aka tashi. ummi har kuka tayi saboda tsananinjin bacci, amma tana tsoran kar ta kama bacci yaxo ya same ta. tun tana layin bacci har ta gyagije. sakamakon tashinta da matan kusa da ita keyi. kafin kwana uku ta saba da sallan dare, lkc nayi xata farka. abba yana xaune ga dinki gabanshi amma yana can tunanin bushira, yarinyan da yake matuqan so ce. amma yana shakkan fada mata,dan iyayanta sunada kudu matuqa. kuma shine yakema duk yan gidansu dinki.

Ahmad abokinshi da ke gefe kuma sai yayi murmushi, yasan tunanin bushiqa ne ke damun sa, dan haka sai ya ce, abba kasan allah, abari ya huce shi ke kawo raban wani. haka kuma ZURFIN KICI, ba xai kai ka gaci ba. ka fada mata kawai. abba ya ce hum ,ina tsoron kada ta ce bata sona, dan bansan ina xansa raina ba. ahmad yace daga ganin yadda take jin kunyanka tana sanka. abba ya kalli ledan da ke dauke da dunkunan su bushiran, yace ina xatan yau xasuxo amsan kayansu, dan tun jiya nace suxo.ahmad yace to in sunxo kayi qoqari ka fada mata mana, indai ba ragon namiji kake ba. abba ya tsurama qasa ido yana tunanin in sunxo mai ce mata? kusan awa biyu sukaje sukai sallan axahar, tungan motan ta tsaya yasan tasu bushurane. shi kadaine a shagon sauran basu dawo ba. bushura ta shigo da qannansu da yarsu aisha. ya taresu da faraa, suka gaisa kan bushura na qasa, sam bata iya kallan abba tela kamar yadda suke kiranshi.
Chapter 4 · 0% Book details